71) Sūrat Nūĥ

Printed format

71) سُورَة نُوح

'Innā 'Arsalnā Nūĥāan 'Ilá Qawmihi 'An 'Andhir Qawmaka Min Qabli 'An Ya'tiyahum `Adhābun 'Alīmun َ071-001 Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu. إِنَّا أَرْسَلْنَا نُوحا ً إِلَى قَوْمِهِ~ِ أَنْ أَنذِرْ قَوْمَكَ مِنْ قَبْلِ أَنْ يَأْتِيَهُمْ عَذَابٌ أَلِيم ٌ
Qāla Yā Qawmi 'Innī Lakum Nadhīrun Mubīnun َ071-002 Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa." قَالَ يَاقَوْمِ إِنِّي لَكُمْ نَذِير ٌ مُبِين ٌ
'Ani A`budū Al-Laha Wa Attaqūhu Wa 'Aţī`ūni َ071-003 "Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni." أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاتَّقُوه ُُ وَأَطِيعُونِ
Yaghfir Lakum Min Dhunūbikum Wa Yu'uakhkhirkum 'Ilá 'Ajalin Musammáan  ۚ  'Inna 'Ajala Al-Lahi 'Idhā Jā'a Lā Yu'uakhkharu  ۖ  Law Kuntum Ta`lamūna َ071-004 "Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)." يَغْفِرْ لَكُمْ مِنْ ذُنُوبِكُمْ وَيُؤَخِّرْكُمْ إِلَى أَجَل ٍ مُسَمّى ً  ۚ  إِنَّ أَجَلَ اللَّهِ إِذَا جَاءَ لاَ يُؤَخَّرُ  ۖ  لَوْ كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Qāla Rabbi 'Innī Da`awtu Qawmī Laylāan Wa Nahārāan َ071-005 Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini." قَالَ رَبِّ إِنِّي دَعَوْتُ قَوْمِي لَيْلا ً وَنَهَارا ً
Falam Yazid/hum Du`ā'ī 'Illā Firārāan َ071-006 "To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)." فَلَمْ يَزِدْهُمْ دُعَائِي إِلاَّ فِرَارا ً
Wa 'Innī Kullamā Da`awtuhum Litaghfira Lahum Ja`alū 'Aşābi`ahum Fī 'Ādhānihim Wa Astaghshaw Thiyābahum Wa 'Aşarrū Wa Astakbarū Astikbārāan َ071-007 "Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai." وَإِنِّي كُلَّمَا دَعَوْتُهُمْ لِتَغْفِرَ لَهُمْ جَعَلُوا أَصَابِعَهُمْ فِي آذَانِهِمْ وَاسْتَغْشَوْا ثِيَابَهُمْ وَأَصَرُّوا وَاسْتَكْبَرُوا اسْتِكْبَارا ً
Thumma 'Innī Da`awtuhum Jihārāan َ071-008 "Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane." ثُمَّ إِنِّي دَعَوْتُهُمْ جِهَارا ً
Thumma 'Innī 'A`lantu Lahum Wa 'Asrartu Lahum 'Isrārāan َ071-009 "Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri." ثُمَّ إِنِّي أَعْلَنتُ لَهُمْ وَأَسْرَرْتُ لَهُمْ إِسْرَارا ً
Faqultu Astaghfirū Rabbakum 'Innahu Kāna Ghaffārāan َ071-010 "Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne." فَقُلْتُ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ إِنَّه ُُ كَانَ غَفَّارا ً
Yursili As-Samā'a `Alaykum Midrārāan َ071-011 "Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga." يُرْسِلِ السَّمَاءَ عَلَيْكُمْ مِدْرَارا ً
Wa Yumdidkum Bi'amwālin Wa Banīna Wa Yaj`al Lakum Jannātin Wa Yaj`al Lakum 'Anhārāan َ071-012 "Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya,Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna." وَيُمْدِدْكُمْ بِأَمْوَال ٍ وَبَنِينَ وَيَجْعَلْ لَكُمْ جَنَّات ٍ وَيَجْعَلْ لَكُمْ أَنْهَارا ً
Mā Lakum Lā Tarjūna Lillahi Waqārāan َ071-013 "Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah," مَا لَكُمْ لاَ تَرْجُونَ لِلَّهِ وَقَارا ً
Wa Qad Khalaqakum 'Aţwārāan َ071-014 "Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?" وَقَدْ خَلَقَكُمْ أَطْوَارا ً
'Alam Taraw Kayfa Khalaqa Al-Lahu Sab`a Samāwātin Ţibāqāan َ071-015 "Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?" أَلَمْ تَرَوْا كَيْفَ خَلَقَ اللَّهُ سَبْعَ سَمَاوَات ٍ طِبَاقا ً
Wa Ja`ala Al-Qamara Fīhinna Nūrāan Wa Ja`ala Ash-Shamsa Sirājāan َ071-016 "Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?" وَجَعَلَ الْقَمَرَ فِيهِنَّ نُورا ً وَجَعَلَ الشَّمْسَ سِرَاجا ً
Wa Allāhu 'Anbatakum Mina Al-'Arđi Nabātāan َ071-017 "Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa." وَاللَّهُ أَنْبَتَكُمْ مِنَ الأَرْضِ نَبَاتا ً
Thumma Yu`īdukum Fīhā Wa Yukhrijukum 'Ikhrājāan َ071-018 "Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa." ثُمَّ يُعِيدُكُمْ فِيهَا وَيُخْرِجُكُمْ إِخْرَاجا ً
Wa Allāhu Ja`ala Lakumu Al-'Arđa Bisāţāan َ071-019 "Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya." وَاللَّهُ جَعَلَ لَكُمُ الأَرْضَ بِسَاطا ً
Litaslukū Minhā Subulāan Fijājāan َ071-020 "Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi." لِتَسْلُكُوا مِنْهَا سُبُلا ً فِجَاجا ً
Qāla Nūĥun Rabbi 'Innahum `Aşawnī Wa Attaba`ū Man Lam Yazid/hu Māluhu Wa Waladuhu 'Illā Khasārāan َ071-021 Nũhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra." قَالَ نُوح ٌ رَبِّ إِنَّهُمْ عَصَوْنِي وَاتَّبَعُوا مَنْ لَمْ يَزِدْهُ مَالُه ُُ وَوَلَدُهُ~ُ إِلاَّ خَسَارا ً
Wa Makarū Makrāan Kubbārāan َ071-022 "Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba." وَمَكَرُوا مَكْرا ً كُبَّارا ً
Wa Qālū Lā Tadharunna 'Ālihatakum Wa Lā Tadharunna Waddāan Wa Lā Suwā`āan Wa Lā Yaghūtha Wa Ya`ūqa Wa Nasrāan َ071-023 "Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Ya'ũƙa da Nasra." وَقَالُوا لاَ تَذَرُنَّ آلِهَتَكُمْ وَلاَ تَذَرُنَّ وَدّا ً وَلاَ سُوَاعا ً وَلاَ يَغُوثَ وَيَعُوقَ وَنَسْرا ً
Wa Qad 'Ađallū Kathīrāan  ۖ  Wa Lā Tazidi Až-Žālimīna 'Illā Đalālāan َ071-024 "Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata." وَقَدْ أَضَلُّوا كَثِيرا ً  ۖ  وَلاَ تَزِدِ الظَّالِمِينَ إِلاَّ ضَلاَلا ً
Mimmā Khī'ātihim 'Ughriqū Fa'udkhilū Nārāan Falam Yajidū Lahum Min Dūni Al-Lahi 'Anşārāan َ071-025 Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba. مِمَّا خَطِيئَاتِهِمْ أُغْرِقُوا فَأُدْخِلُوا نَارا ً فَلَمْ يَجِدُوا لَهُمْ مِنْ دُونِ اللَّهِ أَنْصَارا ً
Wa Qāla Nūĥun Rabbi Lā Tadhar `Alá Al-'Arđi Mina Al-Kāfirīna Dayyārāan َ071-026 Kuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida." وَقَالَ نُوح ٌ رَبِّ لاَ تَذَرْ عَلَى الأَرْضِ مِنَ الْكَافِرِينَ دَيَّارا ً
'Innaka 'In Tadharhum Yuđillū `Ibādaka Wa Lā Yalidū 'Illā Fājirāan Kaffārāan َ071-027 "Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci" إِنَّكَ إِنْ تَذَرْهُمْ يُضِلُّوا عِبَادَكَ وَلاَ يَلِدُوا إِلاَّ فَاجِرا ً كَفَّارا ً
Rabbi Aghfir Lī Wa Liwālidayya Wa Liman Dakhala Baytiya Mu'umināan Wa Lilmu'uminīna Wa Al-Mu'umināti Wa Lā Tazidi Až-Žālimīna 'Illā Tabārāan َ071-028 "Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka." رَبِّ اغْفِرْ لِي وَلِوَالِدَيَّ وَلِمَنْ دَخَلَ بَيْتِيَ مُؤْمِنا ً وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ وَلاَ تَزِدِ الظَّالِمِينَ إِلاَّ تَبَارا ً
Next Sūrah