85) Sūrat Al-Burūj

Printed format

85) سُورَة البُرُوج

Wa As-Samā'i Dhāti Al-Burūji َ085-001 Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara. وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الْبُرُوجِ
Wa Al-Yawmi Al-Maw`ūdi َ085-002 Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa, وَالْيَوْمِ الْمَوْعُودِ
Wa Shāhidin Wa Mash/hūdin َ085-003 Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa وَشَاهِد ٍ وَمَشْهُود ٍ
Qutila 'Aşĥābu Al-'Ukhdūdi َ085-004 An la'ani mutãnen rãmi. قُتِلَ أَصْحَابُ الأُخْدُودِ
An-Nāri Dhāti Al-Waqūdi َ085-005 Wato wuta wadda aka hura. النَّارِ ذَاتِ الْوَقُودِ
'Idh Hum `Alayhā Qu`ūdun َ085-006 A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune. إِذْ هُمْ عَلَيْهَا قُعُود ٌ
Wa Hum `Alá Mā Yaf`alūna Bil-Mu'uminīna Shuhūdun َ085-007 Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce. وَهُمْ عَلَى مَا يَفْعَلُونَ بِالْمُؤْمِنِينَ شُهُود ٌ
Wa Mā Naqamū Minhum 'Illā 'An Yu'uminū Bil-Lahi Al-`Azīzi Al-Ĥamīdi َ085-008 Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa. وَمَا نَقَمُوا مِنْهُمْ إِلاَّ أَنْ يُؤْمِنُوا بِاللَّهِ الْعَزِيزِ الْحَمِيدِ
Al-Ladhī Lahu Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa  ۚ  Allāhu `Alá Kulli Shay'in Shahīdun َ085-009 Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake. الَّذِي لَه ُُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۚ  وَاللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ شَهِيد ٌ
'Inna Al-Ladhīna Fatanū Al-Mu'uminīna Wa Al-Mu'umināti Thumma Lam Yatūbū Falahum `Adhābu Jahannama Wa Lahum `Adhābu Al-Ĥarīqi َ085-010 Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara. إِنَّ الَّذِينَ فَتَنُوا الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ لَمْ يَتُوبُوا فَلَهُمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمْ عَذَابُ الْحَرِيقِ
'Inna Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Lahum Jannātun Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru  ۚ  Dhālika Al-Fawzu Al-Kabīru َ085-011 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba. إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ جَنَّات ٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ  ۚ  ذَلِكَ الْفَوْزُ الْكَبِيرُ
'Inna Baţsha Rabbika Lashadīdun َ085-012 Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai. إِنَّ بَطْشَ رَبِّكَ لَشَدِيد ٌ
'Innahu Huwa Yubdi'u Wa Yu`īdu َ085-013 Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa). إِنَّه ُُ هُوَ يُبْدِئُ وَيُعِيدُ
Wa Huwa Al-Ghafūru Al-Wadūdu َ085-014 Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya. وَهُوَ الْغَفُورُ الْوَدُودُ
Dhū Al-`Arshi Al-Majīdu َ085-015 Mai Al'arshi mai girma ذُو الْعَرْشِ الْمَجِيدُ
Fa``ālun Limā Yurīdu َ085-016 Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi. فَعَّال ٌ لِمَا يُرِيدُ
Hal 'Atāka Ĥadīthu Al-Junūdi َ085-017 Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka. هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْجُنُودِ
Fir`awna Wa Thamūda َ085-018 Fir'auna da samũdãwa? فِرْعَوْنَ وَثَمُودَ
Bali Al-Ladhīna Kafarū Fī Takdhībin َ085-019 Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa. بَلِ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي تَكْذِيب ٍ
Wa Allāhu Min Warā'ihim Muĥīţun َ085-020 Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa). وَاللَّهُ مِنْ وَرَائِهِمْ مُحِيط ٌ
Bal Huwa Qur'ānun Majīdun َ085-021 Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma. بَلْ هُوَ قُرْآن ٌ مَجِيد ٌ
Fī Lawĥin Maĥfūžin َ085-022 A cikin Allo tsararre. فِي لَوْح ٍ مَحْفُوظ ٍ
Next Sūrah