61) Sūrat Aş-Şaf

Printed format

61) سُورَة الصَّف

Sabbaĥa Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi Wa Huwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ061-001 Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah alhãli kuwa, Shi ne Mabuwayi, Mai hikima. سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āamanū Lima Taqūlūna Mā Lā Taf`alūna َ061-002 Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Don me kuke faɗin abin dã ba ku aikatãwa? يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا لِمَ تَقُولُونَ مَا لاَ تَفْعَلُونَ
Kabura Maqtāan `Inda Al-Lahi 'An Taqūlū Mā Lā Taf`alūna َ061-003 Ya girma ga zama abin ƙyãma awurin Allah, ku faɗi abin da bã ku aikatãwa. كَبُرَ مَقْتاً عِنْدَ اللَّهِ أَنْ تَقُولُوا مَا لاَ تَفْعَلُونَ
'Inna Al-Laha Yuĥibbu Al-Ladhīna Yuqātilūna Fī Sabīlihi Şaffāan Ka'annahum Bunyānun Marşūşun َ061-004 Lalle Allah Yanã son waɗanda ke yin yãƙi dõmin ɗaukaka KalmarSa, a cikin safu kamar sũ gini ne mai ɗamfarar jũna. إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الَّذِينَ يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِه ِِ صَفّا ً كَأَنَّهُمْ بُنيَان ٌ مَرْصُوص ٌ
Wa 'Idh Qāla Mūsá Liqawmihi Yā Qawmi Lima Tu'udhūnanī Wa Qad Ta`lamūna 'Annī Rasūlu Al-Lahi 'Ilaykum  ۖ  Falammā Zāghū 'Azāgha Al-Lahu Qulūbahum Wa  ۚ  Allāhu Lā Yahdī Al-Qawma Al-Fāsiqīna َ061-005 Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa mutãnensa: "Yã mutãnena! sabõda me kuke cũtar da ni, alhãli kuwa lalle kun sani cẽwa lalle nĩ Manzon Al1ah ne zuwa gare ku?" To, a lõkacin da suka karkace, Allah Ya karkatar da zukãtansu. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fasiƙai. وَإِذْ قَالَ مُوسَى لِقَوْمِه ِِ يَا قَوْمِ لِمَ تُؤْذُونَنِي وَقَدْ تَعْلَمُونَ أَنِّي رَسُولُ اللَّهِ إِلَيْكُمْ  ۖ  فَلَمَّا زَاغُوا أَزَاغَ اللَّهُ قُلُوبَهُمْ  ۚ  وَاللَّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ
Wa 'Idh Qāla `Īsá Abnu Maryama Yā Banī 'Isrā'īla 'Innī Rasūlu Al-Lahi 'Ilaykum Muşaddiqāan Limā Bayna Yadayya Mina At-Tawrāati Wa Mubashshirāan Birasūlin Ya'tī Min Ba`dī Asmuhu 'Aĥmadu  ۖ  Falammā Jā'ahum Bil-Bayyināti Qālū Hādhā Siĥrun Mubīnun َ061-006 Kuma a lõkacin da Ĩsã ɗan Maryayama ya ce: "Yã BanĩIsrã'ĩla! Lalle nĩ Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bãyar da bushãra da wani Manzo da ke zuwa a bãyãna, SũnasaAhmad (Mashãyabo)." To, a lõkacin da ya jẽ musu da hujjõji, suka ce: "Wannan sihiri ne, bayyananne." وَإِذْ قَالَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ إِنِّي رَسُولُ اللَّهِ إِلَيْكُمْ مُصَدِّقا ً لِمَا بَيْنَ يَدَيَّ مِنَ التَّوْرَاةِ وَمُبَشِّرا ً بِرَسُول ٍ يَأْتِي مِنْ بَعْدِي اسْمُهُ~ُ أَحْمَدُ  ۖ  فَلَمَّا جَاءَهُمْ بِالْبَيِّنَاتِ قَالُوا هَذَا سِحْر ٌ مُبِين ٌ
Wa Man 'Ažlamu Mimmani Aftará `Alá Al-Lahi Al-Kadhiba Wa Huwa Yud`á 'Ilá Al-'Islāmi Wa  ۚ  Allāhu Lā Yahdī Al-Qawma Až-Žālimīna َ061-007 Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya Jingina ta ga Allah, alhãli kuwa shĩ, anã kiran sa zuwa ga Musulunci? Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai. وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللَّهِ الْكَذِبَ وَهُوَ يُدْعَى إِلَى الإِسْلاَمِ  ۚ  وَاللَّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ
Yurīdūna Liyuţfi'ū Nūra Al-Lahi Bi'afwāhihim Wa Allāhu Mutimmu Nūrihi Wa Law Kariha Al-Kāfirūna َ061-008 Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunansu alhãli kuwa Allah Mai kammala haskenSa ne, kuma kõ da kãfirai sun ƙi. يُرِيدُونَ لِيُطْفِئُوا نُورَ اللَّهِ بِأَفْوَاهِهِمْ وَاللَّهُ مُتِمُّ نُورِه ِِ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ
Huwa Al-Ladhī 'Arsala Rasūlahu Bil-Hudá Wa Dīni Al-Ĥaqqi Liyužhirahu `Alá Ad-Dīni Kullihi Wa Law Kariha Al-Mushrikūna َ061-009 Shi ne wanda Ya aiko ManzonSa da shiriya da addĩnin gakiya, dõmin Ya ɗaukaka shi a kan wani addĩni dukansa kuma kõ dã mushirikai sun ƙi. هُوَ الَّذِي أَرْسَلَ رَسُولَه ُُ بِالْهُدَى وَدِينِ الْحَقِّ لِيُظْهِرَه ُُ عَلَى الدِّينِ كُلِّه ِِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُشْرِكُونَ
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āamanū Hal 'Adullukum `Alá Tijāratin Tunjīkum Min `Adhābin 'Alīmin َ061-010 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Shin, in nũna muku wani fatauci wanda zai tsarshe ku daga wata azãba mai raɗaɗi? يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا هَلْ أَدُلُّكُمْ عَلَى تِجَارَة ٍ تُنجِيكُمْ مِنْ عَذَابٍ أَلِيم ٍ
Tu'uminūna Bil-Lahi Wa Rasūlihi Wa Tujāhidūna Fī Sabīli Al-Lahi Bi'amwālikum Wa 'Anfusikum  ۚ  Dhālikum Khayrun Lakum 'In Kuntum Ta`lamūna َ061-011 Ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa, kuma ku yi jihãdi ga ɗaukaka kalmar Allah game da dũkiyõyinku da rãyukanku. Wannan shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna da sani. تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَرَسُولِه ِِ وَتُجَاهِدُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ بِأَمْوَالِكُمْ وَأَنفُسِكُمْ  ۚ  ذَلِكُمْ خَيْر ٌ لَكُمْ إِنْ كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Yaghfir Lakum Dhunūbakum Wa Yudkhilkum Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Wa Masākina Ţayyibatan Fī Jannāti `Adnin  ۚ  Dhālika Al-Fawzu Al-`Ažīmu َ061-012 Sai Allah Ya gãfarta muku zunubbanku, kuma Ya shigar da ku gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, da waɗansu ɗãkuna mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar zama. Wannan shĩ ne babban rabo, mai girma. يَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَيُدْخِلْكُمْ جَنَّات ٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ وَمَسَاكِنَ طَيِّبَة ً فِي جَنَّاتِ عَدْن ٍ  ۚ  ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Wa 'Ukhrá Tuĥibbūnahā  ۖ  Naşrun Mina Al-Lahi Wa Fatĥun Qarībun  ۗ  Wa Bashshiri Al-Mu'uminīna َ061-013 Da wata ( falala) da yake kunã son ta; taimako daga Allah da cin nasara wanda yake kusa. Kuma ka yi bushãra ga mũminai. وَأُخْرَى تُحِبُّونَهَا  ۖ  نَصْر ٌ مِنَ اللَّهِ وَفَتْح ٌ قَرِيب ٌ  ۗ  وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āamanū Kūnw 'Anşāra Al-Lahi Kamā Qāla `Īsá Abnu Maryama Lilĥawārīyīna Man 'Anşārī 'Ilá Al-Lahi  ۖ  Qāla Al-Ĥawārīyūna Naĥnu 'Anşāru Al-Lahi  ۖ  Fa'āamanat Ţā'ifatun Min Banī 'Isrā'īla Wa Kafarat Ţā'ifatun  ۖ  Fa'ayyad Al-Ladhīna 'Āamanū `Alá `Adūwihim Fa'aşbaĥū Žāhirīna َ061-014 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Ku kasance mataimakan Allah kamar abin da Ĩsã ɗanMaryama ya ce ga Hawãriyãwa, "Waɗanne ne mataimakãna zuwa ga (aikin) Allah?" Sai wata ƙungiya daga Banĩ Isrã'ĩla ta yi ĩmãni, kuma wata ƙungiya ta kãfirta. Sai muka ƙarfafa waɗanda suka yi ĩmãni a kan maƙiyansu, sabõda haka suka wãyi gari marinjãya. يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا كُونوا أَنصَارَ اللَّهِ كَمَا قَالَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ لِلْحَوَارِيِّينَ مَنْ أَنصَارِي إِلَى اللَّهِ قَالَ  ۖ  الْحَوَارِيُّونَ نَحْنُ أَنصَارُ اللَّهِ فَآَمَنَتْ  ۖ  طَائِفَة ٌ مِنْ بَنِي إِسْرَائِيلَ وَكَفَرَتْ طَائِفَة ٌ فَأَيَّدْنَا  ۖ  الَّذِينَ آَمَنُوا عَلَى عَدُوِّهِمْ فَأَصْبَحُوا ظَاهِرِينَ
Next Sūrah