89) Sūrat Al-Fajr

Printed format

89) سُورَة الفَجر

Wa Al-Fajri َ089-001 Inã rantsuwa da alfijiri. وَالْفَجْرِ
Wa Layālin `Ashrin َ089-002 Da darũruwa gõma. وَلَيَالٍ عَشْر ٍ
Wa Ash-Shaf`i Wa Al-Watri َ089-003 Da (adadi na) cikã da (na) mãrã. وَالشَّفْعِ وَالْوَتْرِ
Wa Al-Layli 'Idhā Yasri َ089-004 Da dare idan yana shũɗewa. وَاللَّيْلِ إِذَا يَسْرِ
Hal Fī Dhālika Qasamun Lidhī Ĥijrin َ089-005 Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)? هَلْ فِي ذَلِكَ قَسَم ٌ لِذِي حِجْر ٍ
'Alam Tara Kayfa Fa`ala Rabbuka Bi`ādin َ089-006 Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba? أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَاد ٍ
'Irama Dhāti Al-`Imādi َ089-007 Iramawa mãsu sakon ƙĩrar jiki. إِرَمَ ذَاتِ الْعِمَادِ
Allatī Lam Yukhlaq Mithluhā Fī Al-Bilādi َ089-008 Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya). الَّتِي لَمْ يُخْلَقْ مِثْلُهَا فِي الْبِلاَدِ
Wa Thamūda Al-Ladhīna Jābū Aş-Şakhra Bil-Wādi َ089-009 Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi suka yi gidãje)? وَثَمُودَ الَّذِينَ جَابُوا الصَّخْرَ بِالْوَادِ
Wa Fir`awna Dhī Al-'Awtādi َ089-010 Da Fir'auna mai turãku. وَفِرْعَوْنَ ذِي الأَوْتَادِ
Al-Ladhīna Ţaghaw Fī Al-Bilādi َ089-011 Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa? الَّذِينَ طَغَوْا فِي الْبِلاَدِ
Fa'aktharū Fīhā Al-Fasāda َ089-012 Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu. فَأَكْثَرُوا فِيهَا الْفَسَادَ
Faşabba `Alayhim Rabbuka Sawţa `Adhābin َ089-013 Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba. فَصَبَّ عَلَيْهِمْ رَبُّكَ سَوْطَ عَذَاب ٍ
'Inna Rabbaka Labiālmirşādi َ089-014 Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka. إِنَّ رَبَّكَ لَبِالْمِرْصَادِ
Fa'ammā Al-'Insānu 'Idhā Mā Abtalāhu Rabbuhu Fa'akramahu Wa Na``amahu Fayaqūlu Rabbī 'Akramani َ089-015 To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni." فَأَمَّا الإِنسَانُ إِذَا مَا ابْتَلاَه ُُ رَبُّه ُُ فَأَكْرَمَه ُُ وَنَعَّمَه ُُ فَيَقُولُ رَبِّي أَكْرَمَنِ
Wa 'Ammā 'Idhā Mā Abtalāhu Faqadara `Alayhi Rizqahu Fayaqūlu Rabbī 'Ahānani َ089-016 Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni." وَأَمَّا إِذَا مَا ابْتَلاَه ُُ فَقَدَرَ عَلَيْهِ رِزْقَه ُُ فَيَقُولُ رَبِّي أَهَانَنِ
Kallā  ۖ  Bal Lā Tukrimūna Al-Yatīma َ089-017 A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya! كَلاَّ  ۖ  بَل لاَ تُكْرِمُونَ الْيَتِيمَ
Wa Lā Taĥāđđūna `Alá Ţa`āmi Al-Miskīni َ089-018 Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci! وَلاَ تَحَاضُّونَ عَلَى طَعَامِ الْمِسْكِينِ
Wa Ta'kulūna At-Turātha 'Aklāan Lammāan َ089-019 Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa. وَتَأْكُلُونَ التُّرَاثَ أَكْلا ً لَمّا ً
Wa Tuĥibbūna Al-Māla Ĥubbāan Jammāan َ089-020 Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa. وَتُحِبُّونَ الْمَالَ حُبّا ً جَمّا ً
Kallā 'Idhā Dukkati Al-'Arđu Dakkāan Dakkāan َ089-021 A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai. كَلاَّ إِذَا دُكَّتِ الأَرْضُ دَكّا ً دَكّا ً
Wa Jā'a Rabbuka Wa Al-Malaku Şaffāan Şaffāan َ089-022 Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, safũ- safu. وَجَاءَ رَبُّكَ وَالْمَلَكُ صَفّا ً صَفّا ً
Wa Jī'a Yawma'idhin Bijahannama  ۚ  Yawma'idhin Yatadhakkaru Al-'Insānu Wa 'Anná Lahu Adh-Dhikrá َ089-023 Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi! وَجِيءَ يَوْمَئِذ ٍ بِجَهَنَّمَ  ۚ  يَوْمَئِذ ٍ يَتَذَكَّرُ الإِنْسَانُ وَأَنَّى لَهُ الذِّكْرَى
Yaqūlu Yā Laytanī Qaddamtu Liĥayātī َ089-024 Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!" يَقُولُ يَا لَيْتَنِي قَدَّمْتُ لِحَيَاتِي
Fayawma'idhin Lā Yu`adhdhibu `Adhābahu 'Aĥadun َ089-025 To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah. فَيَوْمَئِذ ٍ لاَ يُعَذِّبُ عَذَابَهُ~ُ أَحَد ٌ
Wa Lā Yūthiqu Wathāqahu 'Aĥadun َ089-026 Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa. وَلاَ يُوثِقُ وَثَاقَهُ~ُ أَحَد ٌ
Yā 'Ayyatuhā An-Nafsu Al-Muţma'innahu َ089-027 Yã kai rai mai natsuwa! يَا أَيَّتُهَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ
Arji`ī 'Ilá Rabbiki Rāđiyatan Marđīyahan َ089-028 Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira). ارْجِعِي إِلَى رَبِّكِ رَاضِيَة ً مَرْضِيَّة ً
dkhulī Fī `Ibādī َ089-029 Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa (mãsu bin umurui a dũniya). فَادْخُلِي فِي عِبَادِي
Wa Adkhulī Jannatī َ089-030 Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira). وَادْخُلِي جَنَّتِي
Next Sūrah