35) Sūrat Fāţir

Printed format

35) سُورَة فَاطِر

Al-Ĥamdu Lillahi Fāţiri As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Jā`ili Al-Malā'ikati Rusulāan 'Ūlī 'Ajniĥatin Mathná Wa Thulātha Wa Rubā`a Yazīdu Fī Al-Khalqi Mā Yashā'u 'Inna Al-Laha `Alá Kulli Shay'in Qadīrun َ035-001 Gõdiya ta tabbata ga Allah, Mai fãra halittar sammai da ƙasã, Mai sanya malã'iku manzanni mãsu fukãfukai, bibbiyu, da uku-uku da hurhuɗu. Yanã ƙãrãwar abin da Ya ke so a cikin halittar. Lalle Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme. الْحَمْدُ لِلَّهِ فَاطِرِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ جَاعِلِ الْمَلاَئِكَةِ رُسُلاً أُولِي أَجْنِحَة ٍ مَثْنَى وَثُلاَثَ وَرُبَاعَ يَزِيدُ فِي الْخَلْقِ مَا يَشَاءُ إِنَّ اللَّهَ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِير ٌ
Mā Yaftaĥi Al-Lahu Lilnnāsi Min Raĥmatin Falā Mumsika Lahā  ۖ  Wa Mā Yumsik Falā Mursila Lahu Min Ba`dihi  ۚ  Wa Huwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ035-002 Abin da Allah Ya buɗa wa mutãne daga rahama, to, bãbu mai riƙewa a gare shi, kuma abin da Ya riƙe, to, bãbu mai saki a gare shi, waninSa, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. مَا يَفْتَحِ اللَّهُ لِلنَّاسِ مِنْ رَحْمَة ٍ فَلاَ مُمْسِكَ لَهَا  ۖ  وَمَا يُمْسِكْ فَلاَ مُرْسِلَ لَه ُُ مِنْ بَعْدِه ِِ  ۚ  وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Yā 'Ayyuhā An-Nāsu Adhkurū Ni`mata Al-Lahi `Alaykum  ۚ  Hal Min Khāliqin Ghayru Al-Lahi Yarzuqukum Mina As-Samā'i Wa Al-'Arđi  ۚ  Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۖ  Fa'anná Tu'ufakūna َ035-003 Yã kũ mutãne! Ku tuna ni'imar Allah a kanku. Shin, akwai wani mai halitta wanin Allah da zai azurta ku daga sama da, ƙasã? Bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku? يَاأَيُّهَا النَّاسُ اذْكُرُوا نِعْمَةَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ هَلْ  ۚ  مِنْ خَالِقٍ غَيْرُ اللَّهِ يَرْزُقُكُمْ مِنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ لاَ  ۚ  إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ فَأَنَّى  ۖ  تُؤْفَكُونَ
Wa 'In Yukadhdhibūka Faqad Kudhdhibat Rusulun Min Qablika  ۚ  Wa 'Ilá Al-Lahi Turja`u Al-'Umūru َ035-004 Kuma idan sun ƙaryata ka, to, lalle, an ƙaryata waɗansu Manzanni a gabãninka, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura. وَإِنْ يُكَذِّبُوكَ فَقَدْ كُذِّبَتْ رُسُل ٌ مِنْ قَبْلِكَ  ۚ  وَإِلَى اللَّهِ تُرْجَعُ الأُمُورُ
Yā 'Ayyuhā An-Nāsu 'Inna Wa`da Al-Lahi Ĥaqqun  ۖ  Falā Taghurrannakumu Al-Ĥayā Atu  ۖ  Ad-Dunyā Wa Lā Yaghurrannakum Bil-Lahi Al-Gharūru َ035-005 Yã kũ mutãne! Lalle wa'adin Allah gaskiya ne, sabõda haka kada rãyuwar dũniya ta rũɗar da ku, kuma kada marũɗi ya rũɗe ku game da Allah. يَاأَيُّهَا النَّاسُ إِنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقّ ٌ فَلاَ  ۖ  تَغُرَّنَّكُمُ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا وَلاَ  ۖ  يَغُرَّنَّكُمْ بِاللَّهِ الْغَرُورُ
'Inna Ash-Shayţāna Lakum `Adūwun Fa Attakhidhūhu `Adūwāan  ۚ  'Innamā Yad`ū Ĥizbahu Liyakūnū Min 'Aşĥābi As-Sa`īri َ035-006 Lalle Shaiɗan maƙiyi ne a gare ku, sai ku riƙe shi maƙiyi. Yanã kiran ƙungiyarsa kawai ne, dõmin su kasance 'yan sa'ir. إِنَّ الشَّيْطَانَ لَكُمْ عَدُوّ ٌ فَاتَّخِذُوه ُُ عَدُوّا ً  ۚ  إِنَّمَا يَدْعُو حِزْبَه ُُ لِيَكُونُوا مِنْ أَصْحَابِ السَّعِيرِ
Al-Ladhīna Kafarū Lahum `Adhābun Shadīdun Wa  ۖ  Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Lahum Maghfiratun Wa 'Ajrun Kabīrun َ035-007 Waɗanda suka kãfirta suna da azãba mai tsanani kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wata gãfara da sakamako mai girma. الَّذِينَ كَفَرُوا لَهُمْ عَذَاب ٌ شَدِيد ٌ  ۖ  وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ مَغْفِرَة ٌ وَأَجْر ٌ كَبِير ٌ
'Afaman Zuyyina Lahu Sū'u `Amalihi Fara'āhu Ĥasanāan  ۖ  Fa'inna Al-Laha Yuđillu Man Yashā'u Wa Yahdī Man Yashā'u  ۖ  Falā Tadh/hab Nafsuka `Alayhim Ĥasarātin  ۚ  'Inna Al-Laha `Alīmun Bimā Yaşna`ūna َ035-008 Shin to, wanda aka ƙawãta masa aikinsa, har ya gan shi mai kyau (yanã daidai da waninsa)? Sabõda haka, lalle, Allah Yanã ɓatar da wanda Yake so, kuma Yanã shiryar da wanda Yake so, sabõda haka kada ranka ya halaka a kansu dômin baƙin ciki. Lalle Allah Masani ne ga abin da suke sanã'antawa. أَفَمَنْ زُيِّنَ لَه ُُ سُوءُ عَمَلِه ِِ فَرَآهُ حَسَنا ً  ۖ  فَإِنَّ اللَّهَ يُضِلُّ مَنْ يَشَاءُ وَيَهْدِي مَنْ يَشَاءُ  ۖ  فَلاَ تَذْهَبْ نَفْسُكَ عَلَيْهِمْ حَسَرَات ٍ  ۚ  إِنَّ اللَّهَ عَلِيم ٌ بِمَا يَصْنَعُونَ
Wa Allāhu Al-Ladhī 'Arsala Ar-Riyāĥa Fatuthīru Saĥābāan Fasuqnāhu 'Ilá Baladin Mayyitin Fa'aĥyaynā Bihi Al-'Arđa Ba`da  ۚ  Mawtihā Kadhālika An-Nushūru َ035-009 Kuma Allah ne Ya aika da iskõki har su mõtsar da girgije, sa'an nan Mu kõra shi zuwa ga gari matacce, sa'an nan Mu rãyar da ƙasã game da shi a bayan mutuwarta. Kamar wancan ne Tãshin ¡iyãma yake. وَاللَّهُ الَّذِي أَرْسَلَ الرِّيَاحَ فَتُثِيرُ سَحَابا ً فَسُقْنَاهُ~ُ إِلَى بَلَد ٍ مَيِّت ٍ فَأَحْيَيْنَا بِهِ الأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا  ۚ  كَذَلِكَ النُّشُورُ
Man Kāna Yurīdu Al-`Izzata Falillāhi Al-`Izzatu Jamī`āan  ۚ  'Ilayhi Yaş`adu Al-Kalimu Aţ-Ţayyibu Wa Al-`Amalu Aş-Şāliĥu Yarfa`uhu Wa  ۚ  Al-Ladhīna Yamkurūna As-Sayyi'āti Lahum `Adhābun Shadīdun  ۖ  Wa Makru 'Ūlā'ika Huwa Yabūru َ035-010 Wanda ya kasance yanã nẽman wata izza, to, Allah ne da izza gabã ɗaya. zuwa gare Shi magana mai dãɗi ke hawa, kuma aiki na ƙwarai Yanã ɗaukar ta Kuma waɗanda ke yin mãkircin mũnanan ayyuka, sunã da wata azãba mai tsanani, kuma mãkircin waɗannan yanã yin tasgaro. مَنْ كَانَ يُرِيدُ الْعِزَّةَ فَلِلَّهِ الْعِزَّةُ جَمِيعا ً  ۚ  إِلَيْهِ يَصْعَدُ الْكَلِمُ الطَّيِّبُ وَالْعَمَلُ الصَّالِحُ يَرْفَعُه ُُ  ۚ  وَالَّذِينَ يَمْكُرُونَ السَّيِّئَاتِ لَهُمْ عَذَاب ٌ شَدِيد ٌ  ۖ  وَمَكْرُ أُوْلَائِكَ هُوَ يَبُورُ
Wa Allāhu Khalaqakum Min Turābin Thumma Min Nuţfatin Thumma Ja`alakum  ۚ  'Azwājāan Wa Mā Taĥmilu Min 'Unthá Wa Lā Tađa`u 'Illā  ۚ  Bi`ilmihi Wa Mā Yu`ammaru Min Mu`ammarin Wa Lā Yunqaşu Min `Umurihi 'Illā Fī  ۚ  Kitābin 'Inna Dhālika `Alá Al-Lahi Yasīrun َ035-011 Kuma Allah ne Ya halitta ku daga turɓãya, sa'an nan daga ɗigon maniyyi, sa'an nan Ya sanya ku surkin maza da mãtã. Kuma wata mace bã ta yin ciki, kuma bã ta haihuwa, fãce da saninSa, kuma bã zã a rãyar da wanda ake rãyarwa ba, kuma bã zã a rage tsawon ransa ba fãce yanã a cikin Littãfi. Lalle, wancan mai sauki ne ga Allah. وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ مِنْ تُرَاب ٍ ثُمَّ مِنْ نُطْفَة ٍ ثُمَّ جَعَلَكُمْ أَزْوَاجا ً  ۚ  وَمَا تَحْمِلُ مِنْ أُنْثَى وَلاَ تَضَعُ إِلاَّ بِعِلْمِه ِِ  ۚ  وَمَا يُعَمَّرُ مِنْ مُعَمَّر ٍ وَلاَ يُنْقَصُ مِنْ عُمُرِهِ~ِ إِلاَّ فِي كِتَاب ٍ  ۚ  إِنَّ ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِير ٌ
Wa Mā Yastawī Al-Baĥrāni Hādhā `Adhbun Furātun Sā'ighun Sharābuhu Wa Hadhā Milĥun 'Ujājun  ۖ  Wa Min Kullin Ta'kulūna Laĥmāan Ţarīyāan Wa Tastakhrijūna Ĥilyatan Talbasūnahā  ۖ  Wa Tará Al-Fulka Fīhi Mawākhira Litabtaghū Min Fađlihi Wa La`allakum Tashkurūna َ035-012 Kuma kõguna biyu ba su daidaita: Wannan mai ruwan dãɗi, mai zãƙi, mai sauƙin haɗiya kuma wannan mai ruwan gishiri mai zartsi, kuma daga kõwane, kunã cin wani nama sãbo, kuma kunã fitar da kawa wadda kuke tufantarta, kuma kanã ganin jirãge a cikinsa sunã mãsu gudãna, dõmin ku nẽmo daga falalarSa, kuma ɗammãninku zã ku dinga gõdẽwa. وَمَا يَسْتَوِي الْبَحْرَانِ هَذَا عَذْب ٌ فُرَات ٌ سَائِغ ٌ شَرَابُه ُُ وَهَذَا مِلْحٌ أُجَاج ٌ  ۖ  وَمِنْ كُلّ ٍ تَأْكُلُونَ لَحْما ً طَرِيّا ً وَتَسْتَخْرِجُونَ حِلْيَة ً تَلْبَسُونَهَا  ۖ  وَتَرَى الْفُلْكَ فِيه ِِ مَوَاخِرَ لِتَبْتَغُوا مِنْ فَضْلِه ِِ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Yūliju Al-Layla Fī An-Nahāri Wa Yūliju An-Nahāra Fī Al-Layli Wa Sakhkhara Ash-Shamsa Wa Al-Qamara Kullun Yajrī Li'jalin Musammáan  ۚ  Dhalikumu Al-Lahu Rabbukum Lahu Al-Mulku Wa  ۚ  Al-Ladhīna Tad`ūna Min Dūnihi Mā Yamlikūna Min Qiţmīrin َ035-013 Yanã shigar da dare a cikin rãna, kuma Yanã shigar da rãna a cikin dare. Kuma Ya hõre rãnã da watã kõwannensu yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce Wannan Shĩ ne Allah, Ubangijinku, gare Shi mulki yake, kuma waɗanda kuke kira waninSa bã su mallakar kõ fãtar gurtsun dabĩno. يُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَيُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ وَسَخَّرَ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ كُلّ ٌ يَجْرِي لِأجَل ٍ مُسَمّى ً  ۚ  ذَلِكُمُ اللَّهُ رَبُّكُمْ لَهُ الْمُلْكُ  ۚ  وَالَّذِينَ تَدْعُونَ مِنْ دُونِه ِِ مَا يَمْلِكُونَ مِنْ قِطْمِير ٍ
'In Tad`ūhum Lā Yasma`ū Du`ā'akum Wa Law Sami`ū Mā Astajābū Lakum  ۖ  Wa Yawma Al-Qiyāmati Yakfurūna Bishirkikum  ۚ  Wa Lā Yunabbi'uka Mithlu Khabīrin َ035-014 Idan kun kira su, bã zã su ji kiranku ba, kuma kõ sun jiya, bã zã su karɓa muku ba, kuma a Rãnar ¡iyãma zã su kãfirce wa shirkinku, kuma bãbu mai bã ka lãbãri, kamar wanda ya sani. إِنْ تَدْعُوهُمْ لاَ يَسْمَعُوا دُعَاءَكُمْ وَلَوْ سَمِعُوا مَا اسْتَجَابُوا لَكُمْ  ۖ  وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ يَكْفُرُونَ بِشِرْكِكُمْ  ۚ  وَلاَ يُنَبِّئُكَ مِثْلُ خَبِير ٍ
Yā 'Ayyuhā An-Nāsu 'Antumu Al-Fuqarā'u 'Ilá Al-Lahi Wa  ۖ  Allāhu Huwa Al-Ghanīyu Al-Ĥamīdu َ035-015 Yã kũ mutãne! Kũ ne mãsu bukãta zuwa ga Allah, kuma Allah, Shĩ ne Mawadãci, Gõdadde. يَاأَيُّهَا النَّاسُ أَنْتُمُ الْفُقَرَاءُ إِلَى اللَّهِ وَاللَّهُ  ۖ  هُوَ الْغَنِيُّ الْحَمِيدُ
'In Yasha' Yudh/hibkum Wa Ya'ti Bikhalqin Jadīdin َ035-016 Idan Ya so, zai tafi da ku, kuma Ya zo da wata halitta sãbuwa. إِنْ يَشَأْ يُذْهِبْكُمْ وَيَأْتِ بِخَلْق ٍ جَدِيد ٍ
Wa Mā Dhālika `Alá Al-Lahi Bi`azīzin َ035-017 Kuma wancan bai zama mabuwãyi ba ga Allah. وَمَا ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ بِعَزِيز ٍ
Wa Lā Taziru Wāziratun Wizra 'Ukhrá  ۚ  Wa 'In Tad`u Muthqalatun 'Ilá Ĥimlihā Lā Yuĥmal Minhu Shay'un Wa Law Kāna Dhā Qurbá  ۗ  'Innamā Tundhiru Al-Ladhīna Yakhshawna Rabbahum Bil-Ghaybi Wa 'Aqāmū Aş-Şalāata  ۚ  Wa Man Tazakká Fa'innamā Yatazakká Linafsihi  ۚ  Wa 'Ilá Al-Lahi Al-Maşīru َ035-018 Kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bai ɗaukar nauyin wani rai. Kuma idan ran da aka nauyaya wa kãya ya yi kira (ga wani mataimaki) zuwa ga kãyansa, bã zã a dauki kõme ba daga gare shi, kuma kõ dã (wanda ake kiran) yã kasance makusancin zumunta ne. Kanã gargaɗi kawai ne ga waɗanda ke tsoron Ubangijinsu a fake, kuma suka tsayar da salla. Kuma wanda ya tsarkake, to, yanã tsarkaka ne dõmin kansa. Kuma zuwa ga Allah kawai makõma take. وَلاَ تَزِرُ وَازِرَة ٌ وِزْرَ أُخْرَى  ۚ  وَإِنْ تَدْعُ مُثْقَلَة ٌ إِلَى حِمْلِهَا لاَ يُحْمَلْ مِنْهُ شَيْء ٌ وَلَوْ كَانَ ذَا قُرْبَى  ۗ  إِنَّمَا تُنْذِرُ الَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُمْ بِالغَيْبِ وَأَقَامُوا الصَّلاَةَ  ۚ  وَمَنْ تَزَكَّى فَإِنَّمَا يَتَزَكَّى لِنَفْسِه ِِ  ۚ  وَإِلَى اللَّهِ الْمَصِيرُ
Wa Mā Yastawī Al-'A`má Wa Al-Başīru َ035-019 Kuma makãho bã ya daidaita da mai gani. وَمَا يَسْتَوِي الأَعْمَى وَالْبَصِيرُ
Wa Lā Až-Žulumātu Wa Lā An-Nūr َ035-020 Kuma duffai bã su daidaita, kuma haske bã ya daidaita. وَلاَ الظُّلُمَاتُ وَلاَ النُّور
Wa Lā Až-Žillu Wa Lā Al-Ĥarūru َ035-021 Kuma inuwa bã ta daidaita, kuma iskar zãfi bã ta daidaita. وَلاَ الظِّلُّ وَلاَ الْحَرُورُ
Wa Mā Yastawī Al-'Aĥyā'u Wa Lā Al-'Amwātu  ۚ  'Inna Al-Laha Yusmi`u Man Yashā'u  ۖ  Wa Mā 'Anta Bimusmi`in Man Al-Qubūri َ035-022 Kuma rãyayyu bã su daidaita kuma matattu ba su daidaita. Lalle Allah Yanã jiyar da wa'azi ga wanda Ya so, kuma ba ka jiyar da waɗanda suke a cikin kaburbura. وَمَا يَسْتَوِي الأَحْيَاءُ وَلاَ الأَمْوَاتُ  ۚ  إِنَّ اللَّهَ يُسْمِعُ مَنْ يَشَاءُ  ۖ  وَمَا أَنْتَ بِمُسْمِع ٍ مَنْ فِي الْقُبُورِ
'In 'Anta 'Illā Nadhīrun َ035-023 Ba ka zama ba fãce mai gargaɗi kawai. إِنْ أَنْتَ إِلاَّ نَذِير ٌ
'Innā 'Arsalnāka Bil-Ĥaqqi Bashīrāan Wa Nadhīrāan  ۚ  Wa 'In Min 'Ummatin 'Illā Khalā Fīhā Nadhīrun َ035-024 Lalle Mũ Mun aike ka da gaskiya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Kuma bãbu wata al'umma fãce wani mai gargaɗi yã shũɗe a cikinta. إِنَّا أَرْسَلْنَاكَ بِالْحَقِّ بَشِيرا ً وَنَذِيرا ً  ۚ  وَإِنْ مِنْ أُمَّة ٍ إِلاَّ خَلاَ فِيهَا نَذِير ٌ
Wa 'In Yukadhdhibūka Faqad Kadhdhaba Al-Ladhīna Min Qablihim Jā'at/hum Rusuluhum Bil-Bayyināti Wa Biz-Zuburi Wa Bil-Kitābi Al-Munīri َ035-025 Kuma idan sunã ƙaryata ka, to, haƙĩƙa, waɗanda suke a gabãninsu sun ƙaryata. Manzanninsu sun jẽ musu da hujjõji, kuma da takardu, kuma da Littafi mai haske. وَإِنْ يُكَذِّبُوكَ فَقَدْ كَذَّبَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ جَاءَتْهُمْ رُسُلُهُمْ بِالْبَيِّنَاتِ وَبِالزُّبُرِ وَبِالْكِتَابِ الْمُنِيرِ
Thumma 'Akhadhtu Al-Ladhīna Kafarū  ۖ  Fakayfa Kāna Nakīri َ035-026 Sa'an nan Na kãma waɗanda suka kãfirta. To, yãya musũNa yake? ثُمَّ أَخَذْتُ الَّذِينَ كَفَرُوا  ۖ  فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ
'Alam Tará 'Anna Al-Laha 'Anzala Mina As-Samā'i Mā'an Fa'akhrajnā Bihi Thamarātin Mukhtalifāan 'Alwānuhā  ۚ  Wa Mina Al-Jibāli Judadun Bīđun Wa Ĥumrun Mukhtalifun 'Alwānuhā Wa Gharābību Sūdun َ035-027 Ba ka gani ba, lalle Allah Ya saukar da ruwa daga sama? Sai Muka fitar, game da shi,'yã'yan itãce mãsu sãɓanin launuka kuma daga duwatsu akwai zane-zane, farfaru da jãjãye, mãsu sãɓanin launin, da mãsu launin baƙin ƙarfe, baƙãƙe. أَلَمْ تَرَى أَنَّ اللَّهَ أَنْزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاء ً فَأَخْرَجْنَا بِه ِِ ثَمَرَات ٍ مُخْتَلِفاً أَلْوَانُهَا  ۚ  وَمِنَ الْجِبَالِ جُدَد ٌ بِيض ٌ وَحُمْر ٌ مُخْتَلِفٌ أَلْوَانُهَا وَغَرَابِيبُ سُود ٌ
Wa Mina An-Nāsi Wa Ad-Dawābbi Wa Al-'An`ām Mukhtalifun 'Alwānuhu Kadhālika  ۗ  'Innamā Yakhshá Al-Laha Min `Ibādihi Al-`Ulamā'u  ۗ  'Inna Al-Laha `Azīzun Ghafūrun َ035-028 Kuma daga mutãne da dabbõbi da bisãshen gida, mãsu sãɓãnin launinsu kamar wancan. Malamai kawai ke tsõron Allah daga cikin bãyinSa. Lalle, Allah, Mabuwãyi ne, Mai gãfara. وَمِنَ النَّاسِ وَالدَّوَابِّ وَالأَنعَام مُخْتَلِفٌ أَلْوَانُه ُُ كَذَلِكَ  ۗ  إِنَّمَا يَخْشَى اللَّهَ مِنْ عِبَادِهِ الْعُلَمَاءُ  ۗ  إِنَّ اللَّهَ عَزِيزٌ غَفُور ٌ
'Inna Al-Ladhīna Yatlūna Kitāba Al-Lahi Wa 'Aqāmū Aş-Şalāata Wa 'Anfaqū Mimmā Razaqnāhum Sirrāan Wa `Alāniyatan Yarjūna Tijāratan Lan Tabūra َ035-029 Lalle waɗanda ke karãtun Littãfin Allah kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, sunã fãtan (sãmun) wani fatauci ne wanda bã ya yin tasgaro. إِنَّ الَّذِينَ يَتْلُونَ كِتَابَ اللَّهِ وَأَقَامُوا الصَّلاَةَ وَأَنْفَقُوا مِمَّا رَزَقْنَاهُمْ سِرّا ً وَعَلاَنِيَة ً يَرْجُونَ تِجَارَة ً لَنْ تَبُورَ
Liyuwaffiyahum 'Ujūrahum Wa Yazīdahum Min Fađlihi  ۚ  'Innahu Ghafūrun Shakūrun َ035-030 Dõmin (Allah) zai cika musu sakamakonsu, kuma Ya ƙarã musu daga falalarSa. Lalle Shi Mai gãfara ne, Mai gõdiya. لِيُوَفِّيَهُمْ أُجُورَهُمْ وَيَزِيدَهُمْ مِنْ فَضْلِهِ~ِ  ۚ  إِنَّه ُُ غَفُور ٌ شَكُور ٌ
Wa Al-Ladhī 'Awĥaynā 'Ilayka Mina Al-Kitābi Huwa Al-Ĥaqqu Muşaddiqāan Limā Bayna  ۗ  Yadayhi 'Inna Al-Laha Bi`ibādihi Lakhabīrun Başīrun َ035-031 Kuma abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, daga Littãfi, وَالَّذِي أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ مِنَ الْكِتَابِ هُوَ الْحَقُّ مُصَدِّقا ً لِمَا بَيْنَ يَدَيْهِ  ۗ  إِنَّ اللَّهَ بِعِبَادِه ِِ لَخَبِير ٌ بَصِير ٌ
Thumma 'Awrath Al-Kitāba Al-Ladhīna Aşţafaynā Min `Ibādinā  ۖ  Faminhum Žālimun Linafsihi Wa Minhum Muqtaşidun Wa Minhum Sābiqun Bil-Khayrāti Bi'idhni Al-Lahi  ۚ  Dhālika Huwa Al-Fađlu Al-Kabīru َ035-032 Sa'an nan Mun gãdar da Littãfin, ga waɗanda Muka zãɓa daga bãyinMu, sa'an nan daga cikinsu, akwai mai zãlunci ga kansa, kuma daga cikinsu akwai mai tsakaitãwa, kuma daga cikinsu akwai mai tsẽrẽwa da ayyukan alhẽri da iznin Allah. Waccan ita ce falalar (Allah) mai girma. ثُمَّ أَوْرَثْنَا الْكِتَابَ الَّذِينَ اصْطَفَيْنَا مِنْ عِبَادِنَا  ۖ  فَمِنْهُمْ ظَالِم ٌ لِنَفْسِه ِِ وَمِنْهُمْ مُقْتَصِد ٌ وَمِنْهُمْ سَابِق ٌ بِالْخَيْرَاتِ بِإِذْنِ اللَّهِ  ۚ  ذَلِكَ هُوَ الْفَضْلُ الْكَبِيرُ
Jannātu `Adnin Yadkhulūnahā Yuĥallawna Fīhā Min 'Asāwira Min Dhahabin Wa Lu'ulu'uāan  ۖ  Wa Libāsuhum Fīhā Ĥarīrun َ035-033 Gidãjen Aljannar zamã sunã shigar su. Anã ƙawãce su a cikinsu, da ƙawã ta mundãye daga zĩnãriya da lu'ulu'u, kuma tufãfinsu, a cikinsu alharĩni ne. جَنَّاتُ عَدْن ٍ يَدْخُلُونَهَا يُحَلَّوْنَ فِيهَا مِنْ أَسَاوِرَ مِنْ ذَهَب ٍ وَلُؤْلُؤا ً  ۖ  وَلِبَاسُهُمْ فِيهَا حَرِير ٌ
Wa Qālū Al-Ĥamdu Lillahi Al-Ladhī 'Adh/haba `Annā Al-Ĥazana  ۖ  'Inna Rabbanā Laghafūrun Shakūrun َ035-034 Kuma suka ce: "Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya tafiyar da baƙin ciki daga gare mu. Lalle Ubangijinmu, haƙĩƙa Mai gafarane, Mai godiya." وَقَالُوا الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَذْهَبَ عَنَّا الْحَزَنَ  ۖ  إِنَّ رَبَّنَا لَغَفُور ٌ شَكُور ٌ
Al-Ladhī 'Aĥallanā Dāra Al-Muqāmati Min Fađlihi Lā Yamassunā Fīhā Naşabun Wa Lā Yamassunā Fīhā Lughūbun َ035-035 "Wanda Ya saukar da mu a gidan zamã, daga falalarSa, wata wahala bã ta shãfar mu a cikinsa, kuma wata kãsãwa bã ta shãfar mu a cikinsa." الَّذِي أَحَلَّنَا دَارَ الْمُقَامَةِ مِنْ فَضْلِهِ لاَ يَمَسُّنَا فِيهَا نَصَب ٌ وَلاَ يَمَسُّنَا فِيهَا لُغُوب ٌ
Wa Al-Ladhīna Kafarū Lahum Nāru Jahannama Lā Yuqđá `Alayhim Fayamūtū Wa Lā Yukhaffafu `Anhum Min  ۚ  `Adhābihā Kadhālika Najzī Kulla Kafūrin َ035-036 Kuma waɗanda suka kãfirta sunã da wutar Jahannama, bã a yin hukunci a kansu balle su mutu kuma bã a sauƙaƙa musu daga azãbarta. Kamar haka Muke sãka wa kõwane mai yawan kãfirci. وَالَّذِينَ كَفَرُوا لَهُمْ نَارُ جَهَنَّمَ لاَ يُقْضَى عَلَيْهِمْ فَيَمُوتُوا وَلاَ يُخَفَّفُ عَنْهُمْ مِنْ عَذَابِهَا  ۚ  كَذَلِكَ نَجْزِي كُلَّ كَفُور ٍ
Wa Hum Yaşţarikhūna Fīhā Rabbanā 'Akhrijnā Na`mal Şāliĥāan Ghayra Al-Ladhī Kunnā Na`malu  ۚ  'Awalam Nu`ammirkum Mā Yatadhakkaru Fīhi Man Tadhakkara Wa Jā'akumu An-Nadhīru  ۖ  Fadhūqū Famā Lilžžālimīna Min Naşīr َ035-037 Kuma sũ, sunã hargõwar nẽman ãgaji a cikinta. (Sunã cẽwa) "Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu, mu aikata aiki mai kyau, wanin wanda muka kasance munã aikatãwa." Ashe, kuma, ba Mu rãyar da ku ba, abin da mai tunãni zai iya yin tunãni a ciki, kuma mai gargaɗi yã jẽ muku? To, ku ɗanɗana, sabõda haka bãbu wani mataimaki, ga azzãlumai. وَهُمْ يَصْطَرِخُونَ فِيهَا رَبَّنَا أَخْرِجْنَا نَعْمَلْ صَالِحاً غَيْرَ الَّذِي كُنَّا نَعْمَلُ  ۚ  أَوَلَمْ نُعَمِّرْكُمْ مَا يَتَذَكَّرُ فِيه ِِ مَنْ تَذَكَّرَ وَجَاءَكُمُ النَّذِيرُ  ۖ  فَذُوقُوا فَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ نَصِير
'Inna Al-Laha `Ālimu Ghaybi As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۚ  'Innahu `Alīmun Bidhāti Aş-Şudūri َ035-038 Lalle Allah ne Masanin gaibin sammai da ƙasã. Lalle Shĩ ne Masani ga abin da yake ainihin zukata. إِنَّ اللَّهَ عَالِمُ غَيْبِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۚ  إِنَّه ُُ عَلِيم ٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
Huwa Al-Ladhī Ja`alakum Khalā'ifa Fī Al-'Arđi  ۚ  Faman Kafara Fa`alayhi Kufruhu  ۖ  Wa Lā Yazīdu Al-Kāfirīna Kufruhum `Inda Rabbihim 'Illā Maqtāan  ۖ  Wa Lā Yazīdu Al-Kāfirīna Kufruhum 'Illā Khasārāan َ035-039 Shĩ ne Wanda Ya sanya ku mãsu maye wa junã, a cikin ƙasã. To, wanda ya kãfirta, to, kãfircinsa yanã a kansa. Kuma kãfircin kãfirai bã ya kãra musu kõme fãce baƙin jini, kuma kãfircin kãfirai bã ya kãra musu kõme face hasãra. هُوَ الَّذِي جَعَلَكُمْ خَلاَئِفَ فِي الأَرْضِ  ۚ  فَمَنْ كَفَرَ فَعَلَيْهِ كُفْرُه ُُ  ۖ  وَلاَ يَزِيدُ الْكَافِرِينَ كُفْرُهُمْ عِنْدَ رَبِّهِمْ إِلاَّ مَقْتا ً  ۖ  وَلاَ يَزِيدُ الْكَافِرِينَ كُفْرُهُمْ إِلاَّ خَسَارا ً
Qul 'Ara'aytum Shurakā'akumu Al-Ladhīna Tad`ūna Min Dūni Al-Lahi 'Arūnī Mādhā Khalaqū Mina Al-'Arđi 'Am Lahum Shirkun As-Samāwāti 'Am 'Ātaynāhum Kitābāan Fahum `Alá Bayyinatin Minhu  ۚ  Bal 'In Ya`idu Až-Žālimūna Ba`đuhum Ba`đāan 'Illā Ghurūrāan َ035-040 Ka ce: "Shin, kun ga abũbuwan shirkinku, waɗanda kuke kira, wasun Allah? Ku nũna mini, mẽne ne suka halitta daga ƙasã? Kõ sunã da tãrayya ne a cikin sammai? Kõ kuma Mun bã su wani littãfi ne sabõda haka sunã a kan wata hujja ce daga gare shi? Ã'a, azzãlumai bã su yin wani wa'adi, sãshensu zuwa ga sãshe, fãce rũɗi." قُلْ أَرَأَيْتُمْ شُرَكَاءَكُمُ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُوا مِنَ الأَرْضِ أَمْ لَهُمْ شِرْك ٌ فِي السَّمَاوَاتِ أَمْ آتَيْنَاهُمْ كِتَابا ً فَهُمْ عَلَى بَيِّنَة ٍ مِنْهُ  ۚ  بَلْ إِنْ يَعِدُ الظَّالِمُونَ بَعْضُهُمْ بَعْضا ً إِلاَّ غُرُورا ً
'Inna Al-Laha Yumsiku As-Samāwāti Wa Al-'Arđa 'An Tazūlā  ۚ  Wa La'in Zālatā 'In 'Amsakahumā Min 'Aĥadin Min Ba`dihi  ۚ  'Innahu Kāna Ĥalīmāan Ghafūrāan َ035-041 Lalle Allah Yanã riƙe sammai da ƙasã dõmin kada su gushe. Kuma haƙĩƙa, idan sun gushe, bãbu wani baicinSa da zai riƙe su. Lalle Shi Yã kasance Mai haƙuri, Mai gãfara. إِنَّ اللَّهَ يُمْسِكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ أَنْ تَزُولاَ  ۚ  وَلَئِنْ زَالَتَا إِنْ أَمْسَكَهُمَا مِنْ أَحَد ٍ مِنْ بَعْدِهِ~ِ  ۚ  إِنَّه ُُ كَانَ حَلِيماً غَفُورا ً
Wa 'Aqsamū Bil-Lahi Jahda 'Aymānihim La'in Jā'ahum Nadhīrun Layakūnunna 'Ahdá Min 'Iĥdá Al-'Umami  ۖ  Falammā Jā'ahum Nadhīrun Mā Zādahum 'Illā Nufūrāan َ035-042 Kuma suka yi rantsuwa da Allah, mafi nauyin rantsuwarsu, "Lalle, idan wani mai gargaɗi ya zo musu tabbas zã su kasance mafi shiryuwa, daga ɗayan al'ummõmi." To, a lõkacin da mai gargaɗi ya jẽ musu, bai ƙarã su da kõme ba fãce gudu. وَأَقْسَمُوا بِاللَّهِ جَهْدَ أَيْمَانِهِمْ لَئِنْ جَاءَهُمْ نَذِير ٌ لَيَكُونُنَّ أَهْدَى مِنْ إِحْدَى الأُمَمِ  ۖ  فَلَمَّا جَاءَهُمْ نَذِير ٌ مَا زَادَهُمْ إِلاَّ نُفُورا ً
Astikbārāan Al-'Arđi Wa Makra As-Sayyi'i  ۚ  Wa Lā Yaĥīqu Al-Makru As-Sayyi'u 'Illā Bi'ahlihi  ۚ  Fahal Yanžurūna 'Illā Sunnata Al-'Awwalīna  ۚ  Falan Tajida Lisunnati Al-Lahi Tabdīlāan  ۖ  Wa Lan Tajida Lisunnati Al-Lahi Taĥwīlāan َ035-043 Dõmin nũna girman kai a cikin ƙasã da mãkircin cũta. Kuma mãkirci na cũta bã ya fãdãwa fãce a kan mutãnensa. To shin sunã jiran (wani abu ne) fãce dai hanyar (kãfiran) farko. To, bã zã ka sãmi musanya ba ga hanyar Allah. Kuma bã zã ka sãmi jũyarwa ba ga hanyar Allah. اسْتِكْبَارا ً فِي الأَرْضِ وَمَكْرَ السَّيِّئِ  ۚ  وَلاَ يَحِيقُ الْمَكْرُ السَّيِّئُ إِلاَّ بِأَهْلِه ِِ  ۚ  فَهَلْ يَنْظُرُونَ إِلاَّ سُنَّةَ الأَوَّلِينَ  ۚ  فَلَنْ تَجِدَ لِسُنَّةِ اللَّهِ تَبْدِيلا ً  ۖ  وَلَنْ تَجِدَ لِسُنَّةِ اللَّهِ تَحْوِيلا ً
'Awalam Yasīrū Fī Al-'Arđi Fayanžurū Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Ladhīna Min Qablihim Wa Kānū 'Ashadda Minhum Qūwatan  ۚ  Wa Mā Kāna Al-Lahu Liyu`jizahu Min Shay'in As-Samāwāti Wa Lā Fī Al-'Arđi  ۚ  'Innahu Kāna `Alīmāan Qadīrāan َ035-044 Ashe, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã, dõmin su dũba yadda ãƙibar waɗannan da suke a gabãninsu ta kasance? Alhãli kuwa sun kasance mafĩfĩta ƙarfi daga gare su? Kuma Allah bai kasance wani abu nã iya rinjãyarSa ba, a cikin sammai, kuma haka a cikin kaƙã. Lalle Shi ne Ya kasance Masani, Mai ĩkon yi. أَوَلَمْ يَسِيرُوا فِي الأَرْضِ فَيَنْظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ وَكَانُوا أَشَدَّ مِنْهُمْ قُوَّة ً  ۚ  وَمَا كَانَ اللَّهُ لِيُعْجِزَه ُُ مِنْ شَيْء ٍ فِي السَّمَاوَاتِ وَلاَ فِي الأَرْضِ  ۚ  إِنَّه ُُ كَانَ عَلِيما ً قَدِيرا ً
Wa Law Yu'uākhidhu Al-Lahu An-Nāsa Bimā Kasabū Mā Taraka `Alá Žahrihā Min Dābbatin Wa Lakin Yu'uakhkhiruhum 'Ilá 'Ajalin Musammáan  ۖ  Fa'idhā Jā'a 'Ajaluhum Fa'inna Al-Laha Kāna Bi`ibādihi Başīrāan َ035-045 Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne sabõda abin da suka aikata, dã bai bar wata dabba ba a kanta (kasã). Amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajalin da aka ambatã. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, to, lalle Allah yã kasance Mai gani ga bãyinSa. وَلَوْ يُؤَاخِذُ اللَّهُ النَّاسَ بِمَا كَسَبُوا مَا تَرَكَ عَلَى ظَهْرِهَا مِنْ دَابَّة ٍ وَلَكِنْ يُؤَخِّرُهُمْ إِلَى أَجَل ٍ مُسَمّى ً  ۖ  فَإِذَا جَاءَ أَجَلُهُمْ فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ بِعِبَادِه ِِ بَصِيرا ً
Next Sūrah