44) Sūrat Ad-Dukhān

Printed format

44) سُورَة الدُّخَان

Ĥā-Mīm َ044-001 Ḥ. M̃. حَا-مِيم
Wa Al-Kitābi Al-Mubīni َ044-002 Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani. وَالْكِتَابِ الْمُبِينِ
'Innā 'Anzalnāhu Fī Laylatin Mubārakatin  ۚ  'Innā Kunnā Mundhirīna َ044-003 Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi. إِنَّا أَنزَلْنَاه ُُ فِي لَيْلَة ٍ مُبَارَكَة ٍ  ۚ  إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ
Fīhā Yufraqu Kullu 'Amrin Ĥakīmin َ044-004 A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne. فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيم ٍ
'Amrāan Min `Indinā  ۚ  'Innā Kunnā Mursilīna َ044-005 Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã. أَمْرا ً مِنْ عِنْدِنَا  ۚ  إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ
Raĥmatan Min Rabbika  ۚ  'Innahu Huwa As-Samī`u Al-`Alīmu َ044-006 Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani. رَحْمَة ً مِنْ رَبِّكَ  ۚ  إِنَّه ُُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Rabbi As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Mā Baynahumā  ۖ  'In Kuntum Mūqinīna َ044-007 (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka). رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا  ۖ  إِنْ كُنْتُمْ مُوقِنِينَ
Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Yuĥyī Wa Yumītu  ۖ  Rabbukum Wa Rabbu 'Ābā'ikumu Al-'Awwalīna َ044-008 Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko. لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ  ۖ  رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الأَوَّلِينَ
Bal HumShakkin Yal`abūna َ044-009 A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka. بَلْ هُمْ فِي شَكّ ٍ يَلْعَبُونَ
Fārtaqib Yawma Ta'tī As-Samā'u Bidukhānin Mubīnin َ044-010 Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne. فَارْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِي السَّمَاءُ بِدُخَان ٍ مُبِين ٍ
Yaghshá An-Nāsa  ۖ  Hādhā `Adhābun 'Alīmun َ044-011 Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi. يَغْشَى النَّاسَ  ۖ  هَذَا عَذَابٌ أَلِيم ٌ
Rabbanā Akshif `Annā Al-`Adhāba 'Innā Mu'uminūna َ044-012 Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne. رَبَّنَا اكْشِفْ عَنَّا الْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَ
'Anná Lahumu Adh-Dhikrá Wa Qad Jā'ahum Rasūlun Mubīnun َ044-013 Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)? أَنَّى لَهُمُ الذِّكْرَى وَقَدْ جَاءَهُمْ رَسُول ٌ مُبِين ٌ
Thumma Tawallaw `Anhu Wa Qālū Mu`allamun Majnūnun َ044-014 Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci." ثُمَّ تَوَلَّوْا عَنْهُ وَقَالُوا مُعَلَّم ٌ مَجْنُون ٌ
'Innā Kāshifū Al-`Adhābi Qalīlāan  ۚ  'Innakum `Ā'idūna َ044-015 Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin). إِنَّا كَاشِفُوا الْعَذَابِ قَلِيلا ً  ۚ  إِنَّكُمْ عَائِدُونَ
Yawma Nabţishu Al-Baţshata Al-Kubrá 'Innā Muntaqimūna َ044-016 Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne. يَوْمَ نَبْطِشُ الْبَطْشَةَ الْكُبْرَى إِنَّا مُنتَقِمُونَ
Wa Laqad Fatannā Qablahum Qawma Fir`awna Wa Jā'ahum Rasūlun Karīmun َ044-017 Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu. وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَاءَهُمْ رَسُول ٌ كَرِيم ٌ
'An 'Addū 'Ilayya `Ibāda Al-Lahi  ۖ  'Innī Lakum Rasūlun 'Amīnun َ044-018 (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku." أَنْ أَدُّوا إِلَيَّ عِبَادَ اللَّهِ  ۖ  إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِين ٌ
Wa 'An Lā Ta`lū `Alá Al-Lahi  ۖ  'Innī 'Ātīkum Bisulţānin Mubīnin َ044-019 "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne." وَأَنْ لاَ تَعْلُوا عَلَى اللَّهِ  ۖ  إِنِّي آتِيكُمْ بِسُلْطَان ٍ مُبِين ٍ
Wa 'Innī `Udhtu Birabbī Wa Rabbikum 'An Tarjumūni َ044-020 "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni." وَإِنِّي عُذْتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمْ أَنْ تَرْجُمُونِ
Wa 'In Lam Tu'uminū Lī Fā`tazilūni َ044-021 "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni." وَإِنْ لَمْ تُؤْمِنُوا لِي فَاعْتَزِلُونِ
Fada`ā Rabbahu 'Anna Hā'uulā' Qawmun Mujrimūna َ044-022 Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi. فَدَعَا رَبَّهُ~ُ أَنَّ هَاؤُلاَء قَوْم ٌ مُجْرِمُونَ
Fa'asri Bi`ibādī Laylāan 'Innakum Muttaba`ūna َ044-023 (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)" فَأَسْرِ بِعِبَادِي لَيْلا ً إِنَّكُمْ مُتَّبَعُونَ
Wa Atruki Al-Baĥra Rahwan  ۖ  'Innahum Jundun Mughraqūna َ044-024 "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa." وَاتْرُكِ الْبَحْرَ رَهْوا ً  ۖ  إِنَّهُمْ جُند ٌ مُغْرَقُونَ
Kam Tarakū Min Jannātin Wa `Uyūnin َ044-025 Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari. كَمْ تَرَكُوا مِنْ جَنَّات ٍ وَعُيُون ٍ
Wa Zurū`in Wa Maqāmin Karīmin َ044-026 Da shuke-shuke da matsayi mai kyau. وَزُرُوع ٍ وَمَقَام ٍ كَرِيم ٍ
Wa Na`matin Kānū Fīhā Fākihīna َ044-027 Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu. وَنَعْمَة ٍ كَانُوا فِيهَا فَاكِهِينَ
Kadhālika  ۖ  Wa 'Awrathnāhā Qawmāan 'Ākharīna َ044-028 Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam. كَذَلِكَ  ۖ  وَأَوْرَثْنَاهَا قَوْما ً آخَرِينَ
Famā Bakat `Alayhimu As-Samā'u Wa Al-'Arđu Wa Mā Kānū Munžarīna َ044-029 Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba. فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ السَّمَاءُ وَالأَرْضُ وَمَا كَانُوا مُنظَرِينَ
Wa Laqad Najjaynā Banī 'Isrā'īla Mina Al-`Adhābi Al-Muhīni َ044-030 Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa. وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ مِنَ الْعَذَابِ الْمُهِينِ
Min Fir`awna  ۚ  'Innahu Kāna `Ālīāan Mina Al-Musrifīna َ044-031 Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna. مِنْ فِرْعَوْنَ  ۚ  إِنَّه ُُ كَانَ عَالِيا ً مِنَ الْمُسْرِفِينَ
Wa Laqadi Akhtarnāhum `Alá `Ilmin `Alá Al-`Ālamīna َ044-032 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne. وَلَقَدِ اخْتَرْنَاهُمْ عَلَى عِلْمٍ عَلَى الْعَالَمِينَ
Wa 'Ātaynāhum Mina Al-'Āyāti Mā Fīhi Balā'un Mubīnun َ044-033 Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna وَآتَيْنَاهُمْ مِنَ الآيَاتِ مَا فِيه ِِ بَلاَء ٌ مُبِين ٌ
'Inna Hā'uulā' Layaqūlūna َ044-034 Lalle waɗannan mutãne , haƙĩka, sunã cẽwa, إِنَّ هَاؤُلاَء لَيَقُولُونَ
'In Hiya 'Illā Mawtatunā Al-'Ūlá Wa Mā Naĥnu Bimunsharīna َ044-035 "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba." إِنْ هِيَ إِلاَّ مَوْتَتُنَا الأُولَى وَمَا نَحْنُ بِمُنشَرِينَ
Fa'tū Bi'ābā'inā 'In Kuntum Şādiqīna َ044-036 "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya." فَأْتُوا بِآبَائِنَا إِنْ كُنتُمْ صَادِقِينَ
'Ahum Khayrun 'Am Qawmu Tubba`in Wa Al-Ladhīna Min Qablihim  ۚ  'Ahlaknāhum  ۖ  'Innahum Kānū Mujrimīna َ044-037 shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi. أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّع ٍ وَالَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ  ۚ  أَهْلَكْنَاهُمْ  ۖ  إِنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ
Wa Mā Khalaq As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Wa Mā Baynahumā Lā`ibīna َ044-038 Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã. وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لاَعِبِينَ
Khalaqnāhumā 'Illā Bil-Ĥaqqi Wa Lakinna 'Aktharahum Lā Ya`lamūna َ044-039 Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba. مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلاَّ بِالْحَقِّ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ
'Inna Yawma Al-Faşli Mīqātuhum 'Ajma`īna َ044-040 Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya. إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَ
Yawma Lā Yughnī Mawláan `An Mawláan Shay'āan Wa Lā Hum Yunşarūna َ044-041 Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba. يَوْمَ لاَ يُغْنِي مَوْلىً عَنْ مَوْلى ً شَيْئا ً وَلاَ هُمْ يُنصَرُونَ
'Illā Man Raĥima Al-Lahu  ۚ  'Innahu Huwa Al-`Azīzu Ar-Raĥīmu َ044-042 fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. إِلاَّ مَنْ رَحِمَ اللَّهُ  ۚ  إِنَّه ُُ هُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ
'Inna Shajarata Az-Zaqqūmi َ044-043 Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã), إِنَّ شَجَرَةَ الزَّقُّومِ
Ţa`āmu Al-'Athīmi َ044-044 Ita ce abincin mai laifi. طَعَامُ الأَثِيمِ
Kālmuhli Yaghlī Fī Al-Buţūni َ044-045 Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna. كَالْمُهْلِ يَغْلِي فِي الْبُطُونِ
Kaghalyi Al-Ĥamīmi َ044-046 Kamar tafasar ruwan zãfi. كَغَلْيِ الْحَمِيمِ
Khudhūhu Fā`tilūhu 'Ilá Sawā'i Al-Jaĥīmi َ044-047 (A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm." خُذُوه ُُ فَاعْتِلُوهُ~ُ إِلَى سَوَاءِ الْجَحِيمِ
Thumma Şubbū Fawqa Ra'sihi Min `Adhābi Al-Ĥamīmi َ044-048 "Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi." ثُمَّ صُبُّوا فَوْقَ رَأْسِه ِِ مِنْ عَذَابِ الْحَمِيمِ
Dhuq 'Innaka 'Anta Al-`Azīzu Al-Karīmu َ044-049 (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!" ذُقْ إِنَّكَ أَنْتَ الْعَزِيزُ الْكَرِيمُ
'Inna Hādhā Mā Kuntum Bihi Tamtarūna َ044-050 "Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi." إِنَّ هَذَا مَا كُنتُمْ بِه ِِ تَمْتَرُونَ
'Inna Al-Muttaqīna Fī Maqāmin 'Amīnin َ044-051 Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce. إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِين ٍ
Fī Jannātin Wa `Uyūnin َ044-052 A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari. فِي جَنَّات ٍ وَعُيُون ٍ
Yalbasūna Min Sundusin Wa 'Istabraqin Mutaqābilīna َ044-053 Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna. يَلْبَسُونَ مِنْ سُندُس ٍ وَإِسْتَبْرَق ٍ مُتَقَابِلِينَ
Kadhālika Wa Zawwajnāhum Biĥūrin `Īnin َ044-054 Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu. كَذَلِكَ وَزَوَّجْنَاهُمْ بِحُورٍ عِين ٍ
Yad`ūna Fīhā Bikulli Fākihatin 'Āminīna َ044-055 Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro). يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَاكِهَة ٍ آمِنِينَ
Lā Yadhūqūna Fīhā Al-Mawta 'Illā Al-Mawtata Al-'Ūlá  ۖ  Wa Waqāhum `Adhāba Al-Jaĥīmi َ044-056 Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm. لاَ يَذُوقُونَ فِيهَا الْمَوْتَ إِلاَّ الْمَوْتَةَ الأُولَى  ۖ  وَوَقَاهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ
Fađlāan Min Rabbika  ۚ  Dhālika Huwa Al-Fawzu Al-`Ažīmu َ044-057 Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma. فَضْلا ً مِنْ رَبِّكَ  ۚ  ذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Fa'innamā Yassarnāhu Bilisānika La`allahum Yatadhakkarūna َ044-058 Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa. فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاه ُُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
Fārtaqib 'Innahum Murtaqibūna َ044-059 Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne. فَارْتَقِبْ إِنَّهُمْ مُرْتَقِبُونَ
Next Sūrah