52) Sūrat Aţ-Ţūr

Printed format

52) سُورَة الطُّور

Wa Aţūri َ052-001 Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã). وَالطُّورِ
Wa Kitābin Masţūrin َ052-002 Da wani littãfi rubũtacce. وَكِتَاب ٍ مَسْطُور ٍ
Fī Raqqin Manshūrin َ052-003 A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa. فِي رَقّ ٍ مَنْشُور ٍ
Wa Al-Bayti Al-Ma`mūri َ052-004 Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda). وَالْبَيْتِ الْمَعْمُورِ
Wa As-Saqfi Al-Marfū`i َ052-005 Da rufin nan da aka ɗaukaka. وَالسَّقْفِ الْمَرْفُوعِ
Wa Al-Baĥri Al-Masjūri َ052-006 Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa). وَالْبَحْرِ الْمَسْجُورِ
'Inna `Adhāba Rabbika Lawāqi`un َ052-007 Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce. إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ لَوَاقِع ٌ
Mā Lahu Min Dāfi`in َ052-008 Bã ta da mai tunkuɗẽwa. مَا لَه ُُ مِنْ دَافِع ٍ
Yawma Tamūru As-Samā'u Mawrāan َ052-009 Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo. يَوْمَ تَمُورُ السَّمَاءُ مَوْرا ً
Wa Tasīru Al-Jibālu Sayrāan َ052-010 Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa. وَتَسِيرُ الْجِبَالُ سَيْرا ً
Fawaylun Yawma'idhin Lilmukadhdhibīna َ052-011 To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa. فَوَيْل ٌ يَوْمَئِذ ٍ لِلْمُكَذِّبِينَ
Al-Ladhīna HumKhawđin Yal`abūna َ052-012 Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã. الَّذِينَ هُمْ فِي خَوْض ٍ يَلْعَبُونَ
Yawma Yuda``ūna 'Ilá Nāri Jahannama Da``āan َ052-013 Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa. يَوْمَ يُدَعُّونَ إِلَى نَارِ جَهَنَّمَ دَعّا ً
Hadhihi An-Nāru Allatī Kuntum Bihā Tukadhdhibūna َ052-014 (A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita." هَذِهِ النَّارُ الَّتِي كُنتُمْ بِهَا تُكَذِّبُونَ
'Afasiĥrun Hādhā 'Am 'Antum Lā Tubşirūna َ052-015 "To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani?" أَفَسِحْرٌ هَذَا أَمْ أَنْتُمْ لاَ تُبْصِرُونَ
Aşlawhā Fāşbirū 'Aw Lā Taşbirū Sawā'un `Alaykum  ۖ  'Innamā Tujzawna Mā Kuntum Ta`malūna َ052-016 "Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa." اصْلَوْهَا فَاصْبِرُوا أَوْ لاَ تَصْبِرُوا سَوَاءٌ عَلَيْكُمْ  ۖ  إِنَّمَا تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
'Inna Al-Muttaqīna Fī Jannātin Wa Na`īmin َ052-017 Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima. إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّات ٍ وَنَعِيم ٍ
Fākihīna Bimā 'Ātāhum Rabbuhum Wa Waqāhum Rabbuhum `Adhāba Al-Jaĥīmi َ052-018 Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm. فَاكِهِينَ بِمَا آتَاهُمْ رَبُّهُمْ وَوَقَاهُمْ رَبُّهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ
Kulū Wa Ashrabū Hanī'āan Bimā Kuntum Ta`malūna َ052-019 (A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa." كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئا ً بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Muttaki'īna `Alá Sururin Maşfūfatin  ۖ  Wa Zawwajnāhum Biĥūrin `Īnin َ052-020 Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu. مُتَّكِئِينَ عَلَى سُرُر ٍ مَصْفُوفَة ٍ  ۖ  وَزَوَّجْنَاهُمْ بِحُورٍ عِين ٍ
Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Attaba`at/hum Dhurrīyatuhum Bi'īmānin 'Alĥaqnā Bihim Dhurrīyatahum Wa Mā 'Alatnāhum Min `Amalihim Min  ۚ  Shay'in Kullu Amri'in Bimā Kasaba Rahīnun َ052-021 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta. وَالَّذِينَ آمَنُوا وَاتَّبَعَتْهُمْ ذُرِّيَّتُهُمْ بِإِيمَانٍ أَلْحَقْنَا بِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَمَا أَلَتْنَاهُمْ مِنْ عَمَلِهِمْ مِنْ شَيْء ٍ  ۚ  كُلُّ امْرِئ ٍ بِمَا كَسَبَ رَهِين ٌ
Wa 'Amdadnāhum Bifākihatin Wa Laĥmin Mimmā Yashtahūna َ052-022 Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari. وَأَمْدَدْنَاهُمْ بِفَاكِهَة ٍ وَلَحْم ٍ مِمَّا يَشْتَهُونَ
Yatanāza`ūna Fīhā Ka'sāan Lā Laghwun Fīhā Wa Lā Ta'thīmun َ052-023 Sunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi. يَتَنَازَعُونَ فِيهَا كَأْسا ً لاَ لَغْو ٌ فِيهَا وَلاَ تَأْثِيم ٌ
Wa Yaţūfu `Alayhim Ghilmānun Lahum Ka'annahum Lu'ulu'uun Maknūnun َ052-024 Kuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle. وَيَطُوفُ عَلَيْهِمْ غِلْمَان ٌ لَهُمْ كَأَنَّهُمْ لُؤْلُؤ ٌ مَكْنُون ٌ
Wa 'Aqbala Ba`đuhum `Alá Ba`đin Yatasā'alūna َ052-025 Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna. وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَى بَعْض ٍ يَتَسَاءَلُونَ
Qālū 'Innā Kunnā Qablu Fī 'Ahlinā Mushfiqīna َ052-026 Suka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya ) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro." قَالُوا إِنَّا كُنَّا قَبْلُ فِي أَهْلِنَا مُشْفِقِينَ
Famanna Al-Lahu `Alaynā Wa Waqānā `Adhāba As-Samūmi َ052-027 "To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi." فَمَنَّ اللَّهُ عَلَيْنَا وَوَقَانَا عَذَابَ السَّمُومِ
'Innā Kunnā Min Qablu Nad`ūhu  ۖ  'Innahu Huwa Al-Barru Ar-Raĥīmu َ052-028 "Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama." إِنَّا كُنَّا مِنْ قَبْلُ نَدْعُوهُ~ُ  ۖ  إِنَّه ُُ هُوَ الْبَرُّ الرَّحِيمُ
Fadhakkir Famā 'Anta Bini`mati Rabbika Bikāhinin Wa Lā Majnūnin َ052-029 To, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba. فَذَكِّرْ فَمَا أَنْتَ بِنِعْمَةِ رَبِّكَ بِكَاهِن ٍ وَلاَ مَجْنُون ٍ
'Am Yaqūlūna Shā`irun Natarabbaşu Bihi Rayba Al-Manūni َ052-030 Shin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"? أَمْ يَقُولُونَ شَاعِر ٌ نَتَرَبَّصُ بِه ِِ رَيْبَ الْمَنُونِ
Qul Tarabbaşū Fa'innī Ma`akum Mina Al-Mutarabbişīna َ052-031 Ka ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku." قُلْ تَرَبَّصُوا فَإِنِّي مَعَكُمْ مِنَ الْمُتَرَبِّصِينَ
'Am Ta'muruhum 'Aĥlāmuhum Bihadhā  ۚ  'Am Hum Qawmun Ţāghūna َ052-032 Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi? أَمْ تَأْمُرُهُمْ أَحْلاَمُهُمْ بِهَذَا  ۚ  أَمْ هُمْ قَوْم ٌ طَاغُونَ
'Am Yaqūlūna Taqawwalahu  ۚ  Bal Lā Yu'uminūna َ052-033 Shin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba. أَمْ يَقُولُونَ تَقَوَّلَه ُُ  ۚ  بَل لاَ يُؤْمِنُونَ
Falya'tū Biĥadīthin Mithlihi 'In Kānū Şādiqīna َ052-034 Sai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne. فَلْيَأْتُوا بِحَدِيث ٍ مِثْلِهِ~ِ إِنْ كَانُوا صَادِقِينَ
'Am Khuliqū Min Ghayri Shay'in 'Am Humu Al-Khāliqūna َ052-035 Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta? أَمْ خُلِقُوا مِنْ غَيْرِ شَيْءٍ أَمْ هُمُ الْخَالِقُونَ
'Am Khalaqū As-Samāwāti Wa Al-'Arđa  ۚ  Bal Lā Yūqinūna َ052-036 Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba. أَمْ خَلَقُوا السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ  ۚ  بَل لاَ يُوقِنُونَ
'Am `Indahum Khazā'inu Rabbika 'Am Humu Al-Musayţirūna َ052-037 Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya? أَمْ عِنْدَهُمْ خَزَائِنُ رَبِّكَ أَمْ هُمُ الْمُسَيْطِرُونَ
'Am Lahum Sullamun Yastami`ūna Fīhi  ۖ  Falya'ti Mustami`uhum Bisulţānin Mubīnin َ052-038 Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne. أَمْ لَهُمْ سُلَّم ٌ يَسْتَمِعُونَ فِيه ِِ  ۖ  فَلْيَأْتِ مُسْتَمِعُهُمْ بِسُلْطَان ٍ مُبِين ٍ
'Am Lahu Al-Banātu Wa Lakumu Al-Banūna َ052-039 Shin, Yanã da 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne? أَمْ لَهُ الْبَنَاتُ وَلَكُمُ الْبَنُونَ
'Am Tas'aluhum 'Ajrāan Fahum Min Maghramin Muthqalūna َ052-040 Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar? أَمْ تَسْأَلُهُمْ أَجْرا ً فَهُمْ مِنْ مَغْرَم ٍ مُثْقَلُونَ
'Am `Indahumu Al-Ghaybu Fahum Yaktubūna َ052-041 Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa? أَمْ عِنْدَهُمُ الْغَيْبُ فَهُمْ يَكْتُبُونَ
'Am Yurīdūna Kaydāan  ۖ  Fa-Al-Ladhīna Kafarū Humu Al-Makīdūna َ052-042 Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi. أَمْ يُرِيدُونَ كَيْدا ً  ۖ  فَالَّذِينَ كَفَرُوا هُمُ الْمَكِيدُونَ
'Am Lahum 'Ilahun Ghayru Al-Lahi  ۚ  Subĥāna Al-Lahi `Ammā Yushrikūna َ052-043 Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki! أَمْ لَهُمْ إِلَه ٌٌ غَيْرُ اللَّهِ  ۚ  سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Wa 'In Yaraw Kisfāan Mina As-Samā'i Sāqiţāan Yaqūlū Saĥābun Markūmun َ052-044 Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna. وَإِنْ يَرَوْا كِسْفا ً مِنَ السَّمَاءِ سَاقِطا ً يَقُولُوا سَحَاب ٌ مَرْكُوم ٌ
Fadharhum Ĥattá Yulāqū Yawmahumu Al-Ladhī Fīhi Yuş`aqūna َ052-045 To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa. فَذَرْهُمْ حَتَّى يُلاَقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي فِيه ِِ يُصْعَقُونَ
Yawma Lā Yughnī `Anhum Kayduhum Shay'āan Wa Lā Hum Yunşarūna َ052-046 Rãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su. يَوْمَ لاَ يُغْنِي عَنْهُمْ كَيْدُهُمْ شَيْئا ً وَلاَ هُمْ يُنصَرُونَ
Wa 'Inna Lilladhīna Žalamū `Adhābāan Dūna Dhālika Wa Lakinna 'Aktharahum Lā Ya`lamūna َ052-047 Kuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba. وَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا عَذَابا ً دُونَ ذَلِكَ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ
Wa Aşbir Liĥukmi Rabbika Fa'innaka Bi'a`yuninā  ۖ  Wa Sabbiĥ Biĥamdi Rabbika Ĥīna Taqūmu َ052-048 Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnunMu, kuma ka tsarkake Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu). وَاصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ فَإِنَّكَ بِأَعْيُنِنَا  ۖ  وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ حِينَ تَقُومُ
Wa Mina Al-Layli Fasabbiĥhu Wa 'Idbāra An-Nujūmi َ052-049 Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) dalõkacin jũyãwar taurãri. وَمِنَ اللَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَإِدْبَارَ النُّجُومِ
Next Sūrah