69) Sūrat Al-Ĥāqqah

Printed format

69) سُورَة الحَاقَّه

Al-Ĥāqqahu َ069-001 Kiran gaskiya! الْحَاقَّةُ
Al-Ĥāqqahu َ069-002 Mẽne ne kiran gaskiya? مَا الْحَاقَّةُ
Wa Mā 'Adrāka Mā Al-Ĥāqqahu َ069-003 Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya? وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْحَاقَّةُ
Kadhdhabat Thamūdu Wa `Ādun Bil-Qāri`ahi َ069-004 Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya! كَذَّبَتْ ثَمُودُ وَعَاد ٌ بِالْقَارِعَةِ
Fa'ammā Thamūdu Fa'uhlikū Biţ-Ţāghiyahi َ069-005 To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani. فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهْلِكُوا بِالطَّاغِيَةِ
Wa 'Ammā `Ādun Fa'uhlikū Birīĥin Şarşarin `Ātiyahin َ069-006 Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi. وَأَمَّا عَاد ٌ فَأُهْلِكُوا بِرِيح ٍ صَرْصَرٍ عَاتِيَة ٍ
Sakhkharahā `Alayhim Sab`a Layālin Wa Thamāniyata 'Ayyāmin Ĥusūmāan Fatará Al-Qawma Fīhā Şar`á Ka'annahum 'A`jāzu Nakhlin Khāwiyahin َ069-007 (Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi. سَخَّرَهَا عَلَيْهِمْ سَبْعَ لَيَال ٍ وَثَمَانِيَةَ أَيَّامٍ حُسُوما ً فَتَرَى الْقَوْمَ فِيهَا صَرْعَى كَأَنَّهُمْ أَعْجَازُ نَخْلٍ خَاوِيَة ٍ
Fahal Tará Lahum Min Bāqiyahin َ069-008 To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu? فَهَلْ تَرَى لَهُمْ مِنْ بَاقِيَة ٍ
Wa Jā'a Fir`awnu Wa Man Qablahu Wa Al-Mu'utafikātu Bil-Khāţi'ahi َ069-009 Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi. وَجَاءَ فِرْعَوْنُ وَمَنْ قَبْلَه ُُ وَالْمُؤْتَفِكَاتُ بِالْخَاطِئَةِ
Fa`aşaw Rasūla Rabbihim Fa'akhadhahum 'Akhdhatan Rābiyahan َ069-010 Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani). فَعَصَوْا رَسُولَ رَبِّهِمْ فَأَخَذَهُمْ أَخْذَة ً رَابِيَة ً
'Innā Lammā Ţaghá Al-Mā'u Ĥamalnākum Al-Jāriyahi َ069-011 Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan. إِنَّا لَمَّا طَغَى الْمَاءُ حَمَلْنَاكُمْ فِي الْجَارِيَةِ
Linaj`alahā Lakum Tadhkiratan Wa Ta`iyahā 'Udhunun Wā`iyahun َ069-012 Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi). لِنَجْعَلَهَا لَكُمْ تَذْكِرَة ً وَتَعِيَهَا أُذُن ٌ وَاعِيَة ٌ
Fa'idhā Nufikha Fī Aş-Şūri Nafkhatun Wāĥidahun َ069-013 To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya. فَإِذَا نُفِخَ فِي الصُّورِ نَفْخَة ٌ وَاحِدَة ٌ
Wa Ĥumilati Al-'Arđu Wa Al-Jibālu Fadukkatā Dakkatan Wāĥidahan َ069-014 Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya. وَحُمِلَتِ الأَرْضُ وَالْجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّة ً وَاحِدَة ً
Fayawma'idhin Waqa`ati Al-Wāqi`ahu َ069-015 A ran nan, mai aukuwa zã ta auku. فَيَوْمَئِذ ٍ وَقَعَتِ الْوَاقِعَةُ
Wa Anshaqqati As-Samā'u Fahiya Yawma'idhin Wa Ahiyahun َ069-016 Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce. وَانشَقَّتِ السَّمَاءُ فَهِيَ يَوْمَئِذ ٍ وَاهِيَة ٌ
Wa Al-Malaku `Alá  ۚ  'Arjā'ihā Wa Yaĥmilu `Arsha Rabbika Fawqahum Yawma'idhin Thamāniyahun َ069-017 Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar. وَالْمَلَكُ عَلَى أَرْجَائِهَا  ۚ  وَيَحْمِلُ عَرْشَ رَبِّكَ فَوْقَهُمْ يَوْمَئِذ ٍ ثَمَانِيَة ٌ
Yawma'idhin Tu`rađūna Lā Takhfá Minkum Khāfiyahun َ069-018 A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa. يَوْمَئِذ ٍ تُعْرَضُونَ لاَ تَخْفَى مِنْكُمْ خَافِيَة ٌ
Fa'ammā Man 'Ūtiya Kitābahu Biyamīnihi Fayaqūlu Hā'uum Aqra'ū Kitābī َ069-019 To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina." فَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَه ُُ بِيَمِينِه ِِ فَيَقُولُ هَاؤُمْ اقْرَءُوا كِتَابِي
'Innī Žanantu 'Annī Mulāqin Ĥisābiyah َ069-020 "Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne." إِنِّي ظَنَنتُ أَنِّي مُلاَقٍ حِسَابِيَه
Fahuwa Fī `Īshatin Rāđiyahin َ069-021 Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda. فَهُوَ فِي عِيشَة ٍ رَاضِيَة ٍ
Fī Jannatin `Āliyahin َ069-022 A cikin Aljanna maɗaukakiya. فِي جَنَّةٍ عَالِيَة ٍ
Quţūfuhā Dāniyahun َ069-023 Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba), قُطُوفُهَا دَانِيَة ٌ
Kulū Wa Ashrabū Hanī'āan Bimā 'Aslaftum Al-'Ayyāmi Al-Khāliyahi َ069-024 (Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige." كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئا ً بِمَا أَسْلَفْتُمْ فِي الأَيَّامِ الْخَالِيَةِ
Wa 'Ammā Man 'Ūtiya Kitābahu Bishimālihi Fayaqūlu Yā Laytanī Lam 'Ūta Kitābīh َ069-025 Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!" وَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَه ُُ بِشِمَالِه ِِ فَيَقُولُ يَا لَيْتَنِي لَمْ أُوتَ كِتَابِيهْ
Wa Lam 'Adri Mā Ĥisābīh َ069-026 "Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!" وَلَمْ أَدْرِ مَا حِسَابِيهْ
Yā Laytahā Kānati Al-Qāđiyaha َ069-027 "In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce! يَا لَيْتَهَا كَانَتِ الْقَاضِيَةَ
Mā 'Aghná `Annī Mālīh  ۜ  َ069-028 "Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!" مَا أَغْنَى عَنِّي مَالِيهْ
Halaka `Annī Sulţānīh َ069-029 "Ĩkona ya ɓace mini!" هَلَكَ عَنِّي سُلْطَانِيهْ
Khudhūhu Faghullūhu َ069-030 (Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi." خُذُوه ُُ فَغُلُّوهُ
Thumma Al-Jaĥīma Şallūhu َ069-031 "Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi." ثُمَّ الْجَحِيمَ صَلُّوهُ
Thumma Fī Silsilatin Dhar`uhā Sab`ūna Dhirā`āan Fāslukūhu َ069-032 "Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi." ثُمَّ فِي سِلْسِلَة ٍ ذَرْعُهَا سَبْعُونَ ذِرَاعا ً فَاسْلُكُوهُ
'Innahu Kāna Lā Yu'uminu Bil-Lahi Al-`Ažīmi َ069-033 "Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!" إِنَّه ُُ كَانَ لاَ يُؤْمِنُ بِاللَّهِ الْعَظِيمِ
Wa Lā Yaĥuđđu `Alá Ţa`āmi Al-Miskīni َ069-034 "Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!" وَلاَ يَحُضُّ عَلَى طَعَامِ الْمِسْكِينِ
Falaysa Lahu Al-Yawma Hāhunā Ĥamīmun َ069-035 "Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi." فَلَيْسَ لَهُ الْيَوْمَ هَاهُنَا حَمِيم ٌ
Wa Lā Ţa`āmun 'Illā Min Ghislīnin َ069-036 "Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn." وَلاَ طَعَام ٌ إِلاَّ مِنْ غِسْلِين ٍ
Lā Ya'kuluhu 'Illā Al-Khāţi'ūna َ069-037 "Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci." لاَ يَأْكُلُهُ~ُ إِلاَّ الْخَاطِئُونَ
Falā 'Uqsimu Bimā Tubşirūna َ069-038 To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba, فَلاَ أُقْسِمُ بِمَا تُبْصِرُونَ
Wa Mā Lā Tubşirūna َ069-039 Da abin da bã ku iya gani. وَمَا لاَ تُبْصِرُونَ
'Innahu Laqawlu Rasūlin Karīmin َ069-040 Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne. إِنَّه ُُ لَقَوْلُ رَسُول ٍ كَرِيم ٍ
Wa Mā Huwa Biqawli Shā`irin  ۚ  Qalīlāan Mā Tu'uminūna َ069-041 Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata. وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَاعِر ٍ  ۚ  قَلِيلا ً مَا تُؤْمِنُونَ
Wa Lā Biqawli Kāhinin  ۚ  Qalīlāan Mā Tadhakkarūna َ069-042 Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa. وَلاَ بِقَوْلِ كَاهِن ٍ  ۚ  قَلِيلا ً مَا تَذَكَّرُونَ
Tanzīlun Min Rabbi Al-`Ālamīna َ069-043 Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka. تَنزِيل ٌ مِنْ رَبِّ الْعَالَمِينَ
Wa Law Taqawwala `Alaynā Ba`đa Al-'Aqāwīli َ069-044 Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu. وَلَوْ تَقَوَّلَ عَلَيْنَا بَعْضَ الأَقَاوِيلِ
La'akhadhnā Minhu Bil-Yamīni َ069-045 Dã Mun kãma shi da dãma. لَأَخَذْنَا مِنْهُ بِالْيَمِينِ
Thumma Laqaţa`nā Minhu Al-Watīna َ069-046 sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã. ثُمَّ لَقَطَعْنَا مِنْهُ الْوَتِينَ
Famā Minkum Min 'Aĥadin `Anhu Ĥājizīna َ069-047 Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi. فَمَا مِنْكُمْ مِنْ أَحَدٍ عَنْهُ حَاجِزِينَ
Wa 'Innahu Latadhkiratun Lilmuttaqīna َ069-048 Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa. وَإِنَّه ُُ لَتَذْكِرَة ٌ لِلْمُتَّقِينَ
Wa 'Innā Lana`lamu 'Anna Minkum Mukadhdhibīna َ069-049 Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa. وَإِنَّا لَنَعْلَمُ أَنَّ مِنْكُمْ مُكَذِّبِينَ
Wa 'Innahu Laĥasratun `Alá Al-Kāfirīna َ069-050 Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai. وَإِنَّه ُُ لَحَسْرَةٌ عَلَى الْكَافِرِينَ
Wa 'Innahu Laĥaqqu Al-Yaqīni َ069-051 Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni. وَإِنَّه ُُ لَحَقُّ الْيَقِينِ
Fasabbiĥ Biāsmi Rabbika Al-`Ažīmi َ069-052 Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma. فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ
Next Sūrah