84) Sūrat Al-'Inshiqāq

Printed format

84) سُورَة الإنشِقَاق

'Idhā As-Samā'u Anshaqqat َ084-001 Idan sama ta kẽce, إِذَا السَّمَاءُ انشَقَّتْ
Wa 'Adhinat Lirabbihā Wa Ĥuqqat َ084-002 Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron, وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ
Wa 'Idhā Al-'Arđu Muddat َ084-003 Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta, وَإِذَا الأَرْضُ مُدَّتْ
Wa 'Alqat Mā Fīhā Wa Takhallat َ084-004 Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme. وَأَلْقَتْ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتْ
Wa 'Adhinat Lirabbihā Wa Ĥuqqat َ084-005 Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren, وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ
Yā 'Ayyuhā Al-'Insānu 'Innaka Kādiĥun 'Ilá Rabbika Kadĥāan Famulāqīhi َ084-006 Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne. يَاأَيُّهَا الإِنسَانُ إِنَّكَ كَادِح ٌ إِلَى رَبِّكَ كَدْحا ً فَمُلاَقِيهِ
Fa'ammā Man 'Ūtiya Kitābahu Biyamīnihi َ084-007 To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa. فَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَه ُُ بِيَمِينِهِ
Fasawfa Yuĥāsabu Ĥisābāan Yasīrāan َ084-008 To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi. فَسَوْفَ يُحَاسَبُ حِسَابا ً يَسِيرا ً
Wa Yanqalibu 'Ilá 'Ahlihi Masrūrāan َ084-009 Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha. وَيَنقَلِبُ إِلَى أَهْلِه ِِ مَسْرُورا ً
Wa 'Ammā Man 'Ūtiya Kitābahu Warā'a Žahrihi َ084-010 Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa. وَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَه ُُ وَرَاءَ ظَهْرِهِ
Fasawfa YadThubūrāan َ084-011 To, zã shi dinga kiran halaka! فَسَوْفَ يَدْعُو ثُبُورا ً
Wa Yaşlá Sa`īrāan َ084-012 Kuma ya shiga sa'ĩr. وَيَصْلَى سَعِيرا ً
'Innahu Kāna Fī 'Ahlihi Masrūrāan َ084-013 Lal1e ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha. إِنَّه ُُ كَانَ فِي أَهْلِه ِِ مَسْرُورا ً
'Innahu Žanna 'An Lan Yaĥūra َ084-014 Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba. إِنَّه ُُ ظَنَّ أَنْ لَنْ يَحُورَ
Balá 'Inna Rabbahu Kāna Bihi Başīrāan َ084-015 Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi. بَلَى إِنَّ رَبَّه ُُ كَانَ بِه ِِ بَصِيرا ً
Falā 'Uqsimu Bish-Shafaqi َ084-016 To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba. فَلاَ أُقْسِمُ بِالشَّفَقِ
Wa Al-Layli Wa Mā Wasaqa َ084-017 Da dare, da abin da ya ƙunsa. وَاللَّيْلِ وَمَا وَسَقَ
Wa Al-Qamari 'Idhā Attasaqa َ084-018 Da watã idan (haskensa) ya cika. وَالْقَمَرِ إِذَا اتَّسَقَ
Latarkabunna Ţabaqāan `An Ţabaqin َ084-019 Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli. لَتَرْكَبُنَّ طَبَقاً عَنْ طَبَق ٍ
Famā Lahum Lā Yu'uminūna َ084-020 To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni? فَمَا لَهُمْ لاَ يُؤْمِنُونَ
Wa 'Idhā Quri'a `Alayhimu Al-Qur'ānu Lā Yasjudūna َ084-021 Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u? وَإِذَا قُرِئَ عَلَيْهِمُ الْقُرْآنُ لاَ يَسْجُدُونَ
Bali Al-Ladhīna Kafarū Yukadhdhibūna َ084-022 Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi. بَلِ الَّذِينَ كَفَرُوا يُكَذِّبُونَ
Wa Allāhu 'A`lamu Bimā Yū`ūna َ084-023 Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa. وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يُوعُونَ
Fabashshirhum Bi`adhābin 'Alīmin َ084-024 Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi. فَبَشِّرْهُمْ بِعَذَابٍ أَلِيم ٍ
'Illā Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Lahum 'Ajrun Ghayru Mamnūnin َ084-025 Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa. إِلاَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُون ٍ
Next Sūrah