81) Sūrat At-Takwīr

Printed format

81) سُورَة التَّكوِير

'Idhā Ash-Shamsu Kūwirat َ081-001 Idan rãna aka shafe haskenta إِذَا الشَّمْسُ كُوِّرَتْ
Wa 'Idhā An-Nujūmu Ankadarat َ081-002 Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani). وَإِذَا النُّجُومُ انكَدَرَتْ
Wa 'Idhā Al-Jibālu Suyyirat َ081-003 Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su. وَإِذَا الْجِبَالُ سُيِّرَتْ
Wa 'Idhā Al-`Ishāru `Uţţilat َ081-004 Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba. وَإِذَا الْعِشَارُ عُطِّلَتْ
Wa 'Idhā Al-Wuĥūshu Ĥushirat َ081-005 Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su. وَإِذَا الْوُحُوشُ حُشِرَتْ
Wa 'Idhā Al-Biĥāru Sujjirat َ081-006 Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta. وَإِذَا الْبِحَارُ سُجِّرَتْ
Wa 'Idhā An-Nufūsu Zūwijat َ081-007 Kuma idan rãyuka aka haɗa su da jikunkunansu. وَإِذَا النُّفُوسُ زُوِّجَتْ
Wa 'Idhā Al-Maw'ūdatu Su'ilat َ081-008 Kuma idan wadda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta. وَإِذَا الْمَوْءُودَةُ سُئِلَتْ
Bi'ayyi Dhanbin Qutilat َ081-009 "Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?" بِأَيِّ ذَنْب ٍ قُتِلَتْ
Wa 'Idhā Aş-Şuĥufu Nushirat َ081-010 Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su). وَإِذَا الصُّحُفُ نُشِرَتْ
Wa 'Idhā As-Samā'u Kushiţat َ081-011 Kuma idan sama aka fẽɗe ta. وَإِذَا السَّمَاءُ كُشِطَتْ
Wa 'Idhā Al-Jaĥīmu Su``irat َ081-012 Kuma idan Jahĩm aka hũra ta وَإِذَا الْجَحِيمُ سُعِّرَتْ
Wa 'Idhā Al-Jannatu 'Uzlifat َ081-013 Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita. وَإِذَا الْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ
`Alimat Nafsun Mā 'Aĥđarat َ081-014 Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan). عَلِمَتْ نَفْس ٌ مَا أَحْضَرَتْ
Falā 'Uqsimu Bil-Khunnasi َ081-015 To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã ba. فَلاَ أُقْسِمُ بِالْخُنَّسِ
Al-Jawāri Al-Kunnasi َ081-016 Mãsu gudu suna ɓũya. الْجَوَارِ الْكُنَّسِ
Wa Al-Layli 'Idhā `As`asa َ081-017 Da dare idan ya bãyar da bãya. وَاللَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ
Wa Aş-Şubĥi 'Idhā Tanaffasa َ081-018 Da sãfiya idan ta yi lumfashi. وَالصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ
'Innahu Laqawlu Rasūlin Karīmin َ081-019 Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah. إِنَّه ُُ لَقَوْلُ رَسُول ٍ كَرِيم ٍ
Dhī Qūwatin `Inda Dhī Al-`Arshi Makīnin َ081-020 Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi. ذِي قُوَّةٍ عِنْدَ ذِي الْعَرْشِ مَكِين ٍ
Muţā`in Thamma 'Amīnin َ081-021 Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce. مُطَاع ٍ ثَمَّ أَمِين ٍ
Wa Mā Şāĥibukum Bimajnūnin َ081-022 Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne. وَمَا صَاحِبُكُمْ بِمَجْنُون ٍ
Wa Laqad Ra'āhu Bil-'Ufuqi Al-Mubīni َ081-023 Kuma lalle ne, yã gan shi a cikin sararin sama mabayyani. وَلَقَدْ رَآهُ بِالأُفُقِ الْمُبِينِ
Wa Mā Huwa `Alá Al-Ghaybi Biđanīnin َ081-024 Kuma shi, ga gaibi bã mai rowa ba ne. وَمَا هُوَ عَلَى الْغَيْبِ بِضَنِين ٍ
Wa Mā Huwa Biqawli Shayţānin Rajīmin َ081-025 Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce. وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَان ٍ رَجِيم ٍ
Fa'ayna Tadh/habūna َ081-026 Shin, a inã zã ku tafi? فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ
'In Huwa 'Illā Dhikrun Lil`ālamīna َ081-027 Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai. إِنْ هُوَ إِلاَّ ذِكْر ٌ لِلْعَالَمِينَ
Liman Shā'a Minkum 'An Yastaqīma َ081-028 Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu. لِمَنْ شَاءَ مِنْكُمْ أَنْ يَسْتَقِيمَ
Wa Mā Tashā'ūna 'Illā 'An Yashā'a Al-Lahu Rabbu Al-`Ālamīna َ081-029 Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda. وَمَا تَشَاءُونَ إِلاَّ أَنْ يَشَاءَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ
Next Sūrah