70) Sūrat Al-Ma`ārij

Printed format

70) سُورَة المَعَارِج

Sa'ala Sā'ilun Bi`adhābin Wāqi`in َ070-001 Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa. سَأَلَ سَائِل ٌ بِعَذَاب ٍ وَاقِع ٍ
Lilkāfiryna Laysa Lahu Dāfi`un َ070-002 Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa. لِلْكَافِرينَ لَيْسَ لَه ُُ دَافِع ٌ
Mina Al-Lahi Dhī Al-Ma`āriji َ070-003 Daga Allah Mai matãkala. مِنَ اللَّهِ ذِي الْمَعَارِجِ
Ta`ruju Al-Malā'ikatu Wa Ar-Rūĥu 'Ilayhi Fī Yawmin Kāna Miqdāruhu Khamsīna 'Alfa Sanahin َ070-004 Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne. تَعْرُجُ الْمَلاَئِكَةُ وَالرُّوحُ إِلَيْهِ فِي يَوْم ٍ كَانَ مِقْدَارُه ُُ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَة ٍ
Fāşbir Şabrāan Jamīlāan َ070-005 Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo. فَاصْبِرْ صَبْرا ً جَمِيلا ً
'Innahum Yarawnahu Ba`īdāan َ070-006 Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa. إِنَّهُمْ يَرَوْنَه ُُ بَعِيدا ً
Wa Narāhu Qarībāan َ070-007 Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa. وَنَرَاه ُُ قَرِيبا ً
Yawma Takūnu As-Samā'u Kālmuhli َ070-008 Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa. يَوْمَ تَكُونُ السَّمَاءُ كَالْمُهْلِ
Wa Takūnu Al-Jibālu Kāl`ihni َ070-009 Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi. وَتَكُونُ الْجِبَالُ كَالْعِهْنِ
Wa Lā Yas'alu Ĥamīmun Ĥamīmāan َ070-010 Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake. وَلاَ يَسْأَلُ حَمِيمٌ حَمِيما ً
Yubaşşarūnahum  ۚ  Yawaddu Al-Mujrimu Law Yaftadī Min `Adhābi Yawmi'idhin Bibanīhi َ070-011 Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa, يُبَصَّرُونَهُمْ  ۚ  يَوَدُّ الْمُجْرِمُ لَوْ يَفْتَدِي مِنْ عَذَابِ يَوْمِئِذ ٍ بِبَنِيهِ
Wa Şāĥibatihi Wa 'Akhīhi َ070-012 Da matarsa da ɗan'uwansa. وَصَاحِبَتِه ِِ وَأَخِيهِ
Wa Faşīlatihi Allatī Tu'uwyhi َ070-013 Da danginsa, mãsu tattarã shi. وَفَصِيلَتِهِ الَّتِي تُؤْويهِ
Wa Man Al-'Arđi Jamī`āan Thumma Yunjīhi َ070-014 Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi. وَمَنْ فِي الأَرْضِ جَمِيعا ً ثُمَّ يُنجِيهِ
Kallā  ۖ  'Innahā Lažá َ070-015 A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã, كَلاَّ  ۖ  إِنَّهَا لَظَى
Nazzā`atan Lilshshawá َ070-016 Mai twãle fãtar goshi. نَزَّاعَة ً لِلشَّوَى
Tad`ū Man 'Adbara Wa Tawallá َ070-017 Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai. تَدْعُوا مَنْ أَدْبَرَ وَتَوَلَّى
Wa Jama`a Fa'aw`á َ070-018 Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka. وَجَمَعَ فَأَوْعَى
'Inna Al-'Insāna Khuliqa Halū`āan َ070-019 Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi. إِنَّ الإِنسَانَ خُلِقَ هَلُوعا ً
'Idhā Massahu Ash-Sharru Jazū`āan َ070-020 Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri. إِذَا مَسَّهُ الشَّرُّ جَزُوعا ً
Wa 'Idhā Massahu Al-Khayru Manū`āan َ070-021 Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa. وَإِذَا مَسَّهُ الْخَيْرُ مَنُوعا ً
'Illā Al-Muşallīna َ070-022 Sai mãsu yin salla, إِلاَّ الْمُصَلِّينَ
Al-Ladhīna Hum `Alá Şalātihim Dā'imūna َ070-023 Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne. الَّذِينَ هُمْ عَلَى صَلاَتِهِمْ دَائِمُونَ
Wa Al-Ladhīna Fī 'Amwālihim Ĥaqqun Ma`lūmun َ070-024 Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne. وَالَّذِينَ فِي أَمْوَالِهِمْ حَقّ ٌ مَعْلُوم ٌ
Lilssā'ili Wa Al-Maĥrūmi َ070-025 Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon. لِلسَّائِلِ وَالْمَحْرُومِ
Wa Al-Ladhīna Yuşaddiqūna Biyawmi Ad-Dīni َ070-026 Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako. وَالَّذِينَ يُصَدِّقُونَ بِيَوْمِ الدِّينِ
Wa Al-Ladhīna Hum Min `Adhābi Rabbihim Mushfiqūna َ070-027 Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro. وَالَّذِينَ هُمْ مِنْ عَذَابِ رَبِّهِمْ مُشْفِقُونَ
'Inna `Adhāba Rabbihim Ghayru Ma'mūnin َ070-028 Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce. إِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمْ غَيْرُ مَأْمُون ٍ
Wa Al-Ladhīna Hum Lifurūjihim Ĥāfižūna َ070-029 Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne. وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ
'Illā `Alá 'Azwājihim 'Aw Mā Malakat 'Aymānuhum Fa'innahum Ghayru Malūmīna َ070-030 Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne. إِلاَّ عَلَى أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ
Famani Abtaghá Warā'a Dhālika Fa'ūlā'ika Humu Al-`Ādūna َ070-031 To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka. فَمَنِ ابْتَغَى وَرَاءَ ذَلِكَ فَأُوْلَائِكَ هُمُ الْعَادُونَ
Wa Al-Ladhīna Hum Li'mānātihim Wa `Ahdihim Rā`ūna َ070-032 Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne. وَالَّذِينَ هُمْ لِأمَانَاتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَاعُونَ
Wa Al-Ladhīna Hum Bishahādātihim Qā'imūna َ070-033 Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne. وَالَّذِينَ هُمْ بِشَهَادَاتِهِمْ قَائِمُونَ
Wa Al-Ladhīna Hum `Alá Şalātihim Yuĥāfižūna َ070-034 Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne. وَالَّذِينَ هُمْ عَلَى صَلاَتِهِمْ يُحَافِظُونَ
'Ūlā'ika Fī Jannātin Mukramūna َ070-035 Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne أُوْلَائِكَ فِي جَنَّات ٍ مُكْرَمُونَ
Famāli Al-Ladhīna Kafarū Qibalaka Muhţi`īna َ070-036 Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu). فَمَالِ الَّذِينَ كَفَرُوا قِبَلَكَ مُهْطِعِينَ
`Ani Al-Yamīni Wa `Ani Ash-Shimāli `Izīna َ070-037 Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a! عَنِ الْيَمِينِ وَعَنِ الشِّمَالِ عِزِينَ
'Ayaţma`u Kullu Amri'in Minhum 'An Yudkhala Jannata Na`īmin َ070-038 Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)? أَيَطْمَعُ كُلُّ امْرِئ ٍ مِنْهُمْ أَنْ يُدْخَلَ جَنَّةَ نَعِيم ٍ
Kallā  ۖ  'Innā Khalaqnāhum Mimmā Ya`lamūna َ070-039 A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani. كَلاَّ  ۖ  إِنَّا خَلَقْنَاهُمْ مِمَّا يَعْلَمُونَ
Falā 'Uqsimu Birabbi Al-Mashāriqi Wa Al-Maghāribi 'Innā Laqādirūna َ070-040 Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne. فَلاَ أُقْسِمُ بِرَبِّ الْمَشَارِقِ وَالْمَغَارِبِ إِنَّا لَقَادِرُونَ
`Alá 'An Nubaddila Khayrāan Minhum Wa Mā Naĥnu Bimasbūqīna َ070-041 Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba. عَلَى أَنْ نُبَدِّلَ خَيْرا ً مِنْهُمْ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ
Fadharhum Yakhūđū Wa Yal`abū Ĥattá Yulāqū Yawmahumu Al-Ladhī Yū`adūna َ070-042 Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita) . فَذَرْهُمْ يَخُوضُوا وَيَلْعَبُوا حَتَّى يُلاَقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي يُوعَدُونَ
Yawma Yakhrujūna Mina Al-'Ajthi Sirā`āan Ka'annahum 'Ilá Nuşubin Yūfiđūna َ070-043 Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa. يَوْمَ يَخْرُجُونَ مِنَ الأَجْدَاثِ سِرَاعا ً كَأَنَّهُمْ إِلَى نُصُب ٍ يُوفِضُونَ
Khāshi`atan 'Abşāruhum Tarhaquhum Dhillatun  ۚ  Dhālika Al-Yawmu Al-Ladhī Kānū Yū`adūna َ070-044 Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.) خَاشِعَةً أَبْصَارُهُمْ تَرْهَقُهُمْ ذِلَّة ٌ  ۚ  ذَلِكَ الْيَوْمُ الَّذِي كَانُوا يُوعَدُونَ
Next Sūrah