90) Sūrat Al-Balad

Printed format

90) سُورَة البَلَد

Lā 'Uqsimu Bihadhā Al-Baladi َ090-001 Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari ba. لاَ أُقْسِمُ بِهَذَا الْبَلَدِ
Wa 'Anta Ĥillun Bihadhā Al-Baladi َ090-002 Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari. وَأَنْتَ حِلّ ٌ بِهَذَا الْبَلَدِ
Wa Wālidin Wa Mā Walada َ090-003 Da mahaifi da abin da ya haifa. وَوَالِد ٍ وَمَا وَلَدَ
Laqad Khalaq Al-'Insāna Fī Kabadin َ090-004 Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala. لَقَدْ خَلَقْنَا الإِنسَانَ فِي كَبَد ٍ
'Ayaĥsabu 'An Lan Yaqdira `Alayhi 'Aĥadun َ090-005 Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa? أَيَحْسَبُ أَنْ لَنْ يَقْدِرَ عَلَيْهِ أَحَد ٌ
Yaqūlu 'Ahlaktu Mālāan Lubadāan َ090-006 Yana cẽwa "Na halakarda dũkiya mai yawa," يَقُولُ أَهْلَكْتُ مَالا ً لُبَدا ً
'Ayaĥsabu 'An Lam Yarahu 'Aĥadun َ090-007 Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba? أَيَحْسَبُ أَنْ لَمْ يَرَهُ~ُ أَحَد ٌ
'Alam Naj`al Lahu `Aynayni َ090-008 Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba? أَلَمْ نَجْعَلْ لَه ُُ عَيْنَيْنِ
Wa Lisānāan Wa Shafatayni َ090-009 Da harshe, da leɓɓa biyu. وَلِسَانا ً وَشَفَتَيْنِ
Wa Hadaynāhu An-Najdayni َ090-010 Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi biyu ba? وَهَدَيْنَاهُ النَّجْدَيْنِ
Falā Aqtaĥama Al-`Aqabaha َ090-011 To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba? فَلاَ اقْتَحَمَ الْعَقَبَةَ
Wa Mā 'Adrāka Mā Al-`Aqabahu َ090-012 Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã? وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْعَقَبَةُ
Fakku Raqabahin َ090-013 Ita ce fansar wuyan bãwa. فَكُّ رَقَبَة ٍ
'Aw 'Iţ`āmun Fī Yawmin Dhī Masghabahin َ090-014 Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa. أَوْ إِطْعَام ٌ فِي يَوْم ٍ ذِي مَسْغَبَة ٍ
Yatīmāan Dhā Maqrabahin َ090-015 Ga marãya ma'abũcin zumunta. يَتِيما ً ذَا مَقْرَبَة ٍ
'Aw Miskīnāan Dhā Matrabahin َ090-016 Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya. أَوْ مِسْكِينا ً ذَا مَتْرَبَة ٍ
Thumma Kāna Mina Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Tawāşaw Biş-Şabri Wa Tawāşaw Bil-Marĥamahi َ090-017 Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi. ثُمَّ كَانَ مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ وَتَوَاصَوْا بِالْمَرْحَمَةِ
'Ūlā'ika 'Aşĥābu Al-Maymanahi َ090-018 Waɗannan ne ma'abũta albarka أُوْلَائِكَ أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ
Wa Al-Ladhīna Kafarū Bi'āyātinā Hum 'Aşĥābu Al-Mash'amahi َ090-019 Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma'abũta shu'umci وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِنَا هُمْ أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ
`Alayhim Nārun Mu'uşadahun َ090-020 A kansu akwai wata wuta abar kullewa. عَلَيْهِمْ نَار ٌ مُؤصَدَة ٌ
Next Sūrah