76) Sūrat Al-'Inn

Printed format

76) سُورَة الإنسَان

Hal 'Atá `Alá Al-'Insāni Ĥīnun Mina Ad-Dahri Lam Yakun Shay'āan Madhkūrāan َ076-001 Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata. هَلْ أَتَى عَلَى الإِنسَانِ حِين ٌ مِنَ الدَّهْرِ لَمْ يَكُنْ شَيْئا ً مَذْكُورا ً
'Innā Khalaq Al-'Insāna Min Nuţfatin 'Amshājin Nabtalīhi Faja`alnāhu Samī`āan Başīrāan َ076-002 Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani, إِنَّا خَلَقْنَا الإِنسَانَ مِنْ نُطْفَةٍ أَمْشَاج ٍ نَبْتَلِيه ِِ فَجَعَلْنَاه ُُ سَمِيعا ً بَصِيرا ً
'Innā Hadaynāhu As-Sabīla 'Immā Shākirāan Wa 'Immā Kafūrāan َ076-003 Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci. إِنَّا هَدَيْنَاهُ السَّبِيلَ إِمَّا شَاكِرا ً وَإِمَّا كَفُورا ً
'Innā 'A`tadnā Lilkāfirīna Salāsilāan Wa 'Aghlālāan Wa Sa`īrāan َ076-004 Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr. إِنَّا أَعْتَدْنَا لِلْكَافِرِينَ سَلاَسِلا ً وَأَغْلاَلا ً وَسَعِيرا ً
'Inna Al-'Abrāra Yashrabūna Min Ka'sin Kāna Mizājuhā Kāfūrāan َ076-005 Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne. إِنَّ الأَبْرَارَ يَشْرَبُونَ مِنْ كَأْس ٍ كَانَ مِزَاجُهَا كَافُورا ً
`Aynāan Yashrabu Bihā `Ibādu Al-Lahi Yufajjirūnahā Tafjīrāan َ076-006 Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa. عَيْنا ً يَشْرَبُ بِهَا عِبَادُ اللَّهِ يُفَجِّرُونَهَا تَفْجِيرا ً
Yūfūna Bin-Nadhri Wa Yakhāfūna Yawmāan Kāna Sharruhu Mustaţīrāan َ076-007 Suna cikãwa da alwãshin (da suka bãkanta), kuma suna tsõron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne. يُوفُونَ بِالنَّذْرِ وَيَخَافُونَ يَوْما ً كَانَ شَرُّه ُُ مُسْتَطِيرا ً
Wa Yuţ`imūna Aţ-Ţa`āma `Alá Ĥubbihi Miskīnāan Wa Yatīmāan Wa 'Asīrāan َ076-008 Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme. وَيُطْعِمُونَ الطَّعَامَ عَلَى حُبِّه ِِ مِسْكِينا ً وَيَتِيما ً وَأَسِيرا ً
'Innamā Nuţ`imukum Liwajhi Al-Lahi Lā Nurīdu Minkum Jazā'an Wa Lā Shukūrāan َ076-009 (Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya. إِنَّمَا نُطْعِمُكُمْ لِوَجْهِ اللَّهِ لاَ نُرِيدُ مِنْكُمْ جَزَاء ً وَلاَ شُكُورا ً
'Innā Nakhāfu Min Rabbinā Yawmāan `Abūsāan Qamţarīrāan َ076-010 "Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa." إِنَّا نَخَافُ مِنْ رَبِّنَا يَوْماً عَبُوسا ً قَمْطَرِيرا ً
Fawaqāhumu Al-Lahu Sharra Dhālika Al-Yawmi Wa Laqqāhum Nađratan Wa Surūrāan َ076-011 Sabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin huska da farin ciki, فَوَقَاهُمُ اللَّهُ شَرَّ ذَلِكَ الْيَوْمِ وَلَقَّاهُمْ نَضْرَة ً وَسُرُورا ً
Wa Jazāhum Bimā Şabarū Jannatan Wa Ĥarīrāan َ076-012 Kuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini. وَجَزَاهُمْ بِمَا صَبَرُوا جَنَّة ً وَحَرِيرا ً
Muttaki'īna Fīhā `Alá Al-'Arā'iki  ۖ  Lā Yarawna Fīhā Shamsāan Wa Lā Zamharīrāan َ076-013 Sunã mãsu zaman ginciri, a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta, kuma bã su ganin jaura. مُتَّكِئِينَ فِيهَا عَلَى الأَرَائِكِ  ۖ  لاَ يَرَوْنَ فِيهَا شَمْسا ً وَلاَ زَمْهَرِيرا ً
Wa Dāniyatan `Alayhim Žilāluhā Wa Dhullilat Quţūfuhā Tadhlīlāan َ076-014 Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa. وَدَانِيَةً عَلَيْهِمْ ظِلاَلُهَا وَذُلِّلَتْ قُطُوفُهَا تَذْلِيلا ً
Wa Yuţāfu `Alayhim Bi'āniyatin Min Fiđđatin Wa 'Akwābin Kānat Qawārīra َ076-015 Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau. وَيُطَافُ عَلَيْهِمْ بِآنِيَة ٍ مِنْ فِضَّة ٍ وَأَكْوَاب ٍ كَانَتْ قَوَارِيرَ
Qawārīra Min Fiđđatin Qaddarūhā Taqdīrāan َ076-016 ¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta. قَوَارِيرَ مِنْ فِضَّة ٍ قَدَّرُوهَا تَقْدِيرا ً
Wa Yusqawna Fīhā Ka'sāan Kāna Mizājuhā Zanjabīlāan َ076-017 Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne. وَيُسْقَوْنَ فِيهَا كَأْسا ً كَانَ مِزَاجُهَا زَنجَبِيلا ً
`Aynāan Fīhā Tusammá Salsabīlāan َ076-018 Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil. عَيْنا ً فِيهَا تُسَمَّى سَلْسَبِيلا ً
Wa Yaţūfu `Alayhim Wildānun Mukhalladūna 'Idhā Ra'aytahum Ĥasibtahum Lu'ulu'uāan Manthūrāan َ076-019 Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa. وَيَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَان ٌ مُخَلَّدُونَ إِذَا رَأَيْتَهُمْ حَسِبْتَهُمْ لُؤْلُؤا ً مَنثُورا ً
Wa 'Idhā Ra'ayta Thamma Ra'ayta Na`īmāan Wa Mulkāan Kabīrāan َ076-020 Kuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni'ima da mulki babba. وَإِذَا رَأَيْتَ ثَمَّ رَأَيْتَ نَعِيما ً وَمُلْكا ً كَبِيرا ً
`Āliyahum Thiyābu Sundusin Khuđrun Wa 'Istabraqun  ۖ  Wa Ĥullū 'Asāwira Min Fiđđatin Wa Saqāhum Rabbuhum Sharābāan Ţahūrāan َ076-021 Tufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai tsarkakẽwar (ciki). عَالِيَهُمْ ثِيَابُ سُندُسٍ خُضْر ٌ وَإِسْتَبْرَق ٌ  ۖ  وَحُلُّوا أَسَاوِرَ مِنْ فِضَّة ٍ وَسَقَاهُمْ رَبُّهُمْ شَرَابا ً طَهُورا ً
'Inna Hādhā Kāna Lakum Jazā'an Wa Kāna Sa`yukum Mashkūrāan َ076-022 (A ce musu) "Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin gõdewa." إِنَّ هَذَا كَانَ لَكُمْ جَزَاء ً وَكَانَ سَعْيُكُمْ مَشْكُورا ً
'Innā Naĥnu Nazzalnā `Alayka Al-Qur'āna Tanzīlāan َ076-023 Lalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur'ãni a gare ka, saukarwa. إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا عَلَيْكَ الْقُرْآنَ تَنْزِيلا ً
Fāşbir Liĥukmi Rabbika Wa Lā Tuţi` Minhum 'Āthimāan 'Aw Kafūrāan َ076-024 Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci. فَاصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ وَلاَ تُطِعْ مِنْهُمْ آثِماً أَوْ كَفُورا ً
Wa Adhkur Asma Rabbika Bukratan Wa 'Aşīlāan َ076-025 Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice. وَاذْكُرْ اسْمَ رَبِّكَ بُكْرَة ً وَأَصِيلا ً
Wa Mina Al-Layli Fāsjud Lahu Wa Sabbiĥhu Laylāan Ţawīlāan َ076-026 Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo. وَمِنَ اللَّيْلِ فَاسْجُدْ لَه ُُ وَسَبِّحْهُ لَيْلا ً طَوِيلا ً
'Inna Hā'uulā' Yuĥibbūna Al-`Ājilata Wa Yadharūna Warā'ahum Yawmāan Thaqīlāan َ076-027 Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi. إِنَّ هَاؤُلاَء يُحِبُّونَ الْعَاجِلَةَ وَيَذَرُونَ وَرَاءَهُمْ يَوْما ً ثَقِيلا ً
Naĥnu Khalaqnāhum Wa Shadadnā 'Asrahum  ۖ  Wa 'Idhā Shi'nā Baddalnā 'Amthālahum Tabdīlāan َ076-028 Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa. نَحْنُ خَلَقْنَاهُمْ وَشَدَدْنَا أَسْرَهُمْ  ۖ  وَإِذَا شِئْنَا بَدَّلْنَا أَمْثَالَهُمْ تَبْدِيلا ً
'Inna Hadhihi Tadhkiratun  ۖ  Faman Shā'a Attakhadha 'Ilá Rabbihi Sabīlāan َ076-029 Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa. إِنَّ هَذِه ِِ تَذْكِرَة ٌ  ۖ  فَمَنْ شَاءَ اتَّخَذَ إِلَى رَبِّه ِِ سَبِيلا ً
Wa Mā Tashā'ūna 'Illā 'An Yashā'a Al-Lahu  ۚ  'Inna Al-Laha Kāna `Alīmāan Ĥakīmāan َ076-030 Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima. وَمَا تَشَاءُونَ إِلاَّ أَنْ يَشَاءَ اللَّهُ  ۚ  إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيماً حَكِيما ً
Yudkhilu Man Yashā'u Fī Raĥmatihi Wa  ۚ  Až-Žālimīna 'A`adda Lahum `Adhābāan 'Alīmāan َ076-031 Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi. يُدْخِلُ مَنْ يَشَاءُ فِي رَحْمَتِه ِِ  ۚ  وَالظَّالِمِينَ أَعَدَّ لَهُمْ عَذَاباً أَلِيما ً
Next Sūrah