74) Sūrat Al-Muddaththir

Printed format

74) سُورَة المُدَّثِّر

Yā 'Ayyuhā Al-Muddaththiru َ074-001 Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi. يَاأَيُّهَا الْمُدَّثِّرُ
Qum Fa'andhir َ074-002 Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi قُمْ فَأَنذِرْ
Wa Rabbaka Fakabbir َ074-003 Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi, وَرَبَّكَ فَكَبِّرْ
Wa Thiyābaka Faţahhir َ074-004 Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su, وَثِيَابَكَ فَطَهِّرْ
Wa Ar-Rujza Fāhjur َ074-005 Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu. وَالرُّجْزَ فَاهْجُرْ
Wa Lā Tamnun Tastakthiru َ074-006 Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri وَلاَ تَمْنُنْ تَسْتَكْثِرُ
Wa Lirabbika Fāşbir َ074-007 Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure وَلِرَبِّكَ فَاصْبِرْ
Fa'idhā Nuqira Fī An-Nāqūri َ074-008 To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho. فَإِذَا نُقِرَ فِي النَّاقُورِ
Fadhālika Yawma'idhin Yawmun `Asīrun َ074-009 To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya فَذَلِكَ يَوْمَئِذ ٍ يَوْمٌ عَسِير ٌ
`Alá Al-Kāfirīna Ghayru Yasīrin َ074-010 A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne. عَلَى الْكَافِرِينَ غَيْرُ يَسِير ٍ
Dharnī Wa Man Khalaqtu Waĥīdāan َ074-011 Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai, ذَرْنِي وَمَنْ خَلَقْتُ وَحِيدا ً
Wa Ja`altu Lahu Mālāan Mamdūdāan َ074-012 Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya وَجَعَلْتُ لَه ُُ مَالا ً مَمْدُودا ً
Wa Banīna Shuhūdāan َ074-013 Da ɗiyã halartattu, وَبَنِينَ شُهُودا ً
Wa Mahhadtu Lahu Tamhīdāan َ074-014 Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa. وَمَهَّدْتُ لَه ُُ تَمْهِيدا ً
Thumma Yaţma`u 'An 'Azīda َ074-015 Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri! ثُمَّ يَطْمَعُ أَنْ أَزِيدَ
Kallā  ۖ  'Innahu Kāna Li'yātinā `Anīdāan َ074-016 Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai. كَلاَّ  ۖ  إِنَّه ُُ كَانَ لِأيَاتِنَا عَنِيدا ً
Sa'urhiquhu Şa`ūdāan َ074-017 Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa. سَأُرْهِقُه ُُ صَعُودا ً
'Innahu Fakkara Wa Qaddara َ074-018 Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni) إِنَّه ُُ فَكَّرَ وَقَدَّرَ
Faqutila Kayfa Qaddara َ074-019 Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara. فَقُتِلَ كَيْفَ قَدَّرَ
Thumma Qutila Kayfa Qaddara َ074-020 Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara. ثُمَّ قُتِلَ كَيْفَ قَدَّرَ
Thumma Nažara َ074-021 Sa'an nan, ya yi tunãni ثُمَّ نَظَرَ
Thumma `Abasa Wa Basara َ074-022 Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk. ثُمَّ عَبَسَ وَبَسَرَ
Thumma 'Adbara Wa Astakbara َ074-023 Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa, ثُمَّ أَدْبَرَ وَاسْتَكْبَرَ
Faqāla 'In Hādhā 'Illā Siĥrun Yu'utharu َ074-024 Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito." فَقَالَ إِنْ هَذَا إِلاَّ سِحْر ٌ يُؤْثَرُ
'In Hādhā 'Illā Qawlu Al-Bashari َ074-025 "Wannan maganar mutum dai ce." إِنْ هَذَا إِلاَّ قَوْلُ الْبَشَرِ
Sa'uşlīhi Saqara َ074-026 Zã Ni ƙõna shi da Saƙar. سَأُصْلِيه ِِ سَقَرَ
Wa Mā 'Adrāka Mā Saqaru َ074-027 Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar! وَمَا أَدْرَاكَ مَا سَقَرُ
Lā Tubqī Wa Lā Tadharu َ074-028 Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari. لاَ تُبْقِي وَلاَ تَذَرُ
Lawwāĥatun Lilbashari َ074-029 Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna). لَوَّاحَة ٌ لِلْبَشَرِ
`Alayhā Tis`ata `Ashara َ074-030 A kanta akwai (matsara) gõma shã tara. عَلَيْهَا تِسْعَةَ عَشَرَ
Wa Mā Ja`alnā 'Aşĥāba An-Nāri 'Illā Malā'ikatan  ۙ  Wa Mā Ja`alnā `Iddatahum 'Illā Fitnatan Lilladhīna Kafarū Liyastayqina Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba Wa Yazdāda Al-Ladhīna 'Āmanū 'Īmānāan  ۙ  Wa Lā Yartāba Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba Wa Al-Mu'uminūna  ۙ  Wa Liyaqūla Al-Ladhīna Fī Qulūbihim Marađun Wa Al-Kāfirūna Mādhā 'Arāda Al-Lahu Bihadhā Mathalāan  ۚ  Kadhālika Yuđillu Al-Lahu Man Yashā'u Wa Yahdī Man Yashā'u  ۚ  Wa Mā Ya`lamu Junūda Rabbika 'Illā Huwa  ۚ  Wa Mā Hiya 'Illā Dhikrá Lilbashari َ074-031 Kuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum. وَمَا جَعَلْنَا أَصْحَابَ النَّارِ إِلاَّ مَلاَئِكَة ً  ۙ  وَمَا جَعَلْنَا عِدَّتَهُمْ إِلاَّ فِتْنَة ً لِلَّذِينَ كَفَرُوا لِيَسْتَيْقِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ وَيَزْدَادَ الَّذِينَ آمَنُوا إِيمَانا ً  ۙ  وَلاَ يَرْتَابَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ وَالْمُؤْمِنُونَ  ۙ  وَلِيَقُولَ الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ مَرَض ٌ وَالْكَافِرُونَ مَاذَا أَرَادَ اللَّهُ بِهَذَا مَثَلا ً  ۚ  كَذَلِكَ يُضِلُّ اللَّهُ مَنْ يَشَاءُ وَيَهْدِي مَنْ يَشَاءُ  ۚ  وَمَا يَعْلَمُ جُنُودَ رَبِّكَ إِلاَّ هُوَ  ۚ  وَمَا هِيَ إِلاَّ ذِكْرَى لِلْبَشَرِ
Kallā Wa Al-Qamari َ074-032 A'aha! Ina rantsuwa da watã. كَلاَّ وَالْقَمَرِ
Wa Al-Layli 'Idh 'Adbara َ074-033 Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya. وَاللَّيْلِ إِذْ أَدْبَرَ
Wa Aş-Şubĥi 'Idhā 'Asfara َ074-034 Da sãfiya idan ta wãye. وَالصُّبْحِ إِذَا أَسْفَرَ
'Innahā La'iĥdá Al-Kubari َ074-035 Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce. إِنَّهَا لَإِحْدَى الْكُبَرِ
Nadhīrāan Lilbashari َ074-036 Mai gargaɗĩ ce ga mutum. نَذِيرا ً لِلْبَشَرِ
Liman Shā'a Minkum 'An Yataqaddama 'Aw Yata'akhkhara َ074-037 Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta. لِمَنْ شَاءَ مِنْكُمْ أَنْ يَتَقَدَّمَ أَوْ يَتَأَخَّرَ
Kullu Nafsin Bimā Kasabat Rahīnahun َ074-038 Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce. كُلُّ نَفْس ٍ بِمَا كَسَبَتْ رَهِينَة ٌ
'Illā 'Aşĥāba Al-Yamīni َ074-039 Fãce mutãnen dãma. إِلاَّ أَصْحَابَ الْيَمِينِ
Fī Jannātin Yatasā'alūna َ074-040 A cikin Aljanna suna tambayar jũna. فِي جَنَّات ٍ يَتَسَاءَلُونَ
`Ani Al-Mujrimīna َ074-041 Game da mãsu laifi. عَنِ الْمُجْرِمِينَ
Mā Salakakum Fī Saqara َ074-042 (Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar?" مَا سَلَكَكُمْ فِي سَقَرَ
Qālū Lam Naku Mina Al-Muşallīna َ074-043 Suka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba." قَالُوا لَمْ نَكُ مِنَ الْمُصَلِّينَ
Wa Lam Naku Nuţ`imu Al-Miskīna َ074-044 "Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba." وَلَمْ نَكُ نُطْعِمُ الْمِسْكِينَ
Wa Kunnā Nakhūđu Ma`a Al-Khā'iđīna َ074-045 "Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa." وَكُنَّا نَخُوضُ مَعَ الْخَائِضِينَ
Wa Kunnā Nukadhdhibu Biyawmi Ad-Dīni َ074-046 "Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako." وَكُنَّا نُكَذِّبُ بِيَوْمِ الدِّينِ
Ĥattá 'Atānā Al-Yaqīnu َ074-047 "Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana." حَتَّى أَتَانَا الْيَقِينُ
Famā Tanfa`uhum Shafā`atu Ash-Shāfi`īna َ074-048 Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba. فَمَا تَنْفَعُهُمْ شَفَاعَةُ الشَّافِعِينَ
Famā Lahum `Ani At-Tadhkirati Mu`rīna َ074-049 Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya. فَمَا لَهُمْ عَنِ التَّذْكِرَةِ مُعْرِضِينَ
Ka'annahum Ĥumurun Mustanfirahun َ074-050 Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne. كَأَنَّهُمْ حُمُر ٌ مُسْتَنْفِرَة ٌ
Farrat Min Qaswarahin َ074-051 Sun gudu daga zãki. فَرَّتْ مِنْ قَسْوَرَة ٍ
Bal Yurīdu Kullu Amri'in Minhum 'An Yu'utá Şuĥufāan Munashsharahan َ074-052 A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa)ana wãtsãwa بَلْ يُرِيدُ كُلُّ امْرِئ ٍ مِنْهُمْ أَنْ يُؤْتَى صُحُفا ً مُنَشَّرَة ً
Kallā  ۖ  Bal Lā Yakhāfūna Al-'Ākhiraha َ074-053 A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira. كَلاَّ  ۖ  بَلْ لاَ يَخَافُونَ الآخِرَةَ
Kallā 'Innahu Tadhkirahun َ074-054 A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce. كَلاَّ إِنَّه ُُ تَذْكِرَة ٌ
Faman Shā'a Dhakarahu َ074-055 Dõmin wanda ya so, ya tuna. فَمَنْ شَاءَ ذَكَرَهُ
Wa Mā Yadhkurūna 'Illā 'An Yashā'a Al-Lahu  ۚ  Huwa 'Ahlu At-Taqwá Wa 'Ahlu Al-Maghfirahi َ074-056 Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara. وَمَا يَذْكُرُونَ إِلاَّ أَنْ يَشَاءَ اللَّهُ  ۚ  هُوَ أَهْلُ التَّقْوَى وَأَهْلُ الْمَغْفِرَةِ
Next Sūrah