36) Sūrat Yā -Sīn

Printed format

36) سُورَة يَا-سِين

Yā -Sīn َ036-001 Y. S̃. يَا-سِين
Wa Al-Qur'āni Al-Ĥakīmi َ036-002 Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni Mai hikima. وَالْقُرْآنِ الْحَكِيمِ
'Innaka Lamina Al-Mursalīna َ036-003 Lalle kai, haƙĩƙa kanã cikinManzanni. إِنَّكَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَ
`Alá Şirāţin Mustaqīmin َ036-004 A kan hanya madaidaiciya. عَلَى صِرَاط ٍ مُسْتَقِيم ٍ
Tanzīla Al-`Azīzi Ar-Raĥīmi َ036-005 (Allah Ya saukar da Al-kur'ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai. تَنزِيلَ الْعَزِيزِ الرَّحِيمِ
Litundhira Qawmāan Mā 'Undhira 'Ābā'uuhum Fahum Ghāfilūna َ036-006 Dõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda haka sũmasu rafkana ne. لِتُنذِرَ قَوْما ً مَا أُنذِرَ آبَاؤُهُمْ فَهُمْ غَافِلُونَ
Laqad Ĥaqqa Al-Qawlu `Alá 'Aktharihim Fahum Lā Yu'uminūna َ036-007 Lalle, haƙĩƙa, kalma tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni ba. لَقَدْ حَقَّ الْقَوْلُ عَلَى أَكْثَرِهِمْ فَهُمْ لاَ يُؤْمِنُونَ
'Innā Ja`alnā Fī 'A`nāqihim 'Aghlālāan Fahiya 'Ilá Al-'Adhqāni Fahum Muqmaĥūna َ036-008 Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne. إِنَّا جَعَلْنَا فِي أَعْنَاقِهِمْ أَغْلاَلا ً فَهِيَ إِلَى الأَذْقَانِ فَهُمْ مُقْمَحُونَ
Wa Ja`alnā Min Bayni 'Aydīhim Saddāan Wa Min Khalfihim Saddāan Fa'aghshaynāhum Fahum Lā Yubşirūna َ036-009 Kuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani. وَجَعَلْنَا مِنْ بَيْنِ أَيْدِيهِمْ سَدّا ً وَمِنْ خَلْفِهِمْ سَدّا ً فَأَغْشَيْنَاهُمْ فَهُمْ لاَ يُبْصِرُونَ
Wa Sawā'un `Alayhim 'A'andhartahum 'Am Lam Tundhirhum Lā Yu'uminūna َ036-010 Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba. وَسَوَاءٌ عَلَيْهِمْ أَأَنذَرْتَهُمْ أَمْ لَمْ تُنذِرْهُمْ لاَ يُؤْمِنُونَ
'Innamā Tundhiru Mani Attaba`a Adh-Dhikra Wa Khashiya Ar-Raĥmana Bil-Ghaybi  ۖ  Fabashshirhu Bimaghfiratin Wa 'Ajrin Karīmin َ036-011 Kanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci. إِنَّمَا تُنذِرُ مَنِ اتَّبَعَ الذِّكْرَ وَخَشِيَ الرَّحْمَنَ بِالْغَيْبِ  ۖ  فَبَشِّرْهُ بِمَغْفِرَة ٍ وَأَجْر ٍ كَرِيم ٍ
'Innā Naĥnu Nuĥyi Al-Mawtá Wa Naktubu Mā Qaddamū Wa 'Āthārahum  ۚ  Wa Kulla Shay'in 'Ĥşaynāhu Fī 'Imāmin Mubīnin َ036-012 Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani. إِنَّا نَحْنُ نُحْيِ الْمَوْتَى وَنَكْتُبُ مَا قَدَّمُوا وَآثَارَهُمْ  ۚ  وَكُلَّ شَيْءٍ أحْصَيْنَاه ُُ فِي إِمَام ٍ مُبِين ٍ
Wa Ađrib Lahum Mathalāan 'Aşĥāba Al-Qaryati 'Idh Jā'ahā Al-Mursalūna َ036-013 Kuma ka buga musu misãli: Waɗansu ma'abũta alƙarya, a lõkacin da Manzanni suka jẽ mata. وَاضْرِبْ لَهُمْ مَثَلاً أَصْحَابَ الْقَرْيَةِ إِذْ جَاءَهَا الْمُرْسَلُونَ
'Idh 'Arsalnā 'Ilayhimu Athnayni Fakadhdhabūhumā Fa`azzaznā Bithālithin Faqālū 'Innā 'Ilaykum Mursalūna َ036-014 A lõkacin da Muka aika (Manzannin) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa'an nan Muka ƙarfafa (su) da na uku, sai suka ce: "Lalle mũ, Manzanni ne zuwa gare ku." إِذْ أَرْسَلْنَا إِلَيْهِمُ اثْنَيْنِ فَكَذَّبُوهُمَا فَعَزَّزْنَا بِثَالِث ٍ فَقَالُوا إِنَّا إِلَيْكُمْ مُرْسَلُونَ
Qālū Mā 'Antum 'Illā Basharun Mithlunā Wa Mā 'Anzala Ar-Raĥmānu Min Shay'in 'In 'Antum 'Illā Takdhibūna َ036-015 Suka ce: "Kũ ba ku zamo bafãce mutãne ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da kõme ba, ba ku zamo ba fãce ƙarya kuke yi." قَالُوا مَا أَنْتُمْ إِلاَّ بَشَر ٌ مِثْلُنَا وَمَا أَنزَلَ الرَّحْمَنُ مِنْ شَيْء ٍ إِنْ أَنْتُمْ إِلاَّ تَكْذِبُونَ
Qālū Rabbunā Ya`lamu 'Innā 'Ilaykum Lamursalūna َ036-016 Suka ce: "Ubangijinmu Yã sani, lalle mũ, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku." قَالُوا رَبُّنَا يَعْلَمُ إِنَّا إِلَيْكُمْ لَمُرْسَلُونَ
Wa Mā `Alaynā 'Illā Al-Balāghu Al-Mubīnu َ036-017 "Kuma bãbu abin da ke kanmu, fãce iyar da manzanci bayyananne." وَمَا عَلَيْنَا إِلاَّ الْبَلاَغُ الْمُبِينُ
Qālū 'Innā Taţayyarnā Bikum  ۖ  La'in Lam Tantahū Lanarjumannakum Wa Layamassannakum Minnā `Adhābun 'Alīmun َ036-018 Suka ce: "Lalle mũ munã shu'umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, zã mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku." قَالُوا إِنَّا تَطَيَّرْنَا بِكُمْ  ۖ  لَئِنْ لَمْ تَنتَهُوا لَنَرْجُمَنَّكُمْ وَلَيَمَسَّنَّكُمْ مِنَّا عَذَابٌ أَلِيم ٌ
Qālū Ţā'irukum Ma`akum  ۚ  'A'in Dhukkirtum  ۚ  Bal 'Antum Qawmun Musrifūna َ036-019 Suka ce: "Shu'umcinku, yanã tãre da ku. Ashe, dõmin an tunãtar da ku? Ã'a, kũ dai mutãne ne mãsu ƙẽtare haddi." قَالُوا طَائِرُكُمْ مَعَكُمْ  ۚ  أَئِنْ ذُكِّرْتُمْ  ۚ  بَلْ أَنْتُمْ قَوْم ٌ مُسْرِفُونَ
Wa Jā'a Min 'Aqşá Al-Madīnati Rajulun Yas`á Qāla Yā Qawmi Attabi`ū Al-Mursalīna َ036-020 Kuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yanã tafiya da gaggãwa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bi Manzannin nan. وَجَاءَ مِنْ أَقْصَى الْمَدِينَةِ رَجُل ٌ يَسْعَى قَالَ يَاقَوْمِ اتَّبِعُوا الْمُرْسَلِينَ
Attabi`ū Man Lā Yas'alukum 'Ajrāan Wa Hum Muhtadūna َ036-021 "Ku bi waɗanda bã su tambayar ku wata ijãra kuma sũ shiryayyu ne." اتَّبِعُوا مَنْ لاَ يَسْأَلُكُمْ أَجْرا ً وَهُمْ مُهْتَدُونَ
Wa Mā Liya Lā 'A`budu Al-Ladhī Faţaranī Wa 'Ilayhi Turja`ūna َ036-022 "Kuma mene ne a gare ni, bã zan bauta wa Wanda Ya ƙãga halittata ba, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku?" وَمَا لِيَ لاَ أَعْبُدُ الَّذِي فَطَرَنِي وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
'A'attakhidhu Min Dūnihi 'Ālihatan 'In Yuridni Ar-Raĥmānu Biđurrin Lā Tughni `Annī Shafā`atuhum Shay'āan Wa Lā Yunqidhūni َ036-023 "Shin, zan riƙi waninSa abũbuwan bautãwa? Idan Mai rahama Ya nufe ni da wata cũta, to cẽtonsu bã ya amfanĩna da kõme, kuma bã za su iya tsãmar da ni bã." أَأَتَّخِذُ مِنْ دُونِهِ آلِهَة ً إِنْ يُرِدْنِ الرَّحْمَنُ بِضُرّ ٍ لاَ تُغْنِ عَنِّي شَفَاعَتُهُمْ شَيْئا ً وَلاَ يُنقِذُونِ
'Innī 'Idhāan Lafī Đalālin Mubīnin َ036-024 "Lalle nĩ, a lõkacin nan, tabbas, inã a cikin ɓata bayyananna." إِنِّي إِذا ً لَفِي ضَلاَل ٍ مُبِين ٍ
'Innī 'Āmantu Birabbikum Fāsma`ūni َ036-025 "Lalle ni, nã yi ĩmãni da Ubangijinku, sabõda haka ku saurãre ni." إِنِّي آمَنْتُ بِرَبِّكُمْ فَاسْمَعُونِ
Qīla Adkhuli Al-Jannata  ۖ  Qāla Yā Layta Qawmī Ya`lamūna َ036-026 Aka ce (masa), "Ka shiga Aljanna." Ya ce, "Dã dai a ce mutãnẽna sunã iya sani." قِيلَ ادْخُلِ الْجَنَّةَ  ۖ  قَالَ يَالَيْتَ قَوْمِي يَعْلَمُونَ
Bimā Ghafara Lī Rabbī Wa Ja`alanī Mina Al-Mukramīna َ036-027 "Game da gãfarar da Ubangijjĩna ya yi mini, kuma Ya sanya ni a cikin waɗanda aka girmama." بِمَا غَفَرَ لِي رَبِّي وَجَعَلَنِي مِنَ الْمُكْرَمِينَ
Wa Mā 'Anzalnā `Alá Qawmihi Min Ba`dihi Min Jundin Mina As-Samā'i Wa Mā Kunnā Munzilīna َ036-028 Kuma ba Mu saukar da waɗansu runduna ba daga sama a kan (halaka) mutãnensa, daga bãyansa, kuma bã zã Mu kasance. Mãsu saukarwa ba. وَمَا أَنزَلْنَا عَلَى قَوْمِه ِِ مِنْ بَعْدِه ِِ مِنْ جُند ٍ مِنَ السَّمَاءِ وَمَا كُنَّا مُنزِلِينَ
'In Kānat 'Illā Şayĥatan Wāĥidatan Fa'idhā Hum Khāmidūna َ036-029 Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai gã su sõmammu. إِنْ كَانَتْ إِلاَّ صَيْحَة ً وَاحِدَة ً فَإِذَا هُمْ خَامِدُونَ
Yā Ĥasratan `Alá Al-`Ibādi  ۚ  Mā Ya'tīhim Min Rasūlin 'Illā Kānū Bihi Yastahzi'ūn َ036-030 Yã nadãma a kan bãyĩNa! Wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu yi masa izgili. يَاحَسْرَةً عَلَى الْعِبَادِ مَا  ۚ  يَأْتِيهِمْ مِنْ رَسُول ٍ إِلاَّ كَانُوا بِه ِِ يَسْتَهْزِئُون
'Alam Yaraw Kam 'Ahlaknā Qablahum Mina Al-Qurūni 'Annahum 'Ilayhim Lā Yarji`ūna َ036-031 Ba su gani ba, da yawa Muka halakar da (mutãnen) ƙarnõni a gabãninsu kuma cẽwa su bã zã su kõmo ba? أَلَمْ يَرَوْا كَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُمْ مِنَ الْقُرُونِ أَنَّهُمْ إِلَيْهِمْ لاَ يَرْجِعُونَ
Wa 'In Kullun Lammā Jamī`un Ladaynā Muĥđarūna َ036-032 Kuma lalle bãbu kõwa fãce waɗanda ake halartarwa ne a wurinMu. وَإِنْ كُلّ ٌ لَمَّا جَمِيع ٌ لَدَيْنَا مُحْضَرُونَ
Wa 'Āyatun Lahumu Al-'Arđu Al-Maytatu 'Aĥyaynāhā Wa 'Akhrajnā Minhā Ĥabbāan Faminhu Ya'kulūna َ036-033 Kuma ãyã ce a gare su: ¡asã matacciya, Mu rãyar da ita, Mu fitar da ƙwãya daga gare ta, sai gã shi daga gare ta suke ci. وَآيَة ٌ لَهُمُ الأَرْضُ الْمَيْتَةُ أَحْيَيْنَاهَا وَأَخْرَجْنَا مِنْهَا حَبّا ً فَمِنْهُ يَأْكُلُونَ
Wa Ja`alnā Fīhā Jannātin Min Nakhīlin Wa 'A`nābin Wa Fajjarnā Fīhā Mina Al-`Uyūni َ036-034 Kuma Muka sanya, a cikinta (ƙasã), waɗansu gõnaki na dabĩno da inabõbi, kuma Muka ɓuɓɓugar da ruwa daga marẽmari a cikinta. وَجَعَلْنَا فِيهَا جَنَّات ٍ مِنْ نَخِيل ٍ وَأَعْنَاب ٍ وَفَجَّرْنَا فِيهَا مِنَ الْعُيُونِ
Liya'kulū Min Thamarihi Wa Mā `Amilat/hu 'Aydīhim  ۖ  'Afalā Yashkurūna َ036-035 Dõmin su ci 'ya'yan itãcensa, alhãli kuwa hannãyensu ba su aikata shi ba. Shin, to, bã zã su gõdẽ ba? لِيَأْكُلُوا مِنْ ثَمَرِه ِِ وَمَا عَمِلَتْهُ أَيْدِيهِمْ  ۖ  أَفَلاَ يَشْكُرُونَ
Subĥāna Al-Ladhī Khalaqa Al-'Azwāja Kullahā Mimmā Tunbitu Al-'Arđu Wa Min 'Anfusihim Wa Mimmā Lā Ya`lamūna َ036-036 Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya halitta nau'uka, namiji da mace, dukansu, daga abin da ƙasã ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abin da ba su sani ba. سُبْحَانَ الَّذِي خَلَقَ الأَزْوَاجَ كُلَّهَا مِمَّا تُنْبِتُ الأَرْضُ وَمِنْ أَنفُسِهِمْ وَمِمَّا لاَ يَعْلَمُونَ
Wa 'Āyatun Lahumu Al-Laylu Naslakhu Minhu An-Nahāra Fa'idhā Hum Mužlimūna َ036-037 Kuma ãyã ce a gare su: Dare Muna feɗe rãna daga gare shi, sai gã su sunã mãsu shiga duhu. وَآيَة ٌ لَهُمُ اللَّيْلُ نَسْلَخُ مِنْهُ النَّهَارَ فَإِذَا هُمْ مُظْلِمُونَ
Wa Ash-Shamsu Tajrī Limustaqarrin  ۚ  Lahā Dhālika Taqdīru Al-`Azīzi Al-`Alīmi َ036-038 Kuma rãnã tanã gudãna zuwa ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani. وَالشَّمْسُ تَجْرِي لِمُسْتَقَرّ ٍ لَهَا  ۚ  ذَلِكَ تَقْدِيرُ الْعَزِيزِ الْعَلِيمِ
Wa Al-Qamara Qaddarnāhu Manāzila Ĥattá `Āda Kāl`urjūni Al-Qadīmi َ036-039 Kuma da watã Mun ƙaddara masa manzilõli, har ya kõma kamar tsumagiyar murlin dabĩno wadda ta tsũfa. وَالْقَمَرَ قَدَّرْنَاه ُُ مَنَازِلَ حَتَّى عَادَ كَالْعُرْجُونِ الْقَدِيمِ
Ash-Shamsu Yanbaghī Lahā 'An Tudrika Al-Qamara Wa Lā Al-Laylu Sābiqu An-Nahāri  ۚ  Wa Kullun Fī Falakin Yasbaĥūna َ036-040 Rãnã bã ya kamãta a gare ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya zama mai tsẽre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo. لاَ الشَّمْسُ يَنْبَغِي لَهَا أَنْ تُدْرِكَ الْقَمَرَ وَلاَ اللَّيْلُ سَابِقُ النَّهَارِ  ۚ  وَكُلّ ٌ فِي فَلَك ٍ يَسْبَحُونَ
Wa 'Āyatun Lahum 'Annā Ĥamalnā Dhurrīyatahum Al-Fulki Al-Mashĥūni َ036-041 Kuma ãyã ce a gare su. Lalle Mũ, Mun ɗauki zuriyarsu a cikin jirgin, wanda aka yi wa lõdi. وَآيَة ٌ لَهُمْ أَنَّا حَمَلْنَا ذُرِّيَّتَهُمْ فِي الْفُلْكِ الْمَشْحُونِ
Wa Khalaqnā Lahum Min Mithlihi Mā Yarkabūna َ036-042 Kuma Muka halitta musu, daga irinsa, abin da suke hawa. وَخَلَقْنَا لَهُمْ مِنْ مِثْلِه ِِ مَا يَرْكَبُونَ
Wa 'In Nasha' Nughriqhum Falā Şarīkha Lahum Wa Lā Hum Yunqadhūna َ036-043 Kuma idan Mun so, zã Mu nutsar da su, har bãbu kururuwar neman ãgaji, a gare su, kuma ba su zama anã tsirar da su ba. وَإِنْ نَشَأْ نُغْرِقْهُمْ فَلاَ صَرِيخَ لَهُمْ وَلاَ هُمْ يُنقَذُونَ
'Illā Raĥmatan Minnā Wa Matā`āan 'Ilá Ĥīnin َ036-044 Sai fa bisa ga wata rahama daga gare Mu, da jiyarwa dãɗi zuwa ga wani ɗan lõkaci. إِلاَّ رَحْمَة ً مِنَّا وَمَتَاعا ً إِلَى حِين ٍ
Wa 'Idhā Qīla Lahumu Attaqū Mā Bayna 'Aydīkum Wa Mā Khalfakum La`allakum Turĥamūna َ036-045 Kuma idan aka ce musu, "Ku kãre abin da ke a gaba gare ku da abin da yake a bãyanku, dõmin tsammãninku a ji tausayinku." وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ اتَّقُوا مَا بَيْنَ أَيْدِيكُمْ وَمَا خَلْفَكُمْ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ
Wa Mā Ta'tīhim Min 'Āyatin Min 'Āyāti Rabbihim 'Illā Kānū `Anhā Mu`rīna َ036-046 Kuma wata ãyã daga ãyõyin Ubangijinsu bã ta zuwa a gare su, sai sun kasance sunã mãsu bijirẽwa daga gare ta. وَمَا تَأْتِيهِمْ مِنْ آيَة ٍ مِنْ آيَاتِ رَبِّهِمْ إِلاَّ كَانُوا عَنْهَا مُعْرِضِينَ
Wa 'Idhā Qīla Lahum 'Anfiqū Mimmā Razaqakumu Al-Lahu Qāla Al-Ladhīna Kafarū Lilladhīna 'Āmanū 'Anuţ`imu Man Law Yashā'u Al-Lahu 'Aţ`amahu 'In 'Antum 'Illā Fī Đalālin Mubīnin َ036-047 Kuma idan aka ce musu, "Ku ciyar daga abin da Allah Ya azurta ku," sai waɗanda suka kãfirta su ce ga waɗanda suka yi ĩmãni, "Ashe, zã mu ciyar da wanda idan Allah Ya so Yanã ciyar da shi? Ba ku zama ba fãce a cikin ɓata bayyananniya." وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ أَنفِقُوا مِمَّا رَزَقَكُمُ اللَّهُ قَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلَّذِينَ آمَنُوا أَنُطْعِمُ مَنْ لَوْ يَشَاءُ اللَّهُ أَطْعَمَهُ~ُ إِنْ أَنْتُمْ إِلاَّ فِي ضَلاَل ٍ مُبِين ٍ
Wa Yaqūlūna Matá Hādhā Al-Wa`du 'In Kuntum Şādiqīna َ036-048 Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi yake (aukuwa) idan kun kasance mãsu gaskiya?" وَيَقُولُونَ مَتَى هَذَا الْوَعْدُ إِنْ كُنتُمْ صَادِقِينَ
Mā Yanžurūna 'Illā Şayĥatan Wāĥidatan Ta'khudhuhum Wa Hum Yakhişşimūna َ036-049 Bã su jiran (kõme) fãce wata tsãwa guda, zã ta kãma su, alhãli kuwa sunã yin husũma. مَا يَنظُرُونَ إِلاَّ صَيْحَة ً وَاحِدَة ً تَأْخُذُهُمْ وَهُمْ يَخِصِّمُونَ
Falā Yastaţī`ūna Tawşiyatan Wa Lā 'Ilá 'Ahlihim Yarji`ūna َ036-050 Bã zã su iya yin wasiyya ba, kuma bã zã su iya kõmãwa zuwa ga iyãlansu ba. فَلاَ يَسْتَطِيعُونَ تَوْصِيَة ً وَلاَ إِلَى أَهْلِهِمْ يَرْجِعُونَ
Wa Nufikha Fī Aş-Şūri Fa'idhā Hum Mina Al-'Ajthi 'Ilá Rabbihim Yansilūna َ036-051 Kuma aka yi bũsa a cikin ƙaho, to, sai gã su, daga kaburbura zuwa ga Ubangijinsu, sunã ta gudu. وَنُفِخَ فِي الصُّورِ فَإِذَا هُمْ مِنَ الأَجْدَاثِ إِلَى رَبِّهِمْ يَنسِلُونَ
Qālū Yā Waylanā Man Ba`athanā Min Marqadinā  ۜ  H ۗ  ādhā Mā Wa`ada Ar-Raĥmānu Wa Şadaqa Al-Mursalūna َ036-052 Suka ce: "Yã bonenmu! Wãne ne ya tãyar da mu daga barcinmu?" "Wannan shi ne abin da Mai rahama ya yi wa'adi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya." قَالُوا يَاوَيْلَنَا مَنْ بَعَثَنَا مِنْ مَرْقَدِنَا هَذَا  ۜ  م ۗ  َا وَعَدَ الرَّحْمَنُ وَصَدَقَ الْمُرْسَلُونَ
'In Kānat 'Illā Şayĥatan Wāĥidatan Fa'idhā Hum Jamī`un Ladaynā Muĥđarūna َ036-053 Ba ta kasance ba fãce wata tsãwa ce guda, sai gã su duka, sunã abin halartarwa a gare Mu. إِنْ كَانَتْ إِلاَّ صَيْحَة ً وَاحِدَة ً فَإِذَا هُمْ جَمِيع ٌ لَدَيْنَا مُحْضَرُونَ
Fālyawma Lā Tužlamu Nafsun Shay'āan Wa Lā Tujzawna 'Illā Mā Kuntum Ta`malūna َ036-054 To, a yau, bã zã a zãlunci wani rai da kõme ba. Kuma bã zã a sãkã muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. فَالْيَوْمَ لاَ تُظْلَمُ نَفْس ٌ شَيْئا ً وَلاَ تُجْزَوْنَ إِلاَّ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
'Inna 'Aşĥāba Al-Jannati Al-Yawma Fī Shughulin Fākihūna َ036-055 Lalle, 'yan Aljanna, a yau, sunã cikin shagali, sunã mãsu nishãɗi. إِنَّ أَصْحَابَ الْجَنَّةِ الْيَوْمَ فِي شُغُل ٍ فَاكِهُونَ
Hum Wa 'Azwājuhum Fī Žilālin `Alá Al-'Arā'iki Muttaki'ūna َ036-056 Sũ da mãtan aurensu sunã cikin inuwõwi, a kan karagai, sunã mãsu gincira. هُمْ وَأَزْوَاجُهُمْ فِي ظِلاَلٍ عَلَى الأَرَائِكِ مُتَّكِئُونَ
Lahum Fīhā Fākihatun Wa Lahum Mā Yadda`ūna َ036-057 Sunã da, 'ya'yan itãcen marmari a cikinta kuma sunã sãmun abin da suke kiran a kãwo. لَهُمْ فِيهَا فَاكِهَة ٌ وَلَهُمْ مَا يَدَّعُونَ
Salāmun Qawlāan Min Rabbin Raĥīmin َ036-058 "Aminci," da magana, daga Ubangiji Mai jin ƙai. سَلاَم ٌ قَوْلا ً مِنْ رَبّ ٍ رَحِيم ٍ
Wa Amtāzū Al-Yawma 'Ayyuhā Al-Mujrimūna َ036-059 "Ku rarrabe dabam, a yau, yã kũ mãsu laifi!" وَامْتَازُوا الْيَوْمَ أَيُّهَا الْمُجْرِمُونَ
'Alam 'A`had 'Ilaykum Yā Banī 'Ādama 'An Lā Ta`budū Ash-Shayţāna  ۖ  'Innahu Lakum `Adūwun Mubīnun َ036-060 "Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yã ɗiyan Ãdamu? Cẽwa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne?" أَلَمْ أَعْهَدْ إِلَيْكُمْ يَابَنِي آدَمَ أَنْ لاَ تَعْبُدُوا الشَّيْطَانَ إِنَّه ُُ  ۖ  لَكُمْ عَدُوّ ٌ مُبِين ٌ
Wa 'Ani A`budūnī  ۚ  Hādhā Şirāţun Mustaqīmun َ036-061 "Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya." وَأَنِ اعْبُدُونِي  ۚ  هَذَا صِرَاط ٌ مُسْتَقِيم ٌ
Wa Laqad 'Ađalla Minkum Jibillāan Kathīrāan  ۖ  'Afalam Takūnū Ta`qilūna َ036-062 "Kuma lalle haƙĩƙa, (Shaiɗan) yã ɓatar da jama'a mãsu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kunã yin hankali ba?" وَلَقَدْ أَضَلَّ مِنْكُمْ جِبِلّا ً كَثِيراً  ۖ  أَفَلَمْ تَكُونُوا تَعْقِلُونَ
Hadhihi Jahannamu Allatī Kuntum Tū`adūna َ036-063 "Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance anã yi muku wa'adi da ita." هَذِه ِِ جَهَنَّمُ الَّتِي كُنتُمْ تُوعَدُونَ
Aşlawhā Al-Yawma Bimā Kuntum Takfurūna َ036-064 "Ku shigẽ ta a yau, sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci." اصْلَوْهَا الْيَوْمَ بِمَا كُنتُمْ تَكْفُرُونَ
Al-Yawma Nakhtimu `Alá 'Afwāhihim Wa Tukallimunā 'Aydīhim Wa Tash/hadu 'Arjuluhum Bimā Kānū Yaksibūna َ036-065 A yau, Munã sanya hãtimin rufi a kan bãkunansu, kuma hannãyensu su yi Mana magana, kuma ƙafãfunsu su yi shaidu da abin da suka kasance sunã aikatãwa. الْيَوْمَ نَخْتِمُ عَلَى أَفْوَاهِهِمْ وَتُكَلِّمُنَا أَيْدِيهِمْ وَتَشْهَدُ أَرْجُلُهُمْ بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ
Wa Law Nashā'u Laţamasnā `Alá 'A`yunihim Fāstabaqū Aş-Şirāţa Fa'anná Yubşirūna َ036-066 Dã Mun so, dã Mun shãfe gani daga idãnunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya zã su yi gani? وَلَوْ نَشَاءُ لَطَمَسْنَا عَلَى أَعْيُنِهِمْ فَاسْتَبَقُوا الصِّرَاطَ فَأَنَّى يُبْصِرُونَ
Wa Law Nashā'u Lamasakhnāhum `Alá Makānatihim Famā Astaţā`ū Muđīyāan Wa Lā Yarji`ūna َ036-067 Kuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba zã su iya shuɗewa ba, kuma ba zã su komo ba. وَلَوْ نَشَاءُ لَمَسَخْنَاهُمْ عَلَى مَكَانَتِهِمْ فَمَا اسْتَطَاعُوا مُضِيّا ً وَلاَ يَرْجِعُونَ
Wa Man Nu`ammirhu Nunakkis/hu Fī Al-Khalqi  ۖ  'Afalā Ya`qilūna َ036-068 Kuma wanda Muka rãya shi, Manã sunkuyar da shi ga halittarsa. Ashe, bã su hankalta? وَمَنْ نُعَمِّرْهُ نُنَكِّسْهُ فِي الْخَلْقِ  ۖ  أَفَلاَ يَعْقِلُونَ
Wa Mā `Allamnāhu Ash-Shi`ra Wa Mā Yanbaghī Lahu  ۚ  'In Huwa 'Illā Dhikrun Wa Qur'ānun Mubīnun َ036-069 Ba Mu sanar da shi (Annabi) wãkã ba, kuma wãkã ba ta kamãta da shi (Annabi) ba. Shi (Al-ƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ce, da abin karãtu bayyananne. وَمَا عَلَّمْنَاهُ الشِّعْرَ وَمَا يَنْبَغِي لَهُ~ُ  ۚ  إِنْ هُوَ إِلاَّ ذِكْر ٌ وَقُرْآن ٌ مُبِين ٌ
Liyundhira Man Kāna Ĥayyāan Wa Yaĥiqqa Al-Qawlu `Alá Al-Kāfirīna َ036-070 Dõmin ya yi gargaɗi ga wanda ya kasance mai rai, kuma magana ta wajaba a kan kãfirai. لِيُنْذِرَ مَنْ كَانَ حَيّا ً وَيَحِقَّ الْقَوْلُ عَلَى الْكَافِرِينَ
'Awalam Yaraw 'Annā Khalaqnā Lahum Mimmā `Amilat 'Aydīnā 'An`āmāan Fahum Lahā Mālikūna َ036-071 Shin, ba su gani ba (cẽwa) lalle Mun halitta musu dabbõbi daga abin da HannayenMu suka aikata, sai sunã mallakar su? أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّا خَلَقْنَا لَهُمْ مِمَّا عَمِلَتْ أَيْدِينَا أَنْعَاما ً فَهُمْ لَهَا مَالِكُونَ
Wa Dhallalnāhā Lahum Faminhā Rakūbuhum Wa Minhā Ya'kulūna َ036-072 Kuma Muka hõre su, sabõda su, sabõda haka daga gare su abin hawansu yake, kuma daga gare su suke ci. وَذَلَّلْنَاهَا لَهُمْ فَمِنْهَا رَكُوبُهُمْ وَمِنْهَا يَأْكُلُونَ
Wa Lahum Fīhā Manāfi`u Wa Mashāribu  ۖ  'Afalā Yashkurūna َ036-073 Kuma sunã da waɗansu amfãnõni a cikinsu, da abũbuwan shã. Ashe fa, bã zã; su gõdẽ ba? وَلَهُمْ فِيهَا مَنَافِعُ وَمَشَارِبُ  ۖ  أَفَلاَ يَشْكُرُونَ
Wa Attakhadhū Min Dūni Al-Lahi 'Ālihatan La`allahum Yunşarūna َ036-074 Kuma suka riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa wanin Allah, ɗammãninsu zã su taimake su. وَاتَّخَذُوا مِنْ دُونِ اللَّهِ آلِهَة ً لَعَلَّهُمْ يُنصَرُونَ
Lā Yastaţī`ūna Naşrahum Wa Hum Lahum Jundun Muĥđarūna َ036-075 Bã zã su iya taimakonsu ba, alhãli kuwa sũ runduna ce wadda ake halartarwa (a cikin wutã). لاَ يَسْتَطِيعُونَ نَصْرَهُمْ وَهُمْ لَهُمْ جُند ٌ مُحْضَرُونَ
Falā Yaĥzunka Qawluhum  ۘ  'Innā Na`lamu Mā Yusirrūna Wa Mā Yu`linūna َ036-076 Sabõda haka, kada maganarsu ta ɓãta maka rai. Lalle Mũ, Munã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa. فَلاَ يَحْزُنْكَ قَوْلُهُمْ  ۘ  إِنَّا نَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ
'Awalam Yara Al-'Insānu 'Annā Khalaqnāhu Min Nuţfatin Fa'idhā Huwa Khīmun Mubīnun َ036-077 Ashe, kuma mutum bai ga (cẽwa) lalle Mũ, Mun halitta shi daga maniyyi ba, sai gã shi mai yawan husũma, mai bayyanãwar husũmar. أَوَلَمْ يَرَ الإِنسَانُ أَنَّا خَلَقْنَاه ُُ مِنْ نُطْفَة ٍ فَإِذَا هُوَ خَصِيم ٌ مُبِين ٌ
Wa Đaraba Lanā Mathalāan Wa Nasiya Khalqahu  ۖ  Qāla Man Yuĥyī Al-`Ižāma Wa Hiya Ramīmun َ036-078 Kuma ya buga Mana wani misãli, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: "Wãne ne ke rãyar da ƙasũsuwa alhãli kuwa sunã rududdugaggu?" وَضَرَبَ لَنَا مَثَلا ً وَنَسِيَ خَلْقَه ُُ  ۖ  قَالَ مَنْ يُحْيِي الْعِظَامَ وَهِيَ رَمِيم ٌ
Qul Yuĥyīhā Al-Ladhī 'Ansha'ahā 'Awwala Marratin  ۖ  Wa Huwa Bikulli Khalqin `Alīmun َ036-079 Ka ce: "Wanda ya ƙãga halittarsu a farkon lõkaci Shĩ ke rãyar da su, kuma Shi, game da kõwace halitta, Mai ilmi ne." قُلْ يُحْيِيهَا الَّذِي أَنشَأَهَا أَوَّلَ مَرَّة ٍ  ۖ  وَهُوَ بِكُلِّ خَلْقٍ عَلِيم ٌ
Al-Ladhī Ja`ala Lakum Mina Ash-Shajari Al-'Akhđari Nārāan Fa'idhā 'Antum Minhu Tūqidūna َ036-080 "Wanda ya sanya muku wutã daga itãce kõre, sai gã ku kunã kunnãwa daga gare shi." الَّذِي جَعَلَ لَكُمْ مِنَ الشَّجَرِ الأَخْضَرِ نَارا ً فَإِذَا أَنْتُمْ مِنْهُ تُوقِدُونَ
'Awalaysa Al-Ladhī Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Biqādirin `Alá 'An Yakhluqa Mithlahum  ۚ  Balá Wa Huwa Al-Khallāqu Al-`Alīmu َ036-081 "Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasã bai zama Mai ĩkon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shĩ Mai yawan halittãwa ne,Mai ilmi." أَوَلَيْسَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ بِقَادِرٍ عَلَى أَنْ يَخْلُقَ مِثْلَهُمْ  ۚ  بَلَى وَهُوَ الْخَلاَّقُ الْعَلِيمُ
'Innamā 'Amruhu 'Idhā 'Arāda Shay'āan 'An Yaqūla Lahu Kun Fayakūnu َ036-082 UmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, "Ka kasance," sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi). إِنَّمَا أَمْرُهُ~ُ إِذَا أَرَادَ شَيْئاً أَنْ يَقُولَ لَه ُُ كُنْ فَيَكُونُ
Fasubĥāna Al-Ladhī Biyadihi Malakūtu Kulli Shay'in Wa 'Ilayhi Turja`ūna َ036-083 Sabõda haka, tsarki yã tabbata ga Wanda mallakar kõwane abu take ga HannãyenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku. فَسُبْحَانَ الَّذِي بِيَدِه ِِ مَلَكُوتُ كُلِّ شَيْء ٍ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Next Sūrah