46) Sūrat Al-'Aĥqāf

Printed format

46) سُورَة الأَحقَاف

Ĥā-Mīm َ046-001 Ḥ. M̃. حَا-مِيم
Tanzīlu Al-Kitābi Mina Al-Lahi Al-`Azīzi Al-Ĥakīmi َ046-002 Saukar da littafi daga Allah, Mabuwãyi, Mai hikima yake. تَنْزِيلُ الْكِتَابِ مِنَ اللَّهِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ
Khalaq As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Wa Mā Baynahumā 'Illā Bil-Ĥaqqi Wa 'Ajalin Musammáan Wa  ۚ  Al-Ladhīna Kafarū `Ammā 'Undhirū Mu`rūna َ046-003 Ba Mu halitta sammai da ƙasa ba, da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da wani ajali ambatacce, kuma waɗanda suka kãfirta, mãsu bijirẽwa ne daga abin da aka yi musu gargaɗi (da shi). مَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا إِلاَّ بِالْحَقِّ وَأَجَل ٍ مُسَمّى ً  ۚ  وَالَّذِينَ كَفَرُوا عَمَّا أُنْذِرُوا مُعْرِضُونَ
Qul 'Ara'aytum Mā Tad`ūna Min Dūni Al-Lahi 'Arūnī Mādhā Khalaqū Mina Al-'Arđi 'Am Lahum Shirkun As-Samāwāti  ۖ  Ai'tūnī Bikitābin Min Qabli Hādhā 'Aw 'Athāratin Min `Ilmin 'In Kuntum Şādiqīna َ046-004 Ka ce: "Shin, kun gani, abin da kuke kira, wanda yake baicin Allah? Ku nũna mini, menene suka halitta daga ƙasa? Kõ kuwa sunã da tãrayya a cikin sammai? Ku zo mini da wani littãfi na gabãnin wannan (Alƙur'ãni) kõ wata alãma daga wani ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya." قُلْ أَرَأَيْتُمْ مَا تَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُوا مِنَ الأَرْضِ أَمْ لَهُمْ شِرْك ٌ فِي السَّمَاوَاتِ  ۖ  اِئْتُونِي بِكِتَاب ٍ مِنْ قَبْلِ هَذَا أَوْ أَثَارَة ٍ مِنْ عِلْم ٍ إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ
Wa Man 'Ađallu Mimman Yad`ū Min Dūni Al-Lahi Man Lā Yastajību Lahu 'Ilá Yawmi Al-Qiyāmati Wa Hum `An Du`ā'ihim Ghāfilūna َ046-005 Kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ke kiran wanin Allah wanda da bã zai karɓa masa ba, bar Rãnar Kyama, alhãli sũ (waɗanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiransu? وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّنْ يَدْعُو مِنْ دُونِ اللَّهِ مَنْ لاَ يَسْتَجِيبُ لَهُ~ُ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ وَهُمْ عَنْ دُعَائِهِمْ غَافِلُونَ
Wa 'Idhā Ĥushira An-Nāsu Kānū Lahum 'A`dā'an Wa Kānū Bi`ibādatihim Kāfirīna َ046-006 Kuma idan aka tãra mutãne sai su kasance maƙiya a gare su, alhãli sun kasance mãsu ƙi ga ibãdarsu. وَإِذَا حُشِرَ النَّاسُ كَانُوا لَهُمْ أَعْدَاء ً وَكَانُوا بِعِبَادَتِهِمْ كَافِرِينَ
Wa 'Idhā Tutlá `Alayhim 'Āyātunā Bayyinātin Qāla Al-Ladhīna Kafarū Lilĥaqqi Lammā Jā'ahumdhā Siĥrun Mubīnun َ046-007 Kuma idan anã karãtun ãyõòyinMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta ga gaskiya a lõkacin da ta jẽ musu, su ce, "Wannan sihiri ne bayyananne." وَإِذَا تُتْلَى عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَات ٍ قَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلْحَقِّ لَمَّا جَاءَهُمْ هَذَا سِحْر ٌ مُبِين ٌ
'Am Yaqūlūna Aftarāhu  ۖ  Qul 'Ini Aftaraytuhu Falā Tamlikūna Lī Mina Al-Lahi Shay'āan  ۖ  Huwa 'A`lamu Bimā Tufīđūna Fīhi  ۖ  Kafá Bihi Shahīdāan Baynī Wa Baynakum  ۖ  Wa Huwa Al-Ghafūru Ar-Raĥīmu َ046-008 Kõkuwã sunã cẽwa: "Yã ƙirƙira shi (Alƙur'ãni) ne?" Ka ce: "Idan na ƙirƙira shi ne, to bã ku mallaka mini kõme daga Allah. Shĩ ne Mafi sani ga abin da kuke kũtsãwa a cikinsa na magana. (Allah) Yã isa Ya zama shaida a tsakãnĩnada tsakãninku. Kuma shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." أَمْ يَقُولُونَ افْتَرَاه ُُ  ۖ  قُلْ إِنِ افْتَرَيْتُه ُُ فَلاَ تَمْلِكُونَ لِي مِنَ اللَّهِ شَيْئاً  ۖ  هُوَ أَعْلَمُ بِمَا تُفِيضُونَ فِيه ِِ  ۖ  كَفَى بِه ِِ شَهِيدا ً بَيْنِي وَبَيْنَكُمْ  ۖ  وَهُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
Qul Mā Kuntu Bid`āan Mina Ar-Rusuli Wa Mā 'Adrī Mā Yuf`alu Bī Wa Lā Bikum  ۖ  'In 'Attabi`u 'Illā Mā Yūĥá 'Ilayya Wa Mā 'Anā 'Illā Nadhīrun Mubīnun َ046-009 Ka ce: "Ban kasance fãrau ba daga Manzanni, kuma ban san abin da zã a yi game da ni kõ game da ku (na gaibi) ba, bã ni bin kõme fãce abin da ake yin wahayi zuwa gare ni, kuma ban zama ba, fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa." قُلْ مَا كُنْتُ بِدْعا ً مِنَ الرُّسُلِ وَمَا أَدْرِي مَا يُفْعَلُ بِي وَلاَ بِكُمْ  ۖ  إِنْ أَتَّبِعُ إِلاَّ مَا يُوحَى إِلَيَّ وَمَا أَنَا إِلاَّ نَذِير ٌ مُبِين ٌ
Qul 'Ara'aytum 'In Kāna Min `Indi Al-Lahi Wa Kafartum Bihi Wa Shahida Shāhidun Min Banī 'Isrā'īla `Alá Mithlihi Fa'āmana Wa Astakbartum  ۖ  'Inna Al-Laha Lā Yahdī Al-Qawma Až-Žālimīna َ046-010 Ka ce: "Shin, kun gani, idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga wurin Allah yake, kuma kuka kãfirta da shi, kuma wani mai shaida daga Banĩ Isrã'ĩla ya bãyar da shaida a kan kwatankwacinsa, sa'an nan ya yi ĩmãni, kuma kuka kangare? Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai." قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ كَانَ مِنْ عِنْدِ اللَّهِ وَكَفَرْتُمْ بِه ِِ وَشَهِدَ شَاهِد ٌ مِنْ بَنِي إِسْرَائِيلَ عَلَى مِثْلِه ِِ فَآمَنَ وَاسْتَكْبَرْتُمْ  ۖ  إِنَّ اللَّهَ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ
Wa Qāla Al-Ladhīna Kafarū Lilladhīna 'Āmanū Law Kāna Khayrāan Mā Sabaqūnā 'Ilayhi  ۚ  Wa 'Idh Lam Yahtadū Bihi Fasayaqūlūna Hādhā 'Ifkun Qadīmun َ046-011 Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni: "Da (Alƙur'ãni) ya kasance, wani alhẽri ne," dã ba su riga muzuwa gare shi ba. Kuma tun da ba su shiryu game da shĩ ba, to, zã su ce, "Wannan ƙiren ƙarya ne daɗaɗɗe." وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلَّذِينَ آمَنُوا لَوْ كَانَ خَيْرا ً مَا سَبَقُونَا إِلَيْهِ  ۚ  وَإِذْ لَمْ يَهْتَدُوا بِه ِِ فَسَيَقُولُونَ هَذَا إِفْك ٌ قَدِيم ٌ
Wa Min Qablihi Kitābu Mūsá 'Imāmāan Wa Raĥmatan  ۚ  Wa Hadhā Kitābun Muşaddiqun Lisānāan `Arabīyāan Liyundhira Al-Ladhīna Žalamū Wa Bushrá Lilmuĥsinīna َ046-012 Alhãli kuwa a gabãninsa akwai littãfin Mũsã, wanda ya kasance abin kõyi, kuma rahama. Kuma wannan (Alƙur'ãni) littafi ne mai gaskatãwa (ga littafin Mũsã), a harshe na Larabci dõmin ya gargaɗi waɗanda suka yi zãlunci, kuma ya zama bushãra ga mãsu kyautatãwa. وَمِنْ قَبْلِه ِِ كِتَابُ مُوسَى إِمَاما ً وَرَحْمَة ً  ۚ  وَهَذَا كِتَاب ٌ مُصَدِّق ٌ لِسَاناً عَرَبِيّا ً لِيُنْذِرَ الَّذِينَ ظَلَمُوا وَبُشْرَى لِلْمُحْسِنِينَ
'Inna Al-Ladhīna Qālū Rabbunā Al-Lahu Thumma Astaqāmū Falā Khawfun `Alayhim Wa Lā Hum Yaĥzanūna َ046-013 Lalle ne waɗanda suka ce: "Ubangijinmu Allah ne," sa'an nan suka daidaitu, to, bãbu wani tsõro a kansu, kuma bã zã su yi baƙin ciki ba. إِنَّ الَّذِينَ قَالُوا رَبُّنَا اللَّهُ ثُمَّ اسْتَقَامُوا فَلاَ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ
'Ūlā'ika 'Aşĥābu Al-Jannati Khālidīna Fīhā Jazā'an Bimā Kānū Ya`malūna َ046-014 Waɗannan 'yan Aljanna ne, sunã madawwama a cikinta, a kan sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa. أُوْلَائِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ خَالِدِينَ فِيهَا جَزَاء ً بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Wa Waşşaynā Al-'Insāna Biwālidayhi 'Iĥsānāan  ۖ  Ĥamalat/hu 'Ummuhu Kurhāan Wa Wađa`at/hu Kurhāan  ۖ  Wa Ĥamluhu Wa Fişāluhu Thalāthūna Shahrāan  ۚ  Ĥattá 'Idhā Balagha 'Ashuddahu Wa Balagha 'Arba`īna Sanatan Qāla Rabbi 'Awzi`nī 'An 'Ashkura Ni`mataka Allatī 'An`amta `Alayya Wa `Alá Wa A-Dayya Wa 'An 'A`mala Şāliĥāan Tarđāhu Wa 'Aşliĥ Lī Fī Dhurrīyatī  ۖ  'Innī Tubtu 'Ilayka Wa 'Innī Mina Al-Muslimīna َ046-015 Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu da kyautatãwa, uwarsa tã yi cikinsa wahala, kuma ta haife shi wahala. cikinsa da yãyensa watã talãtin. Har a lõkacin da ya kai ga mafi ƙarfinsa, kuma ya kai shẽkara arba'in,ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka kange nidõmin in gõde wa ni'imarKa, wadda Ka ni'imta a kaina da kuma a kan mahaifãna biyu, kuma dõmin in aikata aikin ƙwarai wanda Kake yarda da shi, kuma Ka kyautata mini a cikin zuriyata. Lalle nĩ, nã tũba zuwa gare Ka, kuma lalle ni, inã daga mãsu sallamãwa (ga umurninKa)." وَوَصَّيْنَا الإِنسَانَ بِوَالِدَيْهِ إِحْسَاناً  ۖ  حَمَلَتْهُ أُمُّه ُُ كُرْها ً وَوَضَعَتْهُ كُرْها ً  ۖ  وَحَمْلُه ُُ وَفِصَالُه ُُ ثَلاَثُونَ شَهْراً  ۚ  حَتَّى إِذَا بَلَغَ أَشُدَّه ُُ وَبَلَغَ أَرْبَعِينَ سَنَة ً قَالَ رَبِّ أَوْزِعْنِي أَنْ أَشْكُرَ نِعْمَتَكَ الَّتِي أَنْعَمْتَ عَلَيَّ وَعَلَى وَالِدَيَّ وَأَنْ أَعْمَلَ صَالِحا ً تَرْضَاه ُُ وَأَصْلِحْ لِي فِي ذُرِّيَّتِي  ۖ  إِنِّي تُبْتُ إِلَيْكَ وَإِنِّي مِنَ الْمُسْلِمِينَ
'Ūlā'ika Al-Ladhīna Nataqabbalu `Anhum 'Aĥsana Mā `Amilū Wa Natajāwazu `An Sayyi'ātihim Fī 'Aşĥābi Al-Jannati  ۖ  Wa`da Aş-Şidqi Al-Ladhī Kānū Yū`adūna َ046-016 Waɗancan ne waɗanda Muke karɓa, daga gare su, mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Muke gãfarta mafi mũnanan ayyukansum (sunã) a cikin 'yan Aljanna, a kan wa'adin gaskiya wanda suka kasance anã yi musu alkawari (da shi). أُوْلَائِكَ الَّذِينَ نَتَقَبَّلُ عَنْهُمْ أَحْسَنَ مَا عَمِلُوا وَنَتَجاوَزُ عَنْ سَيِّئَاتِهِمْ فِي أَصْحَابِ الْجَنَّةِ  ۖ  وَعْدَ الصِّدْقِ الَّذِي كَانُوا يُوعَدُونَ
Wa Al-Ladhī Qāla Liwālidayhi 'Uffin Lakumā 'Ata`idāninī 'An 'Ukhraja Wa Qad Khalati Al-Qurūnu Min Qablī Wa Humā Yastaghīthāni Al-Laha Waylaka 'Āmin 'Inna Wa`da Al-Lahi Ĥaqqun Fayaqūlu Mā Hādhā 'Illā 'Asāţīru Al-'Awwalīna َ046-017 Kuma wanda ya ce wa mahaifansa biyu: "Tir gare ku! shin, kunã tsõratar da ni cẽwa zã a fitar da ni daga (kabari) ne, alhãli kuwa ƙarnõni na mutãne da yawa sun shũɗe a gabãnĩna (ba su kõmo ba)?" Kuma sũ (mahaifan) sunã nẽman Allah taimako (sunãce masa) "Kaitonka! Ka yi ĩmãni, lalle wa'adin Allah gaskiya ne." Sai shi kuma ya ce. "Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko." وَالَّذِي قَالَ لِوَالِدَيْهِ أُفّ ٍ لَكُمَا أَتَعِدَانِنِي أَنْ أُخْرَجَ وَقَدْ خَلَتِ الْقُرُونُ مِنْ قَبْلِي وَهُمَا يَسْتَغِيثَانِ اللَّهَ وَيْلَكَ آمِنْ إِنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقّ ٌ فَيَقُولُ مَا هَذَا إِلاَّ أَسَاطِيرُ الأَوَّلِينَ
'Ūlā'ika Al-Ladhīna Ĥaqqa `Alayhimu Al-Qawlu Fī 'Umamin Qad Khalat Min Qablihim Mina Al-Jinni Wa Al-'Insi  ۖ  'Innahum Kānū Khāsirīna َ046-018 Waɗancan ne waɗanda kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin al'ummõmi waɗanda suka shũɗe, (bã da daɗẽwa ba), a gabãninsu, daga aljannu da mutãne. Lalle sũ, sun kasance mãsu hasãra. أُوْلَائِكَ الَّذِينَ حَقَّ عَلَيْهِمُ الْقَوْلُ فِي أُمَم ٍ قَدْ خَلَتْ مِنْ قَبْلِهِمْ مِنَ الْجِنِّ وَالإِنسِ  ۖ  إِنَّهُمْ كَانُوا خَاسِرِينَ
Wa Likullin Darajātun Mimmā `Amilū  ۖ  Wa Liyuwaffiyahum 'A`mālahum Wa Hum Lā Yužlamūna َ046-019 Kuma ga kõwane nau'i, yanã da darajõji daga abinda suka aikata. Kuma dõmin (Allah) Ya cika musu (sakamakon) ayyukansu, alhãli kuwa sũ, bã zã a zãlunce su ba. وَلِكُلّ ٍ دَرَجَات ٌ مِمَّا عَمِلُوا  ۖ  وَلِيُوَفِّيَهُمْ أَعْمَالَهُمْ وَهُمْ لاَ يُظْلَمُونَ
Wa Yawma Yu`rađu Al-Ladhīna Kafarū `Alá An-Nāri 'Adh/habtum Ţayyibātikum Fī Ĥayātikumu Ad-Dunyā Wa Astamta`tum Bihā Fālyawma Tujzawna `Adhāba Al-Hūni Bimā Kuntum Tastakbirūna Fī Al-'Arđi Bighayri Al-Ĥaqqi Wa Bimā Kuntum Tafsuqūna َ046-020 Kuma rãnar da ake gitta waɗanda suka kãflrta a kan wutã ( a ce musu): "Kun tafiyar da abũbuwanku na jin dãɗi a cikin rayuwarku ta dũniya, kuma kun nẽmi jin dãdi da su, to, ayau anã sãka muka da azãbar wulãkanci, dõmin abin da kuka kasance kanã yi na gmian kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, kuma dõmin abin da kuka kasance kuna yi na fãsiƙansi." وَيَوْمَ يُعْرَضُ الَّذِينَ كَفَرُوا عَلَى النَّارِ أَذْهَبْتُمْ طَيِّبَاتِكُمْ فِي حَيَاتِكُمُ الدُّنْيَا وَاسْتَمْتَعْتُمْ بِهَا فَالْيَوْمَ تُجْزَوْنَ عَذَابَ الْهُونِ بِمَا كُنْتُمْ تَسْتَكْبِرُونَ فِي الأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَبِمَا كُنْتُمْ تَفْسُقُونَ
Wa Adhkur 'Akhā `Ādin 'Idh 'Andhara Qawmahu Bil-'Aĥqāfi Wa Qad Khalati An-Nudhuru Min Bayni Yadayhi Wa Min Khalfihi 'Allā Ta`budū 'Illā Al-Laha 'Innī 'Akhāfu `Alaykum `Adhāba Yawmin `Ažīmin َ046-021 Kuma ka ambaci ɗan'uwan Ãdãwa a lõkacin da ya yi gargaɗi ga mutãnensa, a Tuddan Rairayi, alhãli kuwa waɗansu mãsu gargaɗi sun shũɗe agaba gare shi da bãya gare shi (da cẽwa) "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ inã tsõrata muku azãbar yini mai girma." وَاذْكُرْ أَخَا عَاد ٍ إِذْ أَنْذَرَ قَوْمَه ُُ بِالأَحْقَافِ وَقَدْ خَلَتِ النُّذُرُ مِنْ بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ خَلْفِهِ~ِ أَلاَّ تَعْبُدُوا إِلاَّ اللَّهَ إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيم ٍ
Qālū 'Aji'tanā Lita'fikanā `An 'Ālihatinā Fa'tinā Bimā Ta`idunā 'In Kunta Mina Aş-Şādiqīna َ046-022 Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin ka karkatar da mu daga gumãkaumu? To, ka zo mana da abin da kake yi mana wa'adin, idan kã kasance daga mãsu gaskiya." قَالُوا أَجِئْتَنَا لِتَأْفِكَنَا عَنْ آلِهَتِنَا فَأْتِنَا بِمَا تَعِدُنَا إِنْ كُنْتَ مِنَ الصَّادِقِينَ
Qāla 'Innamā Al-`Ilmu `Inda Al-Lahi Wa 'Uballighukum Mā 'Ursiltu Bihi Wa Lakinnī 'Arākum Qawmāan Tajhalūna َ046-023 Ya ce: "Ilimi a wurin Allah kawai yake, kuma inã iyar maku abin da aka aiko ni da shi, kuma amma inã ganin, kũ, wasu mutãne ne, kunã jãhiltar gaskiya." قَالَ إِنَّمَا الْعِلْمُ عِنْدَ اللَّهِ وَأُبَلِّغُكُمْ مَا أُرْسِلْتُ بِه ِِ وَلَكِنِّي أَرَاكُمْ قَوْما ً تَجْهَلُونَ
Falammā Ra'awhu `Āriđāan Mustaqbila 'Awdiyatihim Qālū Hādhā `Āriđun Mumţirunā  ۚ  Bal Huwa Mā Asta`jaltum Bihi  ۖ  Rīĥun Fīhā `Adhābun 'Alīmun َ046-024 To, a lõkacin da suka ga azãbar, kumar hadari mai fuskantar rãfukansu, suka ce: "Wannan hadari ne mai yi mana ruwa. Ã'a, shĩ na abin da kuke nẽman gaggawar saukarsa; Iska ce, a cikinta akwai wata azaba mai raɗaɗi. فَلَمَّا رَأَوْهُ عَارِضا ً مُسْتَقْبِلَ أَوْدِيَتِهِمْ قَالُوا هَذَا عَارِض ٌ مُمْطِرُنَا  ۚ  بَلْ هُوَ مَا اسْتَعْجَلْتُمْ بِه ِِ  ۖ  رِيح ٌ فِيهَا عَذَابٌ أَلِيم ٌ
Tudammiru Kulla Shay'in Bi'amri Rabbihā Fa'aşbaĥū Lā Yurá 'Illā Masākinuhum  ۚ  Kadhālika Naj Al-Qawma Al-Mujrimīna َ046-025 Tanã darkake kõwane abu da umurnin Ubangijinta. Sai suka wãyi gari, bã a ganin kõme fãce gidãjensu. Kamar wannan ne Muke sãka wa mutãne mãsu laifi. تُدَمِّرُ كُلَّ شَيْء ٍ بِأَمْرِ رَبِّهَا فَأَصْبَحُوا لاَ يُرَى إِلاَّ مَسَاكِنُهُمْ  ۚ  كَذَلِكَ نَجْزِي الْقَوْمَ الْمُجْرِمِينَ
Wa Laqad Makkannāhum Fīmā 'In Makkannākum Fīhi Wa Ja`alnā Lahum Sam`āan Wa 'Abşārāan Wa 'Af'idatan Famā 'Aghná `Anhum Sam`uhum Wa Lā 'Abşāruhum Wa Lā 'Af'idatuhum Min Shay'in 'Idh Kānū Yajĥadūna Bi'āyāti Al-Lahi Wa Ĥāqa Bihim Mā Kānū Bihi Yastahzi'ūn َ046-026 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun ba su ĩko ga abin da ba Mubã ku ĩko gare shi ba, kuma Muka sanya musu wani irin jĩ da gani dazukãta. Sai dai jnsu bai amfãne su ba, kuma zukãtansu ba su amfãne su ba ga kõme, dõmin sun kasance sunã musu game da ãyõyin Allah, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa na izgili game da shi ya wajaba a gare su. وَلَقَدْ مَكَّنَّاهُمْ فِيمَا إِنْ مَكَّنَّاكُمْ فِيه ِِ وَجَعَلْنَا لَهُمْ سَمْعا ً وَأَبْصَارا ً وَأَفْئِدَة ً فَمَا أَغْنَى عَنْهُمْ سَمْعُهُمْ وَلاَ أَبْصَارُهُمْ وَلاَ أَفْئِدَتُهُمْ مِنْ شَيْء ٍ إِذْ كَانُوا يَجْحَدُونَ بِآيَاتِ اللَّهِ وَحَاقَ بِهِمْ مَا كَانُوا بِه ِِ يَسْتَهْزِئُون
Wa Laqad 'Ahlaknā Mā Ĥawlakum Mina Al-Qurá Wa Şarrafnā Al-'Āyāti La`allahum Yarji`ūna َ046-027 Kuma ne, lalle haƙĩƙa, Mun halakar da abin da yake kẽwayenku na alƙaryu kuma Muka jujjũya ãyõyi, tsammãninsu zã su kõmo. وَلَقَدْ أَهْلَكْنَا مَا حَوْلَكُمْ مِنَ الْقُرَى وَصَرَّفْنَا الآيَاتِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ
Falawlā Naşarahumu Al-Ladhīna Attakhadhū Min Dūni Al-Lahi Qurbānāan 'Ālihatan  ۖ  Bal Đallū `Anhum  ۚ  Wa Dhalika 'Ifkuhum Wa Mā Kānū Yaftarūna َ046-028 To, don mẽne ne waɗanda suka riƙa, baicin Allah, abũbuwan yi.wa baiko, gumaka, ba su taimake su ba ? Ã'a, sun ɓace musu Kuma wannan shi ne ƙiren ƙaryarsu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa. فَلَوْلاَ نَصَرَهُمُ الَّذِينَ اتَّخَذُوا مِنْ دُونِ اللَّهِ قُرْبَانا ً آلِهَة ً  ۖ  بَلْ ضَلُّوا عَنْهُمْ  ۚ  وَذَلِكَ إِفْكُهُمْ وَمَا كَانُوا يَفْتَرُونَ
Wa 'Idh Şarafnā 'Ilayka Nafarāan Mina Al-Jinni Yastami`ūna Al-Qur'āna Falammā Ĥađarūhu Qālū 'Anşitū  ۖ  Falammā Quđiya Wa Llaw 'Ilá Qawmihim Mundhirīna َ046-029 Kuma a lõkcin da Muka jũya waɗansu jama'a na aljamiu zuwa gare ka sunã saurãren Alƙur'ãni. To, alõkacin da suka halarce shi suka ce: "Ku yi shiru." Sa'an nan da aka ƙãre, suka jũya zuwa ga jama'arsu sunã mãsu gargaɗi. وَإِذْ صَرَفْنَا إِلَيْكَ نَفَرا ً مِنَ الْجِنِّ يَسْتَمِعُونَ الْقُرْآنَ فَلَمَّا حَضَرُوه ُُ قَالُوا أَنْصِتُوا  ۖ  فَلَمَّا قُضِيَ وَلَّوْا إِلَى قَوْمِهِمْ مُنْذِرِينَ
Qālū Yā Qawmanā 'Innā Sami`nā Kitābāan 'Unzila Min Ba`di Mūsá Muşaddiqāan Limā Bayna Yadayhi Yahdī 'Ilá Al-Ĥaqqi Wa 'Ilá Ţarīqin Mustaqīmin َ046-030 Suka ce: "Ya mutãnenmu! Lalle mũ, mun ji wani littãfi an saukar da shi a bãyãn Mũsã,mai gaskatãwa ga abin da ke a gaba da shi, yanã shiryarwa ga gaskiya da kuma zuwa ga hanya madaidaiciya. قَالُوا يَا قَوْمَنَا إِنَّا سَمِعْنَا كِتَاباً أُنْزِلَ مِنْ بَعْدِ مُوسَى مُصَدِّقا ً لِمَا بَيْنَ يَدَيْهِ يَهْدِي إِلَى الْحَقِّ وَإِلَى طَرِيق ٍ مُسْتَقِيم ٍ
Yā Qawmanā 'Ajībū Dā`iya Al-Lahi Wa 'Āminū Bihi Yaghfir Lakum Min Dhunūbikum Wa Yujirkum Min `Adhābin 'Alīmin َ046-031 "Yã mutãnenmu! Ku karɓa wa mai kiran Allah, kuma ku yi ĩmãni da Shi, Ya gãfarta muku daga zunubanku, kuma ya tserar da ku daga azãba mai raɗaɗi. يَا قَوْمَنَا أَجِيبُوا دَاعِيَ اللَّهِ وَآمِنُوا بِه ِِ يَغْفِرْ لَكُمْ مِنْ ذُنُوبِكُمْ وَيُجِرْكُمْ مِنْ عَذَابٍ أَلِيم ٍ
Wa Man Lā Yujib Dā`iya Al-Lahi Falaysa Bimu`jizin Al-'Arđi Wa Laysa Lahu Min Dūnihi 'Awliyā'u  ۚ  'Ūlā'ika Fī Đalālin Mubīnin َ046-032 "Kuma wanda bai karɓa wa mai kiran Allah ba to bai zama mai buwãya a cikin ƙasa ba, kuma ba ya da waɗansu majiɓinta, baicin Shi. Waɗannnan sunã a cikin ɓata bayyananna." وَمَنْ لاَ يُجِبْ دَاعِيَ اللَّهِ فَلَيْسَ بِمُعْجِز ٍ فِي الأَرْضِ وَلَيْسَ لَه ُُ مِنْ دُونِهِ~ِ أَولِيَاءُ  ۚ  أُوْلَائِكَ فِي ضَلاَل ٍ مُبِين ٍ
'Awalam Yaraw 'Anna Al-Laha Al-Ladhī Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Wa Lam Ya`ya Bikhalqihinna Biqādirin `Alá 'An Yuĥyiya Al-Mawtá  ۚ  Balá 'Innahu `Alá Kulli Shay'in Qadīrun َ046-033 Shin, kuma ba su gani ba cẽwa: "Lalle Allah, Wanda Yã halitta sammai da ƙasa kuma bai kãsa ga halittarsu ba, Mai ĩkon yi ne a kan rãyar da matattu?" Na'am, lalle Shi, Mai ĩkon yi ne a kan kõme. أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّ اللَّهَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَلَمْ يَعْيَ بِخَلْقِهِنَّ بِقَادِرٍ عَلَى أَنْ يُحْيِيَ الْمَوْتَى  ۚ  بَلَى إِنَّه ُُ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِير ٌ
Wa Yawma Yu`rađu Al-Ladhīna Kafarū `Alá An-Nāri 'Alaysa Hādhā Bil-Ĥaqqi  ۖ  Qālū Balá Wa Rabbinā  ۚ  Qāla Fadhūqū Al-`Adhāba Bimā Kuntum Takfurūna َ046-034 Kuma rãnar da ake gittar da waɗanda suka kãfirta a kan wutã, (a ce musu) "Ashe, wannan bã gaskiya ba ne?" Su ce: "Na'am, gaskiya ne, mun rantse da Ubangijinmu!" Sai Ya ce, "To, ku ɗanɗani azãbar sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci." وَيَوْمَ يُعْرَضُ الَّذِينَ كَفَرُوا عَلَى النَّارِ أَلَيْسَ هَذَا بِالْحَقِّ  ۖ  قَالُوا بَلَى وَرَبِّنَا  ۚ  قَالَ فَذُوقُوا الْعَذَابَ بِمَا كُنْتُمْ تَكْفُرُونَ
Fāşbir Kamā Şabara 'Ū Al-`Azmi Mina Ar-Rusuli Wa Lā Tasta`jil Lahum  ۚ  Ka'annahum Yawma Yarawna Mā Yū`adūna Lam Yalbathū 'Illā Sā`atan Min Nahārin  ۚ  Balāghun  ۚ  Fahal Yuhlaku 'Illā Al-Qawmu Al-Fāsiqūna َ046-035 Sabõda haka, ka yi haƙuri kamar yadda mãsu ƙarfin niyya daga Manzanni suka yi haƙuri. Kuma kada ka yi musu gaggãwa. Kamar dai sũ, a rãnar da suke ganin (sakamako) abin da ake yi musu wa'adi ba su zauna ba, fãce sa'a guda daga yini. Iyarwa dai da Manzanci). Shin, akwai wanda za a halakar? (Bãbu), fãce mutãne fasiƙai. فَاصْبِرْ كَمَا صَبَرَ أُوْلُوا الْعَزْمِ مِنَ الرُّسُلِ وَلاَ تَسْتَعْجِلْ لَهُمْ  ۚ  كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَ مَا يُوعَدُونَ لَمْ يَلْبَثُوا إِلاَّ سَاعَة ً مِنْ نَهَار ٍ  ۚ  بَلاَغ ٌ  ۚ  فَهَلْ يُهْلَكُ إِلاَّ الْقَوْمُ الْفَاسِقُونَ
Next Sūrah