75) Sūrat Al-Qiyāmah

Printed format

75) سُورَة الْقِيَامَه

Lā 'Uqsimu Biyawmi Al-Qiyāmahi َ075-001 Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba. لاَ أُقْسِمُ بِيَوْمِ الْقِيَامَةِ
Wa Lā 'Uqsimu Bin-Nafsi Al-Lawwāmahi َ075-002 Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba. وَلاَ أُقْسِمُ بِالنَّفْسِ اللَّوَّامَةِ
'Ayaĥsabu Al-'Insānu 'Allan Najma`a `Ižāmahu َ075-003 Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba? أَيَحْسَبُ الإِنسَانُ أَلَّنْ نَجْمَعَ عِظَامَهُ
Balá Qādirīna `Alá 'An Nusawwiya Banānahu َ075-004 Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa. بَلَى قَادِرِينَ عَلَى أَنْ نُسَوِّيَ بَنَانَهُ
Bal Yurīdu Al-'Insānu Liyafjura 'Amāmahu َ075-005 Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa. بَلْ يُرِيدُ الإِنسَانُ لِيَفْجُرَ أَمَامَهُ
Yas'alu 'Ayyāna Yawmu Al-Qiyāmahi َ075-006 Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?" يَسْأَلُ أَيَّانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ
Fa'idhā Bariqa Al-Başaru َ075-007 To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli). فَإِذَا بَرِقَ الْبَصَرُ
Wa Khasafa Al-Qamaru َ075-008 Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe). وَخَسَفَ الْقَمَرُ
Wa Jumi`a Ash-Shamsu Wa Al-Qamaru َ075-009 Aka tãra rãnã da watã وَجُمِعَ الشَّمْسُ وَالْقَمَرُ
Yaqūlu Al-'Insānu Yawma'idhin 'Ayna Al-Mafarru َ075-010 Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?" يَقُولُ الإِنسَانُ يَوْمَئِذٍ أَيْنَ الْمَفَرُّ
Kallā Lā Wazara َ075-011 A'aha! bãbu mafaka. كَلاَّ لاَ وَزَرَ
'Ilá Rabbika Yawma'idhin Al-Mustaqarru َ075-012 zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake. إِلَى رَبِّكَ يَوْمَئِذ ٍ الْمُسْتَقَرُّ
Yunabba'u Al-'Insānu Yawma'idhin Bimā Qaddama Wa 'Akhkhara َ075-013 Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar. يُنَبَّأُ الإِنسَانُ يَوْمَئِذ ٍ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ
Bali Al-'Insānu `Alá Nafsihi Başīrahun َ075-014 Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne. بَلِ الإِنسَانُ عَلَى نَفْسِه ِِ بَصِيرَة ٌ
Wa Law 'Alqá Ma`ādhīrahu َ075-015 Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba). وَلَوْ أَلْقَى مَعَاذِيرَهُ
Lā Tuĥarrik Bihi Lisānaka Lita`jala Bihi َ075-016 Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni). لاَ تُحَرِّكْ بِه ِِ لِسَانَكَ لِتَعْجَلَ بِهِ
'Inna `Alaynā Jam`ahu Wa Qur'ānahu َ075-017 Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa. إِنَّ عَلَيْنَا جَمْعَه ُُ وَقُرْآنَهُ
Fa'idhā Qara'nāhu Fa Attabi` Qur'ānahu َ075-018 To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa. فَإِذَا قَرَأْنَاه ُُ فَاتَّبِعْ قُرْآنَهُ
Thumma 'Inna `Alaynā Bayānahu َ075-019 sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa. ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا بَيَانَهُ
Kallā Bal Tuĥibbūna Al-`Ājilaha َ075-020 A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne. كَلاَّ بَلْ تُحِبُّونَ الْعَاجِلَةَ
Wa Tadharūna Al-'Ākhiraha َ075-021 Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira). وَتَذَرُونَ الآخِرَةَ
Wujūhun Yawma'idhin Nāđirahun َ075-022 Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne. وُجُوه ٌ ٌ يَوْمَئِذ ٍ نَاضِرَة ٌ
'Ilá Rabbihā Nāžirahun َ075-023 Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne. إِلَى رَبِّهَا نَاظِرَة ٌ
Wa Wujūhun Yawma'idhin Bāsirahun َ075-024 Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne. وَوُجُوه ٌ ٌ يَوْمَئِذ ٍ بَاسِرَة ٌ
Tažunnu 'An Yuf`ala Bihā Fāqirahun َ075-025 Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso. تَظُنُّ أَنْ يُفْعَلَ بِهَا فَاقِرَة ٌ
Kallā 'Idhā Balaghati At-Tarāqī َ075-026 A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai. كَلاَّ إِذَا بَلَغَتِ التَّرَاقِي
Wa Qīla Man  ۜ  Rāqin َ075-027 kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?" وَقِيلَ مَنْ  ۜ  رَاق ٍ
Wa Žanna 'Annahu Al-Firāqu َ075-028 Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce. وَظَنَّ أَنَّهُ الْفِرَاقُ
Wa Altaffati As-Sāqu Bis-Sāqi َ075-029 Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri. وَالْتَفَّتِ السَّاقُ بِالسَّاقِ
'Ilá Rabbika Yawma'idhin Al-Masāqu َ075-030 Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take. إِلَى رَبِّكَ يَوْمَئِذ ٍ الْمَسَاقُ
Falā Şaddaqa Wa Lā Şallá َ075-031 To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba! فَلاَ صَدَّقَ وَلاَ صَلَّى
Wa Lakin Kadhdhaba Wa Tawallá َ075-032 Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya! وَلَكِنْ كَذَّبَ وَتَوَلَّى
Thumma Dhahaba 'Ilá 'Ahlihi Yatamaţţá َ075-033 Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama. ثُمَّ ذَهَبَ إِلَى أَهْلِه ِِ يَتَمَطَّى
'Awlá Laka Fa'awlá َ075-034 Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa. أَوْلَى لَكَ فَأَوْلَى
Thumma 'Awlá Laka Fa'awlá َ075-035 Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa. ثُمَّ أَوْلَى لَكَ فَأَوْلَى
'Ayaĥsabu Al-'Insānu 'An Yutraka Sudáan َ075-036 Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi) ? أَيَحْسَبُ الإِنسَانُ أَنْ يُتْرَكَ سُدى ً
'Alam Yaku Nuţfatan Min Manīyin Yumná َ075-037 Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa( a cikin mahaifa) أَلَمْ يَكُ نُطْفَة ً مِنْ مَنِيّ ٍ يُمْنَى
Thumma Kāna `Alaqatan Fakhalaqa Fasawwá َ075-038 Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa; ثُمَّ كَانَ عَلَقَة ً فَخَلَقَ فَسَوَّى
Faja`ala Minhu Az-Zawjayni Adh-Dhakara Wa Al-'Unthá َ075-039 Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace? فَجَعَلَ مِنْهُ الزَّوْجَيْنِ الذَّكَرَ وَالأُنثَى
'Alaysa Dhālika Biqādirin `Alá 'An Yuĥyiya Al-Mawtá َ075-040 Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu? أَلَيْسَ ذَلِكَ بِقَادِرٍ عَلَى أَنْ يُحْيِيَ الْمَوْتَى
Next Sūrah