15) Sūrat Al-Ĥijr

Printed format

15) سُورَة الحِجر

'Alif-Lām-Rā Tilka 'Āyātu Al-Kitābi Wa Qur'ānin Mubīnin َ015-001 A. L̃. R. Waɗancan ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa. أَلِف-لَام-رَا تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ وَقُرْآن ٍ  ۚ  مُبِين ٍ
Rubamā Yawaddu Al-Ladhīna Kafarū Law Kānū Muslimīna َ015-002 Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi. رُبَمَا يَوَدُّ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْ كَانُوا مُسْلِمِينَ
Dharhum Ya'kulū Wa Yatamatta`ū Wa Yulhihimu Al-'Amalu  ۖ  Fasawfa Ya`lamūna َ015-003 Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani. ذَرْهُمْ يَأْكُلُوا وَيَتَمَتَّعُوا وَيُلْهِهِمُ الأَمَلُ  ۖ  فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ
Wa Mā 'Ahlaknā Min Qaryatin 'Illā Wa Lahā Kitābun Ma`lūmun َ015-004 Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne. وَمَا أَهْلَكْنَا مِنْ قَرْيَة ٍ إِلاَّ وَلَهَا كِتَاب ٌ مَعْلُوم ٌ
Mā Tasbiqu Min 'Ummatin 'Ajalahā Wa Mā Yasta'khirūna َ015-005 Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba. مَا تَسْبِقُ مِنْ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسْتَأْخِرُونَ
Wa Qālū Yā 'Ayyuhā Al-Ladhī Nuzzila `Alayhi Adh-Dhikru 'Innaka Lamajnūnun َ015-006 Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne." وَقَالُوا يَا أَيُّهَا الَّذِي نُزِّلَ عَلَيْهِ الذِّكْرُ إِنَّكَ لَمَجْنُون ٌ
Law Mā Ta'tīnā Bil-Malā'ikati 'In Kunta Mina Aş-Şādiqīna َ015-007 "Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?" لَوْ مَا تَأْتِينَا بِالْمَلاَئِكَةِ إِنْ كُنْتَ مِنَ الصَّادِقِينَ
Mā Nunazzilu Al-Malā'ikata 'Illā Bil-Ĥaqqi Wa Mā Kānū 'Idhāan Munžarīna َ015-008 Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya, bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba. مَا نُنَزِّلُ الْمَلاَئِكَةَ إِلاَّ بِالْحَقِّ وَمَا كَانُوا إِذا ً مُنْظَرِينَ
'Innā Naĥnu Nazzalnā Adh-Dhikra Wa 'Innā Lahu Laĥāfižūna َ015-009 Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lal1e Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi. إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا الذِّكْرَ وَإِنَّا لَه ُُ لَحَافِظُونَ
Wa Laqad 'Arsalnā Min Qablika Fī Shiya`i Al-'Awwalīna َ015-010 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãninka. وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ فِي شِيَعِ الأَوَّلِينَ
Wa Mā Ya'tīhim Min Rasūlin 'Illā Kānū Bihi Yastahzi'ūna َ015-011 Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi. وَمَا يَأْتِيهِمْ مِنْ رَسُول ٍ إِلاَّ كَانُوا بِه ِِ يَسْتَهْزِئُونَ
Kadhālika Naslukuhu Fī Qulūbi Al-Mujrimīna َ015-012 Kamar wancan ne Muke shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi. كَذَلِكَ نَسْلُكُه ُُ فِي قُلُوبِ الْمُجْرِمِينَ
Lā Yu'uminūna Bihi  ۖ  Wa Qad Khalat Sunnatu Al-'Awwalīna َ015-013 Bã su yin ĩmãni da shi, kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige. لاَ يُؤْمِنُونَ بِه ِِ  ۖ  وَقَدْ خَلَتْ سُنَّةُ الأَوَّلِينَ
Wa Law Fataĥnā `Alayhim Bābāan Mina As-Samā'i Fažallū Fīhi Ya`rujūna َ015-014 Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa. وَلَوْ فَتَحْنَا عَلَيْهِمْ بَابا ً مِنَ السَّمَاءِ فَظَلُّوا فِيه ِِ يَعْرُجُونَ
Laqālū 'Innamā Sukkirat 'Abşārunā Bal Naĥnu Qawmun Masĥūrūna َ015-015 Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce." لَقَالُوا إِنَّمَا سُكِّرَتْ أَبْصَارُنَا بَلْ نَحْنُ قَوْم ٌ مَسْحُورُونَ
Wa Laqad Ja`alnā Fī As-Samā'i Burūjāan Wa Zayyannāhā Lilnnāžirīna َ015-016 Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo. وَلَقَدْ جَعَلْنَا فِي السَّمَاءِ بُرُوجا ً وَزَيَّنَّاهَا لِلنَّاظِرِينَ
Wa Ĥafižnāhā Min Kulli Shayţānin Rajīmin َ015-017 Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa. وَحَفِظْنَاهَا مِنْ كُلِّ شَيْطَان ٍ رَجِيم ٍ
'Illā Mani Astaraqa As-Sam`a Fa'atba`ahu Shihābun Mubīnun َ015-018 Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi. إِلاَّ مَنِ اسْتَرَقَ السَّمْعَ فَأَتْبَعَه ُُ شِهَاب ٌ مُبِين ٌ
Wa Al-'Arđa Madadnāhā Wa 'Alqaynā Fīhā Rawāsiya Wa 'Anbatnā Fīhā Min Kulli Shay'in Mawzūnin َ015-019 Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli. وَالأَرْضَ مَدَدْنَاهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ وَأَنْبَتْنَا فِيهَا مِنْ كُلِّ شَيْء ٍ مَوْزُون ٍ
Wa Ja`alnā Lakum Fīhā Ma`āyisha Wa Man Lastum Lahu Birāziqīna َ015-020 Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba. وَجَعَلْنَا لَكُمْ فِيهَا مَعَايِشَ وَمَنْ لَسْتُمْ لَه ُُ بِرَازِقِينَ
Wa 'In Min Shay'in 'Illā `Indanā Khazā'inuhu Wa Mā Nunazziluhu 'Illā Biqadarin Ma`lūmin َ015-021 Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne. وَإِنْ مِنْ شَيْء ٍ إِلاَّ عِنْدَنَا خَزَائِنُه ُُ وَمَا نُنَزِّلُهُ~ُ إِلاَّ بِقَدَر ٍ مَعْلُوم ٍ
Wa 'Arsalnā Ar-Riyāĥa Lawāqiĥa Fa'anzalnā Mina As-Samā'i Mā'an Fa'asqaynākumūhu Wa Mā 'Antum Lahu Bikhāzinīna َ015-022 Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba. وَأَرْسَلْنَا الرِّيَاحَ لَوَاقِحَ فَأَنْزَلْنَا مِنَ السَّمَاءِ مَاء ً فَأَسْقَيْنَاكُمُوه ُُ وَمَا أَنْتُمْ لَه ُُ بِخَازِنِينَ
Wa 'Innā Lanaĥnu Nuĥyī Wa Numītu Wa Naĥnu Al-Wārithūna َ015-023 Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada. وَإِنَّا لَنَحْنُ نُحْيِي وَنُمِيتُ وَنَحْنُ الْوَارِثُونَ
Wa Laqad `Alim Al-Mustaqdimīna Minkum Wa Laqad `Alim Al-Musta'khirīna َ015-024 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri. وَلَقَدْ عَلِمْنَا الْمُسْتَقْدِمِينَ مِنْكُمْ وَلَقَدْ عَلِمْنَا الْمُسْتَأْخِرِينَ
Wa 'Inna Rabbaka Huwa Yaĥshuruhum  ۚ  'Innahu Ĥakīmun `Alīmun َ015-025 Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani. وَإِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَحْشُرُهُمْ  ۚ  إِنَّه ُُ حَكِيمٌ عَلِيم ٌ
Wa Laqad Khalaq Al-'Insāna Min Şalşālin Min Ĥama'iin Masnūnin َ015-026 Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja. وَلَقَدْ خَلَقْنَا الإِنسَانَ مِنْ صَلْصَال ٍ مِنْ حَمَإ ٍ مَسْنُون ٍ
Wa Al-Jānna Khalaqnāhu Min Qablu Min Nāri As-Samūmi َ015-027 Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar iskar zafi. وَالْجَانَّ خَلَقْنَاه ُُ مِنْ قَبْلُ مِنْ نَارِ السَّمُومِ
Wa 'Idh Qāla Rabbuka Lilmalā'ikati 'Innī Khāliqun Basharāan Min Şalşālin Min Ĥama'iin Masnūnin َ015-028 Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja." وَإِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلاَئِكَةِ إِنِّي خَالِق ٌ بَشَرا ً مِنْ صَلْصَال ٍ مِنْ حَمَإ ٍ مَسْنُون ٍ
Fa'idhā Sawwaytuhu Wa Nafakhtu Fīhi Min Rūĥī Faqa`ū Lahu Sājidīna َ015-029 "To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada." فَإِذَا سَوَّيْتُه ُُ وَنَفَخْتُ فِيه ِِ مِنْ رُوحِي فَقَعُوا لَه ُُ سَاجِدِينَ
Fasajada Al-Malā'ikatu Kulluhum 'Ajma`ūna َ015-030 Sai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya. فَسَجَدَ الْمَلاَئِكَةُ كُلُّهُمْ أَجْمَعُونَ
'Illā 'Iblīsa 'Abá 'An Yakūna Ma`a As-Sājidīna َ015-031 Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar. إِلاَّ إِبْلِيسَ أَبَى أَنْ يَكُونَ مَعَ السَّاجِدِينَ
Qāla Yā 'Iblīsu Mā Laka 'Allā Takūna Ma`a As-Sājidīna َ015-032 Ya ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?" قَالَ يَا إِبْلِيسُ مَا لَكَ أَلاَّ تَكُونَ مَعَ السَّاجِدِينَ
Qāla Lam 'Akun Li'sjuda Libasharin Khalaqtahu Min Şalşālin Min Ĥama'iin Masnūnin َ015-033 Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja." قَالَ لَمْ أَكُنْ لِأسْجُدَ لِبَشَرٍ خَلَقْتَه ُُ مِنْ صَلْصَال ٍ مِنْ حَمَإ ٍ مَسْنُون ٍ
Qāla Fākhruj Minhā Fa'innaka Rajīmun َ015-034 Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne." قَالَ فَاخْرُجْ مِنْهَا فَإِنَّكَ رَجِيم ٌ
Wa 'Inna `Alayka Al-La`nata 'Ilá Yawmi Ad-Dīni َ015-035 "Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako." وَإِنَّ عَلَيْكَ اللَّعْنَةَ إِلَى يَوْمِ الدِّينِ
Qāla Rabbi Fa'anžirnī 'Ilá Yawmi Yub`athūna َ015-036 Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su." قَالَ رَبِّ فَأَنْظِرْنِي إِلَى يَوْمِ يُبْعَثُونَ
Qāla Fa'innaka Mina Al-Munžarīna َ015-037 Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri." قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ الْمُنْظَرِينَ
'Ilá Yawmi Al-Waqti Al-Ma`lūmi َ015-038 "Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sananne." إِلَى يَوْمِ الْوَقْتِ الْمَعْلُومِ
Qāla Rabbi Bimā 'Aghwaytanī La'uzayyinanna Lahum Al-'Arđi Wa La'ughwiyannahum 'Ajma`īna َ015-039 Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya." قَالَ رَبِّ بِمَا أَغْوَيْتَنِي لَأُزَيِّنَنَّ لَهُمْ فِي الأَرْضِ وَلَأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ
'Illā `Ibādaka Minhumu Al-Mukhlaşīna َ015-040 "Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake." إِلاَّ عِبَادَكَ مِنْهُمُ الْمُخْلَصِينَ
Qāla Hādhā Şirāţun `Alayya Mustaqīmun َ015-041 Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici." قَالَ هَذَا صِرَاطٌ عَلَيَّ مُسْتَقِيم ٌ
'Inna `Ibādī Laysa Laka `Alayhim Sulţānun 'Illā Mani Attaba`aka Mina Al-Ghāwīna َ015-042 "Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu." إِنَّ عِبَادِي لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَان ٌ إِلاَّ مَنِ اتَّبَعَكَ مِنَ الْغَاوِينَ
Wa 'Inna Jahannama Lamaw`iduhum 'Ajma`īna َ015-043 Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'a1kawartarsu gabã ɗaya. وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمَوْعِدُهُمْ أَجْمَعِينَ
Lahā Sab`atu 'Abwābin Likulli Bābin Minhum Juz'un Maqsūmun َ015-044 Tanã da ƙõfõfi bakwai, ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe. لَهَا سَبْعَةُ أَبْوَاب ٍ لِكُلِّ بَاب ٍ مِنْهُمْ جُزْء ٌ مَقْسُوم ٌ
'Inna Al-Muttaqīna Fī Jannātin Wa `Uyūnin َ015-045 Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa. إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّات ٍ وَعُيُون ٍ
Adkhulūhā Bisalāmin 'Āminīna َ015-046 "Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu." ادْخُلُوهَا بِسَلاَم ٍ آمِنِينَ
Wa Naza`nā Mā Fī Şudūrihim Min Ghillin 'Ikhwānāan `Alá Sururin Mutaqābilīna َ015-047 Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã. وَنَزَعْنَا مَا فِي صُدُورِهِمْ مِنْ غِلّ ٍ إِخْوَاناً عَلَى سُرُر ٍ مُتَقَابِلِينَ
Lā Yamassuhum Fīhā Naşabun Wa Mā Hum Minhā Bimukhrajīna َ015-048 Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikinta ba. لاَ يَمَسُّهُمْ فِيهَا نَصَب ٌ وَمَا هُمْ مِنْهَا بِمُخْرَجِينَ
Nabbi' `Ibādī 'Annī 'Anā Al-Ghafūru Ar-Raĥīmu َ015-049 Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai. نَبِّئْ عِبَادِي أَنِّي أَنَا الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
Wa 'Anna `Adhābī Huwa Al-`Adhābu Al-'Alīmu َ015-050 Kuma azãbãTa ita ce azãba mai raɗaɗi. وَأَنَّ عَذَابِي هُوَ الْعَذَابُ الأَلِيمُ
Wa Nabbi'hum `An Đayfi 'Ibrāhīma َ015-051 Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm. وَنَبِّئْهُمْ عَنْ ضَيْفِ إِبْرَاهِيمَ
'Idh Dakhalū `Alayhi Faqālū Salāmāan Qāla 'Innā Minkum Wajilūna َ015-052 A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne." إِذْ دَخَلُوا عَلَيْهِ فَقَالُوا سَلاَما ً قَالَ إِنَّا مِنْكُمْ وَجِلُونَ
Qālū Lā Tawjal 'Innā Nubashshiruka Bighulāmin `Alīmin َ015-053 Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani." قَالُوا لاَ تَوْجَلْ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلاَمٍ عَلِيم ٍ
Qāla 'Abashshartumūnī `Alá 'An Massaniya Al-Kibaru Fabima Tubashshirūna َ015-054 Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?" قَالَ أَبَشَّرْتُمُونِي عَلَى أَنْ مَسَّنِيَ الْكِبَرُ فَبِمَ تُبَشِّرُونَ
Qālū Bashsharnāka Bil-Ĥaqqi Falā Takun Mina Al-Qāniţīna َ015-055 Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni." قَالُوا بَشَّرْنَاكَ بِالْحَقِّ فَلاَ تَكُنْ مِنَ الْقَانِطِينَ
Qāla Wa Man Yaqnaţu Min Raĥmati Rabbihi 'Illā Ađ-Đāllūna َ015-056 Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijinsa, fãce ɓatattu?" قَالَ وَمَنْ يَقْنَطُ مِنْ رَحْمَةِ رَبِّهِ~ِ إِلاَّ الضَّالُّونَ
Qāla Famā Khaţbukum 'Ayyuhā Al-Mursalūna َ015-057 Ya ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni!" قَالَ فَمَا خَطْبُكُمْ أَيُّهَا الْمُرْسَلُونَ
Qālū 'Innā 'Ursilnā 'Ilá Qawmin Mujrimīna َ015-058 Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi." قَالُوا إِنَّا أُرْسِلْنَا إِلَى قَوْم ٍ مُجْرِمِينَ
'Illā 'Āla Lūţin 'Innā Lamunajjūhum 'Ajma`īna َ015-059 "Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ,haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya." إِلاَّ آلَ لُوط ٍ إِنَّا لَمُنَجُّوهُمْ أَجْمَعِينَ
'Illā Amra'atahu Qaddarnā  ۙ  'Innahā Lamina Al-Ghābirīna َ015-060 "Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka." إِلاَّ امْرَأَتَه ُُ قَدَّرْنَا  ۙ  إِنَّهَا لَمِنَ الْغَابِرِينَ
Falammā Jā'a 'Āla Lūţin Al-Mursalūna َ015-061 To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu, فَلَمَّا جَاءَ آلَ لُوط ٍ الْمُرْسَلُونَ
Qāla 'Innakum Qawmun Munkarūna َ015-062 Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba." قَالَ إِنَّكُمْ قَوْم ٌ مُنْكَرُونَ
Qālū Bal Ji'nāka Bimā Kānū Fīhi Yamtarūna َ015-063 Suka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa." قَالُوا بَلْ جِئْنَاكَ بِمَا كَانُوا فِيه ِِ يَمْتَرُونَ
Wa 'Ataynāka Bil-Ĥaqqi Wa 'Innā Laşādiqūna َ015-064 "Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne." وَأَتَيْنَاكَ بِالْحَقِّ وَإِنَّا لَصَادِقُونَ
Fa'asri Bi'ahlika Biqiţ`in Mina Al-Layli Wa Attabi` 'Adbārahum Wa Lā Yaltafit Minkum 'Aĥadun Wa Amđū Ĥaythu Tu'umarūna َ015-065 "Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku." فَأَسْرِ بِأَهْلِكَ بِقِطْع ٍ مِنَ اللَّيْلِ وَاتَّبِعْ أَدْبَارَهُمْ وَلاَ يَلْتَفِتْ مِنْكُمْ أَحَد ٌ وَامْضُوا حَيْثُ تُؤْمَرُونَ
Wa Qađaynā 'Ilayhi Dhālika Al-'Amra 'Anna Dābira Hā'uulā' Maqţū`un Muşbiĥīna َ015-066 Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba. وَقَضَيْنَا إِلَيْهِ ذَلِكَ الأَمْرَ أَنَّ دَابِرَ هَاؤُلاَء مَقْطُوع ٌ مُصْبِحِينَ
Wa Jā'a 'Ahlu Al-Madīnati Yastabshirūna َ015-067 Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra. وَجَاءَ أَهْلُ الْمَدِينَةِ يَسْتَبْشِرُونَ
Qāla 'Inna Hā'uulā' Đayfī Falā Tafđaĥūni َ015-068 Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni." قَالَ إِنَّ هَاؤُلاَء ضَيْفِي فَلاَ تَفْضَحُونِ
Wa Attaqū Al-Laha Wa Lā Tukhzūni َ015-069 "Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki." وَاتَّقُوا اللَّهَ وَلاَ تُخْزُونِ
Qālū 'Awalam Nanhaka `Ani Al-`Ālamīna َ015-070 Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?" قَالُوا أَوَلَمْ نَنْهَكَ عَنِ الْعَالَمِينَ
Qāla Hā'uulā' Banātī 'In Kuntum Fā`ilīna َ015-071 Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna idan kun kasance mãsu aikatãwa ne." قَالَ هَاؤُلاَء بَنَاتِي إِنْ كُنْتُمْ فَاعِلِينَ
La`amruka 'Innahum Lafī Sakratihim Ya`mahūna َ015-072 Rantsuwa da rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa. لَعَمْرُكَ إِنَّهُمْ لَفِي سَكْرَتِهِمْ يَعْمَهُونَ
Fa'akhadhat/humu Aş-Şayĥatu Mushriqīna َ015-073 Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã. فَأَخَذَتْهُمُ الصَّيْحَةُ مُشْرِقِينَ
Faja`alnā `Āliyahā Sāfilahā Wa 'Amţarnā `Alayhim Ĥijāratan Min Sijjīlin َ015-074 Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu. فَجَعَلْنَا عَالِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِمْ حِجَارَة ً مِنْ سِجِّيل ٍ
'Inna Fī Dhālika La'āyātin Lilmutawassimīna َ015-075 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali. إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَات ٍ لِلْمُتَوَسِّمِينَ
Wa 'Innahā Labisabīlin Muqīmin َ015-076 Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya. وَإِنَّهَا لَبِسَبِيل ٍ مُقِيم ٍ
'Inna Fī Dhālika La'āyatan Lilmu'uminīna َ015-077 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni. إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَة ً لِلْمُؤْمِنِينَ
Wa 'In Kāna 'Aşĥābu Al-'Aykati Lažālimīna َ015-078 Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci! وَإِنْ كَانَ أَصْحَابُ الأَيْكَةِ لَظَالِمِينَ
ntaqamnā Minhum Wa 'Innahumā Labi'imāmin Mubīnin َ015-079 Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani. فَانْتَقَمْنَا مِنْهُمْ وَإِنَّهُمَا لَبِإِمَام ٍ مُبِين ٍ
Wa Laqad Kadhdhaba 'Aşĥābu Al-Ĥijri Al-Mursalīna َ015-080 Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri sun ƙaryata Manzanni. وَلَقَدْ كَذَّبَ أَصْحَابُ الْحِجْرِ الْمُرْسَلِينَ
Wa 'Ātaynāhum 'Āyātinā Fakānū `Anhā Mu`rīna َ015-081 Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su. وَآتَيْنَاهُمْ آيَاتِنَا فَكَانُوا عَنْهَا مُعْرِضِينَ
Wa Kānū Yanĥitūna Mina Al-Jibāli Buyūtāan 'Āminīna َ015-082 Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu. وَكَانُوا يَنْحِتُونَ مِنَ الْجِبَالِ بُيُوتا ً آمِنِينَ
Fa'akhadhat/humu Aş-Şayĥatu Muşbiĥīna َ015-083 Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba. فَأَخَذَتْهُمُ الصَّيْحَةُ مُصْبِحِينَ
Famā 'Aghná `Anhum Mā Kānū Yaksibūna َ015-084 Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba. فَمَا أَغْنَى عَنْهُمْ مَا كَانُوا يَكْسِبُونَ
Wa Mā Khalaq As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Wa Mā Baynahumā 'Illā Bil-Ĥaqqi  ۗ  Wa 'Inna As-Sā`ata La'ātiyatun  ۖ  Fāşfaĥi Aş-Şafĥa Al-Jamīla َ015-085 Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau. وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا إِلاَّ بِالْحَقِّ  ۗ  وَإِنَّ السَّاعَةَ لَآتِيَة ٌ  ۖ  فَاصْفَحِ الصَّفْحَ الْجَمِيلَ
'Inna Rabbaka Huwa Al-Khallāqu Al-`Alīmu َ015-086 Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani. إِنَّ رَبَّكَ هُوَ الْخَلاَّقُ الْعَلِيمُ
Wa Laqad 'Ātaynāka Sab`āan Mina Al-Mathānī Wa Al-Qur'āna Al-`Ažīma َ015-087 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu da Alƙur'ãni mai girma. وَلَقَدْ آتَيْنَاكَ سَبْعا ً مِنَ الْمَثَانِي وَالْقُرْآنَ الْعَظِيمَ
Lā Tamuddanna `Aynayka 'Ilá Mā Matta`nā Bihi 'Azwājāan Minhum Wa Lā Taĥzan `Alayhim Wa Akhfiđ Janāĥaka Lilmu'uminīna َ015-088 Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni. لاَ تَمُدَّنَّ عَيْنَيْكَ إِلَى مَا مَتَّعْنَا بِهِ~ِ أَزْوَاجا ً مِنْهُمْ وَلاَ تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَاخْفِضْ جَنَاحَكَ لِلْمُؤْمِنِينَ
Wa Qul 'Innī 'Anā An-Nadhīru Al-Mubīnu َ015-089 Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne." وَقُلْ إِنِّي أَنَا النَّذِيرُ الْمُبِينُ
Kamā 'Anzalnā `Alá Al-Muqtasimīna َ015-090 Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa, كَمَا أَنْزَلْنَا عَلَى الْمُقْتَسِمِينَ
Al-Ladhīna Ja`alū Al-Qur'āna `Iđīna َ015-091 Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi. الَّذِينَ جَعَلُوا الْقُرْآنَ عِضِينَ
Fawarabbika Lanas'alannahum 'Ajma`īna َ015-092 To, rantsuwa da Ubangijinka! Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya. فَوَرَبِّكَ لَنَسْأَلَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ
`Ammā Kānū Ya`malūna َ015-093 Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa. عَمَّا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Fāşda` Bimā Tu'umaru Wa 'A`riđ `Ani Al-Mushrikīna َ015-094 Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki. فَاصْدَعْ بِمَا تُؤْمَرُ وَأَعْرِضْ عَنِ الْمُشْرِكِينَ
'Innā Kafaynāka Al-Mustahzi'īna َ015-095 Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu izgili. إِنَّا كَفَيْنَاكَ الْمُسْتَهْزِئِينَ
Al-Ladhīna Yaj`alūna Ma`a Al-Lahi 'Ilahāan 'Ākhara  ۚ  Fasawfa Ya`lamūna َ015-096 Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani. الَّذِينَ يَجْعَلُونَ مَعَ اللَّهِ إِلَها ً آخَرَ  ۚ  فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ
Wa Laqad Na`lamu 'Annaka Yađīqu Şadruka Bimā Yaqūlūna َ015-097 Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili). وَلَقَدْ نَعْلَمُ أَنَّكَ يَضِيقُ صَدْرُكَ بِمَا يَقُولُونَ
Fasabbiĥ Biĥamdi Rabbika Wa Kun Mina As-Sājidīna َ015-098 Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada. فَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ وَكُنْ مِنَ السَّاجِدِينَ
Wa A`bud Rabbaka Ĥattá Ya'tiyaka Al-Yaqīnu َ015-099 Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka. وَاعْبُدْ رَبَّكَ حَتَّى يَأْتِيَكَ الْيَقِينُ
Next Sūrah