80) Sūrat `Abasa

Printed format

80) سُورَة عَبَسَ

`Abasa Wa Tawallá َ080-001 Yã game huska kuma ya jũya bãya. عَبَسَ وَتَوَلَّى
'An Jā'ahu Al-'A`má َ080-002 Sabõda makãho yã je masa. أَنْ جَاءَهُ الأَعْمَى
Wa Mā Yudrīka La`allahu Yazzakká َ080-003 To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka. وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّه ُُ يَزَّكَّى
'Aw Yadhdhakkaru Fatanfa`ahu Adh-Dhikrá َ080-004 Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi? أَوْ يَذَّكَّرُ فَتَنْفَعَهُ الذِّكْرَى
'Ammā Mani Astaghná َ080-005 Amma wanda ya wadãtu da dũkiya. أَمَّا مَنِ اسْتَغْنَى
Fa'anta Lahu Taşaddá َ080-006 Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi! فَأَنْتَ لَه ُُ تَصَدَّى
Wa Mā `Alayka 'Allā Yazzakká َ080-007 To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba? وَمَا عَلَيْكَ أَلاَّ يَزَّكَّى
Wa 'Ammā Man Jā'aka Yas`á َ080-008 Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa. وَأَمَّا مَنْ جَاءَكَ يَسْعَى
Wa Huwa Yakhshá َ080-009 Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah. وَهُوَ يَخْشَى
Fa'anta `Anhu Talahhá َ080-010 Kai kuma kã shagala ga barinsa! فَأَنْتَ عَنْهُ تَلَهَّى
Kallā 'Innahā Tadhkirahun َ080-011 A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce. كَلاَّ إِنَّهَا تَذْكِرَة ٌ
Faman Shā'a Dhakarahu َ080-012 Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah). فَمَنْ شَاءَ ذَكَرَهُ
Fī Şuĥufin Mukarramahin َ080-013 (Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa, فِي صُحُف ٍ مُكَرَّمَة ٍ
Marfū`atin Muţahharahin َ080-014 Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa. مَرْفُوعَة ٍ مُطَهَّرَة ٍ
Bi'aydī Safarahin َ080-015 A cikin hannãyen mala'iku marubũta. بِأَيْدِي سَفَرَة ٍ
Kirāmin Bararahin َ080-016 Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah. كِرَام ٍ بَرَرَة ٍ
Qutila Al-'Insānu Mā 'Akfarahu َ080-017 An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa! قُتِلَ الإِنْسَانُ مَا أَكْفَرَهُ
Min 'Ayyi Shay'in Khalaqahu َ080-018 Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi? مِنْ أَيِّ شَيْءٍ خَلَقَهُ
Min Nuţfatin Khalaqahu Faqaddarahu َ080-019 Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye). مِنْ نُطْفَةٍ خَلَقَه ُُ فَقَدَّرَهُ
Thumma As-Sabīla Yassarahu َ080-020 Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa. ثُمَّ السَّبِيلَ يَسَّرَهُ
Thumma 'Amātahu Fa'aqbarahu َ080-021 Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari. ثُمَّ أَمَاتَه ُُ فَأَقْبَرَهُ
Thumma 'Idhā Shā'a 'Ansharahu َ080-022 Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi. ثُمَّ إِذَا شَاءَ أَنْشَرَهُ
Kallā Lammā Yaqđi Mā 'Amarahu َ080-023 Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari). كَلاَّ لَمَّا يَقْضِ مَا أَمَرَهُ
Falyanžuri Al-'Insānu 'Ilá Ţa`āmihi َ080-024 To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa. فَلْيَنْظُرِ الإِنسَانُ إِلَى طَعَامِهِ
'Annā Şabab Al-Mā'a Şabbāan َ080-025 Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa. أَنَّا صَبَبْنَا الْمَاءَ صَبّا ً
Thumma Shaqaq Al-'Arđa Shaqqāan َ080-026 Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa. ثُمَّ شَقَقْنَا الأَرْضَ شَقّا ً
Fa'anbatnā Fīhā Ĥabbāan َ080-027 Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya ,a cikinta. فَأَنْبَتْنَا فِيهَا حَبّا ً
Wa `Inabāan Wa Qađbāan َ080-028 Da inabi da ciyãwa. وَعِنَبا ً وَقَضْبا ً
Wa Zaytūnāan Wa Nakhan َ080-029 Da zaitũni da itãcen dabĩno. وَزَيْتُونا ً وَنَخْلا ً
Wa Ĥadā'iqa Ghulbāan َ080-030 Da lambuna, mãsu yawan itãce. وَحَدَائِقَ غُلْبا ً
Wa Fākihatan Wa 'Abbāan َ080-031 Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi. وَفَاكِهَة ً وَأَبّا ً
Matā`āan Lakum Wa Li'an`āmikum َ080-032 Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku. مَتَاعا ً لَكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ
Fa'idhā Jā'ati Aş-Şākhkhahu َ080-033 To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo. فَإِذَا جَاءَتِ الصَّاخَّةُ
Yawma Yafirru Al-Mar'u Min 'Akhīhi َ080-034 Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa. يَوْمَ يَفِرُّ الْمَرْءُ مِنْ أَخِيهِ
Wa 'Ummihi Wa 'Abīhi َ080-035 Da uwarsa da ubansa. وَأُمِّه ِِ وَأَبِيهِ
Wa Şāĥibatihi Wa Banīhi َ080-036 Da mãtarsa da ɗiyansa. وَصَاحِبَتِه ِِ وَبَنِيهِ
Likulli Amri'in Minhum Yawma'idhin Sha'nun Yughnīhi َ080-037 Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi. لِكُلِّ امْرِئ ٍ مِنْهُمْ يَوْمَئِذ ٍ شَأْن ٌ يُغْنِيهِ
Wujūhun Yawma'idhin Musfirahun َ080-038 Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne. وُجُوه ٌ ٌ يَوْمَئِذ ٍ مُسْفِرَة ٌ
Đāĥikatun Mustabshirahun َ080-039 Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra. ضَاحِكَة ٌ مُسْتَبْشِرَة ٌ
Wa Wujūhun Yawma'idhin `Alayhā Ghabarahun َ080-040 Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu. وَوُجُوه ٌ ٌ يَوْمَئِذٍ عَلَيْهَا غَبَرَة ٌ
Tarhaquhā Qatarahun َ080-041 Baƙi zai rufe su. تَرْهَقُهَا قَتَرَة ٌ
'Ūlā'ika Humu Al-Kafaratu Al-Fajarahu َ080-042 Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu). أُوْلَائِكَ هُمُ الْكَفَرَةُ الْفَجَرَةُ
Next Sūrah