34) Sūrat Saba'

Printed format

34) سُورَة سَبَأ

Al-Ĥamdu Lillahi Al-Ladhī Lahu Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi Wa Lahu Al-Ĥamdu Fī Al-'Ākhirati Wa Huwa Al-Ĥakīmu Al-Khabīru َ034-001 Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Yake abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã Nãsa ne, kuma shĩ ne Mai hikima, Mai labartawa. الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي لَه ُُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ وَلَهُ الْحَمْدُ فِي الآخِرَةِ وَهُوَ الْحَكِيمُ الْخَبِيرُ
Ya`lamu Mā Yaliju Fī Al-'Arđi Wa Mā Yakhruju Minhā Wa Mā Yanzilu Mina As-Samā'i Wa Mā Ya`ruju Fīhā  ۚ  Wa Huwa Ar-Raĥīmu Al-Ghafūru َ034-002 Yã san abin da yake shiga a cikin ƙasã da abin da yake fita daga gare ta, da abin da yake sauka daga sama da abin da yake hawa a cikinta, kuma Shĩ ne Mai jin ƙai, Mai gãfara. يَعْلَمُ مَا يَلِجُ فِي الأَرْضِ وَمَا يَخْرُجُ مِنْهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وَمَا يَعْرُجُ فِيهَا  ۚ  وَهُوَ الرَّحِيمُ الْغَفُورُ
Wa Qāla Al-Ladhīna Kafarū Lā Ta'tīnā As-Sā`atu  ۖ  Qul Balá Wa Rabbī Lata'tiyannakum `Ālimi Al-Ghaybi  ۖ  Lā Ya`zubu `Anhu Mithqālu Dharratin As-Samāwāti Wa Lā Fī Al-'Arđi Wa Lā 'Aşgharu Min Dhālika Wa Lā 'Akbaru 'Illā Fī Kitābin Mubīnin َ034-003 Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Sã'a bã zã ta zo mana ba." Ka ce: "Kayya! Na rantse da Ubangijĩna, lalle, zã ta zõ muku." Masanin gaibi, gwargwadon zarra bã ta nĩsanta daga gare Shi a cikin sammai kuma bã ta nĩsanta a cikin ƙasã, kuma bãbu mafi ƙaranci daga wancan kuma bãbu mafi girma fãce yanã a cikin Littãfi bayyananne. وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لاَ تَأْتِينَا السَّاعَةُ  ۖ  قُلْ بَلَى وَرَبِّي لَتَأْتِيَنَّكُمْ عَالِمِ الْغَيْبِ  ۖ  لاَ يَعْزُبُ عَنْهُ مِثْقَالُ ذَرَّة ٍ فِي السَّمَاوَاتِ وَلاَ فِي الأَرْضِ وَلاَ أَصْغَرُ مِنْ ذَلِكَ وَلاَ أَكْبَرُ إِلاَّ فِي كِتَاب ٍ مُبِين ٍ
Liyajziya Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti  ۚ  'Ūlā'ika Lahum Maghfiratun Wa Rizqun Karīmun َ034-004 Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Waɗancan suna da wata gãfara da wani arziki mai karimci. لِيَجْزِيَ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ  ۚ  أُوْلَائِكَ لَهُمْ مَغْفِرَة ٌ وَرِزْق ٌ كَرِيم ٌ
Wa Al-Ladhīna Sa`aw Fī 'Āyātinā Mu`ājizīna 'Ūlā'ika Lahum `Adhābun Min Rijzin 'Alīmun َ034-005 Kuma waɗanda suka yi mãkirci ga ãyõyinMu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗannan sunã da wata azãba daga azãba mai raɗaɗi. وَالَّذِينَ سَعَوْا فِي آيَاتِنَا مُعَاجِزِينَ أُوْلَائِكَ لَهُمْ عَذَاب ٌ مِنْ رِجْزٍ أَلِيم ٌ
Wa Yará Al-Ladhīna 'Ū Al-`Ilma Al-Ladhī 'Unzila 'Ilayka Min Rabbika Huwa Al-Ĥaqqa Wa Yahdī 'Ilá Şirāţi Al-`Azīzi Al-Ĥamīdi َ034-006 Kuma waɗanda aka bai wa ilmi sunã ganin abin nan da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, shi ne gaskiya, kuma yanã shiryarwa zuwa ga hanyar Mabuwãyi, Gõdadde. وَيَرَى الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ الَّذِي أُنزِلَ إِلَيْكَ مِنْ رَبِّكَ هُوَ الْحَقَّ وَيَهْدِي إِلَى صِرَاطِ الْعَزِيزِ الْحَمِيدِ
Wa Qāla Al-Ladhīna Kafarū Hal Nadullukum `Alá Rajulin Yunabbi'ukum 'Idhā Muzziqtum Kulla Mumazzaqin 'Innakum Lafī Khalqin Jadīdin َ034-007 Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin zã mu nũna muku wani namiji wanda yake gaya muku wai idan an tsattsãge ku, kõwace irin tsattsãgẽwa, lalle kũ, tabbas, kunã a cikin wata halitta sãbuwa.?" وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا هَلْ نَدُلُّكُمْ عَلَى رَجُل ٍ يُنَبِّئُكُمْ إِذَا مُزِّقْتُمْ كُلَّ مُمَزَّق ٍ إِنَّكُمْ لَفِي خَلْق ٍ جَدِيد ٍ
'Āftará `Alá Al-Lahi Kadhibāan 'Am Bihi Jinnatun  ۗ  Bali Al-Ladhīna Lā Yu'uminūna Bil-'Ākhirati Fī Al-`Adhābi Wa Ađ-Đalāli Al-Ba`īdi َ034-008 "Ya ƙãga ƙarya ga Allah ne kõ kuwa akwai wata hauka a gare shi?" Ã'a, waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba, sunã a cikin azãba da ɓãta mai nĩsa. أَافْتَرَى عَلَى اللَّهِ كَذِباً أَمْ بِه ِِ جِنَّة ٌ  ۗ  بَلِ الَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ بِالآخِرَةِ فِي الْعَذَابِ وَالضَّلاَلِ الْبَعِيدِ
'Afalam Yaraw 'Ilá Mā Bayna 'Aydīhim Wa Mā Khalfahum Mina As-Samā'i Wa Al-'Arđi  ۚ  'In Nasha' Nakhsif Bihimu Al-'Arđa 'Aw Nusqiţ `Alayhim Kisafāan Mina As-Samā'i  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyatan Likulli `Abdin Munībin َ034-009 Ashe fa, ba su yi dũbi ba zuwa ga abin da ke a gaba gare su da abin da ke a bãyansu daga sama da ƙasã? idan Mun so, sai Mu shãfe ƙasã da su, kõ kuma Mu kãyar da wani ɓaɓɓake daga sama a kansu. Lalle, a cikin wancan akwai ãyã ga dukan bãwã mai maida al'amarinsa ga Allah. أَفَلَمْ يَرَوْا إِلَى مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ مِنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ  ۚ  إِنْ نَشَأْ نَخْسِفْ بِهِمُ الأَرْضَ أَوْ نُسْقِطْ عَلَيْهِمْ كِسَفا ً مِنَ السَّمَاءِ  ۚ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَة ً لِكُلِّ عَبْد ٍ مُنِيب ٍ
Wa Laqad 'Ātaynā Dāwūda Minnā Fađlāan  ۖ  Yā Jibālu 'Awwibī Ma`ahu Wa Aţ-Ţayra  ۖ  Wa 'Alannā Lahu Al-Ĥadīda َ034-010 Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda wata falala dagagare Mu. Yã duwatsu, ku konkõma sautin tasbihi tãre da shi kuma da tsuntsãye. Kuma Muka tausasa masa baƙin ƙarfe. وَلَقَدْ آتَيْنَا دَاوُودَ مِنَّا فَضْلا ً  ۖ  يَاجِبَالُ أَوِّبِي مَعَه ُُ وَالطَّيْرَ وَأَلَنَّا  ۖ  لَهُ الْحَدِيدَ
'Ani A`mal Sābighātin Wa Qaddir Fī As-Sardi  ۖ  Wa A`malū Şāliĥāan  ۖ  'Innī Bimā Ta`malūna Başīrun َ034-011 Ka aikata sulkuna kuma ka ƙaddara lissãfi ga tsãrawa, kuma ka aikata aikin ƙwarai. Lalle NĩMai gani ne ga abin da kuke aikatãwa. أَنِ اعْمَلْ سَابِغَات ٍ وَقَدِّرْ فِي السَّرْدِ  ۖ  وَاعْمَلُوا صَالِحا ً  ۖ  إِنِّي بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِير ٌ
Wa Lisulaymāna Ar-Rīĥa Ghudūwuhā Shahrun Wa Rawāĥuhā Shahrun  ۖ  Wa 'Asalnā Lahu `Ayna Al-Qiţri  ۖ  Wa Mina Al-Jinni Man Ya`malu Bayna Yadayhi Bi'idhni Rabbihi  ۖ  Wa Man Yazigh Minhum `An 'Amrinā Nudhiqhu Min `Adhābi As-Sa`īri َ034-012 Kuma ga Sulaimãn, Mun hõre masa iska, tafiyarta ta safiya daidai da wata, kuma ta maraice daidai da wata. Kuma Muka gudãnar masa da marmaron gaci, kuma daga aljannu (Muka hõre masa) waɗanda ke aiki a gaba gare shi, da iznin Ubangijinsa. Wanda ya karkata daga cikinsu, daga umurninMu, sai Mu ɗanɗana masa daga azãbar sa'ĩr. وَلِسُلَيْمَانَ الرِّيحَ غُدُوُّهَا شَهْر ٌ وَرَوَاحُهَا شَهْر ٌ  ۖ  وَأَسَلْنَا لَه ُُ عَيْنَ الْقِطْرِ  ۖ  وَمِنَ الْجِنِّ مَنْ يَعْمَلُ بَيْنَ يَدَيْهِ بِإِذْنِ رَبِّه ِِ  ۖ  وَمَنْ يَزِغْ مِنْهُمْ عَنْ أَمْرِنَا نُذِقْهُ مِنْ عَذَابِ السَّعِيرِ
Ya`malūna Lahu Mā Yashā'u Min Maĥārība Wa Tamāthīla Wa Jifānin Kāljawābi Wa Qudūrin Rāsiyātin  ۚ  A`malū 'Āla Dāwūda Shukrāan  ۚ  Wa Qalīlun Min `Ibādiya Ash-Shakūru َ034-013 Sunã aikata masa abin da yake so, na masallatai da mutummutumai da akussa kamar kududdufai, da tukwãne kafaffu. Ku aikata gõdiya, yã ɗiyan Dãwũda, kuma kaɗan ne mai gõdiya daga bãyĩNa. يَعْمَلُونَ لَه ُُ مَا يَشَاءُ مِنْ مَحَارِيبَ وَتَمَاثِيلَ وَجِفَان ٍ كَالْجَوَابِ وَقُدُور ٍ رَاسِيَات ٍ  ۚ  اعْمَلُوا آلَ دَاوُودَ شُكْرا ً  ۚ  وَقَلِيل ٌ مِنْ عِبَادِيَ الشَّكُورُ
Falammā Qađaynā `Alayhi Al-Mawta Mā Dallahum `Alá Mawtihi 'Illā Dābbatu Al-'Arđi Ta'kulu Minsa'atahu  ۖ  Falammā Kharra Tabayyanati Al-Jinnu 'An Law Kānū Ya`lamūna Al-Ghayba Mā Labithū Fī Al-`Adhābi Al-Muhīni َ034-014 Sa'an nan a lõkacin da Muka hukunta mutuwa a kansa bãbu abin da ya ja hankalinsu, a kan mutuwarsa, fãce dabbar ƙasa (gara) wadda take cin sandarsa. To a lõkacin da ya fãɗi, sai aljannu suka bayyana (ga mutãne) cẽwa dã sun kasance sun san gaibi, dã ba su zauna ba a cikin azãba mai wulãkantarwa. فَلَمَّا قَضَيْنَا عَلَيْهِ الْمَوْتَ مَا دَلَّهُمْ عَلَى مَوْتِهِ~ِ إِلاَّ دَابَّةُ الأَرْضِ تَأْكُلُ مِنسَأَتَه ُُ  ۖ  فَلَمَّا خَرَّ تَبَيَّنَتِ الْجِنُّ أَنْ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ الْغَيْبَ مَا لَبِثُوا فِي الْعَذَابِ الْمُهِينِ
Laqad Kāna Lisaba'iin Fī Maskanihim 'Āyatun  ۖ  Jannatāni `An Yamīnin Wa Shimālin  ۖ  Kulū Min Rizqi Rabbikum Wa Ashkurū Lahu  ۚ  Baldatun Ţayyibatun Wa Rabbun Ghafūrun َ034-015 Lalle, haƙĩƙa, akwai ãyã ga saba'ãwa a cikin mazauninsu: gõnakin lambu biyu, dama da hagu. "Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi gõdiya gare shi. Gari mai dãɗin zama, da Ubangiji Mai gãfara." لَقَدْ كَانَ لِسَبَإ ٍ فِي مَسْكَنِهِمْ آيَة ٌ  ۖ  جَنَّتَانِ عَنْ يَمِين ٍ وَشِمَال ٍ  ۖ  كُلُوا مِنْ رِزْقِ رَبِّكُمْ وَاشْكُرُوا لَه ُُ  ۚ  بَلْدَة ٌ طَيِّبَة ٌ وَرَبٌّ غَفُور ٌ
Fa'a`rađū Fa'arsalnā `Alayhim Sayla Al-`Arimi Wa Baddalnāhum Bijannatayhim Jannatayni Dhawātá 'Ukulin Khamţin Wa 'Athlin Wa Shay'in Min Sidrin Qalīlin َ034-016 Sai suka bijire sabõda haka Muka saki Mãlãlin Arimi (dam) a kansu, kuma Muka musanya musu gõnakinsu biyu da waɗansu gõnaki biyu mãsu 'ya'yan itãce kaɗan: talãkiya da gõriba da wani abu na magarya kaɗan. فَأَعْرَضُوا فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ سَيْلَ الْعَرِمِ وَبَدَّلْنَاهُمْ بِجَنَّتَيْهِمْ جَنَّتَيْنِ ذَوَاتَى أُكُلٍ خَمْط ٍ وَأَثْل ٍ وَشَيْء ٍ مِنْ سِدْر ٍ قَلِيل ٍ
Dhālika Jazaynāhum Bimā Kafarū  ۖ  Wa Hal Nujāzī 'Illā Al-Kafūra َ034-017 Wancan, da shi Muka yi musu sakamako sabõda kãfircinsu. Kuma lalle, bã Mu yi wa kõwa irin wannan sakamako, fãce kafirai. ذَلِكَ جَزَيْنَاهُمْ بِمَا كَفَرُوا  ۖ  وَهَلْ نُجَازِي إِلاَّ الْكَفُورَ
Wa Ja`alnā Baynahum Wa Bayna Al-Qurá Allatī Bāraknā Fīhā Quráan Žāhiratan Wa Qaddarnā Fīhā As-Sayra  ۖ  Sīrū Fīhā Layāliya Wa 'Ayyāmāan 'Āminīna َ034-018 Kuma Muka sanya, a tsakaninsu da tsakãnin garũruwan da Muka Sanya albarka a cikinsu, waɗansu garũruwa mãsuganin jũna kuma Muka ƙaddara tafiya a cikinsu, "Ku yi tafiya a cikinsu, darũruwa da rãnaiku, kunã amintattu." وَجَعَلْنَا بَيْنَهُمْ وَبَيْنَ الْقُرَى الَّتِي بَارَكْنَا فِيهَا قُرى ً ظَاهِرَة ً وَقَدَّرْنَا فِيهَا السَّيْرَ  ۖ  سِيرُوا فِيهَا لَيَالِيَ وَأَيَّاما ً آمِنِينَ
Faqālū Rabbanā Bā`id Bayna 'Asfārinā Wa Žalamū 'Anfusahum Faja`alnāhum 'Aĥādītha Wa Mazzaqnāhum Kulla Mumazzaqin  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Likulli Şabbārin Shakūrin َ034-019 Sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakãnin tafiyõyinmu," kuma suka zãlunci kansu, sabõda haka Muka sanya su lãbãran hĩra kuma Muka kekkẽce su kõwace, irin kekkẽcewa. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan gõdiya. فَقَالُوا رَبَّنَا بَاعِدْ بَيْنَ أَسْفَارِنَا وَظَلَمُوا أَنفُسَهُمْ فَجَعَلْنَاهُمْ أَحَادِيثَ وَمَزَّقْنَاهُمْ كُلَّ مُمَزَّق ٍ  ۚ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَات ٍ لِكُلِّ صَبَّار ٍ شَكُور ٍ
Wa Laqad Şaddaqa `Alayhim 'Iblīsu Žannahu Fa Attaba`ūhu 'Illā Farīqāan Mina Al-Mu'uminīna َ034-020 Kuma lalle, haƙĩƙa, Iblĩs ya gaskata zatonsa a kansu, sai suka bi shi fãce wani ɓangare na mũminai. وَلَقَدْ صَدَّقَ عَلَيْهِمْ إِبْلِيسُ ظَنَّه ُُ فَاتَّبَعُوهُ~ُ إِلاَّ فَرِيقا ً مِنَ الْمُؤْمِنِينَ
Wa Mā Kāna Lahu `Alayhim Min Sulţānin 'Illā Lina`lama Man Yu'uminu Bil-'Ākhirati Mimman Huwa Minhā Fī Shakkin  ۗ  Wa Rabbuka `Alá Kulli Shay'in Ĥafīžun َ034-021 Kuma bã ya da wani dalĩli a kansu fãce dai dõmin Mu san wanda yake yin ĩmãni da Lãhira daga wanda yake a cikin shakka daga gare ta. Kuma Ubangijinka, a kan kõme, Mai tsaro ne. وَمَا كَانَ لَه ُُ عَلَيْهِمْ مِنْ سُلْطَان ٍ إِلاَّ لِنَعْلَمَ مَنْ يُؤْمِنُ بِالآخِرَةِ مِمَّنْ هُوَ مِنْهَا فِي شَكّ ٍ  ۗ  وَرَبُّكَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ حَفِيظ ٌ
Qul Ad Al-Ladhīna Za`amtum Min Dūni Al-Lahi  ۖ  Lā Yamlikūna Mithqāla Dharratin As-Samāwāti Wa Lā Fī Al-'Arđi Wa Mā Lahum Fīhimā Min Shirkin Wa Mā Lahu Minhum Min Žahīrin َ034-022 Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya (cẽwa abũbuwan bautãwa ne) baicin Allah, bã su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma bã su Mallakarsa a cikin ƙasa kuma bã su da wani rabon tãrẽwa a cikinsu (sammai da ƙasa),kuma bã Shi da wani mataimaki daga gare su. قُلْ ادْعُوا الَّذِينَ زَعَمْتُمْ مِنْ دُونِ اللَّهِ  ۖ  لاَ يَمْلِكُونَ مِثْقَالَ ذَرَّة ٍ فِي السَّمَاوَاتِ وَلاَ فِي الأَرْضِ وَمَا لَهُمْ فِيهِمَا مِنْ شِرْك ٍ وَمَا لَه ُُ مِنْهُمْ مِنْ ظَهِير ٍ
Wa Lā Tanfa`u Ash-Shafā`atu `Indahu 'Illā Liman 'Adhina Lahu  ۚ  Ĥattá 'Idhā Fuzzi`a `An Qulūbihim Qālū Mādhā Qāla Rabbukum  ۖ  Qālū Al-Ĥaqqa  ۖ  Wa Huwa Al-`Alīyu Al-Kabīru َ034-023 "Kuma wani cẽto bã ya amfãni a wurinSa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi. Har a lõkacin da aka kuranye tsõro daga zukãtansu, sai su ce, 'Mẽne ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma," وَلاَ تَنفَعُ الشَّفَاعَةُ عِنْدَهُ~ُ إِلاَّ لِمَنْ أَذِنَ لَه ُُ  ۚ  حَتَّى إِذَا فُزِّعَ عَنْ قُلُوبِهِمْ قَالُوا مَاذَا قَالَ رَبُّكُمْ  ۖ  قَالُوا الْحَقَّ  ۖ  وَهُوَ الْعَلِيُّ الْكَبِيرُ
Qul Man Yarzuqukum Mina As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۖ  Quli Al-Lahu  ۖ  Wa 'Innā 'Aw 'Īyākum La`alá Hudáan 'Aw Fī Đalālin Mubīnin َ034-024 Ka ce: "Wãne ne yake azurta ku daga sama da ƙasa?" Ka ce: "Allah kuma lalle mũ kõ ku, wani yanã a kan shiriya, kõ yana a cikin ɓata bayyananniya." قُلْ مَنْ يَرْزُقُكُمْ مِنَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۖ  قُلِ اللَّهُ  ۖ  وَإِنَّا أَوْ إِيَّاكُمْ لَعَلَى هُدىً أَوْ فِي ضَلاَل ٍ مُبِين ٍ
Qul Lā Tus'alūna `Ammā 'Ajramnā Wa Lā Nus'alu `Ammā Ta`malūna َ034-025 Ka ce: "Bã zã a tambaye ku ba ga abin da muka aikata daga laifi, kuma bã zã a tambaye mu daga abin da kuke aikatawa ba." قُلْ لاَ تُسْأَلُونَ عَمَّا أَجْرَمْنَا وَلاَ نُسْأَلُ عَمَّا تَعْمَلُونَ
Qul Yajma`u Baynanā Rabbunā Thumma Yaftaĥu Baynanā Bil-Ĥaqqi Wa Huwa Al-Fattāĥu Al-`Alīmu َ034-026 Ka ce: "Ubangijinmu zai tãra tsakãninmu, sa'an nan Ya yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya. Kuma Shĩ ne Mahukunci, Masani." قُلْ يَجْمَعُ بَيْنَنَا رَبُّنَا ثُمَّ يَفْتَحُ بَيْنَنَا بِالْحَقِّ وَهُوَ الْفَتَّاحُ الْعَلِيمُ
Qul 'Arūniya Al-Ladhīna 'Alĥaqtum Bihi Shurakā'a  ۖ  Kallā  ۚ  Bal Huwa Al-Lahu Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ034-027 Ka ce: "Ku nũna mini waɗanda kuka riskar da Shi, su zama abõkan tãrayya. Ã'a, Shĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima." قُلْ أَرُونِيَ الَّذِينَ أَلْحَقْتُمْ بِه ِِ شُرَكَاءَ  ۖ  كَلاَّ  ۚ  بَلْ هُوَ اللَّهُ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Wa Mā 'Arsalnāka 'Illā Kāffatan Lilnnāsi Bashīrāan Wa Nadhīrāan Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Ya`lamūna َ034-028 Kuma ba Mu aika ka ba fãce zuwa ga mutãne gabã ɗaya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلاَّ كَافَّة ً لِلنَّاسِ بَشِيرا ً وَنَذِيرا ً وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يَعْلَمُونَ
Wa Yaqūlūna Matá Hādhā Al-Wa`du 'In Kuntum Şādiqīna َ034-029 Sunã cẽwa, "Yaushe ne wannan wa'adi zai auku idan kun kasance mãsu gaskiya?" وَيَقُولُونَ مَتَى هَذَا الْوَعْدُ إِنْ كُنتُمْ صَادِقِينَ
Qul Lakum Mī`ādu Yawmin Lā Tasta'khirūna `Anhu Sā`atan Wa Lā Tastaqdimūna َ034-030 Ka ce: "Kunã da mi'ãdin wani yini wanda bã ku jinkirta daga gare shi kõ da sa'a ɗaya, kuma bã ku gabãta." قُلْ لَكُمْ مِيعَادُ يَوْم ٍ لاَ تَسْتَأْخِرُونَ عَنْهُ سَاعَة ً وَلاَ تَسْتَقْدِمُونَ
Wa Qāla Al-Ladhīna Kafarū Lan Nu'umina Bihadhā Al-Qur'āni Wa Lā Bial-Ladhī Bayna Yadayhi  ۗ  Wa Law Tará 'Idhi Až-Žālimūna Mawqūfūna `Inda Rabbihim Yarji`u Ba`đuhum 'Ilá Ba`đin Al-Qawla Yaqūlu Al-Ladhīna Astuđ`ifū Lilladhīna Astakbarū Lawlā 'Antum Lakunnā Mu'uminīna َ034-031 Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Bã zã mu yi ĩmanida wannan Alƙur'ãni ba, kuma bã zã mu yi ĩmani da abin da yakea gabãninsa ba (na waɗansu littattafan sama)." Kuma dã kã gani a lõkacin da azzãlumai suke abin tsayarwa wurin Ubangijinka, sashensu na mayar wa sãshe maganar maraunana (mabiya) suke cẽwa makangara (shũgabanni) "Ba dõminku ba, lalle, dã mun kasance mũminai." وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لَنْ نُؤْمِنَ بِهَذَا الْقُرْآنِ وَلاَ بِالَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ  ۗ  وَلَوْ تَرَى إِذِ الظَّالِمُونَ مَوْقُوفُونَ عِنْدَ رَبِّهِمْ يَرْجِعُ بَعْضُهُمْ إِلَى بَعْض ٍ الْقَوْلَ يَقُولُ الَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا لِلَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا لَوْلاَ أَنْتُمْ لَكُنَّا مُؤْمِنِينَ
Qāla Al-Ladhīna Astakbarū Lilladhīna Astuđ`ifū 'Anaĥnu Şadadnākum `Ani Al-Hudá Ba`da 'Idh Jā'akum  ۖ  Bal Kuntum Mujrimīna َ034-032 Makangara suka ce wa maraunana, "Ashe, mũ ne muka kange ku daga shiriya a bãyan ya zo muku? Ã,a' kun dai kasance mãsu laifi." قَالَ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا لِلَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا أَنَحْنُ صَدَدْنَاكُمْ عَنِ الْهُدَى بَعْدَ إِذْ جَاءَكُمْ  ۖ  بَلْ كُنتُمْ مُجْرِمِينَ
Wa Qāla Al-Ladhīna Astuđ`ifū Lilladhīna Astakbarū Bal Makru Al-Layli Wa An-Nahāri 'Idh Ta'murūnanā 'An Nakfura Bil-Lahi Wa Naj`ala Lahu 'Andādāan  ۚ  Wa 'Asarrū An-Nadāmata Lammā Ra'aw Al-`Adhāba Wa Ja`alnā Al-'Aghlāla Fī 'A`nāqi Al-Ladhīna Kafarū  ۚ  Hal Yujzawna 'Illā Mā Kānū Ya`malūna َ034-033 Kuma maraunana suka ce wa makangara. "Ã'a, (ku tuna) mãkircin dare da na rãna a lõkacin da kuke umurnin mu da mu kãfirta da Allah, kuma mu sanya Masa abõkan tãrayya." Kuma suka assirtar da nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Kuma Muka sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyin waɗanda suka kãfirta. Lalle, bã zã a yi musu sakamako ba fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa. وَقَالَ الَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا لِلَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا بَلْ مَكْرُ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ إِذْ تَأْمُرُونَنَا أَنْ نَكْفُرَ بِاللَّهِ وَنَجْعَلَ لَهُ~ُ أَندَادا ً  ۚ  وَأَسَرُّوا النَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوْا الْعَذَابَ وَجَعَلْنَا الأَغْلاَلَ فِي أَعْنَاقِ الَّذِينَ كَفَرُوا  ۚ  هَلْ يُجْزَوْنَ إِلاَّ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Wa Mā 'Arsalnā Fī Qaryatin Min Nadhīrin 'Illā Qāla Mutrafūhā 'Innā Bimā 'Ursiltum Bihi Kāfirūna َ034-034 Kuma ba mu aika wani mai gargaɗi ba a cikin wata alƙarya fãce mani'imtanta (shũgabanni) sunce, "Lalle mũ, mãsu kãfirta ne da abin da aka aiko ku da shi." وَمَا أَرْسَلْنَا فِي قَرْيَة ٍ مِنْ نَذِير ٍ إِلاَّ قَالَ مُتْرَفُوهَا إِنَّا بِمَا أُرْسِلْتُمْ بِه ِِ كَافِرُونَ
Wa Qālū Naĥnu 'Aktharu 'Amwālāan Wa 'Awlādāan Wa Mā Naĥnu Bimu`adhdhabīna َ034-035 Kuma suka ce: "Mũ ne mafiya yawa ga dũkiya da ɗiya, kuma mu ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba." وَقَالُوا نَحْنُ أَكْثَرُ أَمْوَالا ً وَأَوْلاَدا ً وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ
Qul 'Inna Rabbī Yabsuţu Ar-Rizqa Liman Yashā'u Wa Yaqdiru Wa Lakinna 'Akthara An-Nāsi Lā Ya`lamūna َ034-036 Ka ce: "Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfiɗa arziki ga wanda Ya so, kuma Yanã ƙuntatãwa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba." قُلْ إِنَّ رَبِّي يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَنْ يَشَاءُ وَيَقْدِرُ وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يَعْلَمُونَ
Wa Mā 'Amwālukum Wa Lā 'Awlādukum Bi-Atī Tuqarribukum `Indanā Zulfá 'Illā Man 'Āmana Wa `Amila Şāliĥāan Fa'ūlā'ika Lahum Jazā'u Ađ-Đi`fi Bimā `Amilū Wa Hum Al-Ghurufāti 'Āminūna َ034-037 Kuma dũkiyarku ba ta zamo ba, haka ɗiyanku ba su zamo abin da yake kusantar da ku ba a wurinMu, kusantarwar muƙãmi fãce wanda, ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai. To, waɗannan sunã da sakamakon ninkawa sabõda abin da suka aikata. Kuma su amintattu ne a cikin bẽnãye. وَمَا أَمْوَالُكُمْ وَلاَ أَوْلاَدُكُمْ بِالَّتِي تُقَرِّبُكُمْ عِنْدَنَا زُلْفَى إِلاَّ مَنْ آمَنَ وَعَمِلَ صَالِحا ً فَأُوْلَائِكَ لَهُمْ جَزَاءُ الضِّعْفِ بِمَا عَمِلُوا وَهُمْ فِي الْغُرُفَاتِ آمِنُونَ
Wa Al-Ladhīna Yas`awna Fī 'Āyātinā Mu`ājizīna 'Ūlā'ika Fī Al-`Adhābi Muĥđarūna َ034-038 Kuma waɗanda suke mãkirci a cikin ãyõyinMu, sunã nẽman gajiyarwa, waɗannan abin halartãwa ne a cikin azãba. وَالَّذِينَ يَسْعَوْنَ فِي آيَاتِنَا مُعَاجِزِينَ أُوْلَائِكَ فِي الْعَذَابِ مُحْضَرُونَ
Qul 'Inna Rabbī Yabsuţu Ar-Rizqa Liman Yashā'u Min `Ibādihi Wa Yaqdiru Lahu  ۚ  Wa Mā 'Anfaqtum Min Shay'in Fahuwa Yukhlifuhu  ۖ  Wa Huwa Khayru Ar-Rāziqīna َ034-039 Ka ce: "Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfida arziki ga wanda Ya so daga bãyinSa, kuma Yanã ƙuntatãwa a gare shi, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu, to, Shĩ ne zai musanya shi, kuma Shĩ ne Mafi fĩcin mãsu azurtawa." قُلْ إِنَّ رَبِّي يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَنْ يَشَاءُ مِنْ عِبَادِه ِِ وَيَقْدِرُ لَه ُُ  ۚ  وَمَا أَنفَقْتُمْ مِنْ شَيْء ٍ فَهُوَ يُخْلِفُه ُُ  ۖ  وَهُوَ خَيْرُ الرَّازِقِينَ
Wa Yawma Yaĥshuruhum Jamī`āan Thumma Yaqūlu Lilmalā'ikati 'Ahā'uulā' 'Īyākum Kānū Ya`budūna َ034-040 Kuma rãnar da Allah Ya ke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Ya ce wa Malã'iku, "Shin, waɗannan kũ ne suka kasance sunã bauta wa?" وَيَوْمَ يَحْشُرُهُمْ جَمِيعا ً ثُمَّ يَقُولُ لِلْمَلاَئِكَةِ أَهَاؤُلاَء إِيَّاكُمْ كَانُوا يَعْبُدُونَ
Qālū Subĥānaka 'Anta Walīyunā Min Dūnihim  ۖ  Bal Kānū Ya`budūna Al-Jinna  ۖ  'Aktharuhum Bihim Mu'uminūna َ034-041 Sukace: "Tsarki ya tabbata a gare Ka. Kai ne Majiɓincinmu, bã su ba. Ã'a,sun kasance sunã bauta wa aljannu. Mafi yawansu, da sũ suka yi ĩmani." قَالُوا سُبْحَانَكَ أَنْتَ وَلِيُّنَا مِنْ دُونِهِمْ  ۖ  بَلْ كَانُوا يَعْبُدُونَ الْجِنَّ  ۖ  أَكْثَرُهُمْ بِهِمْ مُؤْمِنُونَ
Fālyawma Lā Yamliku Ba`đukum Liba`đin Naf`āan Wa Lā Đarrāan Wa Naqūlu Lilladhīna Žalamū Dhūqū `Adhāba An-Nāri Allatī Kuntum Bihā Tukadhdhibūn َ034-042 Sabõda haka, a yau sãshenku bã ya mallakar wani amfãni ga wani sãshen, kuma bã ya mallakar wata cũta, kuma Munã cẽwa ga waɗanda suka yi zalunci, Ku ɗanɗani azabar wutã wadda "kuka kasance game da ita, kunã ƙaryatãwa." فَالْيَوْمَ لاَ يَمْلِكُ بَعْضُكُمْ لِبَعْض ٍ نَفْعا ً وَلاَ ضَرّا ً وَنَقُولُ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا ذُوقُوا عَذَابَ النَّارِ الَّتِي كُنتُمْ بِهَا تُكَذِّبُون
Wa 'Idhā Tutlá `Alayhim 'Āyātunā Bayyinātin Qālū Mā Hādhā 'Illā Rajulun Yurīdu 'An Yaşuddakum `Ammā Kāna Ya`budu 'Ābā'uukum Wa Qālū Mā Hādhā 'Illā 'Ifkun Muftaráan  ۚ  Wa Qāla Al-Ladhīna Kafarū Lilĥaqqi Lammā Jā'ahum 'In Hādhā 'Illā Siĥrun Mubīnun َ034-043 Kuma idan an karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu, sai su ce: "Wannan bai zama ba fãce namiji ne yanã son ya kange ku daga abin da ubanninku suka kasance sunã bauta wa." Kuma su ce: "Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya da aka ƙãga." Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: ga gaskiya a lõkacin da ta je musu: "Wannan bã kõme ba fãce sihiri ne bayyananne." وَإِذَا تُتْلَى عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَات ٍ قَالُوا مَا هَذَا إِلاَّ رَجُل ٌ يُرِيدُ أَنْ يَصُدَّكُمْ عَمَّا كَانَ يَعْبُدُ آبَاؤُكُمْ وَقَالُوا مَا هَذَا إِلاَّ إِفْك ٌ مُفْتَرى ً  ۚ  وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلْحَقِّ لَمَّا جَاءَهُمْ إِنْ هَذَا إِلاَّ سِحْر ٌ مُبِين ٌ
Wa Mā 'Ātaynāhum Min Kutubin Yadrusūnahā  ۖ  Wa Mā 'Arsalnā 'Ilayhim Qablaka Min Nadhīrin َ034-044 Kuma ba Mu bã su waɗansu littattafai ba waɗanda suke karãtun su, kuma ba Mu aika wani mai gargaɗi ba zuwa gare su a gabãninka! وَمَا آتَيْنَاهُمْ مِنْ كُتُب ٍ يَدْرُسُونَهَا  ۖ  وَمَا أَرْسَلْنَا إِلَيْهِمْ قَبْلَكَ مِنْ نَذِير ٍ
Wa Kadhdhaba Al-Ladhīna Min Qablihim Wa Mā Balaghū Mi`shāra Mā 'Ātaynāhum Fakadhdhabū Rusulī  ۖ  Fakayfa Kāna Nakīri َ034-045 Kuma waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata ,alhãli kuwa ba su kai ushurin-ushurin abin da Muka bã su ba, sai suka ƙaryata ManzanniNa! To, yãya musũNa (ga maƙaryata) ya kasance? وَكَذَّبَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ وَمَا بَلَغُوا مِعْشَارَ مَا آتَيْنَاهُمْ فَكَذَّبُوا رُسُلِي  ۖ  فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ
Qul 'Innamā 'A`ižukum Biwāĥidatin  ۖ  'An Taqūmū Lillahi Mathná Wa Furādá Thumma Tatafakkarū  ۚ  Mā Bişāĥibikum Min Jinnatin  ۚ  'In Huwa 'Illā Nadhīrun Lakum Bayna Yaday `Adhābin Shadīdin َ034-046 Ka ce: "Ina yi muku wa'azi ne kawai da kalma guda! watau ku tsayu dõmin Allah, bibbiyu da ɗaiɗai, sa'an nan ku yi tunãni, bãbu wata hauka ga ma'abũcinku. Shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi ne a gare ku a gaba ga wata azãba mai tsanani. قُلْ إِنَّمَا أَعِظُكُمْ بِوَاحِدَةٍ  ۖ  أَنْ تَقُومُوا لِلَّهِ مَثْنَى وَفُرَادَى ثُمَّ تَتَفَكَّرُوا  ۚ  مَا بِصَاحِبِكُمْ مِنْ جِنَّة ٍ  ۚ  إِنْ هُوَ إِلاَّ نَذِير ٌ لَكُمْ بَيْنَ يَدَيْ عَذَاب ٍ شَدِيد ٍ
Qul Mā Sa'altukum Min 'Ajrin Fahuwa Lakum  ۖ  'In 'Ajriya 'Illā `Alá Al-Lahi  ۖ  Wa Huwa `Alá Kulli Shay'in Shahīdun َ034-047 Ka ce: "Abin da na rõƙe ku na wani sakamako, to, amfãninsa nãku ne. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma shi Mahalarci ne a kan dukan kõme." قُلْ مَا سَأَلْتُكُمْ مِنْ أَجْر ٍ فَهُوَ لَكُمْ  ۖ  إِنْ أَجْرِيَ إِلاَّ عَلَى اللَّهِ  ۖ  وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ شَهِيد ٌ
Qul 'Inna Rabbī Yaqdhifu Bil-Ĥaqqi `Allāmu Al-Ghuyūbi َ034-048 Ka ce: "Lalle Ubangijina Yanã jẽfa gaskiya.(Shi) Masanin abũbuwan fake ne." قُلْ إِنَّ رَبِّي يَقْذِفُ بِالْحَقِّ عَلاَّمُ الْغُيُوبِ
Qul Jā'a Al-Ĥaqqu Wa Mā Yubdi'u Al-Bāţilu Wa Mā Yu`īdu َ034-049 Ka ce: "Gaskiya ta zo, kuma ƙarya bã ta iya fara (kome) kuma bã ta iya mayarwa." قُلْ جَاءَ الْحَقُّ وَمَا يُبْدِئُ الْبَاطِلُ وَمَا يُعِيدُ
Qul 'In Đalaltu Fa'innamā 'Ađillu `Alá Nafsī  ۖ  Wa 'Ini Ahtadaytu Fabimā Yūĥī 'Ilayya Rabbī  ۚ  'Innahu Samī`un Qarībun َ034-050 Ka ce: "Idan na ɓace, to, inã ɓacẽwa ne kawai a kan kaina. Kuma idan na shiryu, to, sabõda abin da Ubangijina Yake yõwar wahayi ne zuwa a gare ni. Lalle Shĩ Mai ji ne, Makusanci." قُلْ إِنْ ضَلَلْتُ فَإِنَّمَا أَضِلُّ عَلَى نَفْسِي  ۖ  وَإِنِ اهْتَدَيْتُ فَبِمَا يُوحِي إِلَيَّ رَبِّي  ۚ  إِنَّه ُُ سَمِيع ٌ قَرِيب ٌ
Wa Law Tará 'Idh Fazi`ū Falā Fawta Wa 'Ukhidhū Min Makānin Qarībin َ034-051 Kuma dã kã gani, a lõkacin da suka firgita, to, bãbu kuɓuta, kuma aka kãma su daga wuri makusanci. وَلَوْ تَرَى إِذْ فَزِعُوا فَلاَ فَوْتَ وَأُخِذُوا مِنْ مَكَان ٍ قَرِيب ٍ
Wa Qālū 'Āmannā Bihi Wa 'Anná Lahumu At-Tanāwushu Min Makānin Ba`īdin َ034-052 Kuma suka ce: "Mun yi ĩmãni da Shi." To inã zã su sãmu kãmãwa daga wuri mai nisa? وَقَالُوا آمَنَّا بِه ِِ وَأَنَّى لَهُمُ التَّنَاوُشُ مِنْ مَكَان ٍ بَعِيد ٍ
Wa Qad Kafarū Bihi Min Qablu  ۖ  Wa Yaqdhifūna Bil-Ghaybi Min Makānin Ba`īdin َ034-053 Kuma lalle sun kãfirta da Shi a gabãnin haka, kuma sunã jĩfa da jãhilci daga wuri mai nĩsa. وَقَدْ كَفَرُوا بِه ِِ مِنْ قَبْلُ  ۖ  وَيَقْذِفُونَ بِالْغَيْبِ مِنْ مَكَان ٍ بَعِيد ٍ
Wa Ĥīla Baynahum Wa Bayna Mā Yashtahūna Kamā Fu`ila Bi'ashyā`ihim Min Qablu  ۚ  'Innahum Kānū Fī Shakkin Murībin َ034-054 Kuma an shãmakance a tsakãninsu da tsakãnin abin da suke marmari, kamar yadda aka aikata da irin ƙungiyõyinsu a gabãninsu. Lalle sũ sun kasance a cikin shakka mai sanya kõkanto. وَحِيلَ بَيْنَهُمْ وَبَيْنَ مَا يَشْتَهُونَ كَمَا فُعِلَ بِأَشْيَاعِهِمْ مِنْ قَبْلُ  ۚ  إِنَّهُمْ كَانُوا فِي شَكّ ٍ مُرِيب ٍ
Next Sūrah