88) Sūrat Al-Ghāshiyah

Printed format

88) سُورَة الْغَاشِيَه

Hal 'Atāka Ĥadīthu Al-Ghāshiyahi َ088-001 Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka? هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْغَاشِيَةِ
Wujūhun Yawma'idhin Khāshi`ahun َ088-002 Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne. وُجُوه ٌ ٌ يَوْمَئِذٍ خَاشِعَة ٌ
`Āmilatun Nāşibahun َ088-003 Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya. عَامِلَة ٌ نَاصِبَة ٌ
Taşlá Nārāan Ĥāmiyahan َ088-004 Zã su shiga wata wuta mai zãfi. تَصْلَى نَاراً حَامِيَة ً
Tusqá Min `Aynin 'Āniyahin َ088-005 Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa. تُسْقَى مِنْ عَيْن ٍ آنِيَة ٍ
Laysa Lahum Ţa`āmun 'Illā Min Đarī`in َ088-006 Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi. لَيْسَ لَهُمْ طَعَام ٌ إِلاَّ مِنْ ضَرِيع ٍ
Lā Yusminu Wa Lā Yughnī Min Jū`in َ088-007 Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba. لاَ يُسْمِنُ وَلاَ يُغْنِي مِنْ جُوع ٍ
Wujūhun Yawma'idhin Nā`imahun َ088-008 Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne. وُجُوه ٌ ٌ يَوْمَئِذ ٍ نَاعِمَة ٌ
Lisa`yihā Rāđiyahun َ088-009 Game da aikinsu, masu yarda ne. لِسَعْيِهَا رَاضِيَة ٌ
Fī Jannatin `Āliyahin َ088-010 (Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya. فِي جَنَّةٍ عَالِيَة ٍ
Lā Tasma`u Fīhā Lāghiyahan َ088-011 Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta. لاَ تَسْمَعُ فِيهَا لاَغِيَة ً
Fīhā `Aynunriyahun َ088-012 A cikinta akwai marmaro mai gudãna. فِيهَا عَيْن ٌ جَارِيَة ٌ
Fīhā Sururun Marfū`ahun َ088-013 A cikinta akwai gadãje maɗaukaka. فِيهَا سُرُر ٌ مَرْفُوعَة ٌ
Wa 'Akwābun Mawđū`ahun َ088-014 Da kõfuna ar'aje. وَأَكْوَاب ٌ مَوْضُوعَة ٌ
Wa Namāriqu Maşfūfahun َ088-015 Da filõli jẽre, وَنَمَارِقُ مَصْفُوفَة ٌ
Wa Zarābīyu Mabthūthahun َ088-016 Da katifu shimfiɗe. وَزَرَابِيُّ مَبْثُوثَة ٌ
'Afalā Yanžurūna 'Ilá Al-'Ibili Kayfa Khuliqat َ088-017 Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su? أَفَلاَ يَنْظُرُونَ إِلَى الإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ
Wa 'Ilá As-Samā'i Kayfa Rufi`at َ088-018 Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta? وَإِلَى السَّمَاءِ كَيْفَ رُفِعَتْ
Wa 'Ilá Al-Jibāli Kayfa Nuşibat َ088-019 Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su? وَإِلَى الْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ
Wa 'Ilá Al-'Arđi Kayfa Suţiĥat َ088-020 Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta? وَإِلَى الأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ
Fadhakkir 'Innamā 'Anta Mudhakkirun َ088-021 sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai. فَذَكِّرْ إِنَّمَا أَنْتَ مُذَكِّر ٌ
Lasta `Alayhim Bimusayţirin َ088-022 Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba. لَسْتَ عَلَيْهِمْ بِمُسَيْطِر ٍ
'Illā Man Tawallá Wa Kafara َ088-023 Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta. إِلاَّ مَنْ تَوَلَّى وَكَفَرَ
Fayu`adhdhibuhu Al-Lahu Al-`Adhāba Al-'Akbara َ088-024 To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma. فَيُعَذِّبُهُ اللَّهُ الْعَذَابَ الأَكْبَرَ
'Inna 'Ilaynā 'Īābahum َ088-025 Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take. إِنَّ إِلَيْنَا إِيَابَهُمْ
Thumma 'Inna `Alaynā Ĥisābahum َ088-026 Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi. ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا حِسَابَهُمْ
Next Sūrah