38) Sūrat Şād

Printed format

38) سُورَة صَاد

Şād Wa Al-Qur'āni Dhī Adh-Dhikri َ038-001 Ṣ̃, Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni mai hukunce-hukunce. صَاد وَالْقُرْآنِ ذِي الذِّكْرِ
Bali Al-Ladhīna Kafarū Fī `Izzatin Wa Shiqāqin َ038-002 Ã'a, waɗanda suka kãfirta sunã cikin girman kai (ga rikon al'ãdunsu) da sãɓãni (tsakãnin jũnansu). بَلِ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي عِزَّة ٍ وَشِقَاق ٍ
Kam 'Ahlaknā Min Qablihim Min Qarnin Fanādaw Walāta Ĥīna Manāşin َ038-003 Da yawa Muka halakar da wani ƙarni, a gabãninsu, suka yi kira (nẽman cẽto), bãbu lõkacin kuɓucewa. كَمْ أَهْلَكْنَا مِنْ قَبْلِهِمْ مِنْ قَرْن ٍ فَنَادَوْا وَلاَتَ حِينَ مَنَاص ٍ
Wa `Ajibū 'An Jā'ahum Mundhirun Minhum  ۖ  Wa Qāla Al-Kāfirūna Hādhā Sāĥirun Kadhdhābun َ038-004 Kuma suka yi mãmãki dõmin Mai gargaɗi, daga cikinsu, ya je musu. Kuma kãfirai sukace, "Wannan mai sihiri ne, maƙaryaci." وَعَجِبُوا أَنْ جَاءَهُمْ مُنْذِر ٌ مِنْهُمْ  ۖ  وَقَالَ الْكَافِرُونَ هَذَا سَاحِر ٌ كَذَّاب ٌ
'Aja`ala Al-'Ālihata 'Ilahāan Wāĥidāan  ۖ  'Inna Hādhā Lashay'un `Ujābun َ038-005 "Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki!" أَجَعَلَ الآلِهَةَ إِلَها ً وَاحِدا ً  ۖ  إِنَّ هَذَا لَشَيْءٌ عُجَاب ٌ
Wa Anţalaqa Al-Mala'u Minhum 'Ani Amshū Wa Aşbirū `Alá 'Ālihatikum  ۖ  'Inna Hādhā Lashay'un Yurādu َ038-006 Shũgabanni daga cikinsu, suka tafi (suka ce),"Ku yi tafiyarku, ku yi haƙuri a kan abũbuwan bautawarku. Lalle wannan, haƙiƙa, wani abu ne ake nufi!" وَانطَلَقَ الْمَلَأُ مِنْهُمْ أَنِ امْشُوا وَاصْبِرُوا عَلَى آلِهَتِكُمْ  ۖ  إِنَّ هَذَا لَشَيْء ٌ يُرَادُ
Mā Sami`nā Bihadhā Fī Al-Millati Al-'Ākhirati 'In Hādhā 'Illā Akhtilāqun َ038-007 "Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya." مَا سَمِعْنَا بِهَذَا فِي الْمِلَّةِ الآخِرَةِ إِنْ هَذَا إِلاَّ اخْتِلاَق ٌ
'A'uunzila `Alayhi Adh-Dhikru Min Bayninā  ۚ  Bal HumShakkin Min Dhikrī  ۖ  Bal Lammā Yadhūqū `Adhābi َ038-008 "Shin, an saukar da Alƙur'ãni ne a kansa, a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba )?" Ã'a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã'a, ba su i da ɗanɗanar azãba ba. أَؤُنزِلَ عَلَيْهِ الذِّكْرُ مِنْ بَيْنِنَا  ۚ  بَلْ هُمْ فِي شَكّ ٍ مِنْ ذِكْرِي  ۖ  بَلْ لَمَّا يَذُوقُوا عَذَابِ
'Am `Indahum Khazā'inu Raĥmati Rabbika Al-`Azīzi Al-Wahhābi َ038-009 Ko kuma a wurinsu ne ake ajiye taskõkin rahamar Ubangijinka, Mabuwãyi, Mai yawan kyauta? أَمْ عِنْدَهُمْ خَزَائِنُ رَحْمَةِ رَبِّكَ الْعَزِيزِ الْوَهَّابِ
'Am Lahum Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Mā Baynahumā  ۖ  Falyartaqū Fī Al-'Asbābi َ038-010 Kõ kuma sũ ne da mallakar sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu? To sai su hau a cikin sammai (dõmin, su hana saukar Alƙur'ãni ga Muhammadu). أَمْ لَهُمْ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا  ۖ  فَلْيَرْتَقُوا فِي الأَسْبَابِ
Jundun Mā Hunālika Mahzūmun Mina Al-'Aĥzābi َ038-011 Rundunõni ne abin da ke can, rusassu, na ƙungiyõyinsu. جُند ٌ مَا هُنَالِكَ مَهْزُوم ٌ مِنَ الأَحْزَابِ
Kadhdhabat Qablahum Qawmu Nūĥin Wa `Ādun Wa Fir`awnu Dhū Al-'Awtādi َ038-012 Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, da Ãdãwa da Fir'auna mai turãkun (da suka kafe mulkinsa). كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوح ٍ وَعَاد ٌ وَفِرْعَوْنُ ذُو الأَوْتَادِ
Wa Thamūdu Wa Qawmu Lūţin Wa 'Aşĥābu Al-'Aykati  ۚ  'Ūlā'ika Al-'Aĥzābu َ038-013 Da Samũdãwa da mutãnen Luɗu da ma'abũta ƙunci, waɗancan ne ƙungiyõyin. وَثَمُودُ وَقَوْمُ لُوط ٍ وَأَصْحَابُ الأَيْكَةِ  ۚ  أُوْلَائِكَ الأَحْزَابُ
'In Kullun 'Illā Kadhdhaba Ar-Rusula Faĥaqqa `Iqābi َ038-014 Bãbu kõwa a cikinsu fãce ya ƙaryata Manzanni, sabõda haka azãbãTa ta wajaba. إِنْ كُلّ ٌ إِلاَّ كَذَّبَ الرُّسُلَ فَحَقَّ عِقَابِ
Wa Mā Yanžuru Hā'uulā' 'Illā Şayĥatan Wāĥidatan Mā Lahā Min Fawāqin َ038-015 Kuma waɗannan bã su jiran kõme fãce tsãwã guda, wadda bã ta da hani. وَمَا يَنظُرُ هَاؤُلاَء إِلاَّ صَيْحَة ً وَاحِدَة ً مَا لَهَا مِنْ فَوَاق ٍ
Wa Qālū Rabbanā `Ajjil Lanā Qiţţanā Qabla Yawmi Al-Ĥisābi َ038-016 Kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabãnin rãnar bincike." وَقَالُوا رَبَّنَا عَجِّلْ لَنَا قِطَّنَا قَبْلَ يَوْمِ الْحِسَابِ
Aşbir `Alá Mā Yaqūlūna Wa Adhkur `Abdanā Dāwūda Dhā Al-'Aydi  ۖ  'Innahu 'Awwābun َ038-017 Ka yi haƙuri bisa ga abin da suke faɗa (na izgili), kuma ka ambaci bãwanMu Dãwũda ma'abũcin ƙarfin ibãda. Lalle, shi, mai mayar da al'amari ga Allah ne. اصْبِرْ عَلَى مَا يَقُولُونَ وَاذْكُرْ عَبْدَنَا دَاوُودَ ذَا الأَيْدِ  ۖ  إِنَّهُ~ُ أَوَّاب ٌ
'Innā Sakhkharnā Al-Jibāla Ma`ahu Yusabbiĥna Bil-`Ashīyi Wa Al-'Ishrāqi َ038-018 Lalle Mũ, Mun hõre duwãtsu tãre da shi, sunã yin tasbĩhi maraice da fitõwar rãnã. إِنَّا سَخَّرْنَا الْجِبَالَ مَعَه ُُ يُسَبِّحْنَ بِالْعَشِيِّ وَالإِشْرَاقِ
Wa Aţ-Ţayra  ۖ  Maĥshūratan Kullun Lahu 'Awwābun َ038-019 Da tsuntsãye waɗanda ake tattarawa, kõwannensu mai kõmãwa ne a gare shi. وَالطَّيْرَ مَحْشُورَة ً  ۖ  كُلّ ٌ لَهُ~ُ أَوَّاب ٌ
Wa Shadadnā Mulkahu Wa 'Ātaynāhu Al-Ĥikmata Wa Faşla Al-Khābi َ038-020 Kuma Muka ƙarfafa mulkinsa, kuma Muka bã shi hikima da rarrabẽwar magana. وَشَدَدْنَا مُلْكَه ُُ وَآتَيْنَاهُ الْحِكْمَةَ وَفَصْلَ الْخِطَابِ
Wa Hal 'Atāka Naba'u Al-Khaşmi 'Idh Tasawwarū Al-Miĥrāba َ038-021 Kuma shin, lãbãrin mãsu husũma ya zo maka, a lõkacin da suka haura gãrun masallaci? وَهَلْ أَتَاكَ نَبَأُ الْخَصْمِ إِذْ تَسَوَّرُوا الْمِحْرَابَ
'Idh Dakhalū `Alá Dāwūda Fafazi`a Minhum  ۖ  Qālū Lā Takhaf  ۖ  Khaşmāni Baghá Ba`đunā `Alá Ba`đin Fāĥkum Baynanā Bil-Ĥaqqi Wa Lā Tushţiţ Wa Ahdinā 'Ilá Sawā'i Aş-Şirāţi َ038-022 A lõkacin da suka shiga ga Dãwũda, sai ya firgita daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro, masu husuma biyu ne; sãshenmu ya zãlunci sãshe. Sabõda haka, ka yi hakunci a tsakãninmu da gaskiya. Kada ka ƙẽtare haddi kuma ka shiryar da mu zuwa, ga tsakar hanya." إِذْ دَخَلُوا عَلَى دَاوُودَ فَفَزِعَ مِنْهُمْ  ۖ  قَالُوا لاَ تَخَفْ  ۖ  خَصْمَانِ بَغَى بَعْضُنَا عَلَى بَعْض ٍ فَاحْكُمْ بَيْنَنَا بِالْحَقِّ وَلاَ تُشْطِطْ وَاهْدِنَا إِلَى سَوَاءِ الصِّرَاطِ
'Inna Hādhā 'Akhī Lahu Tis`un Wa Tis`ūna Na`jatan Wa Liya Na`jatun Wāĥidatun Faqāla 'Akfilnīhā Wa `Azzanī Fī Al-Khābi َ038-023 "Lalle wannan dan'uwãna ne, yanã da tunkiya casa'in da tara, kuma inã da tunkiya guda, sai ya ce: 'Ka lãmunce mini ita. Kuma ya buwãye ni ga magana." إِنَّ هَذَا أَخِي لَه ُُ تِسْع ٌ وَتِسْعُونَ نَعْجَة ً وَلِيَ نَعْجَة ٌ وَاحِدَة ٌ فَقَالَ أَكْفِلْنِيهَا وَعَزَّنِي فِي الْخِطَابِ
Qāla Laqad Žalamaka Bisu'uāli Na`jatika 'Ilá Ni`ājihi  ۖ  Wa 'Inna Kathīrāan Mina Al-Khulaţā'i Layabghī Ba`đuhum `Alá Ba`đin 'Illā Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Wa Qalīlun Mā Hum  ۗ  Wa Žanna Dāwūdu 'Annamā Fatannāhu Fāstaghfara Rabbahu Wa Kharra Rāki`āan Wa 'Anāba َ038-024 (Dãwũda) ya ce: "Lalle, haƙiƙa ya zãlunce ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga tumakinsa. Kuma lalle ne mãsu yawa daga abõkan tarayya, haƙiƙa, sãshensu na zambatar sãshe fãce waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai." Kuma Dãwũda ya tabbata cẽwa Mun fitine shi ne, sabõda haka, ya nẽmi Ubangijinsa gãfara,kuma ya fãɗi yanã mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah. قَالَ لَقَدْ ظَلَمَكَ بِسُؤَالِ نَعْجَتِكَ إِلَى نِعَاجِه ِِ  ۖ  وَإِنَّ كَثِيرا ً مِنَ الْخُلَطَاءِ لَيَبْغِي بَعْضُهُمْ عَلَى بَعْض ٍ إِلاَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَقَلِيل ٌ مَا هُمْ  ۗ  وَظَنَّ دَاوُودُ أَنَّمَا فَتَنَّاه ُُ فَاسْتَغْفَرَ رَبَّه ُُ وَخَرَّ رَاكِعا ً وَأَنَابَ
Faghafarnā Lahu Dhālika  ۖ  Wa 'Inna Lahu `Indanā Lazulfá Wa Ĥusna Ma'ābin َ038-025 Sabõda haka Muka gãfarta masa wancan, kuma lalle yanã da wata kusantar daraja a wurinMu, da kyaun makõma. فَغَفَرْنَا لَه ُُ ذَلِكَ  ۖ  وَإِنَّ لَه ُُ عِنْدَنَا لَزُلْفَى وَحُسْنَ مَآب ٍ
Yā Dāwūdu 'Innā Ja`alnāka Khalīfatan Al-'Arđi Fāĥkum Bayna An-Nāsi Bil-Ĥaqqi Wa Lā Tattabi`i Al-Hawá Fayuđillaka `An Sabīli Al-Lahi  ۚ  'Inna Al-Ladhīna Yađillūna `An Sabīli Al-Lahi Lahum `Adhābun Shadīdun Bimā Nasū Yawma Al-Ĥisābi َ038-026 Yã Dãwũda! Lalle Mũ Mun sanya ka Halĩfa a cikin ƙasã. To, ka yi hukunci tsakãnin mutãne da gaskiya, kuma kada ka biye wa son zũciyar, har ya ɓatar dakai daga hanyar Allah. Lalle waɗanda ke ɓacẽwa daga hanyar Allah sunã da wata azãba mai tsanani dõmin abin da suka manta, a rãnar hisãbi يَادَاوُودُ إِنَّا جَعَلْنَاكَ خَلِيفَة ً فِي الأَرْضِ فَاحْكُمْ بَيْنَ النَّاسِ بِالْحَقِّ وَلاَ تَتَّبِعِ الْهَوَى فَيُضِلَّكَ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ إِنَّ  ۚ  الَّذِينَ يَضِلُّونَ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ لَهُمْ عَذَاب ٌ شَدِيد ٌ بِمَا نَسُوا يَوْمَ الْحِسَابِ
Wa Mā Khalaq As-Samā'a Wa Al-'Arđa Wa Mā Baynahumā Bāţilāan  ۚ  Dhālika Žannu Al-Ladhīna Kafarū  ۚ  Fawaylun Lilladhīna Kafarū Mina An-Nāri َ038-027 Kuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya. Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga wutã. وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاءَ وَالأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا بَاطِلا ً  ۚ  ذَلِكَ ظَنُّ الَّذِينَ كَفَرُوا  ۚ  فَوَيْل ٌ لِلَّذِينَ كَفَرُوا مِنَ النَّارِ
'Am Naj`alu Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Kālmufsidīna Fī Al-'Arđi 'Am Naj`alu Al-Muttaqīna Kālfujjāri َ038-028 Kõ zã Mu sanya waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar waɗanda suke mãsu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da taƙawa kamar fãjirai makarkata? أَمْ نَجْعَلُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ كَالْمُفْسِدِينَ فِي الأَرْضِ أَمْ نَجْعَلُ الْمُتَّقِينَ كَالْفُجَّارِ
Kitābun 'Anzalnāhu 'Ilayka Mubārakun Liyaddabbarū 'Āyātihi Wa Liyatadhakkara 'Ū Al-'Albābi َ038-029 (Wannan) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni. كِتَابٌ أَنزَلْنَاهُ~ُ إِلَيْكَ مُبَارَك ٌ لِيَدَّبَّرُوا آيَاتِه ِِ وَلِيَتَذَكَّرَ أُوْلُوا الأَلْبَابِ
Wa Wahabnā Lidāwūda Sulaymāna  ۚ  Ni`ma Al-`Abdu  ۖ  'Innahu 'Awwābun َ038-030 Kuma Muka bai wa Dãwũda Sulaimãn. Mãdalla da bãwanMu, shi. Lalle shi (Sulaimãn) mai mayar da al'amari ne ga Allah. وَوَهَبْنَا لِدَاوُودَ سُلَيْمَانَ  ۚ  نِعْمَ الْعَبْدُ  ۖ  إِنَّهُ~ُ أَوَّاب ٌ
'Idh `Uriđa `Alayhi Bil-`Ashīyi Aş-Şāfinātu Al-Jiyādu َ038-031 A lõkacin da aka gitta masa dawãki mãsu asali, a lõkacin maraice. إِذْ عُرِضَ عَلَيْهِ بِالْعَشِيِّ الصَّافِنَاتُ الْجِيَادُ
Faqāla 'Innī 'Aĥbabtu Ĥubba Al-Khayri `An Dhikri Rabbī Ĥattá Tawārat Bil-Ĥijābi َ038-032 Sai ya ce: "Lalle nĩ, na fĩfĩta son dũkiya daga tunãwar Ubangijina, har (rãnã) ta faku da shãmaki!" فَقَالَ إِنِّي أَحْبَبْتُ حُبَّ الْخَيْرِ عَنْ ذِكْرِ رَبِّي حَتَّى تَوَارَتْ بِالْحِجَابِ
Ruddūhā `Alayya  ۖ  Faţafiqa Masĥāan Bis-Sūqi Wa Al-'A`nāqi َ038-033 "Ku mayar da su a gare ni." Sai ya shiga yankansu da takõbi ga ƙwabrukansu da wuyõyinsu. رُدُّوهَا عَلَيَّ  ۖ  فَطَفِقَ مَسْحا ً بِالسُّوقِ وَالأَعْنَاقِ
Wa Laqad Fatannā Sulaymāna Wa 'Alqaynā `Alá Kursīyihi Jasadāan Thumma 'Anāba َ038-034 Kuma lalle haƙĩƙa, Mun fitini Sulaiman kuma Muka jẽfa wani jikin mutum a kan karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu. وَلَقَدْ فَتَنَّا سُلَيْمَانَ وَأَلْقَيْنَا عَلَى كُرْسِيِّه ِِ جَسَدا ً ثُمَّ أَنَابَ
Qāla Rabbi Aghfir Lī Wa Hab Lī Mulkāan Lā Yanbaghī Li'ĥadin Min Ba`dī  ۖ  'Innaka 'Anta Al-Wahhābu َ038-035 Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna. Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta. قَالَ رَبِّ اغْفِرْ لِي وَهَبْ لِي مُلْكا ً لاَ يَنْبَغِي لِأحَد ٍ مِنْ بَعْدِي  ۖ  إِنَّكَ أَنْتَ الْوَهَّابُ
Fasakhkharnā Lahu Ar-Rīĥa Tajrī Bi'amrihi Rukhā'an Ĥaythu 'Aşāba َ038-036 Sabõda haka Muka hõre masa iska tanã gudu da umurninsa, tãna tãshi da sauƙi, inda ya nufa. فَسَخَّرْنَا لَهُ الرِّيحَ تَجْرِي بِأَمْرِه ِِ رُخَاءً حَيْثُ أَصَابَ
Wa Ash-Shayāţīna Kulla Bannā'in Wa Ghawwāşin َ038-037 Da shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa (a cikin kõguna.) وَالشَّيَاطِينَ كُلَّ بَنَّاء ٍ وَغَوَّاص ٍ
Wa 'Ākharīna Muqarranīna Fī Al-'Aşfādi َ038-038 Waɗansu, ɗaɗɗaure a cikin marũruwa. وَآخَرِينَ مُقَرَّنِينَ فِي الأَصْفَادِ
dhā `Aţā'uunā Fāmnun 'Aw 'Amsik Bighayri Ĥisābin َ038-039 Wannan kyautarMu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, bãbu wani bincike. هَذَا عَطَاؤُنَا فَامْنُنْ أَوْ أَمْسِكْ بِغَيْرِ حِسَاب ٍ
Wa 'Inna Lahu `Indanā Lazulfá Wa Ĥusna Ma'ābin َ038-040 Kuma lalle, haƙĩƙa yanã da kusantar daraja a wurinMu da kyaun makõma. وَإِنَّ لَه ُُ عِنْدَنَا لَزُلْفَى وَحُسْنَ مَآب ٍ
Wa Adhkur `Abdanā 'Ayyūba 'Idh Nādá Rabbahu 'Annī Massanī Ash-Shayţānu Binuşbin Wa `Adhābin َ038-041 Kuma ka ambaci bãwanMu Ayyũba a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba." وَاذْكُرْ عَبْدَنَا أَيُّوبَ إِذْ نَادَى رَبَّهُ~ُ أَنِّي مَسَّنِي الشَّيْطَانُ بِنُصْب ٍ وَعَذَاب ٍ
Arkuđ Birijlika  ۖ  Hādhā Mughtasalunridun Wa Sharābun َ038-042 Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã. ارْكُضْ بِرِجْلِكَ  ۖ  هَذَا مُغْتَسَل ٌ بَارِد ٌ وَشَرَاب ٌ
Wa Wahabnā Lahu 'Ahlahu Wa Mithlahum Ma`ahum Raĥmatan Minnā Wa Dhikrá Li'wlī Al-'Albābi َ038-043 Kuma Muka bã shi iyalansa da kwatankwacinsu tãre da su sabõda rahama daga gare Mu, da tunãtarwa ga mãsu hankali. وَوَهَبْنَا لَهُ~ُ أَهْلَه ُُ وَمِثْلَهُمْ مَعَهُمْ رَحْمَة ً مِنَّا وَذِكْرَى لِأوْلِي الأَلْبَابِ
Wa Khudh Biyadika Đighthāan Fāđrib Bihi Wa Lā Taĥnath  ۗ  'Innā Wa Jadnāhu Şābirāan  ۚ  Ni`ma Al-`Abdu  ۖ  'Innahu 'Awwābun َ038-044 Kuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi dũka da ita kuma kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mũ, Mun sãme shi mai haƙuri. Madalla da bãwa, shĩ Lalle shĩ mai mayar da al'amari ga Allah ne. وَخُذْ بِيَدِكَ ضِغْثا ً فَاضْرِبْ بِه ِِ وَلاَ تَحْنَثْ  ۗ  إِنَّا وَجَدْنَاه ُُ صَابِرا ً  ۚ  نِعْمَ الْعَبْدُ  ۖ  إِنَّهُ~ُ أَوَّاب ٌ
Wa Adhkur `Ibādanā 'Ibrāhīma Wa 'Isĥāqa Wa Ya`qūba 'Ū Al-'Aydī Wa Al-'Abşāri َ038-045 Kuma ka ambaci bãyinMu: Ibrahĩm da ls'hãƙa da Ya'aƙũba, ma'abũta ƙarfin (ɗaukar umurninMu) da basĩra. وَاذْكُرْ عِبَادَنَا إبْرَاهِيمَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ أُوْلِي الأَيْدِي وَالأَبْصَارِ
'Innā 'Akhlaşnāhum Bikhālişatin Dhikrá Ad-Dāri َ038-046 Lalle Mũ, Mun keɓance su game da wata, tsattsarkar aba: Hukunce-hukuncen gidan dũniya (mai tunãtar da su Lãhira). إِنَّا أَخْلَصْنَاهُمْ بِخَالِصَة ٍ ذِكْرَى الدَّارِ
Wa 'Innahum `Indanā Lamina Al-Muşţafayna Al-'Akhyāri َ038-047 Kuma lalle sũ a wurinMu, tabbas, sunã daga zãɓaɓɓu, mafĩfĩta. وَإِنَّهُمْ عِنْدَنَا لَمِنَ الْمُصْطَفَيْنَ الأَخْيَارِ
Wa Adhkur 'Ismā`īla Wa Al-Yasa`a Wa Dhā Al-Kifli  ۖ  Wa Kullun Mina Al-'Akhyāri َ038-048 Kuma ka ambaci Isma'ĩla da llyãs da Zulkifli, kuma dukansu sunã daga zãɓaɓɓu. وَاذْكُرْ إِسْمَاعِيلَ وَالْيَسَعَ وَذَا الْكِفْلِ  ۖ  وَكُلّ ٌ مِنَ الأَخْيَارِ
dhā Dhikrun  ۚ  Wa 'Inna Lilmuttaqīna Laĥusna Ma'ābin َ038-049 Wannan tunãtarwa ce, kuma lalle mãsu bin Allah da taƙawa, sunã da kyakkyawar makõma. هَذَا ذِكْر ٌ  ۚ  وَإِنَّ لِلْمُتَّقِينَ لَحُسْنَ مَآب ٍ
Jannāti `Adnin Mufattaĥatan Lahumu Al-'Abwābu َ038-050 Gidãjen Aljannar zama , alhãli kuwa tanã abar buɗe wa kõfõfi sabõda su. جَنَّاتِ عَدْن ٍ مُفَتَّحَة ً لَهُمُ الأَبْوَابُ
Muttaki'īna Fīhā Yad`ūna Fīhā Bifākihatin Kathīratin Wa Sharābin َ038-051 Sunã gingincire a cikinsu, sunã kira a cikinsu, ga 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, da abin shã. مُتَّكِئِينَ فِيهَا يَدْعُونَ فِيهَا بِفَاكِهَة ٍ كَثِيرَة ٍ وَشَرَاب ٍ
Wa `Indahum Qāşirātu Aţ-Ţarfi 'Atrābun َ038-052 Kuma a wurinsu akwai mãtan aure mãsu gajarta ganinsu ga mazansu, tsãrar jũna. وَعِنْدَهُمْ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ أَتْرَاب ٌ
dhā Mā Tū`adūna Liyawmi Al-Ĥisābi َ038-053 Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi ga rãnar hisãbi. هَذَا مَا تُوعَدُونَ لِيَوْمِ الْحِسَابِ
'Inna Hādhā Larizqunā Mā Lahu Min Nafādin َ038-054 Lalle wannan, haƙĩƙa, azurtarwarMu ce, bã ta ƙãrẽwa. إِنَّ هَذَا لَرِزْقُنَا مَا لَه ُُ مِنْ نَفَاد ٍ
dhā  ۚ  Wa 'Inna Lilţţāghīna Lasharra Ma'ābin َ038-055 Wannan shĩ ne kuma lalle makangara, haƙĩƙa, sunã da mafi sharrin makõma. هَذَا  ۚ  وَإِنَّ لِلطَّاغِينَ لَشَرَّ مَآب ٍ
Jahannama Yaşlawnahā Fabi'sa Al-Mihādu َ038-056 Jahannama, sunã shigarta. To, shimfiɗar tã mũnana, ita. جَهَنَّمَ يَصْلَوْنَهَا فَبِئْسَ الْمِهَادُ
dhā Falyadhūqūhu Ĥamīmun Wa Ghassāqun َ038-057 Wannan shĩ ne! To, su ɗanɗane shi: ruwan zãfi ne da ruɓaɓɓen jini. هَذَا فَلْيَذُوقُوه ُُ حَمِيم ٌ وَغَسَّاق ٌ
Wa 'Ākharu Min Shaklihi 'Azwājun َ038-058 Da wani daga siffarsa nau'i-nau'i. وَآخَرُ مِنْ شَكْلِهِ~ِ أَزْوَاج ٌ
dhā Fawjun Muqtaĥimun Ma`akum  ۖ  Lā Marĥabāan Bihim  ۚ  'Innahum Şālū An-Nāri َ038-059 Wannan wani yanki ne mai kũtsawa tãre da ku, bãbu marãba a gare su, lalle sũ, mãsu shiga Wutã ne. هَذَا فَوْج ٌ مُقْتَحِم ٌ مَعَكُمْ  ۖ  لاَ مَرْحَبا ً بِهِمْ  ۚ  إِنَّهُمْ صَالُوا النَّارِ
Qālū Bal 'Antum Lā Marĥabāan Bikum  ۖ  'Antum Qaddamtumūhu Lanā  ۖ  Fabi'sa Al-Qarāru َ038-060 Suka ce: "Ã'a, ku ne bãbu marãba a gare ku, kũ ne kuka gabãtar da shi a gare mu." To, matabbatar tã mũnana (ita wutar). قَالُوا بَلْ أَنْتُمْ لاَ مَرْحَبا ً بِكُمْ  ۖ  أَنْتُمْ قَدَّمْتُمُوه ُُ لَنَا  ۖ  فَبِئْسَ الْقَرَارُ
Qālū Rabbanā Man Qaddama Lanā Hādhā Fazid/hu `Adhābāan Đi`fāan An-Nāri َ038-061 Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Wanda ya gabãtar da wannan a gare mu, to, Ka ƙãra masa azãba, ninki, a cikin wutã." قَالُوا رَبَّنَا مَنْ قَدَّمَ لَنَا هَذَا فَزِدْهُ عَذَابا ً ضِعْفا ً فِي النَّارِ
Wa Qālū Mā Lanā Lā Nará Rijālāan Kunnā Na`udduhum Mina Al-'Ashrār َ038-062 Kuma suka ce: "Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai?" وَقَالُوا مَا لَنَا لاَ نَرَى رِجَالا ً كُنَّا نَعُدُّهُمْ مِنَ الأَشْرَار
'Āttakhadhnāhum Sikhrīyāan 'Amghat `Anhumu Al-'Abşāru َ038-063 "Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne?" أَاتَّخَذْنَاهُمْ سِخْرِيّاً أَمْ زَاغَتْ عَنْهُمُ الأَبْصَارُ
'Inna Dhālika Laĥaqqun Takhāşumu 'Ahli An-Nāri َ038-064 Lalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã. إِنَّ ذَلِكَ لَحَقّ ٌ تَخَاصُمُ أَهْلِ النَّارِ
Qul 'Innamā 'Anā Mundhirun  ۖ  Wa Mā Min 'Ilahin 'Illā Al-Lahu Al-Wāĥidu Al-Qahhāru َ038-065 Ka ce: "Nĩ mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa." قُلْ إِنَّمَا أَنَا مُنذِر ٌ  ۖ  وَمَا مِنْ إِلَهٍ~ ٍ إِلاَّ اللَّهُ الْوَاحِدُ الْقَهَّارُ
Rabbu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Mā Baynahumā Al-`Azīzu Al-Ghaffāru َ038-066 "Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu Mabuwãyi, Mai gãfara." رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا الْعَزِيزُ الْغَفَّارُ
Qul Huwa Naba'un `Ažīmun َ038-067 Ka ce: "Shĩ (Alkur'ãni) babban lãbãri ne mai girma". قُلْ هُوَ نَبَأٌ عَظِيم ٌ
'Antum `Anhu Mu`rūna َ038-068 "Kũ, mãsu bijirẽwa ne daga gare shi!" أَنْتُمْ عَنْهُ مُعْرِضُونَ
Mā Kāna Liya Min `Ilmin Bil-Mala'i Al-'A`lá 'Idh Yakhtaşimūna َ038-069 "Wani ilmi bai kasance a gare ni ba game da jama'a (malã'iku) mafi ɗaukaka a lõkacin da suke yin husũma." مَا كَانَ لِيَ مِنْ عِلْم ٍ بِالْمَلَإِ الأَعْلَى إِذْ يَخْتَصِمُونَ
'In Yūĥá 'Ilayya 'Illā 'Annamā 'Anā Nadhīrun Mubīnun َ038-070 "Ba a yi mini wahayin kõme ba face cẽwa ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa." إِنْ يُوحَى إِلَيَّ إِلاَّ أَنَّمَا أَنَا نَذِير ٌ مُبِين ٌ
'Idh Qāla Rabbuka Lilmalā'ikati 'Innī Khāliqun Basharāan Min Ţīnin َ038-071 A lõkacin da Ubangijinka Ya ce wa malã'iku, "Lalle Nĩ Mai halitta mutum ne daga lãkã. إِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلاَئِكَةِ إِنِّي خَالِق ٌ بَشَرا ً مِنْ طِين ٍ
Fa'idhā Sawwaytuhu Wa Nafakhtu Fīhi Min Rūĥī Faqa`ū Lahu Sājidīna َ038-072 "Sa'an nan idan Nã daidaita shi, kuma Na hũra (wani abu) daga RuhĩNa a cikinsa to ku fãɗi kunã mãsu sujada a gare; shi." فَإِذَا سَوَّيْتُه ُُ وَنَفَخْتُ فِيه ِِ مِنْ رُوحِي فَقَعُوا لَه ُُ سَاجِدِينَ
Fasajada Al-Malā'ikatu Kulluhum 'Ajma`ūna َ038-073 Sai malã'ikun suka yi sujada dukansu, gabã ɗaya. فَسَجَدَ الْمَلاَئِكَةُ كُلُّهُمْ أَجْمَعُونَ
'Illā 'Iblīsa Astakbara Wa Kāna Mina Al-Kāfirīna َ038-074 Fãce Iblis, ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai. إِلاَّ إِبْلِيسَ اسْتَكْبَرَ وَكَانَ مِنَ الْكَافِرِينَ
Qāla Yā 'Iblīsu Mā Mana`aka 'An Tasjuda Limā Khalaqtu Biyadayya  ۖ  'Āstakbarta 'Am Kunta Mina Al-`Ālīna َ038-075 (Allah) Ya ce, "Yã Ibilis! Mẽ ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Nã halitta da HannayeNa biyu? Shin, kã yi girman kai ne, kõ kuwa kã kasance daga maɗaukaka ne?" قَالَ يَاإِبْلِيسُ مَا مَنَعَكَ أَنْ تَسْجُدَ لِمَا خَلَقْتُ بِيَدَيَّ أَاسْتَكْبَرْتَ  ۖ  أَمْ كُنتَ مِنَ الْعَالِينَ
Qāla 'Anā Khayrun Minhu  ۖ  Khalaqtanī Min Nārin Wa Khalaqtahu Min Ţīnin َ038-076 Ya ce, "Nĩ, mafifici ne daga gare shi: Kã halitta ni daga wutã, kuma Kã halitta shi daga lãkã." قَالَ أَنَا خَيْر ٌ مِنْهُ  ۖ  خَلَقْتَنِي مِنْ نَار ٍ وَخَلَقْتَه ُُ مِنْ طِين ٍ
Qāla Fākhruj Minhā Fa'innaka Rajīmun َ038-077 Ya ce, "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai la'ananne ne." قَالَ فَاخْرُجْ مِنْهَا فَإِنَّكَ رَجِيم ٌ
Wa 'Inna `Alayka La`natī 'Ilá Yawmi Ad-Dīni َ038-078 "Kuma lalle a kanka akwai la'anaTa har zuwa rãnar sakamako." وَإِنَّ عَلَيْكَ لَعْنَتِي إِلَى يَوْمِ الدِّينِ
Qāla Rabbi Fa'anžirnī 'Ilá Yawmi Yub`athūna َ038-079 Ya ce, "Ya Ubangijina! To, Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su." قَالَ رَبِّ فَأَنظِرْنِي إِلَى يَوْمِ يُبْعَثُونَ
Qāla Fa'innaka Mina Al-Munžarīna َ038-080 Ya ce, "To, lalle kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri, قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ الْمُنظَرِينَ
'Ilá Yawmi Al-Waqti Al-Ma`lūmi َ038-081 "Zuwa ga yinin lõkaci sananne." إِلَى يَوْمِ الْوَقْتِ الْمَعْلُومِ
Qāla Fabi`izzatika La'ughwiyannahum 'Ajma`īna َ038-082 Ya ce, "To, inã rantsuwa da buwãyarKa, lalle, inã ɓatar da su gabã ɗaya. قَالَ فَبِعِزَّتِكَ لَأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ
'Illā `Ibādaka Minhumu Al-Mukhlaşīna َ038-083 "Fãce bãyinKa tsarkakakku daga gare su." إِلاَّ عِبَادَكَ مِنْهُمُ الْمُخْلَصِينَ
Qāla Fālĥaqqu Wa Al-Ĥaqqa 'Aqūlu َ038-084 (Allah) Ya ce, "To, (wannan magana ita ce) gaskiya. Kuma gaskiya Nake faɗa." قَالَ فَالْحَقُّ وَالْحَقَّ أَقُولُ
La'amla'anna Jahannama Minka Wa Mimman Tabi`aka Minhum 'Ajma`īna َ038-085 "Lalle zã Ni cika Jahannama daga gare ka, kuma daga wanda ya bĩ ka daga gare su, gabã ɗaya" لَأَمْلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنْكَ وَمِمَّنْ تَبِعَكَ مِنْهُمْ أَجْمَعِينَ
Qul Mā 'As'alukum `Alayhi Min 'Ajrin Wa Mā 'Anā Mina Al-Mutakallifīna َ038-086 Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra, a kansa kuma bã ni daga mãsu ƙãƙalen faɗarsa." قُلْ مَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْر ٍ وَمَا أَنَا مِنَ الْمُتَكَلِّفِينَ
'In Huwa 'Illā Dhikrun Lil`ālamīna َ038-087 "Shĩ (Alkur'ãn) bai zama ba fãce ambato ne ga dukan halitta." إِنْ هُوَ إِلاَّ ذِكْر ٌ لِلْعَالَمِينَ
Wa Lata`lamunna Naba'ahu Ba`da Ĥīnin َ038-088 "Kuma lalle zã ku san babban lãbãrinsa a bayan ɗan lõkaci." وَلَتَعْلَمُنَّ نَبَأَه ُُ بَعْدَ حِين ٍ
Next Sūrah