14) Sūrat 'Ibrāhīm

Printed format

14) سُورَة إبرَاهِيم

'Alif-Lām-Rā Kitābun 'Anzalnāhu 'Ilayka Litukhrija An-Nāsa Mina Až-Žulumāti 'Ilá An-Nūr Bi'idhni Rabbihim 'Ilá Şirāţi Al-`Azīzi Al-Ĥamīdi َ014-001 A. L̃. R. Littãfi ne mun saukar da shi zuwa gare ka dõmin ka fitar da mutãne daga duhunhuna zuwa ga haske, da iznin Ubangijinsu, zuwa ga tafarkin Mabuwãyi,Abin gõdẽwa. أَلِف-لَام-رَا كِتَابٌ أَنزَلْنَاهُ~ُ إِلَيْكَ لِتُخْرِجَ  ۚ  النَّاسَ مِنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّور بِإِذْنِ رَبِّهِمْ إِلَى صِرَاطِ الْعَزِيزِ الْحَمِيدِ
Al-Lahi Al-Ladhī Lahu Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi  ۗ  Wa Waylun Lilkāfirīna Min `Adhābin Shadīdin َ014-002 Allah wanda Yake Yanã da abin da ke cikin sammai da cikin ƙasa. Kuma bone yã tabbata ga kãfirai daga azãba mai tsanani. اللَّهِ الَّذِي لَه ُُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ  ۗ  وَوَيْل ٌ لِلْكَافِرِينَ مِنْ عَذَاب ٍ شَدِيد ٍ
Al-Ladhīna Yastaĥibbūna Al-Ĥayāata Ad-Dunyā `Alá Al-'Ākhirati Wa Yaşuddūna `An Sabīli Al-Lahi Wa Yabghūnahā `Iwajāan  ۚ  'Ūlā'ika Fī Đalālin Ba`īdin َ014-003 Waɗanda suka fi son rãyuwar dũniya fiye da ta Lãhira, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah,kuma sunã nẽman ta karkace. Waɗancan na a cikin ɓata mai nĩsa. الَّذِينَ يَسْتَحِبُّونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا عَلَى الآخِرَةِ وَيَصُدُّونَ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ وَيَبْغُونَهَا عِوَجاً  ۚ  أُوْلَائِكَ فِي ضَلاَل ٍ بَعِيد ٍ
Wa Mā 'Arsalnā Min Rasūlin 'Illā Bilisāni Qawmihi Liyubayyina Lahum  ۖ  Fayuđillu Al-Lahu Man Yashā'u Wa Yahdī Man Yashā'u  ۚ  Wa Huwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ014-004 Kuma ba Mu aika wani Manzo ba fãce da harshen mutãnensa dõmin ya bayyanã musu. Sa'an nan Allah Ya ɓatar da wanda Yake so kuma Ya shiryar da wanda Yake so,Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. وَمَا أَرْسَلْنَا مِنْ رَسُول ٍ إِلاَّ بِلِسَانِ قَوْمِه ِِ لِيُبَيِّنَ لَهُمْ  ۖ  فَيُضِلُّ اللَّهُ مَنْ يَشَاءُ وَيَهْدِي مَنْ يَشَاءُ  ۚ  وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Wa Laqad 'Arsalnā Mūsá Bi'āyātinā 'An 'Akhrij Qawmaka Mina Až-Žulumāti 'Ilá An-Nūri Wa Dhakkirhum Bi'ayyāmi Al-Lahi  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Likulli Şabbārin Shakūrin َ014-005 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Mũsã game, da ãyõin Mu cẽwa, "Ka fitar da mutãnenkadaga duhu zuwa ga haske. Kuma ka tunar musu da kwãnukan (masĩfun) Allah." Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi dõmin dukan mai yawan haƙuri, mai gõdiya. وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مُوسَى بِآيَاتِنَا أَنْ أَخْرِجْ قَوْمَكَ مِنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ وَذَكِّرْهُمْ بِأَيَّامِ اللَّهِ  ۚ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَات ٍ لِكُلِّ صَبَّار ٍ شَكُور ٍ
Wa 'Idh Qāla Mūsá Liqawmihi Adhkurū Ni`mata Al-Lahi `Alaykum 'Idh 'Anjākum Min 'Āli Fir`awna Yasūmūnakum Sū'a Al-`Adhābi Wa Yudhabbiĥūna 'Abnā'akum Wa Yastaĥyūna Nisā'akum  ۚ  Wa Fī Dhālikum Balā'un Min Rabbikum `Ažīmun َ014-006 Kuma a lõkacin da Mũsã yace wa mutãnensa, "Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da Ya tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã yi muku mummunar azãba, kuma sunã yanyanka ɗiyanku, kuma sunã rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa mai girmã daga Ubangijinku." وَإِذْ قَالَ مُوسَى لِقَوْمِهِ اذْكُرُوا نِعْمَةَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ أَنجَاكُمْ مِنْ آلِ فِرْعَوْنَ يَسُومُونَكُمْ سُوءَ الْعَذَابِ وَيُذَبِّحُونَ أَبْنَاءَكُمْ وَيَسْتَحْيُونَ نِسَاءَكُمْ  ۚ  وَفِي ذَلِكُمْ بَلاَء ٌ مِنْ رَبِّكُمْ عَظِيم ٌ
Wa 'Idh Ta'adhdhana Rabbukum La'in Shakartum La'azīdannakum  ۖ  Wa La'in Kafartum 'Inna `Adhābī Lashadīdun َ014-007 Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, "Lalle ne idan kun gõde, haƙĩƙa, Inã ƙãramuku, kuma lalle ne idan kun kãfirta haƙĩƙa azãbãta, tabbas, mai tsanani ce." وَإِذْ تَأَذَّنَ رَبُّكُمْ لَئِنْ شَكَرْتُمْ لَأَزِيدَنَّكُمْ  ۖ  وَلَئِنْ كَفَرْتُمْ إِنَّ عَذَابِي لَشَدِيد ٌ
Wa Qāla Mūsá 'In Takfurū 'Antum Wa Man Al-'Arđi Jamī`āan Fa'inna Al-Laha Laghanīyun Ĥamīdun َ014-008 Kuma Mũsã ya ce: "Idan kun kãfirta kũ da waɗanda suke a cikin ƙasa, gabã ɗaya, to, lalle ne Allah haƙĩƙa Mawadãci ne, Mai yawan gõdiya." وَقَالَ مُوسَى إِنْ تَكْفُرُوا أَنْتُمْ وَمَنْ فِي الأَرْضِ جَمِيعا ً فَإِنَّ اللَّهَ لَغَنِيٌّ حَمِيد ٌ
'Alam Ya'tikum Naba'u Al-Ladhīna Min Qablikum Qawmi Nūĥin Wa `Ādin Wa Thamūda Wa  ۛ  Al-Ladhīna Min Ba`dihim  ۛ  Lā Ya`lamuhum 'Illā Al-Lahu  ۚ  Jā'at/hum Rusuluhum Bil-Bayyināti Faraddū 'Aydiyahum Fī 'Afwāhihim Wa Qālū 'Innā Kafarnā Bimā 'Ursiltum Bihi Wa 'Innā Lafī Shakkin Mimmā Tad`ūnanā 'Ilayhi Murībin َ014-009 Shin lãbãrin waɗanda suke a gabãninku, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdawa bai zomuku ba? Kuma da waɗanda suke daga bãyansu bãbu wanda yake sanin su fãce Allah? Manzanninsu sun jẽ musu da hujjõji mabayyana, sai suka mayar da hannayensu a cikin bãkunansu, kuma suka ce: "Lalle ne mũ, mun kãfirta da abinda aka aiko ku da shi. Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa munã a cikin shakkada abin do kuke kiran mu zuwa gare shi, mai sanya kõkanto." أَلَمْ يَأْتِكُمْ نَبَأُ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ قَوْمِ نُوح ٍ وَعَاد ٍ وَثَمُودَ  ۛ  وَالَّذِينَ مِنْ بَعْدِهِمْ  ۛ  لاَ يَعْلَمُهُمْ إِلاَّ اللَّهُ  ۚ  جَاءَتْهُمْ رُسُلُهُمْ بِالْبَيِّنَاتِ فَرَدُّوا أَيْدِيَهُمْ فِي أَفْوَاهِهِمْ وَقَالُوا إِنَّا كَفَرْنَا بِمَا أُرْسِلْتُمْ بِه ِِ وَإِنَّا لَفِي شَكّ ٍ مِمَّا تَدْعُونَنَا إِلَيْهِ مُرِيب ٍ
Qālat Rusuluhum 'Afī Al-Lahi Shakkun Fāţiri As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۖ  Yad`ūkum Liyaghfira Lakum Min Dhunūbikum Wa Yu'uakhkhirakum 'Ilá 'Ajalin Musammáan  ۚ  Qālū 'In 'Antum 'Illā Basharun Mithlunā Turīdūna 'An Taşuddūnā `Ammā Kāna Ya`budu 'Ābā'uunā Fa'tūnā Bisulţānin Mubīnin َ014-010 Manzanninsu suka ce "Ashe, akwai shakka a cikin (sha'anin) Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa Yanã kiran ku dõmin Ya gãfarta muku zunubanku, kuma Ya jinkirtã muku zuwa ga ajali ambatacce?" Suka ce: "Ba ku zama ba fãce mutãne misãlinmu kuma nufinku ku kange mu daga abin da iyãyenmu suka kasance sunã bautãwa sai ku zo mana da dalĩli mabayyani." قَالَتْ رُسُلُهُمْ أَفِي اللَّهِ شَكّ ٌ فَاطِرِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۖ  يَدْعُوكُمْ لِيَغْفِرَ لَكُمْ مِنْ ذُنُوبِكُمْ وَيُؤَخِّرَكُمْ إِلَى أَجَل ٍ مُسَمّى ً  ۚ  قَالُوا إِنْ أَنْتُمْ إِلاَّ بَشَر ٌ مِثْلُنَا تُرِيدُونَ أَنْ تَصُدُّونَا عَمَّا كَانَ يَعْبُدُ آبَاؤُنَا فَأْتُونَا بِسُلْطَان ٍ مُبِين ٍ
Qālat Lahum Rusuluhum 'In Naĥnu 'Illā Basharun Mithlukum Wa Lakinna Al-Laha Yamunnu `Alá Man Yashā'u Min `Ibādihi  ۖ  Wa Mā Kāna Lanā 'An Na'tiyakum Bisulţānin 'Illā Bi'idhni Al-Lahi  ۚ  Wa `Alá Al-Lahi Falyatawakkali Al-Mu'uminūna َ014-011 Manzanninsu suka ce musu, "Bã mu zama ba fãce mutãne misã, linku, kuma amma Allah Yanã yin falala a kan wanda Yake so daga bãyinsa, kuma bã ya kasancẽwa a gare mu, mu zo muku da wani dalĩli fãce da iznin Allah. Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara. قَالَتْ لَهُمْ رُسُلُهُمْ إِنْ نَحْنُ إِلاَّ بَشَر ٌ مِثْلُكُمْ وَلَكِنَّ اللَّهَ يَمُنُّ عَلَى مَنْ يَشَاءُ مِنْ عِبَادِه ِِ  ۖ  وَمَا كَانَ لَنَا أَنْ نَأْتِيَكُمْ بِسُلْطَان ٍ إِلاَّ بِإِذْنِ اللَّهِ  ۚ  وَعَلَى اللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ
Wa Mā Lanā 'Allā Natawakkala `Alá Al-Lahi Wa Qad Hadānā Subulanā  ۚ  Wa Lanaşbiranna `Alá Mā 'Ādhaytumūnā  ۚ  Wa `Alá Al-Lahi Falyatawakkali Al-Mutawakkilūna َ014-012 "Kuma mẽne ne a gare mu, bã zã mu dõgara ga Allah ba, alhãli kuwa haƙĩƙa Yã shiryar da mu ga hanyõyinmu? Kuma lalle ne munã yin haƙuri a kan abin da kuka cũtar da mu, kuma ga Allah sai mãsu dõgaro su dõgara." وَمَا لَنَا أَلاَّ نَتَوَكَّلَ عَلَى اللَّهِ وَقَدْ هَدَانَا سُبُلَنَا  ۚ  وَلَنَصْبِرَنَّ عَلَى مَا آذَيْتُمُونَا  ۚ  وَعَلَى اللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُتَوَكِّلُونَ
Wa Qāla Al-Ladhīna Kafarū Lirusulihim Lanukhrijannakum Min 'Arđinā 'Aw Lata`ūdunna Fī Millatinā  ۖ  Fa'awĥá 'Ilayhim Rabbuhum Lanuhlikanna Až-Žālimīna َ014-013 Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa Manzanninsu, "Lalle ne munã fitar da ku daga ƙasarmu, kõ kuwa haƙĩƙa, kunã kõmowã acikin addininmu." Sai Ubangijinsu Ya yi wahayi zuwa gare su, "Lalle ne, Munã halakar da azzãlumai." وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِرُسُلِهِمْ لَنُخْرِجَنَّكُمْ مِنْ أَرْضِنَا أَوْ لَتَعُودُنَّ فِي مِلَّتِنَا  ۖ  فَأَوْحَى إِلَيْهِمْ رَبُّهُمْ لَنُهْلِكَنَّ الظَّالِمِينَ
Wa Lanuskinannakumu Al-'Arđa Min Ba`dihim  ۚ  Dhālika Liman Khāfa Maqāmī Wa Khāfa Wa`īdi َ014-014 Kuma haƙĩƙa, Munã zaunar da ku ga ƙasa a bãyansu. Wancan ne abin gargaɗi ga wanda ya ji tsõron matsayiNa, kuma ya ji tsõron ƙyacẽwãTa. وَلَنُسْكِنَنَّكُمُ الأَرْضَ مِنْ بَعْدِهِمْ  ۚ  ذَلِكَ لِمَنْ خَافَ مَقَامِي وَخَافَ وَعِيدِ
Wa Astaftaĥū Wa Khāba Kullu Jabbārin `Anīdin َ014-015 Kuma suka yi addu'ar alfãnu. Kuma kõwane kangararre mai tsaurin kai ya tãɓe. وَاسْتَفْتَحُوا وَخَابَ كُلُّ جَبَّارٍ عَنِيد ٍ
Min Warā'ihi Jahannamu Wa Yusqá Min Mā'in Şadīdin َ014-016 Daga bãyansa akwai Jahannama, kuma anã shãyar da shi daga wani ruwa, surkin jini. مِنْ وَرَائِه ِِ جَهَنَّمُ وَيُسْقَى مِنْ مَاء ٍ صَدِيد ٍ
Yatajarra`uhu Wa Lā Yakādu Yusīghuhu Wa Ya'tīhi Al-Mawtu Min Kulli Makānin Wa Mā Huwa Bimayyitin  ۖ  Wa Min Warā'ihi `Adhābun Ghalīžun َ014-017 Yanã kwankwaɗarsa, kuma bã ya jin sauƙin haɗiyarsa, kuma mutuwa ta jẽ masa daga kõwane wuri kuma bai zama mai mutuwa ba, kuma daga bãyansa akwai azãba mai kauri. يَتَجَرَّعُه ُُ وَلاَ يَكَادُ يُسِيغُه ُُ وَيَأْتِيهِ الْمَوْتُ مِنْ كُلِّ مَكَان ٍ وَمَا هُوَ بِمَيِّت ٍ  ۖ  وَمِنْ وَرَائِه ِِ عَذَابٌ غَلِيظ ٌ
Mathalu Al-Ladhīna Kafarū Birabbihim  ۖ  'A`māluhum Karamādin Ashtaddat Bihi Ar-Rīĥu Fī Yawmin `Āşifin  ۖ  Lā Yaqdirūna Mimmā Kasabū `Alá Shay'in  ۚ  Dhālika Huwa Ađ-Đalālu Al-Ba`īdu َ014-018 Misãlin waɗanda suka kãfirta da Ubangijinsu, ayyukansu sun yi kama da tõka wadda iska ta yi tsananin bugãwa da ita a cikin yini mai gũguwa. Ba su iya amfãni daga abin da suka yi tsirfa a kan kõme.Wancan ita ce ɓata mai nĩsa. مَثَلُ الَّذِينَ كَفَرُوا بِرَبِّهِمْ  ۖ  أَعْمَالُهُمْ كَرَمَاد ٍ اشْتَدَّتْ بِهِ الرِّيحُ فِي يَوْمٍ عَاصِف ٍ  ۖ  لاَ يَقْدِرُونَ مِمَّا كَسَبُوا عَلَى شَيْء ٍ  ۚ  ذَلِكَ هُوَ الضَّلاَلُ الْبَعِيدُ
'Alam Tará 'Anna Al-Laha Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Bil-Ĥaqqi  ۚ  'In Yasha' Yudh/hibkum Wa Ya'ti Bikhalqin Jadīdin َ014-019 Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle ne Allah Yã halicci sammai bakwai da ƙasa da mallakarSa. Idan Yã so zai tafiyar da ku, kuma Ya zo da wata halitta sãbuwa. أَلَمْ تَرَى أَنَّ اللَّهَ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ بِالْحَقِّ  ۚ  إِنْ يَشَأْ يُذْهِبْكُمْ وَيَأْتِ بِخَلْق ٍ جَدِيد ٍ
Wa Mā Dhālika `Alá Al-Lahi Bi`azīzin َ014-020 Kuma wancan bai zama mabuwãyi ba ga Allah. وَمَا ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ بِعَزِيز ٍ
Wa Barazū Lillahi Jamī`āan Faqāla Ađ-Đu`afā'u Lilladhīna Astakbarū 'Innā Kunnā Lakum Taba`āan Fahal 'Antum Mughnūna `Annā Min `Adhābi Al-Lahi Min Shay'in  ۚ  Qālū Law Hadānā Al-Lahu Lahadaynākum  ۖ  Sawā'un `Alaynā 'Ajazi`nā 'Am Şabarnā Mā Lanā Min Maĥīşin َ014-021 Kuma suka bayyana ga Allah gabã daya, sai mãsu rauni suka ce wa waɗanda suka kangara, "Lalle ne mũ, mun kasance mãsu bi a gare ku, to, shin, kũ mãsu kãrewa ga barinmu ne daga azãbar Allah daga wani abu?" Suka ce: "Dã Allah Ya shiryar da mu, dã mun shiryar da ku, daidai ne a kanmu, mun yi rãki ko mun yi haƙuri ba mu da wata mafaka." وَبَرَزُوا لِلَّهِ جَمِيعا ً فَقَالَ الضُّعَفَاءُ لِلَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا إِنَّا كُنَّا لَكُمْ تَبَعا ً فَهَلْ أَنْتُمْ مُغْنُونَ عَنَّا مِنْ عَذَابِ اللَّهِ مِنْ شَيْء ٍ  ۚ  قَالُوا لَوْ هَدَانَا اللَّهُ لَهَدَيْنَاكُمْ  ۖ  سَوَاءٌ عَلَيْنَا أَجَزِعْنَا أَمْ صَبَرْنَا مَا لَنَا مِنْ مَحِيص ٍ
Wa Qāla Ash-Shayţānu Lammā Quđiya Al-'Amru 'Inna Al-Laha Wa`adakum Wa`da Al-Ĥaqqi Wa Wa`adtukum Fa'akhlaftukum  ۖ  Wa Mā Kāna Lī `Alaykum Min Sulţānin 'Illā 'An Da`awtukum Fāstajabtum Lī  ۖ  Falā Talūmūnī Wa Lūmū 'Anfusakum  ۖ  Mā 'Anā Bimuşrikhikum Wa Mā 'Antum Bimuşrikhīya  ۖ  'Innī Kafartu Bimā 'Ashraktumūnī Min Qablu  ۗ  'Inna Až-Žālimīna Lahum `Adhābun 'Alīmun َ014-022 Kuma Shaiɗan ya ce a lõkacin da aka ƙãre al'amarin, "Lalle ne Allah Ya yi muku wa'adi, wa'adin gaskiyã, kuma na yi muku wa'adi, sa'an nan na sãɓã muku. Kuma bãbu wani dalĩli a gare ni a kanku fãce na kirã ku, sa'an nan kun karɓã mini. Sabõda haka kada ku zarge ni, kuma ku zargi kanku. Ban zama mai amfaninku ba, kuma ba ku zama mãsu amfãnĩna ba. Lalle na barranta da abin da kuka haɗã ni da shi gabanin wannan(matsayi). Lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi." وَقَالَ الشَّيْطَانُ لَمَّا قُضِيَ الأَمْرُ إِنَّ اللَّهَ وَعَدَكُمْ وَعْدَ الْحَقِّ وَوَعَدْتُكُمْ فَأَخْلَفْتُكُمْ  ۖ  وَمَا كَانَ لِي عَلَيْكُمْ مِنْ سُلْطَان ٍ إِلاَّ أَنْ دَعَوْتُكُمْ فَاسْتَجَبْتُمْ لِي  ۖ  فَلاَ تَلُومُونِي وَلُومُوا أَنْفُسَكُمْ  ۖ  مَا أَنَا بِمُصْرِخِكُمْ وَمَا أَنْتُمْ بِمُصْرِخِيَّ  ۖ  إِنِّي كَفَرْتُ بِمَا أَشْرَكْتُمُونِي مِنْ قَبْلُ  ۗ  إِنَّ الظَّالِمِينَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيم ٌ
Wa 'Udkhila Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā Bi'idhni Rabbihim  ۖ  Taĥīyatuhum Fīhā Salāmun َ014-023 Kuma aka shigar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, a gidãjen Aljanna, kõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwamã a cikinsu da iznin Ubangijinsu, gaisuwarsu a cikinta "Salãm",(wãtau Aminci). وَأُدْخِلَ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ جَنَّات ٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا بِإِذْنِ رَبِّهِمْ  ۖ  تَحِيَّتُهُمْ فِيهَا سَلاَم ٌ
'Alam Tará Kayfa Đaraba Al-Lahu Mathalāan Kalimatan Ţayyibatan Kashajaratin Ţayyibatin 'Aşluhā Thābitun Wa Far`uhā Fī As-Samā'i َ014-024 Shin, ba ka ganĩ ba, yadda Allah Ya buga wani mĩsali, kalma mai kyau kamar itãciya ce mai kyau, asalinta yanã tabbatacce, kuma rẽshenta yanã cikin sama? أَلَمْ تَرَى كَيْفَ ضَرَبَ اللَّهُ مَثَلا ً كَلِمَة ً طَيِّبَة ً كَشَجَرَة ٍ طَيِّبَةٍ أَصْلُهَا ثَابِت ٌ وَفَرْعُهَا فِي السَّمَاءِ
Tu'utī 'Ukulahā Kulla Ĥīnin Bi'idhni Rabbihā  ۗ  Wa Yađribu Al-Lahu Al-'Amthāla Lilnnāsi La`allahum Yatadhakkarūna َ014-025 Tanã bãyar da abincinta a kõwane lõkaci da iznin Ubangijinta! Kuma Allah Yanã buga misãli ga mutãne, mai yiwuwã ne, sunã tunãwa. تُؤْتِي أُكُلَهَا كُلَّ حِين ٍ بِإِذْنِ رَبِّهَا  ۗ  وَيَضْرِبُ اللَّهُ الأَمْثَالَ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
Wa Mathalu Kalimatin Khabīthatin Kashajaratin Khabīthatin Ajtuththat Min Fawqi Al-'Arđi Mā Lahā Min Qarārin َ014-026 Kuma misalin kalma mummũnã kamar itãciya mummũnã ce, an tumɓuke ta daga bisa ga ƙasa, bã ta da wata tabbata. وَمَثَلُ كَلِمَةٍ خَبِيثَة ٍ كَشَجَرَةٍ خَبِيثَة ٍ اجْتُثَّتْ مِنْ فَوْقِ الأَرْضِ مَا لَهَا مِنْ قَرَار ٍ
Yuthabbitu Al-Lahu Al-Ladhīna 'Āmanū Bil-Qawli Ath-Thābiti Fī Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Wa Fī Al-'Ākhirati  ۖ  Wa Yuđillu Al-Lahu Až-Žālimīna  ۚ  Wa Yaf`alu Al-Lahu Mā Yashā'u َ014-027 Allah Yanã tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni da magana tabbatacciya a cikin rãyuwar dũniya, da cikin Lãhira, Kuma Allah Yanã ɓatar da azzãlumai, kuma Allah Yanã aikata abin da Yake so. يُثَبِّتُ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا بِالْقَوْلِ الثَّابِتِ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَفِي الآخِرَةِ  ۖ  وَيُضِلُّ اللَّهُ الظَّالِمِينَ  ۚ  وَيَفْعَلُ اللَّهُ مَا يَشَاءُ
'Alam Tará 'Ilá Al-Ladhīna Baddalū Ni`mata Al-Lahi Kufrāan Wa 'Aĥallū Qawmahum Dāra Al-Bawāri َ014-028 Shin ba ka lura ba da waɗanda suka musanya ni'imar Allah da kãfirci kuma suka saukar da mutãnensu a gidan halakã? أَلَمْ تَرَى إِلَى الَّذِينَ بَدَّلُوا نِعْمَةَ اللَّهِ كُفْرا ً وَأَحَلُّوا قَوْمَهُمْ دَارَ الْبَوَارِ
Jahannama Yaşlawnahā  ۖ  Wa Bi'sa Al-Qarāru َ014-029 Sunã ƙõnuwa a wutar jahannama, kuma tir da matabbatarsu. جَهَنَّمَ يَصْلَوْنَهَا  ۖ  وَبِئْسَ الْقَرَارُ
Wa Ja`alū Lillahi 'Andādāan Liyuđillū `An Sabīlihi  ۗ  Qul Tamatta`ū Fa'inna Maşīrakum 'Ilá An-Nāri َ014-030 Kuma suka sanya wa Allah kĩshiyõyi, dõmin ɓatarwa daga hanyarSa, Ka ce: "Ku ji dãɗi, sa'an nan, lalle ne, makõmarku Wutar ce." وَجَعَلُوا لِلَّهِ أَندَادا ً لِيُضِلُّوا عَنْ سَبِيلِه ِِ  ۗ  قُلْ تَمَتَّعُوا فَإِنَّ مَصِيرَكُمْ إِلَى النَّارِ
Qul Li`ibādiya Al-Ladhīna 'Āmanū Yuqīmū Aş-Şalāata Wa Yunfiqū Mimmā Razaqnāhum Sirrāan Wa `Alāniyatan Min Qabli 'An Ya'tiya Yawmun Lā Bay`un Fīhi Wa Lā Khilālun َ014-031 Ka ce wa bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni su tsayar da salla kuma su ciyar daga abin da Muka azurtã su,a asirce da bayyane, daga gabãnin wani wuni ya zo, bãbu ciniki a ciki, kuma bãbu abõtaka. قُلْ لِعِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا يُقِيمُوا الصَّلاَةَ وَيُنفِقُوا مِمَّا رَزَقْنَاهُمْ سِرّا ً وَعَلاَنِيَة ً مِنْ قَبْلِ أَنْ يَأْتِيَ يَوْم ٌ لاَ بَيْع ٌ فِيه ِِ وَلاَ خِلاَل ٌ
Al-Lahu Al-Ladhī Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Wa 'Anzala Mina As-Samā'i Mā'an Fa'akhraja Bihi Mina Ath-Thamarāti Rizqāan Lakum  ۖ  Wa Sakhkhara Lakumu Al-Fulka Litajriya Fī Al-Baĥri Bi'amrihi  ۖ  Wa Sakhkhara Lakumu Al-'Anhāra َ014-032 Allah ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar game da shi, daga 'ya'yan itãce arziki dõminku kuma Ya hõrẽ jirgin ruwa dõmin ya yi gudu a cikin tẽku da umurninSa, kuma Ya hõrẽ muku kõguna. اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَأَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاء ً فَأَخْرَجَ بِه ِِ مِنَ الثَّمَرَاتِ رِزْقا ً لَكُمْ  ۖ  وَسَخَّرَ لَكُمُ الْفُلْكَ لِتَجْرِيَ فِي الْبَحْرِ بِأَمْرِه ِِ  ۖ  وَسَخَّرَ لَكُمُ الأَنهَارَ
Wa Sakhkhara Lakumu Ash-Shamsa Wa Al-Qamara Dā'ibayni  ۖ  Wa Sakhkhara Lakumu Al-Layla Wa An-Nahār َ014-033 Kuma Ya hõrẽ muku rãnã da watã sunã madawwama biyu, kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni. وَسَخَّرَ لَكُمُ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ دَائِبَيْنِ  ۖ  وَسَخَّرَ لَكُمُ اللَّيْلَ وَالنَّهَار
Wa 'Ātākum Min Kulli Mā Sa'altumūhu  ۚ  Wa 'In Ta`uddū Ni`mata Al-Lahi Lā Tuĥşūhā  ۗ  'Inna Al-'Insāna Lažalūmun Kaffārun َ014-034 Kuma Ya bã ku dukkan abin da kuka rõƙe Shi kuma idan kun ƙidaya, ni'imar Allah bã zã ku lissafe ta ba. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan zãlunci ne, mai yawan kãfirci. وَآتَاكُمْ مِنْ كُلِّ مَا سَأَلْتُمُوه ُُ  ۚ  وَإِنْ تَعُدُّوا نِعْمَةَ اللَّهِ لاَ تُحْصُوهَا  ۗ  إِنَّ الإِنسَانَ لَظَلُوم ٌ كَفَّار ٌ
Wa 'Idh Qāla 'Ibrāhīmu Rabbi Aj`al Hādhā Al-Balada 'Āmināan Wa Ajnubnī Wa Banīya 'An Na`buda Al-'Aşnāma َ014-035 Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanyã wannan gari amintacce kuma Ka nĩsanta ni, nĩ da ɗiyãna daga bauta wa gumãka. وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ رَبِّ اجْعَلْ هَذَا الْبَلَدَ آمِنا ً وَاجْنُبْنِي وَبَنِيَّ أَنْ نَعْبُدَ الأَصْنَامَ
Rabbi 'Innahunna 'Ađlalna Kathīrāan Mina An-Nāsi  ۖ  Faman Tabi`anī Fa'innahu Minnī  ۖ  Wa Man `Aşānī Fa'innaka Ghafūrun Raĥīmun َ014-036 "Yã Ubangijina! Lalle ne sũ, sun ɓatar da mãsu yawa daga mutãne sa'an nan wanda ya bĩ ni, to,lalle shi, yanã daga gare ni, kuma wanda ya sãɓa mini, to, lalle ne Kai Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. رَبِّ إِنَّهُنَّ أَضْلَلْنَ كَثِيرا ً مِنَ النَّاسِ  ۖ  فَمَنْ تَبِعَنِي فَإِنَّه ُُ مِنِّي  ۖ  وَمَنْ عَصَانِي فَإِنَّكَ غَفُور ٌ رَحِيم ٌ
Rabbanā 'Innī 'Askantu Min Dhurrīyatī Biwādin Ghayri Dhī Zar`in `Inda Baytika Al-Muĥarrami Rabbanā Liyuqīmū Aş-Şalāata Fāj`al 'Af'idatan Mina An-Nāsi Tahwī 'Ilayhim Wa Arzuqhum Mina Ath-Thamarāti La`allahum Yashkurūna َ014-037 "Yã Ubangijinmu! Lalle ne ni, na zaunar da zuriyata ga rãfi wanda ba ma'abũcin shũka ba, a wurin ¦ãkinka mai alfarma. Yã Ubangijinmu! Dõmin su tsayar da salla. Sai Ka sanya zukãta daga mutãne sunã gaggãwar bẽgenzuwa gare su, kuma ka azurtã su daga 'ya'yan itãce, mai yiwuwã ne sunã gõdẽwã." رَبَّنَا إِنِّي أَسْكَنتُ مِنْ ذُرِّيَّتِي بِوَادٍ غَيْرِ ذِي زَرْعٍ عِنْدَ بَيْتِكَ الْمُحَرَّمِ رَبَّنَا لِيُقِيمُوا الصَّلاَةَ فَاجْعَلْ أَفْئِدَة ً مِنَ النَّاسِ تَهْوِي إِلَيْهِمْ وَارْزُقْهُمْ مِنَ الثَّمَرَاتِ لَعَلَّهُمْ يَشْكُرُونَ
Rabbanā 'Innaka Ta`lamu Mā Nukhfī Wa Mā Nu`linu  ۗ  Wa Mā Yakhfá `Alá Al-Lahi Min Shay'in Al-'Arđi Wa Lā Fī As-Samā'i َ014-038 "Yã Ubangijinmu! Lalle ne Kai Kanã sanin abin da muke ɓõyẽwa, da abin da muke bayyanãwa. Kuma bãbu abin da yake ɓõyẽwa ga A1lah, daga wani abu a cikin ƙasa, kuma bãbu a cikin sama." رَبَّنَا إِنَّكَ تَعْلَمُ مَا نُخْفِي وَمَا نُعْلِنُ  ۗ  وَمَا يَخْفَى عَلَى اللَّهِ مِنْ شَيْء ٍ فِي الأَرْضِ وَلاَ فِي السَّمَاءِ
Al-Ĥamdu Lillahi Al-Ladhī Wahaba Lī `Alá Al-Kibari 'Ismā`īla Wa 'Isĥāqa  ۚ  'Inna Rabbī Lasamī`u Ad-Du`ā'i َ014-039 "Gõdiyã ta tabbata ga Allah wanda Yake Ya bã ni inã a cikin tsufa Ismã'ila da Is'hãƙa. Lalle ne Ubangijina, haƙĩƙa, Mai jin addu'a ne." الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي وَهَبَ لِي عَلَى الْكِبَرِ إِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ  ۚ  إِنَّ رَبِّي لَسَمِيعُ الدُّعَاءِ
Rabbi Aj`alnī Muqīma Aş-Şalāati Wa Min Dhurrīyatī  ۚ  Rabbanā Wa Taqabbal Du`ā'i َ014-040 "Yã Ubangijina! Ka sanyã ni mai tsayar da salla. Kuma daga zũriyyata. Yã Ubangijinmu! Kuma Ka karɓi addu'ata." رَبِّ اجْعَلْنِي مُقِيمَ الصَّلاَةِ وَمِنْ ذُرِّيَّتِي  ۚ  رَبَّنَا وَتَقَبَّلْ دُعَاءِ
Rabbanā Aghfir Lī Wa Liwālidayya Wa Lilmu'uminīna Yawma Yaqūmu Al-Ĥisābu َ014-041 "Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara gare ni, kuma ga mahaifãna, kuma da mũminai, a rãnar da hisãbi yake tsayãwa." رَبَّنَا اغْفِرْ لِي وَلِوَالِدَيَّ وَلِلْمُؤْمِنِينَ يَوْمَ يَقُومُ الْحِسَابُ
Wa Lā Taĥsabanna Al-Laha Ghāfilāan `Ammā Ya`malu Až-Žālimūna  ۚ  'Innamā Yu'uakhkhiruhum Liyawmin Tashkhaşu Fīhi Al-'Abşāru َ014-042 "Kuma kada ka yi zaton Allah Mai shagalã ne daga abin da azzalumai suke aikatãwã. Abin sani kawai, Yanã jinkirta musu ne zuwa ga wani wuni, wanda idãnuwa suke fita turu- turu a cikinsa." وَلاَ تَحْسَبَنَّ اللَّهَ غَافِلاً عَمَّا يَعْمَلُ الظَّالِمُونَ  ۚ  إِنَّمَا يُؤَخِّرُهُمْ لِيَوْم ٍ تَشْخَصُ فِيهِ الأَبْصَارُ
Muhţi`īna Muqni`ī Ru'ūsihim Lā Yartaddu 'Ilayhim Ţarfuhum  ۖ  Wa 'Af'idatuhum Hawā'un َ014-043 "Sunã mãsu gaggãwa, mãsu ɗaukaka kãwunansu zuwa sama ƙiftawar ganinsu ba ta kõmãwa gare su. Kuma zukãtansu wõfintattu." مُهْطِعِينَ مُقْنِعِي رُءُوسِهِمْ لاَ يَرْتَدُّ إِلَيْهِمْ طَرْفُهُمْ  ۖ  وَأَفْئِدَتُهُمْ هَوَاء ٌ
Wa 'Andhiri An-Nāsa Yawma Ya'tīhimu Al-`Adhābu Fayaqūlu Al-Ladhīna Žalamū Rabbanā 'Akhkhirnā 'Ilá 'Ajalin Qarībin Nujib Da`wataka Wa Nattabi`i Ar-Rusula  ۗ  'Awalam Takūnū 'Aqsamtum Min Qablu Mā Lakum Min Zawālin َ014-044 Kuma ka yi gargaɗi ga mutãne ga rãnar da azãba take jẽ musu, sai waɗanda suka yi zãlunci su ce: "Yã Ubangijinmu! Ka yi mana jinkiri zuwa ga wani ajali makusanci, mu karɓa wa kiranKa, kuma mu bi Manzanni."(Allah Ya ce musu) "Ashe, ba ku kasance kun yi rantsuwã ba daga gabãni, cẽwa bã ku da wata gushẽwa? وَأَنذِرِ النَّاسَ يَوْمَ يَأْتِيهِمُ الْعَذَابُ فَيَقُولُ الَّذِينَ ظَلَمُوا رَبَّنَا أَخِّرْنَا إِلَى أَجَل ٍ قَرِيب ٍ نُجِبْ دَعْوَتَكَ وَنَتَّبِعِ الرُّسُلَ  ۗ  أَوَلَمْ تَكُونُوا أَقْسَمْتُمْ مِنْ قَبْلُ مَا لَكُمْ مِنْ زَوَال ٍ
Wa Sakantum Fī Masākini Al-Ladhīna Žalamū 'Anfusahum Wa Tabayyana Lakum Kayfa Fa`alnā Bihim Wa Đarabnā Lakumu Al-'Amthāla َ014-045 "Kuma kuka zaunã a cikin gidãjen waɗanda suka zãlunci kansu, kuma ya bayyana a gare ku yadda Muka aikatã game da su, kuma Muka buga muku misãlai." وَسَكَنتُمْ فِي مَسَاكِنِ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَنفُسَهُمْ وَتَبَيَّنَ لَكُمْ كَيْفَ فَعَلْنَا بِهِمْ وَضَرَبْنَا لَكُمُ الأَمْثَالَ
Wa Qad Makarū Makrahum Wa `Inda Al-Lahi Makruhum Wa 'In Kāna Makruhum Litazūla Minhu Al-Jibālu َ014-046 Kuma lalle sun yi mãkirci irin makircinSu kuma a wurin Allah makircinsu, yake, kuma lalle ne makircinsu yã kasance, haƙĩƙa, duwãtsu sunã gushẽwã sabõda shi. وَقَدْ مَكَرُوا مَكْرَهُمْ وَعِنْدَ اللَّهِ مَكْرُهُمْ وَإِنْ كَانَ مَكْرُهُمْ لِتَزُولَ مِنْهُ الْجِبَالُ
Falā Taĥsabanna Al-Laha Mukhlifa Wa`dihi Rusulahu  ۗ  'Inna Al-Laha `Azīzun Dhū Antiqāmin َ014-047 Sabõda haka, kada ka ƙarfafa zaton Allah Mai sãɓa wa'adinSa ne ga ManzanninSa. Lalle ne Allah ne Mabuwãyi, Ma'abũcin azãbar rãmuwa. فَلاَ تَحْسَبَنَّ اللَّهَ مُخْلِفَ وَعْدِه ِِ رُسُلَهُ~ُ  ۗ  إِنَّ اللَّهَ عَزِيز ٌ ذُو انتِقَام ٍ
Yawma Tubaddalu Al-'Arđu Ghayra Al-'Arđi Wa As-Samāwātu  ۖ  Wa Barazū Lillahi Al-Wāĥidi Al-Qahhāri َ014-048 A rãnar da ake musanya ƙasa bã ƙasar nan ba, da sammai kuma su bayyana ga Allah Makaɗaici, Mai tanƙwasãwa. يَوْمَ تُبَدَّلُ الأَرْضُ غَيْرَ الأَرْضِ وَالسَّمَاوَاتُ  ۖ  وَبَرَزُوا لِلَّهِ الْوَاحِدِ الْقَهَّارِ
Wa Tará Al-Mujrimīna Yawma'idhin Muqarranīna Fī Al-'Aşfādi َ014-049 Kuma kana ganin mãsu laifi, a rãnar nan, sunã waɗanda aka yi wa ciri daidai a cikin marũruwa. وَتَرَى الْمُجْرِمِينَ يَوْمَئِذ ٍ مُقَرَّنِينَ فِي الأَصْفَادِ
Sarābīluhum Min Qaţirānin Wa Taghshá Wujūhahumu An-Nāru َ014-050 Rigunansu daga farar wutã ne, kuma wuta ta rufe fuskõkinsu. سَرَابِيلُهُمْ مِنْ قَطِرَان ٍ وَتَغْشَى وُجُوهَهُمُ النَّارُ
Liyajziya Al-Lahu Kulla Nafsin Mā Kasabat  ۚ  'Inna Al-Laha Sarī`u Al-Ĥisābi َ014-051 Dõmin Allah Ya sãkã wa kõwane rai da abin da ya tsuwurwurta. Lalle ne, Allah Mai gaggãwar hisãbi ne. لِيَجْزِيَ اللَّهُ كُلَّ نَفْس ٍ مَا كَسَبَتْ  ۚ  إِنَّ اللَّهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ
dhā Balāghun Lilnnāsi Wa Liyundharū Bihi Wa Liya`lamū 'Annamā Huwa 'Ilahun Wāĥidun Wa Liyadhdhakkara 'Ū Al-'Albābi َ014-052 Wannan iyarwa ce ga mutãne, kuma dõmin a yi musu gargaɗi da shi, kuma dõmin su sani cẽwa, abin sani kawai, shĩ ne abin bautawa guda. Kuma dõmin masu hankali su riƙa tunãwa. هَذَا بَلاَغ ٌ لِلنَّاسِ وَلِيُنذَرُوا بِه ِِ وَلِيَعْلَمُوا أَنَّمَا هُوَ إِلَه ٌ ٌ وَاحِد ٌ وَلِيَذَّكَّرَ أُوْلُوا الأَلْبَابِ
Next Sūrah