48) Sūrat Al-Fatĥ

Printed format

48) سُورَة الفَتح

'Innā Fataĥnā Laka Fatĥāan Mubīnāan َ048-001 Lalle Mũ, Mun yi maka rinjãye (a kan maƙiyanka), rinjaye bayyananne. إِنَّا فَتَحْنَا لَكَ فَتْحا ً مُبِينا ً
Liyaghfira Laka Al-Lahu Mā Taqaddama Min Dhanbika Wa Mā Ta'akhkhara Wa Yutimma Ni`matahu `Alayka Wa Yahdiyaka Şirāţāan Mustaqīmāan َ048-002 Dõmin Allah Ya shãfe abin da ya gabãta na laifinka da abin da ya jinkirta, kuma Ya cika ni'imarSa a kanka, kuma Ya shiryar da kai ga hanya madaidaiciya. لِيَغْفِرَ لَكَ اللَّهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ وَيُتِمَّ نِعْمَتَه ُُ عَلَيْكَ وَيَهْدِيَكَ صِرَاطا ً مُسْتَقِيما ً
Wa Yanşuraka Al-Lahu Naşrāan `Azīzāan َ048-003 Kuma Allah Ya taimake ka, taimako mabuwãyi. وَيَنْصُرَكَ اللَّهُ نَصْراً عَزِيزا ً
Huwa Al-Ladhī 'Anzala As-Sakīnata Fī Qulūbi Al-Mu'uminīna Liyazdādū 'Īmānāan Ma`a 'Īmānihim  ۗ  Wa Lillahi Junūdu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu `Alīmāan Ĥakīmāan َ048-004 Shĩ ne wanda Ya saukar da natsuwa a cikin zukãtan mũminai dõmin su ƙãra wani ĩmãni tãre da imãninsu, alhãli kuwa rundunõnin sammai da ƙasa, na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Masani, Mai hikima. هُوَ الَّذِي أَنْزَلَ السَّكِينَةَ فِي قُلُوبِ الْمُؤْمِنِينَ لِيَزْدَادُوا إِيمَانا ً مَعَ إِيمَانِهِمْ  ۗ  وَلِلَّهِ جُنُودُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۚ  وَكَانَ اللَّهُ عَلِيماً حَكِيما ً
Liyudkhila Al-Mu'uminīna Wa Al-Mu'umināti Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā Wa Yukaffira `Anhum Sayyi'ātihim  ۚ  Wa Kāna Dhālika `Inda Al-Lahi Fawzāan `Ažīmāan َ048-005 Dõmin Ya shigar da mũminai maza da mũminai mãtã gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen, sunã madawwama a cikinsu kuma Ya kankare musu mũnãnan ayyukansu. wannan abu ya kasance a wurin Allah babban rabo, mai gimia. لِيُدْخِلَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ جَنَّات ٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا وَيُكَفِّرَ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ  ۚ  وَكَانَ ذَلِكَ عِنْدَ اللَّهِ فَوْزاً عَظِيما ً
Wa Yu`adhdhiba Al-Munāfiqīna Wa Al-Munāfiqāti Wa Al-Mushrikīna Wa Al-Mushrikāti Až-Žānnīna Bil-Lahi Žanna As-Saw'i  ۚ  `Alayhim Dā'iratu As-Saw'i  ۖ  Wa Ghađiba Al-Lahu `Alayhim Wa La`anahum Wa 'A`adda Lahum Jahannama  ۖ  Wa Sā'at Maşīrāan َ048-006 Kuma Ya yi azãba ga munãfikai maza da munãfikai mãtã da mushirikai maza da musbirikai mãtã, mãsu zaton mugun zato game da Allah, mugunyar masĩfa mai kẽwayẽwa ta tabbata a kansu, kuma Allah Ya yi hushi da su, kuma Ya la'ane su, kuma Ya yi musu tattlain Jahannama kuma ta mũnana ta zama makõma (gare su). وَيُعَذِّبَ الْمُنَافِقِينَ وَالْمُنَافِقَاتِ وَالْمُشْرِكِينَ وَالْمُشْرِكَاتِ الظَّانِّينَ بِاللَّهِ ظَنَّ السَّوْءِ  ۚ  عَلَيْهِمْ دَائِرَةُ السَّوْءِ  ۖ  وَغَضِبَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ وَلَعَنَهُمْ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَهَنَّمَ  ۖ  وَسَاءَتْ مَصِيرا ً
Wa Lillahi Junūdu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu `Azīzāan Ĥakīmāan َ048-007 Rundunõnin sammai da ƙasã na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Mabuwãyi, Mai hikima. وَلِلَّهِ جُنُودُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۚ  وَكَانَ اللَّهُ عَزِيزاً حَكِيما ً
'Innā 'Arsalnāka Shāhidāan Wa Mubashshirāan Wa Nadhīrāan َ048-008 Lalle Mũ Mun aike ka, kanã mai shaida, kuma mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. إِنَّا أَرْسَلْنَاكَ شَاهِدا ً وَمُبَشِّرا ً وَنَذِيرا ً
Litu'uminū Bil-Lahi Wa Rasūlihi Wa Tu`azzirūhu Wa Tuwaqqirūhu Wa Tusabbiĥūhu Bukratan Wa 'Aşīlāan َ048-009 Dõmin ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa, kuma ku ƙarfafa shi, kuma ku girmama Shi, kuma ku tsarkake Shi (Allah) sãfiya da maraice. لِتُؤْمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِه ِِ وَتُعَزِّرُوه ُُ وَتُوَقِّرُوه ُُ وَتُسَبِّحُوه ُُ بُكْرَة ً وَأَصِيلا ً
'Inna Al-Ladhīna Yubāyi`ūnaka 'Innamā Yubāyi`ūna Al-Laha Yadu Al-Lahi Fawqa 'Aydīhim  ۚ  Faman Nakatha Fa'innamā Yankuthu `Alá Nafsihi  ۖ  Wa Man 'Awfá Bimā `Āhada `Alayhu Al-Laha Fasayu'utīhi 'Ajrāan `Ažīmāan َ048-010 Lalle waɗanda ke yi maka mubãya'a, Allah kawai ne suke yi wa mubãya'a, Hannun Allah nã bisa hannayensu, sabõda haka wanda ya warware, to, yanã warwarẽwa ne a kan kansa kawai, kuma wanda ya cika ga alkawarin da ya yi wa Allah a kansa, to, (Allah) zai kãwo masa ijãra mai girma. إِنَّ الَّذِينَ يُبَايِعُونَكَ إِنَّمَا يُبَايِعُونَ اللَّهَ يَدُ اللَّهِ فَوْقَ أَيْدِيهِمْ  ۚ  فَمَنْ نَكَثَ فَإِنَّمَا يَنْكُثُ عَلَى نَفْسِه ِِ  ۖ  وَمَنْ أَوْفَى بِمَا عَاهَدَ عَلَيْهُ اللَّهَ فَسَيُؤْتِيهِ~ِ أَجْراً عَظِيما ً
Sayaqūlu Laka Al-Mukhallafūna Mina Al-'A`rābi Shaghalatnā 'Amwālunā Wa 'Ahlūnā Fāstaghfir Lanā  ۚ  Yaqūlūna Bi'alsinatihim Mā Laysa Fī Qulūbihim  ۚ  Qul Faman Yamliku Lakum Mina Al-Lahi Shay'āan 'In 'Arāda Bikum Đarrāan 'Aw 'Arāda Bikum Naf`āan  ۚ  Bal Kāna Al-Lahu Bimā Ta`malūna Khabīrāan َ048-011 Waɗanda aka bari daga ƙauyãwa zã su ce maka, "Dũkiyõyinmu da iyãlanmu sun shagaltar da mu, sai ka nẽma mana gãfara." Sunã faɗã, da harsunansu, abin da bã shĩ ne a cikin zukãtansu ba. Kace: "To, wãne ne ke mallakar wani abu daga Allah sabõda kũ, idan Yã yi nufin wata cũta agare ku kõ kuma (idan) Ya yi nufin wani amfãni a gare ku? Ã'a, Allah Ya kasance Mai labartawa ne ga abin da kuke aikatãwa." سَيَقُولُ لَكَ الْمُخَلَّفُونَ مِنَ الأَعْرَابِ شَغَلَتْنَا أَمْوَالُنَا وَأَهْلُونَا فَاسْتَغْفِرْ لَنَا  ۚ  يَقُولُونَ بِأَلْسِنَتِهِمْ مَا لَيْسَ فِي قُلُوبِهِمْ  ۚ  قُلْ فَمَنْ يَمْلِكُ لَكُمْ مِنَ اللَّهِ شَيْئا ً إِنْ أَرَادَ بِكُمْ ضَرّاً أَوْ أَرَادَ بِكُمْ نَفْعا ً  ۚ  بَلْ كَانَ اللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرا ً
Bal Žanantum 'An Lan Yanqaliba Ar-Rasūlu Wa Al-Mu'uminūna 'Ilá 'Ahlīhim 'Abadāan Wa Zuyyina Dhālika Fī Qulūbikum Wa Žanantum Žanna As-Saw'i Wa Kuntum Qawmāan Būrāan َ048-012 Ã'a kun yi zaton Annabi da mũminai, bã za su kõmo zuwa ga iyãlansu ba, har abada. Kuma an ƙawãta wannan (tunãni) a cikin zukãtanku, kuma kun yi zato, zaton mugunta, kuma kun kasance mutãne halakakku. بَلْ ظَنَنْتُمْ أَنْ لَنْ يَنْقَلِبَ الرَّسُولُ وَالْمُؤْمِنُونَ إِلَى أَهْلِيهِمْ أَبَدا ً وَزُيِّنَ ذَلِكَ فِي قُلُوبِكُمْ وَظَنَنْتُمْ ظَنَّ السَّوْءِ وَكُنْتُمْ قَوْما ً بُورا ً
Wa Man Lam Yu'umin Bil-Lahi Wa Rasūlihi Fa'innā 'A`tadnā Lilkāfirīna Sa`īrāan َ048-013 Kuma wanda bai yi ĩmãni da Allah da kuma Manzonsa ba, to, lalle Mũ, Mun yi tattalin wutã mai tsananin ƙũna, dõmin kafirai. وَمَنْ لَمْ يُؤْمِنْ بِاللَّهِ وَرَسُولِه ِِ فَإِنَّا أَعْتَدْنَا لِلْكَافِرِينَ سَعِيرا ً
Wa Lillahi Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۚ  Yaghfiru Liman Yashā'u Wa Yu`adhdhibu Man Yashā'u  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu Ghafūrāan Raĥīmāan َ048-014 Mulkin sammai da ƙasã na Allah kawai ne, Yanã gãfartawa ga wanda Yake so, kuma Yanã azabta wanda Yake so alhãli kuwa Allah Ya kasance Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. وَلِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۚ  يَغْفِرُ لِمَنْ يَشَاءُ وَيُعَذِّبُ مَنْ يَشَاءُ  ۚ  وَكَانَ اللَّهُ غَفُورا ً رَحِيما ً
Sayaqūlu Al-Mukhallafūna 'Idhā Anţalaqtum 'Ilá Maghānima Lita'khudhūhā Dharūnā Nattabi`kum  ۖ  Yurīdūna 'An Yubaddilū Kalāma Al-Lahi  ۚ  Qul Lan Tattabi`ūnā Kadhālikum Qāla Al-Lahu Min Qablu  ۖ  Fasayaqūlūna Bal Taĥsudūnanā  ۚ  Bal Kānū Lā Yafqahūna 'Illā Qalīlāan َ048-015 Waɗanda aka bari zã su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganĩmõmi dõmin ku karɓo su, "Ku bar mu, mu bĩ ku." Sunã son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: "Bã zã ku bĩ mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabãnin haka." Sa'an nan zã su ce: "Ã'a, kunã dai hãssadar mu ne." Ã'a, sun kasance bã su fahimtar (abũbuwa) sai kaɗan. سَيَقُولُ الْمُخَلَّفُونَ إِذَا انطَلَقْتُمْ إِلَى مَغَانِمَ لِتَأْخُذُوهَا ذَرُونَا نَتَّبِعْكُمْ  ۖ  يُرِيدُونَ أَنْ يُبَدِّلُوا كَلاَمَ اللَّهِ  ۚ  قُلْ لَنْ تَتَّبِعُونَا كَذَلِكُمْ قَالَ اللَّهُ مِنْ قَبْلُ  ۖ  فَسَيَقُولُونَ بَلْ تَحْسُدُونَنَا  ۚ  بَلْ كَانُوا لاَ يَفْقَهُونَ إِلاَّ قَلِيلا ً
Qul Lilmukhallafīna Mina Al-'A`rābi Satud`awna 'Ilá Qawmin 'Ūlī Ba'sin Shadīdin Tuqātilūnahum 'Aw Yuslimūna  ۖ  Fa'in Tuţī`ū Yu'utikumu Al-Lahu 'Ajrāan Ĥasanāan  ۖ  Wa 'In Tatawallaw Kamā Tawallaytum Min Qablu Yu`adhdhibkum `Adhābāan 'Alīmāan َ048-016 Ka ce wa waɗanda aka bari daga ƙauyãwa: "Za a kira ku zuwa ga waɗansu mutãne mãsu tsananin yãƙi (dõmin) ku yãƙe su kõ kuwa su musulunta. To, idan kun yi ɗã'a, Allah zai kãwo muku wata ijãra mai kyau, kuma idan kuka jũya bãya kamar yadda kuka jũya a gabãnin wancan, zai azãbtã ku, azãba mai raɗadi." قُلْ لِلْمُخَلَّفِينَ مِنَ الأَعْرَابِ سَتُدْعَوْنَ إِلَى قَوْمٍ أُوْلِي بَأْس ٍ شَدِيد ٍ تُقَاتِلُونَهُمْ أَوْ يُسْلِمُونَ  ۖ  فَإِنْ تُطِيعُوا يُؤْتِكُمُ اللَّهُ أَجْراً حَسَنا ً  ۖ  وَإِنْ تَتَوَلَّوْا كَمَا تَوَلَّيْتُمْ مِنْ قَبْلُ يُعَذِّبْكُمْ عَذَاباً أَلِيما ً
Laysa `Alá Al-'A`má Ĥarajun Wa Lā `Alá Al-'A`raji Ĥarajun Wa Lā `Alá Al-Marīđi Ĥarajun  ۗ  Wa Man Yuţi`i Al-Laha Wa Rasūlahu Yudkhilhu Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru  ۖ  Wa Man Yatawalla Yu`adhdhibhu `Adhābāan 'Alīmāan َ048-017 Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi a gidãjen Aljanna, kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu. Kuma wanda ya jũya bãya, ( Allah) zai azabtãshi, azãba mai raɗãɗi. لَيْسَ عَلَى الأَعْمَى حَرَج ٌ وَلاَ عَلَى الأَعْرَجِ حَرَج ٌ وَلاَ عَلَى الْمَرِيضِ حَرَج ٌ  ۗ  وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَه ُُ يُدْخِلْهُ جَنَّات ٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ  ۖ  وَمَنْ يَتَوَلَّ يُعَذِّبْهُ عَذَاباً أَلِيما ً
Laqad Rađiya Al-Lahu `Ani Al-Mu'uminīna 'Idh Yubāyi`ūnaka Taĥta Ash-Shajarati Fa`alima Mā Fī Qulūbihim Fa'anzala As-Sakīnata `Alayhim Wa 'Athābahum Fatĥāan Qarībāan َ048-018 Lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yarda da muminai a lõkacin da suke yi maka mubãya, a a ƙarƙashin itãciyar nan dõmin Yã san abin da ke cikin zukãtansu sai Yã saukar da natsuwa a kansu, kuma Ya sãka musu da wani cin nasara makusanci. لَقَدْ رَضِيَ اللَّهُ عَنِ الْمُؤْمِنِينَ إِذْ يُبَايِعُونَكَ تَحْتَ الشَّجَرَةِ فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِمْ فَأَنْزَلَ السَّكِينَةَ عَلَيْهِمْ وَأَثَابَهُمْ فَتْحا ً قَرِيبا ً
Wa Maghānima Kathīratan Ya'khudhūnahā  ۗ  Wa Kāna Al-Lahu `Azīzāan Ĥakīmāan َ048-019 Da waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa da zã su karɓo su. Kuma Allah Yã kasance Mabuwayi, Mai hikima. وَمَغَانِمَ كَثِيرَة ً يَأْخُذُونَهَا  ۗ  وَكَانَ اللَّهُ عَزِيزاً حَكِيما ً
Wa`adakumu Al-Lahu Maghānima Kathīratan Ta'khudhūnahā Fa`ajjala Lakum Hadhihi Wa Kaffa 'Aydiya An-Nāsi `Ankum Wa Litakūna 'Āyatan Lilmu'uminīna Wa Yahdiyakum Şirāţāan Mustaqīmāan َ048-020 Kuma Allah Yã yi muku wa'adin waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa, waɗanda zã ku karɓo su, kuma Ya gaggauta muku wannan. Kuma Ya kange hannãyen mutãne daga gare ku, kuma dõmin ta kasance wata ãyã ce ga mũminai, kuma Yã shiryar da ku ga hanya madaidaiciya. وَعَدَكُمُ اللَّهُ مَغَانِمَ كَثِيرَة ً تَأْخُذُونَهَا فَعَجَّلَ لَكُمْ هَذِه ِِ وَكَفَّ أَيْدِيَ النَّاسِ عَنْكُمْ وَلِتَكُونَ آيَة ً لِلْمُؤْمِنِينَ وَيَهْدِيَكُمْ صِرَاطا ً مُسْتَقِيما ً
Wa 'Ukhrá Lam Taqdirū `Alayhā Qad 'Aĥāţa Al-Lahu Bihā  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu `Alá Kulli Shay'in Qadīrāan َ048-021 Da waɗansu (ganĩmõmin) da bã ku da ĩko a kansu lalle Allah Ya kẽwaye su da saninSa, kuma Allah Ya kasance Mai ikon yi ne a kan dukan kõme. وَأُخْرَى لَمْ تَقْدِرُوا عَلَيْهَا قَدْ أَحَاطَ اللَّهُ بِهَا  ۚ  وَكَانَ اللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِيرا ً
Wa Law Qātalakumu Al-Ladhīna Kafarū Lawallaw Al-'Adbāra Thumma Lā Yajidūna Walīyāan Wa Lā Naşīrāan َ048-022 Kuma dã waɗanda suka kãfirta sun yãke ku, dã sun jũyar da ɗuwaiwai (dõmin gudu) sa'an nan bã zã su sãmi majiɓinci ba, kuma bã zã su sãmi mataimaki ba. وَلَوْ قَاتَلَكُمُ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوَلَّوْا الأَدْبَارَ ثُمَّ لاَ يَجِدُونَ وَلِيّا ً وَلاَ نَصِيرا ً
Sunnata Al-Lahi Allatī Qad Khalat Min Qablu  ۖ  Wa Lan Tajida Lisunnati Al-Lahi Tabdīlāan َ048-023 Hanyar Allah wadda ta shũɗe daga gabãnin wannan, kuma bã zã ka sãmi musanya ba ga hanyar Allah (ta taimakon mũminai akan mai zãluntarsu). سُنَّةَ اللَّهِ الَّتِي قَدْ خَلَتْ مِنْ قَبْلُ  ۖ  وَلَنْ تَجِدَ لِسُنَّةِ اللَّهِ تَبْدِيلا ً
Wa Huwa Al-Ladhī Kaffa 'Aydiyahum `Ankum Wa 'Aydiyakum `Anhum Bibaţni Makkata Min Ba`di 'An 'Ažfarakum `Alayhim  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu Bimā Ta`malūna Başīrāan َ048-024 Kuma Shĩ ne Ya kange hannayensu daga gare ku, kuma da hannayenku daga gare su, a cikin Makka, bãyan Ya rinjãyar da ku a kansu. Kuma Allah Ya kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa. وَهُوَ الَّذِي كَفَّ أَيْدِيَهُمْ عَنْكُمْ وَأَيْدِيَكُمْ عَنْهُمْ بِبَطْنِ مَكَّةَ مِنْ بَعْدِ أَنْ أَظْفَرَكُمْ عَلَيْهِمْ  ۚ  وَكَانَ اللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرا ً
Humu Al-Ladhīna Kafarū Wa Şaddūkum `Ani Al-Masjidi Al-Ĥarāmi Wa Al-Hadya Ma`kūfāan 'An Yablugha Maĥillahu  ۚ  Wa Lawlā Rijālun Mu'uminūna Wa Nisā'un Mu'uminātun Lam Ta`lamūhum 'An Taţa'ūhum Fatuşībakum Minhum Ma`arratun Bighayri `Ilmin  ۖ  Liyudkhila Al-Lahu Fī Raĥmatihi Man Yashā'u  ۚ  Law Tazayyalū La`adhdhab Al-Ladhīna Kafarū Minhum `Adhābāan 'Alīmāan َ048-025 Sũ ne waɗanda suka kãfirta kuma suka kange ku daga Masallacin Harami, da hadaya tanã tsare (sun hana ta) ta isa ga wurinta. Kuma bã dõmin waɗansu maza mũminai da waɗansu mãtã mũminai ba ba ku sansu ba ku tãkã su har wani aibi ya sãme ku daga gare su, bã da sani ba, (dã Allah Yã yi muku iznin yãƙi), dõmin Allah Ya shigar da wanda Yake so a cikin rahamarSa. Da (mũminai) sun tsabbace dã Mun azabtar da waɗanda suka kãfirta daga gare su da azãba mai raɗiɗi. هُمُ الَّذِينَ كَفَرُوا وَصَدُّوكُمْ عَنِ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ وَالْهَدْيَ مَعْكُوفاً أَنْ يَبْلُغَ مَحِلَّه ُُ  ۚ  وَلَوْلاَ رِجَال ٌ مُؤْمِنُونَ وَنِسَاء ٌ مُؤْمِنَات ٌ لَمْ تَعْلَمُوهُمْ أَنْ تَطَئُوهُمْ فَتُصِيبَكُمْ مِنْهُمْ مَعَرَّة ٌ بِغَيْرِ عِلْم ٍ  ۖ  لِيُدْخِلَ اللَّهُ فِي رَحْمَتِه ِِ مَنْ يَشَاءُ  ۚ  لَوْ تَزَيَّلُوا لَعَذَّبْنَا الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْهُمْ عَذَاباً أَلِيما ً
'Idh Ja`ala Al-Ladhīna Kafarū Fī Qulūbihimu Al-Ĥamīyata Ĥamīyata Al-Jāhilīyati Fa'anzala Al-Lahu Sakīnatahu `Alá Rasūlihi Wa `Alá Al-Mu'uminīna Wa 'Alzamahum Kalimata At-Taqwá Wa Kānū 'Aĥaqqa Bihā Wa 'Ahlahā  ۚ  Wa Kāna Al-Lahu Bikulli Shay'in `Alīmāan َ048-026 A lõkacin da waɗanda suka kãfirta suka sanya hanãnar ƙabĩ lanci a cikin zukãtansu hanãnar ƙabĩlanci irin na Jãhiliyya sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan ManzonSa, kuma da a kan mũminai kuma Ya lazimta musu kalmar taƙawa alhãli kuwa sun kasance mafi dãcẽwa da ita kuma ma'abutanta. Kuma Allah ya kasance Masani game da dukan kõme. إِذْ جَعَلَ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي قُلُوبِهِمُ الْحَمِيَّةَ حَمِيَّةَ الْجَاهِلِيَّةِ فَأَنْزَلَ اللَّهُ سَكِينَتَه ُُ عَلَى رَسُولِه ِِ وَعَلَى الْمُؤْمِنِينَ وَأَلْزَمَهُمْ كَلِمَةَ التَّقْوَى وَكَانُوا أَحَقَّ بِهَا وَأَهْلَهَا  ۚ  وَكَانَ اللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيما ً
Laqad Şadaqa Al-Lahu Rasūlahu Ar-Ru'uyā Bil-Ĥaqqi  ۖ  Latadkhulunna Al-Masjida Al-Ĥarāma 'In Shā'a Al-Lahu 'Āminīna Muĥalliqīna Ru'ūsakum Wa Muqaşşirīna Lā Takhāfūna  ۖ  Fa`alima Mā Lam Ta`lamū Faja`ala Min Dūni Dhālika Fatĥāan Qarībāan َ048-027 Lalle ne haƙĩƙa Allah Ya gaskata wa ManzonSa mafarkinsa da gaskiya: Lalle zã ku shiga Masallacin Harami, in Allah Ya so, kunã mãsu natsuwa, mãsu aske kawunanku da mãsu suisuye, bã ku jin tsõro, dõmin (Allah) Ya san abin da ba ku sani ba, sa'an nan Ya sanya wani cin nasara makusanci a bãyan wannan. لَقَدْ صَدَقَ اللَّهُ رَسُولَهُ الرُّؤْيَا بِالْحَقِّ  ۖ  لَتَدْخُلُنَّ الْمَسْجِدَ الْحَرَامَ إِنْ شَاءَ اللَّهُ آمِنِينَ مُحَلِّقِينَ رُءُوسَكُمْ وَمُقَصِّرِينَ لاَ تَخَافُونَ  ۖ  فَعَلِمَ مَا لَمْ تَعْلَمُوا فَجَعَلَ مِنْ دُونِ ذَلِكَ فَتْحا ً قَرِيبا ً
Huwa Al-Ladhī 'Arsala Rasūlahu Bil-Hudá Wa Dīni Al-Ĥaqqi Liyužhirahu `Alá Ad-Dīni Kullihi  ۚ  Wa Kafá Bil-Lahi Shahīdāan َ048-028 Shĩ ne wanda Ya aiki ManzonSa da shiriya da addinin gaskiya dõmin Ya rinjãyar da shi a kan addinai dukansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai shaida. هُوَ الَّذِي أَرْسَلَ رَسُولَه ُُ بِالْهُدَى وَدِينِ الْحَقِّ لِيُظْهِرَه ُُ عَلَى الدِّينِ كُلِّه ِِ  ۚ  وَكَفَى بِاللَّهِ شَهِيدا ً
Muĥammadun Rasūlu Al-Lahi Wa  ۚ  Al-Ladhīna Ma`ahu 'Ashiddā'u `Alá Al-Kuffāri Ruĥamā'u Baynahum  ۖ  Tarāhum Rukka`āan Sujjadāan Yabtaghūna Fađlāan Mina Al-Lahi Wa Riđwānāan  ۖ  Sīmāhum Fī Wujūhihim Min 'Athari As-Sujūdi  ۚ  Dhālika Mathaluhum At-Tawrāati  ۚ  Wa Mathaluhum Al-'Injīli Kazar`in 'Akhraja Shaţ'ahu Fa'āzarahu Fāstaghlaža Fāstawá `Alá Sūqihi Yu`jibu Az-Zurrā`a Liyaghīža Bihimu Al-Kuffāra  ۗ  Wa`ada Al-Lahu Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Minhum Maghfiratan Wa 'Ajrāan `Ažīmāan َ048-029 Muhammadu Manron Allah ne. Kuma waɗannan da ke tãre da shi mãsu tsanani ne a kan kãfirai, mãsu rahama ne a tsakãninsu, kanã ganin su sunã mãsu rukũ'i mãsu sujada, sunã nẽman falala daga Ubangijinsu, da yardarSa. Alãmarsu tanã a cikin fuskõkinsu, daga kufan sujuda. Wannan shĩ ne siffarsu a cikin Attaura. Kuma siffarsu,a cikin Injĩla ita ce kamar tsiron shũka wanda ya fitar da rẽshensa, sa'an nan ya ƙarfafa shi, ya yi kauri, sa'an nan ya daidaita a kan ƙafãfunsa, yanã bãyar da sha'awa ga mãsu shũkar' dõmin (Allah) Ya fusãtar da kãfirai game da su. Kuma Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga cikinsu, da gãfara da ijãra mai girma. مُحَمَّد ٌ رَسُولُ اللَّهِ  ۚ  وَالَّذِينَ مَعَهُ~ُ أَشِدَّاءُ عَلَى الْكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَيْنَهُمْ  ۖ  تَرَاهُمْ رُكَّعا ً سُجَّدا ً يَبْتَغُونَ فَضْلا ً مِنَ اللَّهِ وَرِضْوَانا ً  ۖ  سِيمَاهُمْ فِي وُجُوهِهِمْ مِنْ أَثَرِ السُّجُودِ  ۚ  ذَلِكَ مَثَلُهُمْ فِي التَّوْرَاةِ  ۚ  وَمَثَلُهُمْ فِي الإِنجِيلِ كَزَرْعٍ أَخْرَجَ شَطْأَه ُُ فَآزَرَه ُُ فَاسْتَغْلَظَ فَاسْتَوَى عَلَى سُوقِه ِِ يُعْجِبُ الزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ الْكُفَّارَ  ۗ  وَعَدَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ مِنْهُمْ مَغْفِرَة ً وَأَجْراً عَظِيما ً
Next Sūrah