3) Sūrat 'Āli `Imn

Printed format

3) سُورَة آلِ عِمرَان

'Alif-Lām-Mīm َ003-001 A. L̃. M̃. أَلِف-لَام-مِيم
Al-Lahu Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Al-Ĥayyu Al-Qayyūmu َ003-002 Allah, bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Rãyayye Mai tsayuwa da kõme. اللَّهُ لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ
Nazzala `Alayka Al-Kitāba Bil-Ĥaqqi Muşaddiqāan Limā Bayna Yadayhi Wa 'Anzala At-Tawrāata Wa Al-'Injīla َ003-003 Yã sassaukar da Littãfi a gare ka da gaskiya, yana mai gaskatãwa ga abin da ke gaba gare shi, kuma Allah Yã saukar da Attaura da Linjĩlã. نَزَّلَ عَلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ مُصَدِّقا ً لِمَا بَيْنَ يَدَيْهِ وَأَنْزَلَ التَّوْرَاةَ وَالإِنْجِيلَ
Min Qablu Hudáan Lilnnāsi Wa 'Anzala Al-Furqāna  ۗ  'Inna Al-Ladhīna Kafarū Bi'āyāti Al-Lahi Lahum `Adhābun Shadīdun Wa  ۗ  Allāhu `Azīzun Dhū Antiqāmin َ003-004 A gabãni, suna shiryar da mutãne, kuma Ya saukar da littattafai mãsu rarrabẽwa. Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, suna da azãba mai tsanani. Kuma Allah Mabuwayi ne, Ma'abucin azãbar rãmuwa. مِنْ قَبْلُ هُدى ً لِلنَّاسِ وَأَنْزَلَ الْفُرْقَانَ  ۗ  إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِ اللَّهِ لَهُمْ عَذَاب ٌ شَدِيد ٌ  ۗ  وَاللَّهُ عَزِيز ٌ ذُو انْتِقَام ٍ
'Inna Al-Laha Lā Yakhfá `Alayhi Shay'un Al-'Arđi Wa Lā Fī As-Samā'i َ003-005 Lalle ne, Allah bãbu wani abin da ke ɓõyuwa gare Shi a cikin ƙasa, kuma bãbu a cikin sama. إِنَّ اللَّهَ لاَ يَخْفَى عَلَيْهِ شَيْء ٌ فِي الأَرْضِ وَلاَ فِي السَّمَاءِ
Huwa Al-Ladhī Yuşawwirukum Al-'Arĥāmi Kayfa Yashā'u  ۚ  Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ003-006 Shi ne wanda Yake suranta ku a cikin mahaifu yadda Yake so. Bãbu abin bautãwa fãce Shi Mabuwãyi, Mai hikima. هُوَ الَّذِي يُصَوِّرُكُمْ فِي الأَرْحَامِ كَيْفَ يَشَاءُ  ۚ  لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Huwa Al-Ladhī 'Anzala `Alayka Al-Kitāba Minhu 'Āyātun Muĥkamātun Hunna 'Ummu Al-Kitābi Wa 'Ukharu Mutashābihātun  ۖ  Fa'ammā Al-Ladhīna Fī Qulūbihim Zayghun Fayattabi`ūna Mā Tashābaha Minhu Abtighā'a Al-Fitnati Wa Abtighā'a Ta'wīlihi  ۗ  Wa Mā Ya`lamu Ta'wīlahu 'Illā Al-Lahu Wa  ۗ  Ar-Rāsikhūna Fī Al-`Ilmi Yaqūlūna 'Āmannā Bihi Kullun Min `Indi Rabbinā  ۗ  Wa Mā Yadhdhakkaru 'Illā 'Ū Al-'Albābi َ003-007 Shi ne wanda ya saukar da Littãfi a gare ka, daga cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu, su ne mafi yawan Littãfin, da wasu mãsu kamã da jũna. To, amma waɗanda yake a cikin zukãtansu akwai karkata sai suna bin abin da yake da kamã da jũna daga gare shi, dõmin nẽman yin fitina da tãwĩlinsa. Kuma bãbu wanda ya san tãwĩlinsafãce Allah. Kuma matabbata a cikin ilmi sunã cẽwa: "Mun yi ĩmãni da Shi; dukkansa daga wurin Ubangijinmu yake." Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abũta hankula. هُوَ الَّذِي أَنْزَلَ عَلَيْكَ الْكِتَابَ مِنْهُ آيَات ٌ مُحْكَمَاتٌ هُنَّ أُمُّ الْكِتَابِ وَأُخَرُ مُتَشَابِهَات ٌ  ۖ  فَأَمَّا الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ زَيْغ ٌ فَيَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَه ََ مِنْهُ ابْتِغَاءَ الْفِتْنَةِ وَابْتِغَاءَ تَأْوِيلِه ِِ  ۗ  وَمَا يَعْلَمُ تَأْوِيلَهُ~ُ إِلاَّ اللَّهُ  ۗ  وَالرَّاسِخُونَ فِي الْعِلْمِ يَقُولُونَ آمَنَّا بِه ِِ كُلّ ٌ مِنْ عِنْدِ رَبِّنَا  ۗ  وَمَا يَذَّكَّرُ إِلاَّ أُوْلُوا الأَلْبَابِ
Rabbanā Lā Tuzigh Qulūbanā Ba`da 'Idh Hadaytanā Wa Hab Lanā Min Ladunka Raĥmatan  ۚ  'Innaka 'Anta Al-Wahhābu َ003-008 Yã Ubangijinmu! Kada Ka karkatar da zukãtanmu bãyan har Kã shiryar da mu, kuma Ka bã mu rahama daga gunKa. Lalle ne, Kai, Kai ne Mai yawan kyauta. رَبَّنَا لاَ تُزِغْ قُلُوبَنَا بَعْدَ إِذْ هَدَيْتَنَا وَهَبْ لَنَا مِنْ لَدُنْكَ رَحْمَة ً  ۚ  إِنَّكَ أَنْتَ الْوَهَّابُ
Rabbanā 'Innaka Jāmi`u An-Nāsi Liyawmin Lā Rayba Fīhi  ۚ  'Inna Al-Laha Lā Yukhlifu Al-Mī`āda َ003-009 "Yã Ubangijimu! Lalle ne Kai, Mai tãra mutãne ne dõmin wani yini wanda bãbu shakka a gare shi, Lalle ne Allah bã Ya sãɓãwar lõkacin alkawari." رَبَّنَا إِنَّكَ جَامِعُ النَّاسِ لِيَوْم ٍ لاَ رَيْبَ فِيهِ~ِ  ۚ  إِنَّ اللَّهَ لاَ يُخْلِفُ الْمِيعَادَ
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Lan Tughniya `Anhum 'Amwāluhum Wa Lā 'Awlāduhum Mina Al-Lahi Shay'āan  ۖ  Wa 'Ūlā'ika Hum Wa Qūdu An-Nāri َ003-010 Lalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu bã su tunkuɗe musu kõme daga Allah, kuma 'ya'yansu bã su tunkuɗẽwa, kuma waɗannan, sũ ne makãmashin wuta. إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا لَنْ تُغْنِيَ عَنْهُمْ أَمْوَالُهُمْ وَلاَ أَوْلاَدُهُمْ مِنَ اللَّهِ شَيْئا ً  ۖ  وَأُوْلَائِكَ هُمْ وَقُودُ النَّارِ
Kada'bi 'Āli Fir`awna Wa Al-Ladhīna Min Qablihim  ۚ  Kadhdhabū Bi'āyātinā Fa'akhadhahumu Al-Lahu Bidhunūbihim Wa  ۗ  Allāhu Shadīdu Al-`Iqābi َ003-011 Kamar ɗabi'ar mutãnen Fir'auna da waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata ãyõyinMu, sai Allah Ya kãmã su sabõda zunubansu, kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne. كَدَأْبِ آلِ فِرْعَوْنَ وَالَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ  ۚ  كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا فَأَخَذَهُمُ اللَّهُ بِذُنُوبِهِمْ  ۗ  وَاللَّهُ شَدِيدُ الْعِقَابِ
Qul Lilladhīna Kafarū Satughlabūna Wa Tuĥsharūna 'Ilá Jahannama  ۚ  Wa Bi'sa Al-Mihādu َ003-012 Ka ce wa waɗanda suka kãfirta: "Za a rinjãye ku, kuma a tãraku zuwa Jahannama, kuma shimfiɗar tã mũnana! قُلْ لِلَّذِينَ كَفَرُوا سَتُغْلَبُونَ وَتُحْشَرُونَ إِلَى جَهَنَّمَ  ۚ  وَبِئْسَ الْمِهَادُ
Qad Kāna Lakum 'Āyatun Fī Fi'atayni At-Taqatā  ۖ  Fi'atun Tuqātilu Fī Sabīli Al-Lahi Wa 'Ukhrá Kāfiratun Yarawnahum Mithlayhim Ra'ya Al-`Ayni Wa  ۚ  Allāhu Yu'uayyidu Binaşrihi Man Yashā'u  ۗ  'Inna Fī Dhālika La`ibratan Li'wlī Al-'Abşāri َ003-013 "Lalle ne wata ãyã tã kasance a gare ku a cikin ƙungiyõyi biyu da suka haɗu; ƙungiya guda tana yãƙi a cikin hanyar Allah, da wata kãfira, suna ganin su ninki biyu nãsu, a ganin ido. Kuma Allah Yana ƙarfafa wanda Yake so da taimakonSa. Lalle ne a cikin wannan, hakĩƙa, akwai abin kula ga maabũta basĩra. قَدْ كَانَ لَكُمْ آيَة ٌ فِي فِئَتَيْنِ الْتَقَتَا  ۖ  فِئَة ٌ تُقَاتِلُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَأُخْرَى كَافِرَة ٌ يَرَوْنَهُمْ مِثْلَيْهِمْ رَأْيَ الْعَيْنِ  ۚ  وَاللَّهُ يُؤَيِّدُ بِنَصْرِه ِِ مَنْ يَشَاءُ  ۗ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَعِبْرَة ً لِأوْلِي الأَبْصَارِ
Zuyyina Lilnnāsi Ĥubbu Ash-Shahawāti Mina An-Nisā' Wa Al-Banīna Wa Al-Qanāţīri Al-Muqanţarati Mina Adh-Dhahabi Wa Al-Fiđđati Wa Al-Khayli Al-Musawwamati Wa Al-'An`āmi Wa Al-Ĥarthi  ۗ  Dhālika Matā`u Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Wa  ۖ  Allāhu `Indahu Ĥusnu Al-Ma'ābi َ003-014 An ƙawata wa mutãne son sha'awõyi daga mãtã da ɗiya da dũkiyõyi abũbuwan tãrãwa daga zinariya da azurfa, da dawãki kiwãtattu da dabbõbin ci da hatsi. Wannan shi ne dãɗin rãyuwar dũniya. Kuma Allah a wurinsa kyakkyãwar makõma take. زُيِّنَ لِلنَّاسِ حُبُّ الشَّهَوَاتِ مِنَ النِسَاء وَالْبَنِينَ وَالْقَنَاطِيرِ الْمُقَنْطَرَةِ مِنَ الذَّهَبِ وَالْفِضَّةِ وَالْخَيْلِ الْمُسَوَّمَةِ وَالأَنعَامِ وَالْحَرْثِ  ۗ  ذَلِكَ مَتَاعُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا  ۖ  وَاللَّهُ عِنْدَه ُُ حُسْنُ الْمَآبِ
Qul 'A'uunabbi'ukum Bikhayrin Min Dhālikum  ۚ  Lilladhīna Attaqaw `Inda Rabbihim Jannātun Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā Wa 'Azwājun Muţahharatun Wa Riđwānun Mina Al-Lahi Wa  ۗ  Allāhu Başīrun Bil-`Ibādi َ003-015 Ka ce: Shin kuma, in gaya muku mafi alhẽri daga wannan? Akwai gidãjen Aljanna a wurin Ubangiji sabõda waɗanda suka bi Shi da taƙawa, kõguna suna gudãna daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, da mãtan aure tsarkakakku, da yarda daga Allah. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa. قُلْ أَؤُنَبِّئُكُمْ بِخَيْر ٍ مِنْ ذَلِكُمْ  ۚ  لِلَّذِينَ اتَّقَوْا عِنْدَ رَبِّهِمْ جَنَّات ٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا وَأَزْوَاج ٌ مُطَهَّرَة ٌ وَرِضْوَان ٌ مِنَ اللَّهِ  ۗ  وَاللَّهُ بَصِير ٌ بِالْعِبَادِ
Al-Ladhīna Yaqūlūna Rabbanā 'Innanā 'Āmannā Fāghfir Lanā Dhunūbanā Wa Qinā `Adhāba An-Nāri َ003-016 Waɗanda suke cẽwa: "Ya Ubangijinmu! Lalle ne mu, mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana zunubanmu kuma Ka tsare mu daga azãbar wuta." الَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا إِنَّنَا آمَنَّا فَاغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ
Aş-Şābirīna Wa Aş-Şādiqīna Wa Al-Qānitīna Wa Al-Munfiqīna Wa Al-Mustaghfirīna Bil-'Asĥāri َ003-017 Mãsu haƙuri, da mãsu gaskiya, da mãsu ƙanƙan da kai, da mãsu ciyarwa da mãsu istingifari a lõkutan asuba. الصَّابِرِينَ وَالصَّادِقِينَ وَالْقَانِتِينَ وَالْمُنْفِقِينَ وَالْمُسْتَغْفِرِينَ بِالأَسْحَارِ
Shahida Al-Lahu 'Annahu Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Wa Al-Malā'ikatu Wa 'Ū Al-`Ilmi Qā'imāan Bil-Qisţi  ۚ  Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ003-018 Allah Ya shaida cẽwa: Lalle ne bãbu abin bautãwa fãce Shi kuma malãiku da ma'abũta ilmi sun shaida, yana tsaye da ãdalci, bãbu abin bautãwa face Shi, Mabuwãyi, Mai hikima. شَهِدَ اللَّهُ أَنَّهُ لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ وَالْمَلاَئِكَةُ وَأُوْلُوا الْعِلْمِ قَائِما ً بِالْقِسْطِ  ۚ  لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
'Inna Ad-Dīna `Inda Al-Lahi Al-'Islāmu  ۗ  Wa Mā Akhtalafa Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba 'Illā Min Ba`di Mā Jā'ahumu Al-`Ilmu Baghyāan Baynahum  ۗ  Wa Man Yakfur Bi'āyāti Al-Lahi Fa'inna Al-Laha Sarī`u Al-Ĥisābi َ003-019 Lalle ne, addini a wurin Allah, Shi ne Musulunci. Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓã ba, fãce a bãyan ilmi ya je musu, bisa zãlunci a tsakãninsu. Kuma wanda ya kãfirta da ãyõyin Allah, to, lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako ne. إِنَّ الدِّينَ عِنْدَ اللَّهِ الإِسْلاَمُ  ۗ  وَمَا اخْتَلَفَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ إِلاَّ مِنْ بَعْدِ مَا جَاءَهُمُ الْعِلْمُ بَغْيا ً بَيْنَهُمْ  ۗ  وَمَنْ يَكْفُرْ بِآيَاتِ اللَّهِ فَإِنَّ اللَّهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ
Fa'in Ĥājjūka Faqul 'Aslamtu Wajhiya Lillahi Wa Mani Attaba`ani Wa Qul  ۗ  Lilladhīna 'Ū Al-Kitāba Wa Al-'Ummīyīna 'A'aslamtum Fa'in  ۚ  'Aslamū Faqadi Ahtadaw Wa 'In  ۖ  Tawallaw Fa'innamā `Alayka Al-Balāghu Wa Allāhu  ۗ  Başīrun Bil-`Ibādi َ003-020 To, idan sun yi musu da kai, sai ka ce: "Nã sallama fuskata ga Allah, kuma wanda ya bi ni (haka)." Kuma ka ce wa waɗanda aka bai wa littãfi da Ummiyyai: "Shin kun sallama?" To, idan sun sallama, haƙĩƙa, sun shiryu kuma idan sun jũya, to, kawai abinda ke kanka, shi ne iyarwa. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa. فَإِنْ حَاجُّوكَ فَقُلْ أَسْلَمْتُ وَجْهِيَ لِلَّهِ وَمَنِ اتَّبَعَنِ  ۗ  وَقُلْ لِلَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ وَالأُمِّيِّينَ أَأَسْلَمْتُمْ  ۚ  فَإِنْ أَسْلَمُوا فَقَدِ اهْتَدَوا  ۖ  وَإِنْ تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا عَلَيْكَ الْبَلاَغُ  ۗ  وَاللَّهُ بَصِير ٌ بِالْعِبَادِ
'Inna Al-Ladhīna Yakfurūna Bi'āyāti Al-Lahi Wa Yaqtulūna An-Nabīyīna Bighayri Ĥaqqin Wa Yaqtulūna Al-Ladhīna Ya'murūna Bil-Qisţi Mina An-Nāsi Fabashshirhum Bi`adhābin 'Alīmin َ003-021 Lalle ne waɗanda suke kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Annabãwa bã da wani hakki ba, kuma suna kashe waɗanda ke umurni da yin ãdalci daga mutãne, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi. إِنَّ الَّذِينَ يَكْفُرُونَ بِآيَاتِ اللَّهِ وَيَقْتُلُونَ النَّبِيِّينَ بِغَيْرِ حَقّ ٍ وَيَقْتُلُونَ الَّذِينَ يَأْمُرُونَ بِالْقِسْطِ مِنَ النَّاسِ فَبَشِّرْهُمْ بِعَذَابٍ أَلِيم ٍ
'Ūlā'ika Al-Ladhīna Ĥabiţat 'A`māluhum Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati Wa Mā Lahum Min Nāşirīna َ003-022 Waɗannan ne waɗanda ayyukansu suka ɓãci a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wasu mataimaka. أُوْلَائِكَ الَّذِينَ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَمَا لَهُمْ مِنْ نَاصِرِينَ
'Alam Tara 'Ilá Al-Ladhīna 'Ūtū Naşībāan Mina Al-Kitābi Yud`awna 'Ilá Kitābi Al-Lahi Liyaĥkuma Baynahum Thumma Yatawallá Farīqun Minhum Wa Hum Mu`rūna َ003-023 Shin, ba ka ga waɗanda aka bai wa rabo daga littãfi ba ana kiran su zuwa ga Littãfin Allah dõmin ya yi hukunci a tsakãninsu sa'an nan wata ƙungiya daga cikinsu ta jũya bãya, kuma sunã mãsu bijirẽwa? أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ أُوتُوا نَصِيبا ً مِنَ الْكِتَابِ يُدْعَوْنَ إِلَى كِتَابِ اللَّهِ لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ ثُمَّ يَتَوَلَّى فَرِيق ٌ مِنْهُمْ وَهُمْ مُعْرِضُونَ
Dhālika Bi'annahum Qālū Lan Tamassanā An-Nāru 'Illā 'Ayyāmāan Ma`dūdātin  ۖ  Wa Gharrahum Fī Dīnihim Mā Kānū Yaftarūna َ003-024 Wannan kuwa, dõmin lalle ne su sun ce: "Wutã bã zã ta shãfe mu ba, fãce a 'yan kwãnaki ƙidãyayyu." Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya rũɗẽ su a cikin addininsu. ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوا لَنْ تَمَسَّنَا النَّارُ إِلاَّ أَيَّاما ً مَعْدُودَات ٍ  ۖ  وَغَرَّهُمْ فِي دِينِهِمْ مَا كَانُوا يَفْتَرُونَ
Fakayfa 'Idhā Jama`nāhum Liyawmin Lā Rayba Fīhi Wa Wuffiyat Kullu Nafsin Mā Kasabat Wa Hum Lā Yužlamūna َ003-025 To, yãya idan Mun tãra su a yini wanda bãbu shakka a cikinsa, kuma aka cikã wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta, alhãli kuwa, sũ bã zã a zãlunce su ba? فَكَيْفَ إِذَا جَمَعْنَاهُمْ لِيَوْم ٍ لاَ رَيْبَ فِيه ِِ وَوُفِّيَتْ كُلُّ نَفْس ٍ مَا كَسَبَتْ وَهُمْ لاَ يُظْلَمُونَ
Quli Al-Lahumma Mālika Al-Mulki Tu'utī Al-Mulka Man Tashā'u Wa Tanzi`u Al-Mulka Mimman Tashā'u Wa Tu`izzu Man Tashā'u Wa Tudhillu Man Tashā'u  ۖ  Biyadika Al-Khayru  ۖ  'Innaka `Alá Kulli Shay'in Qadīrun َ003-026 Ka ce: "Yã Allah Mamallakin mulki, Kanã bayar da mulki ga wanda Kake so, Kanã zãre mulki daga wanda Kake so, kuma Kanã buwãyar da wanda Kake so, kuma Kanã ƙasƙantar da wanda Kake so, ga hannunKa alhẽri yake. Lalle ne Kai, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne." "Kanã shigar da dare a cikin yini, kuma Kanã shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga mamaci, kuma Kanã fitar da mamaci daga mai rai, kuma Kanã azurta wanda Kake so bã da lissafi ba." قُلِ اللَّهُمَّ مَالِكَ الْمُلْكِ تُؤْتِي الْمُلْكَ مَنْ تَشَاءُ وَتَنْزِعُ الْمُلْكَ مِمَّنْ تَشَاءُ وَتُعِزُّ مَنْ تَشَاءُ وَتُذِلُّ مَنْ تَشَاءُ  ۖ  بِيَدِكَ الْخَيْرُ  ۖ  إِنَّكَ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِير ٌ
Tūliju Al-Layla Fī An-Nahāri Wa Tūliju An-Nahāra Fī Al-Layli  ۖ  Wa Tukhriju Al-Ĥayya Mina Al-Mayyiti Wa Tukhriju Al-Mayyita Mina Al-Ĥayyi  ۖ  Wa Tarzuqu Man Tashā'u Bighayri Ĥisābin َ003-027 Kada mũminai su riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Kuma wanda ya yi wannan, to, bai zama a cikin kõme ba daga Allah, fãce fa dõmin ku yi tsaro daga gare su da 'yar kãriya. Kuma Allah yana tsõratar da ku kanSa. Kuma zuwa ga Allah makõma take. تُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَتُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ  ۖ  وَتُخْرِجُ الْحَيَّ مِنَ الْمَيِّتِ وَتُخْرِجُ الْمَيِّتَ مِنَ الْحَيِّ  ۖ  وَتَرْزُقُ مَنْ تَشَاءُ بِغَيْرِ حِسَاب ٍ
Lā Yattakhidhi Al-Mu'uminūna Al-Kāfirīna 'Awliyā'a Min Dūni Al-Mu'uminīna  ۖ  Wa Man Yaf`al Dhālika Falaysa Mina Al-Lahi Fī Shay'in 'Illā 'An Tattaqū Minhum Tuqāatan  ۗ  Wa Yuĥadhdhirukumu Al-Lahu Nafsahu  ۗ  Wa 'Ilá Al-Lahi Al-Maşīru َ003-028 Ka ce: "Idan kun ɓõye abin da ke a cikin ƙirãzanku, kõ kuwa kun bayyana shi, Allah Yana sanin sa. Kuma Yana sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah a kan kõwane abu Mai ĩkon yi ne." لاَ يَتَّخِذِ الْمُؤْمِنُونَ الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِنْ دُونِ الْمُؤْمِنِينَ  ۖ  وَمَنْ يَفْعَلْ ذَلِكَ فَلَيْسَ مِنَ اللَّهِ فِي شَيْء ٍ إِلاَّ أَنْ تَتَّقُوا مِنْهُمْ تُقَاة ً  ۗ  وَيُحَذِّرُكُمُ اللَّهُ نَفْسَه ُُ  ۗ  وَإِلَى اللَّهِ الْمَصِيرُ
Qul 'In Tukhfū Mā Fī Şudūrikum 'Aw Tubdūhu Ya`lamhu Al-Lahu  ۗ  Wa Ya`lamu Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi Wa  ۗ  Allāhu `Alá Kulli Shay'in Qadīrun َ003-029 - Missing - قُلْ إِنْ تُخْفُوا مَا فِي صُدُورِكُمْ أَوْ تُبْدُوه ُُ يَعْلَمْهُ اللَّهُ  ۗ  وَيَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ  ۗ  وَاللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِير ٌ
Yawma Tajidu Kullu Nafsin Mā `Amilat Min Khayrin Muĥđarāan Wa Mā `Amilat Min Sū'in Tawaddu Law 'Anna Baynahā Wa Baynahu 'Amadāan Ba`īdāan  ۗ  Wa Yuĥadhdhirukumu Al-Lahu Nafsahu Wa  ۗ  Allāhu Ra'ūfun Bil-`Ibādi َ003-030 A Rãnar da kõwane rai yake sãmun abin da ya aikata daga alhẽri, a halarce, da kuma abin da ya aikata daga sharri, alhãli yana gũrin, dã dai lalle a ce akwai fage mai nĩsa a tsakãninsa da abin daya aikata na sharrin! Kuma Allah Yanã tsõratar da kũ kanSa. Kuma Allah Mai tausayi ne ga bãyinSa. يَوْمَ تَجِدُ كُلُّ نَفْس ٍ مَا عَمِلَتْ مِنْ خَيْر ٍ مُحْضَرا ً وَمَا عَمِلَتْ مِنْ سُوء ٍ تَوَدُّ لَوْ أَنَّ بَيْنَهَا وَبَيْنَهُ~ُ أَمَدا ً بَعِيدا ً  ۗ  وَيُحَذِّرُكُمُ اللَّهُ نَفْسَه ُُ  ۗ  وَاللَّهُ رَءُوف ٌ بِالْعِبَادِ
Qul 'In Kuntum Tuĥibbūna Al-Laha Fa Attabi`ūnī Yuĥbibkumu Al-Lahu Wa Yaghfir Lakum Dhunūbakum Wa  ۗ  Allāhu Ghafūrun Raĥīmun َ003-031 Ka ce: "Idan kun kasance kunã son Allah to, ku bĩ ni, Allah Ya sõ ku, kuma Ya gãfarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai." قُلْ إِنْ كُنْتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ  ۗ  وَاللَّهُ غَفُور ٌ رَحِيم ٌ
Qul 'Aţī`ū Al-Laha Wa Ar-Rasūla  ۖ  Fa'in Tawallaw Fa'inna Al-Laha Lā Yuĥibbu Al-Kāfirīna َ003-032 Ka ce: "Ku yi ɗã'a ga Allah da Manzo." To, amma idan sun jũya bãya, to, lalle ne Allah bã Ya son kãfirai. قُلْ أَطِيعُوا اللَّهَ وَالرَّسُولَ  ۖ  فَإِنْ تَوَلَّوْا فَإِنَّ اللَّهَ لاَ يُحِبُّ الْكَافِرِينَ
'Inna Al-Laha Aşţafá 'Ādama Wa Nūĥāan Wa 'Āla 'Ibrāhīma Wa 'Āla `Imrān `Alá Al-`Ālamīna َ003-033 Lalle ne Allah Yã zãɓi Ãdama da Nũhu da Gidan Ibrãhĩma da Gidan Imrãna a kan tãlikai. إِنَّ اللَّهَ اصْطَفَى آدَمَ وَنُوحا ً وَآلَ إِبْرَاهِيمَ وَآلَ عِمرَان عَلَى الْعَالَمِينَ
Dhurrīyatan Ba`đuhā Min Ba`đin Wa  ۗ  Allāhu Samī`un `Alīmun َ003-034 Zuriyya ce sãshensu daga sãshe, kuma Allah Mai ji ne, Masani. ذُرِّيَّة ً بَعْضُهَا مِنْ بَعْض ٍ  ۗ  وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيم ٌ
'Idh Qālati Amra'atu `Imrāna Rabbi 'Innī Nadhartu Laka Mā Fī Baţnī Muĥarrarāan Fataqabbal Minnī  ۖ  'Innaka 'Anta As-Samī`u Al-`Alīmu َ003-035 A lõkacin da mãtar Imrãna ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ni, nã yi bãkancen abin da ke cikin cikĩna gare Ka; ya zama 'yantacce, sai Ka karɓa daga gare ni. Lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Masani." إِذْ قَالَتِ امْرَأَةُ عِمْرَانَ رَبِّ إِنِّي نَذَرْتُ لَكَ مَا فِي بَطْنِي مُحَرَّرا ً فَتَقَبَّلْ مِنِّي  ۖ  إِنَّكَ أَنْتَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Falammā Wađa`at/hā Qālat Rabbi 'Innī Wađa`tuhā 'Unthá Wa Allāhu 'A`lamu Bimā Wađa`at Wa Laysa Adh-Dhakaru Kāl'unthá  ۖ  Wa 'Innī Sammaytuhā Maryama Wa 'Innī 'U`īdhuhā Bika Wa Dhurrīyatahā Mina Ash-Shayţāni Ar-Rajīmi َ003-036 To, a lõkacin da ta haife ta sai ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne nĩ, nã haife ta mace!"KumaAllah ne Mafi sanin abin da ta haifa." Kuma namiji bai zama kamar mace ba. Kuma nĩ nã yi mata suna Maryamu kuma lalle ne ni, ina nẽma mata tsari gare Ka, ita da zũriyarta daga Shaiɗan jẽfaffe." فَلَمَّا وَضَعَتْهَا قَالَتْ رَبِّ إِنِّي وَضَعْتُهَا أُنْثَى وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا وَضَعَتْ وَلَيْسَ الذَّكَرُ كَالأُنْثَى  ۖ  وَإِنِّي سَمَّيْتُهَا مَرْيَمَ وَإِنِّي أُعِيذُهَا بِكَ وَذُرِّيَّتَهَا مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ
Fataqabbalahā Rabbuhā Biqabūlin Ĥasanin Wa 'Anbatahā Nabātāan Ĥasanāan Wa Kaffalahā Zakarīyā  ۖ  Kullamā Dakhala `Alayhā Zakarīyā Al-Miĥrāba Wajada `Indahā Rizqāan  ۖ  Qāla Yā Maryamu 'Anná Laki Hādhā  ۖ  Qālat Huwa Min `Indi Al-Lahi  ۖ  'Inna Al-Laha Yarzuqu Man Yashā'u Bighayri Ĥisābin َ003-037 Sai Ubangijinta Ya karɓe ta karɓa mai kyau. Kuma Ya yabanyartar da ita yabanyartarwa mai kyau, kuma Ya sanya rẽnonta ga Zakariyya. Ko da yaushe Zakariyya ya shiga masallãci, a gare ta, sai ya sãmi abinci a wurinta. (Sai kuwa) ya ce: "Yã Maryamu! Daga ina wannan yake gare ki?" (Sai) ta ce: "Daga wurin Allah yake. Lalle ne Allah yana azurta wanda Ya so ba da lissafi ba." فَتَقَبَّلَهَا رَبُّهَا بِقَبُولٍ حَسَن ٍ وَأَنْبَتَهَا نَبَاتاً حَسَنا ً وَكَفَّلَهَا زَكَرِيَّا  ۖ  كُلَّمَا دَخَلَ عَلَيْهَا زَكَرِيَّا الْمِحْرَابَ وَجَدَ عِنْدَهَا رِزْقا ً  ۖ  قَالَ يَا مَرْيَمُ أَنَّى لَكِ هَذَا  ۖ  قَالَتْ هُوَ مِنْ عِنْدِ اللَّهِ  ۖ  إِنَّ اللَّهَ يَرْزُقُ مَنْ يَشَاءُ بِغَيْرِ حِسَاب ٍ
Hunālika Da`ā Zakarīyā Rabbahu  ۖ  Qāla Rabbi Hab Lī Min Ladunka Dhurrīyatan Ţayyibatan  ۖ  'Innaka Samī`u Ad-Du`ā'i َ003-038 A can ne Zakariyya ya rõki Ubangijinsa, ya ce: "Ya Ubangijina! Ka bã ni zuriyya mai kyau daga gunKa. Lalle ne Kai Mai jin addu'a Kake." هُنَالِكَ دَعَا زَكَرِيَّا رَبَّه ُُ  ۖ  قَالَ رَبِّ هَبْ لِي مِنْ لَدُنْكَ ذُرِّيَّة ً طَيِّبَة ً  ۖ  إِنَّكَ سَمِيعُ الدُّعَاءِ
Fanādat/hu Al-Malā'ikatu Wa Huwa Qā'imun Yuşallī Fī Al-Miĥrābi 'Anna Al-Laha Yubashshiruka Biyaĥyá Muşaddiqāan Bikalimatin Mina Al-Lahi Wa Sayyidāan Wa Ĥaşūrāan Wa Nabīyāan Mina Aş-Şāliĥīna َ003-039 Sai malã'iku suka kirãye shi, alhãli kuwa shĩ yanã tsaye yana salla a cikin masallãci. (Suka ce), "Lalle ne Allah yana bã ka bushãra da Yahaya, alhãli yana mai gaskatãwar wata kalma daga Allah, kuma shugaba, kuma tsarkakke kuma annabi daga sãlihai." فَنَادَتْهُ الْمَلاَئِكَةُ وَهُوَ قَائِم ٌ يُصَلِّي فِي الْمِحْرَابِ أَنَّ اللَّهَ يُبَشِّرُكَ بِيَحْيَى مُصَدِّقا ً بِكَلِمَة ٍ مِنَ اللَّهِ وَسَيِّدا ً وَحَصُورا ً وَنَبِيّا ً مِنَ الصَّالِحِينَ
Qāla Rabbi 'Anná Yakūnu Lī Ghulāmun Wa Qad Balaghaniya Al-Kibaru Wa Amra'atī `Āqirun  ۖ  Qāla Kadhālika Al-Lahu Yaf`alu Mā Yashā'u َ003-040 Ya ce: "Yã Ubangijina! Yãya yãro zai sãmu a gare ni, alhãli kuwa, lalle tsũfa ya sãme ni,kuma mãtãta bakarãriya ce?" Allah ya ce, "Kamar hakan ne, Allah yana aikata abin da Yake so." قَالَ رَبِّ أَنَّى يَكُونُ لِي غُلاَم ٌ وَقَدْ بَلَغَنِيَ الْكِبَرُ وَامْرَأَتِي عَاقِر ٌ  ۖ  قَالَ كَذَلِكَ اللَّهُ يَفْعَلُ مَا يَشَاءُ
Qāla Rabbi Aj`al Lī 'Āyatan  ۖ  Qāla 'Āyatuka 'Allā Tukallima An-Nāsa Thalāthata 'Ayyāmin 'Illā Ramzāan  ۗ  Wa Adhkur Rabbaka Kathīrāan Wa Sabbiĥ Bil-`Ashīyi Wa Al-'Ibkāri َ003-041 Ya ce: "Yã Ubangijinã! Ka sanya mini wata alãma!" (Allah) Ya ce "Alãmarka ita ce ba zã ka iya yi wa mutãne magana ba har yini uku face da ishãra. Sai ka ambaci Ubangijinka da yawa. Kuma ka yi tasbĩhi da marece da sãfe." قَالَ رَبِّ اجْعَلْ لِي آيَة ً  ۖ  قَالَ آيَتُكَ أَلاَّ تُكَلِّمَ النَّاسَ ثَلاَثَةَ أَيَّام ٍ إِلاَّ رَمْزا ً  ۗ  وَاذْكُرْ رَبَّكَ كَثِيرا ً وَسَبِّحْ بِالْعَشِيِّ وَالإِبْكَارِ
Wa 'Idh Qālati Al-Malā'ikatu Yā Maryamu 'Inna Al-Laha Aşţafāki Wa Ţahharaki Wa Aşţafāki `Alá Nisā'i Al-`Ālamīna َ003-042 Kuma a lõkacin da malã'iku suka ce: "Ya Maryamu! Lalle ne, Allah Ya zãɓe ki, kuma Ya tsarkake ki, kuma Ya zaɓe ki a kan mãtan tãlikai." وَإِذْ قَالَتِ الْمَلاَئِكَةُ يَا مَرْيَمُ إِنَّ اللَّهَ اصْطَفَاكِ وَطَهَّرَكِ وَاصْطَفَاكِ عَلَى نِسَاءِ الْعَالَمِينَ
Yā Maryamu Aqnutī Lirabbiki Wa Asjudī Wa Arka`ī Ma`a Ar-Rāki`īna َ003-043 "Yã Maryamu! Ki yi ƙanƙan da kai ga Ubangijinki, kuma ki yi sujada, kuma ki yi rukũ'i tãre da mãsu rukũ'i." يَا مَرْيَمُ اقْنُتِي لِرَبِّكِ وَاسْجُدِي وَارْكَعِي مَعَ الرَّاكِعِينَ
Dhālika Min 'Nbā'i Al-Ghaybi Nūĥīhi 'Ilayka  ۚ  Wa Mā Kunta Ladayhim 'Idh Yulqūna 'Aqlāmahum 'Ayyuhum Yakfulu Maryama Wa Mā Kunta Ladayhim 'Idh Yakhtaşimūna َ003-044 Wannan yana daga lãbarun gaibi, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance ba a wurinsu a lõkacin da suke jẽfa alƙalumansu (domin ƙuri'a) wãne ne zai yi rẽnon Maryam. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke ta yin husũma . ذَلِكَ مِنْ أنْبَاءِ الْغَيْبِ نُوحِيهِ~ِ إِلَيْكَ  ۚ  وَمَا كُنْتَ لَدَيْهِمْ إِذْ يُلْقُونَ أَقْلاَمَهُمْ أَيُّهُمْ يَكْفُلُ مَرْيَمَ وَمَا كُنْتَ لَدَيْهِمْ إِذْ يَخْتَصِمُونَ
'Idh Qālati Al-Malā'ikatu Yā Maryamu 'Inna Al-Laha Yubashshiruki Bikalimatin Minhu Asmuhu Al-Masīĥu `Īsá Abnu Maryama Wajīhāan Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati Wa Mina Al-Muqarrabīna َ003-045 A lõkacin da malã'iku suka ce "Yã Maryamu! Lalle ne Allah Yana bã ki bushãra da wata kalma daga gare Shi; sũnansa Masĩhu ĩsa ɗan Maryama, yana mai daraja a dũniya da Lãhira kuma daga Makusanta. إِذْ قَالَتِ الْمَلاَئِكَةُ يَامَرْيَمُ إِنَّ اللَّهَ يُبَشِّرُكِ بِكَلِمَة ٍ مِنْهُ اسْمُهُ الْمَسِيحُ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ وَجِيها ً فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَمِنَ الْمُقَرَّبِينَ
Wa Yukallimu An-Nāsa Fī Al-Mahdi Wa Kahlāan Wa Mina Aş-Şāliĥīna َ003-046 "Kuma yana yi wa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma lõkacin da yana dattijo, kuma yana daga sãlihai." وَيُكَلِّمُ النَّاسَ فِي الْمَهْدِ وَكَهْلا ً وَمِنَ الصَّالِحِينَ
Qālat Rabbi 'Anná Yakūnu Lī Waladun Wa Lam Yamsasnī Basharun  ۖ  Qāla Kadhāliki Al-Lahu Yakhluqu Mā Yashā'u  ۚ  'Idhā Qađá 'Amrāan Fa'innamā Yaqūlu Lahu Kun Fayakūnu َ003-047 Ta ce: "Yã Ubangijina! Yãya yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba?" (Allah) Ya ce: "Kamar wannan ne, Allah yana halittar abin da Yake so. Idan Ya hukunta wani al'amari, sai ya ce masa, "Ka kasance!, Sai yana kasancẽwa." قَالَتْ رَبِّ أَنَّى يَكُونُ لِي وَلَد ٌ وَلَمْ يَمْسَسْنِي بَشَر ٌ  ۖ  قَالَ كَذَلِكِ اللَّهُ يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ  ۚ  إِذَا قَضَى أَمْرا ً فَإِنَّمَا يَقُولُ لَه ُُ كُنْ فَيَكُونُ
Wa Yu`allimuhu Al-Kitāba Wa Al-Ĥikmata Wa At-Tawrāata Wa Al-'Injīla َ003-048 Kuma Ya sanar da shi rubũtu da hikima da Taurata da injĩla. وَيُعَلِّمُهُ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَالتَّوْرَاةَ وَالإِنجِيلَ
Wa Rasūlāan 'Ilá Banī 'Isrā'īla 'Annī Qad Ji'tukum Bi'āyatin Min Rabbikum  ۖ  'Annī 'Akhluqu Lakum Mina Aţīni Kahay'ati Aţ-Ţayri Fa'anfukhu Fīhi Fayakūnu Ţayrāan Bi'idhni Al-Lahi  ۖ  Wa 'Ubri'u Al-'Akmaha Wa Al-'Abraşa Wa 'Uĥyi Al-Mawtá Bi'idhni Al-Lahi  ۖ  Wa 'Unabbi'ukum Bimā Ta'kulūna Wa Mā Taddakhirūna Fī Buyūtikum  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyatan Lakum 'In Kuntum Mu'uminyna َ003-049 Kuma (Ya sanya shi) manzo zuwa ga Bani Isrãila'ĩla (da sãko, cẽwa), Lalle ne, ni haƙĩƙa nã zõ muku, da wata ãyã daga Ubangijinku. Lalle ne ni ina halitta muku daga lãka, kamar siffar tsuntsu sa'an nan in hũra a cikinsa, sai ya kasance tsuntsu, da izinin Allah. Kuma ina warkar da wanda aka haifa makãho da kuturu, kuma ina rãyar da matottu, da izibin Allah. Kuma ina gayã muku abin da kuke ci da abin da kuke ajiyẽwa acikin gidãjenku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyã a gare ku, idan kun kasance mãsu yin ĩmãni. وَرَسُولا ً إِلَى بَنِي إِسْرَائِيلَ أَنِّي قَدْ جِئْتُكُمْ بِآيَة ٍ مِنْ رَبِّكُمْ  ۖ  أَنِّي أَخْلُقُ لَكُمْ مِنَ الطِّينِ كَهَيْئَةِ الطَّيْرِ فَأَنفُخُ فِيه ِِ فَيَكُونُ طَيْرا ً بِإِذْنِ اللَّهِ  ۖ  وَأُبْرِئُ الأَكْمَه ََ وَالأَبْرَصَ وَأُحْيِ الْمَوْتَى بِإِذْنِ اللَّهِ  ۖ  وَأُنَبِّئُكُمْ بِمَا تَأْكُلُونَ وَمَا تَدَّخِرُونَ فِي بُيُوتِكُمْ  ۚ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَة ً لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنينَ
Wa Muşaddiqāan Limā Bayna Yadayya Mina At-Tawrāati Wa Li'uĥilla Lakum Ba`đa Al-Ladhī Ĥurrima `Alaykum  ۚ  Wa Ji'tukum Bi'āyatin Min Rabbikum Fa Attaqū Al-Laha Wa 'Aţī`ūni َ003-050 "Kuma inã mai gaskatãwa ga abin da yake a gabãnina daga Taurata. Kuma (nãzo) dõmin in halatta muku sãshen abin da aka haramta muku. Kuma nã tafo muku da wata ãyã daga Ubangijinku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã. وَمُصَدِّقا ً لِمَا بَيْنَ يَدَيَّ مِنَ التَّوْرَاةِ وَلِأُحِلَّ لَكُمْ بَعْضَ الَّذِي حُرِّمَ عَلَيْكُمْ  ۚ  وَجِئْتُكُمْ بِآيَة ٍ مِنْ رَبِّكُمْ فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ
'Inna Al-Laha Rabbī Wa Rabbukum Fā`budūhu  ۗ  Hādhā Şirāţun Mustaqīmun َ003-051 "Lalle Allah shi ne Ubangijina, kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan ce hanya madaidaiciya." إِنَّ اللَّهَ رَبِّي وَرَبُّكُمْ فَاعْبُدُوه ُُ  ۗ  هَذَا صِرَاط ٌ مُسْتَقِيم ٌ
Falammā 'Aĥassa `Īsá Minhumu Al-Kufra Qāla Man 'Anşārī 'Ilá Al-Lahi  ۖ  Qāla Al-Ĥawārīyūna Naĥnu 'Anşāru Al-Lahi 'Āmannā Bil-Lahi Wa Ash/had Bi'annā Muslimūna َ003-052 To, a lõkacin da Ĩsa ya gane kãfirci daga gare su, sai ya ce: "Su wãne ne mataimakãna zuwa ga Allah?" Hawãriyãwa suka ce: "Mu ne mataimakan Allah. Mun yi ĩmani da Allah. Kuma ka shaida cẽwa lalle ne mu, mãsu sallamãwa ne. فَلَمَّا أَحَسَّ عِيسَى مِنْهُمُ الْكُفْرَ قَالَ مَنْ أَنْصَارِي إِلَى اللَّهِ  ۖ  قَالَ الْحَوَارِيُّونَ نَحْنُ أَنْصَارُ اللَّهِ آمَنَّا بِاللَّهِ وَاشْهَدْ بِأَنَّا مُسْلِمُونَ
Rabbanā 'Āmannā Bimā 'Anzalta Wa Attaba`nā Ar-Rasūla Fāktubnā Ma`a Ash-Shāhidīna َ003-053 "Yã Ubangijinmu! Mun yi imãni da abin da Ka saukar, kuma mun bi ManzonKa, sai Ka rubũta mu tãre da mãsu shaida. . رَبَّنَا آمَنَّا بِمَا أَنْزَلْتَ وَاتَّبَعْنَا الرَّسُولَ فَاكْتُبْنَا مَعَ الشَّاهِدِينَ
Wa Makarū Wa Makara Al-Lahu Wa  ۖ  Allāhu Khayru Al-Mākirīna َ003-054 Kuma (Kãfirai) suka yi mãkirci, Allah kuma Ya yi musu (sakamakon) makircin, kuma Allah ne Mafi alhẽrin mãsu sãka wamãkirci. وَمَكَرُوا وَمَكَرَ اللَّهُ  ۖ  وَاللَّهُ خَيْرُ الْمَاكِرِينَ
'Idh Qāla Al-Lahu Yā `Īsá 'Innī Mutawaffīka Wa Rāfi`uka 'Ilayya Wa Muţahhiruka Mina Al-Ladhīna Kafarū Wa Jā`ilu Al-Ladhīna Attaba`ūka Fawqa Al-Ladhīna Kafarū 'Ilá Yawmi Al-Qiyā  ۖ  Mati Thumma 'Ilayya Marji`ukum Fa'aĥkumu Baynakum Fīmā Kuntum Fīhi Takhtalifūna َ003-055 A lõkacin da Ubangiji Ya ce: "Ya Ĩsa! Lalle NĨ Mai karɓar ranka ne, kuma Mai ɗauke ka ne zuwa gare Ni, kuma Mai tsarkake ka daga waɗanda suka kãfirta, kuma Mai sanya waɗanda suka bĩ ka a bisa waɗanda suka kãfirta har Rãnar ¡iyãma. Sa'an nan kuma zuwa gare Ni makõmarku take, sa'an nan in yi hukunci a tsakãninku, a cikin abin da kuka kasance kuna sãɓã wa jũna. إِذْ قَالَ اللَّهُ يَاعِيسَى إِنِّي مُتَوَفِّيكَ وَرَافِعُكَ إِلَيَّ وَمُطَهِّرُكَ مِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا وَجَاعِلُ الَّذِينَ اتَّبَعُوكَ فَوْقَ الَّذِينَ كَفَرُوا إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ ثُمَّ  ۖ  إِلَيَّ مَرْجِعُكُمْ فَأَحْكُمُ بَيْنَكُمْ فِيمَا كُنْتُمْ فِيه ِِ تَخْتَلِفُونَ
Fa'ammā Al-Ladhīna Kafarū Fa'u`adhdhibuhum `Adhābāan Shadīdāan Ad-Dunyā Wa Al-'Ākhirati Wa Mā Lahum Min Nāşirīna َ003-056 "To, amma waɗanda suka kãfirta sai In azabta su da azãba mai tsanani, a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wasu mãsu taimako. فَأَمَّا الَّذِينَ كَفَرُوا فَأُعَذِّبُهُمْ عَذَابا ً شَدِيدا ً فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَمَا لَهُمْ مِنْ نَاصِرِينَ
Wa 'Ammā Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Fayuwaffīhim 'Ujūrahum Wa  ۗ  Allāhu Lā Yuĥibbu Až-Žālimīna َ003-057 Kuma amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sai (Allah) Ya cikã musu ijãrõrinsu. Kuma Allah bã Ya son azzãlumai. وَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَيُوَفِّيهِمْ أُجُورَهُمْ  ۗ  وَاللَّهُ لاَ يُحِبُّ الظَّالِمِينَ
Dhālika Natlūhu `Alayka Mina Al-'Āyāti Wa Adh-Dhikri Al-Ĥakīmi َ003-058 "Wannan Muna karanta shi a gare ka (Muhammad) daga ãyõyi, da Tunatarwa mai hikima (Alƙur'ãni)." ذَلِكَ نَتْلُوه ُُ عَلَيْكَ مِنَ الآيَاتِ وَالذِّكْرِ الْحَكِيمِ
'Inna Mathala `Īsá `Inda Al-Lahi Kamathali 'Ādama  ۖ  Khalaqahu Min Turābin Thumma Qāla Lahu Kun Fayakūnu َ003-059 Lalle ne misãlin Ĩsã a wurin Allah kamar misãlin Ãdama ne, (Allah) Yã halitta shi daga turɓãya, sa'an nan kuma Ya ce masa: "Ka kasance: "Sai yana kasancewa. إِنَّ مَثَلَ عِيسَى عِنْدَ اللَّهِ كَمَثَلِ آدَمَ  ۖ  خَلَقَه ُُ مِنْ تُرَاب ٍ ثُمَّ قَالَ لَه ُُ كُنْ فَيَكُونُ
Al-Ĥaqqu Min Rabbika Falā Takun Mina Al-Mumtarīna َ003-060 Gaskiya daga Ubangijinka take sabõda haka kada ka kasance daga mãsu shakka. الْحَقُّ مِنْ رَبِّكَ فَلاَ تَكُنْ مِنَ الْمُمْتَرِينَ
Faman Ĥājjaka Fīhi Min Ba`di Mā Jā'aka Mina Al-`Ilmi Faqul Ta`ālaw Nad`u 'Abnā'anā Wa 'Abnā'akum Wa Nisā'anā Wa Nisā'akum Wa 'Anfusanā Wa 'Anfusakum Thumma Nabtahil Fanaj`al La`nata Al-Lahi `Alá Al-Kādhibīna َ003-061 To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirãyi, 'yã'yanmu da 'yã'yanku da mãtanmu da mãtanku da kanmu da kanku sa'an nan kuma mu ƙanƙantar da kai sa'an nan kuma mu sanya la'anar, Allah a kan maƙaryata." فَمَنْ حَاجَّكَ فِيه ِِ مِنْ بَعْدِ مَا جَاءَكَ مِنَ الْعِلْمِ فَقُلْ تَعَالَوْا نَدْعُ أَبْنَاءَنَا وَأَبْنَاءَكُمْ وَنِسَاءَنَا وَنِسَاءَكُمْ وَأَنْفُسَنَا وَأَنْفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَلْ لَعْنَةَ اللَّهِ عَلَى الْكَاذِبِينَ
'Inna Hādhā Lahuwa Al-Qaşaşu Al-Ĥaqqu  ۚ  Wa Mā Min 'Ilahin 'Illā Al-Lahu  ۚ  Wa 'Inna Al-Laha Lahuwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ003-062 Lalle ne wannan, haƙĩƙa, shi ne lãbãri tabbatacce, kuma bãbu wani abin bautawa fãce Allah, kuma lalle ne, Allah, haƙĩƙa,Shi ne Mabuwãyi Mai hikima. إِنَّ هَذَا لَهُوَ الْقَصَصُ الْحَقُّ  ۚ  وَمَا مِنْ إِلَهٍ~ ٍ إِلاَّ اللَّهُ  ۚ  وَإِنَّ اللَّهَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Fa'in Tawallaw Fa'inna Al-Laha `Alīmun Bil-Mufsidīna َ003-063 To, idan sun jũya bãya, to, lalle Allah Masani ne ga maɓannata. فَإِنْ تَوَلَّوْا فَإِنَّ اللَّهَ عَلِيم ٌ بِالْمُفْسِدِينَ
Qul Yā 'Ahla Al-Kitābi Ta`ālaw 'Ilá Kalimatin Sawā'in Baynanā Wa Baynakum 'Allā Na`buda 'Illā Al-Laha Wa Lā Nushrika Bihi Shay'āan Wa Lā Yattakhidha Ba`đunā Ba`đāan 'Arbābāan Min Dūni Al-Lahi  ۚ  Fa'in Tawallaw Faqūlū Ash/hadū Bi'annā Muslimūna َ003-064 Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ku tafo zuwa ga kalma mai daidaitãwa a tsakã ninmu da ku; kada mu bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji, baicin Allah." To, idan sun jũya bã ya sai ku ce: "ku yi shaida cẽwa, lalle ne mu masu sallamã wa ne." قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْا إِلَى كَلِمَة ٍ سَوَاء ٍ بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ أَلاَّ نَعْبُدَ إِلاَّ اللَّهَ وَلاَ نُشْرِكَ بِه ِِ شَيْئا ً وَلاَ يَتَّخِذَ بَعْضُنَا بَعْضاً أَرْبَابا ً مِنْ دُونِ اللَّهِ  ۚ  فَإِنْ تَوَلَّوْا فَقُولُوا اشْهَدُوا بِأَنَّا مُسْلِمُونَ
Yā 'Ahla Al-Kitābi Lima Tuĥājjūna Fī 'Ibrāhīma Wa Mā 'Unzilati At-Tawrāatu Wa Al-'Injīlu 'Illā Min Ba`dihi  ۚ  'Afalā Ta`qilūna َ003-065 Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuke hujjacẽwa a cikin sha'anin lbrãhĩma, alhãli kuwa ba a saukar da Attaura da injĩla ba fãce daga bãyansa? Shin bã ku hankalta? يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لِمَ تُحَاجُّونَ فِي إِبْرَاهِيمَ وَمَا أُنْزِلَتِ التَّوْرَاةُ وَالإِنجِيلُ إِلاَّ مِنْ بَعْدِهِ~ِ  ۚ  أَفَلاَ تَعْقِلُونَ
Hā'antum Hā'uulā' Ĥājajtum Fīmā Lakum Bihi `Ilmun Falima Tuĥājjūna Fīmā Laysa Lakum Bihi `Ilmun Wa Allāhu  ۚ  Ya`lamu Wa 'Antum Lā Ta`lamūna َ003-066 Gã ku yã waɗannan! Kun yi hujjacẽwa a cikin abin da yake kunã da wani ilmi game da shi, to, don me kuma kuke yin hujjacẽwa a cikin abin da bã ku da wani ilmi game da shi? Allah yana sani, kuma kũ, ba ku sani ba! هَاأَنْتُمْ هَاؤُلاَء حَاجَجْتُمْ فِيمَا لَكُمْ بِه ِِ عِلْم ٌ فَلِمَ تُحَاجُّونَ فِيمَا لَيْسَ لَكُمْ بِه ِِ عِلْم ٌ وَاللَّهُ  ۚ  يَعْلَمُ وَأَنْتُمْ لاَ تَعْلَمُونَ
Mā Kāna 'Ibrāhīmu Yahūdīyāan Wa Lā Naşrānīyāan Wa Lakin Kāna Ĥanīfāan Muslimāan Wa Mā Kāna Mina Al-Mushrikīna َ003-067 Ibrãhĩma bai kasance Bayahũde ba, kuma bai kasance Banasãre ba, amma yã kasance mai karkata zuwa ga gaskiya, mai sallamãwa, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba. مَا كَانَ إِبْرَاهِيمُ يَهُودِيّا ً وَلاَ نَصْرَانِيّا ً وَلَكِنْ كَانَ حَنِيفا ً مُسْلِما ً وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ
'Inna 'Awlá An-Nāsi Bi'ibrāhīma Lalladhīna Attaba`ūhu Wa Hadhā An-Nabīyu Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Wa  ۗ  Allāhu Wa Līyu Al-Mu'uminīna َ003-068 Lalle ne mafi hakkin mutãne da Ibrãhĩma haƙĩƙa, sũ ne waɗanda suka bi shi a (zamaninsa) da wannan Annabi (Muhammadu) da waɗanda suka yi ĩmãni.Kuma Allah ne Majiɓincin mũminai. إِنَّ أَوْلَى النَّاسِ بِإِبْرَاهِيمَ لَلَّذِينَ اتَّبَعُوه ُُ وَهَذَا النَّبِيُّ وَالَّذِينَ آمَنُوا  ۗ  وَاللَّهُ وَلِيُّ الْمُؤْمِنِينَ
Waddat Ţā'ifatun Min 'Ahli Al-Kitābi Law Yuđillūnakum Wa Mā Yuđillūna 'Illā 'Anfusahum Wa Mā Yash`urūn َ003-069 Wata ƙungiya daga Mutãnen Littãfi sun yi gũrin su ɓatar da ku, to, ba su ɓatar da kõwa ba fãce kansu, kuma bã su sansancewa! وَدَّتْ طَائِفَة ٌ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ لَوْ يُضِلُّونَكُمْ وَمَا يُضِلُّونَ إِلاَّ أَنْفُسَهُمْ وَمَا يَشْعُرُون
Yā 'Ahla Al-Kitābi Lima Takfurūna Bi'āyāti Al-Lahi Wa 'Antum Tash/hadūna َ003-070 Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuka kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa kũ, kuna shaida (cẽwa sũ gaskiya ne)? يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لِمَ تَكْفُرُونَ بِآيَاتِ اللَّهِ وَأَنْتُمْ تَشْهَدُونَ
Yā 'Ahla Al-Kitābi Lima Talbisūna Al-Ĥaqqa Bil-Bāţili Wa Taktumūna Al-Ĥaqqa Wa 'Antum Ta`lamūna َ003-071 Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuke lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma kuke ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane? يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لِمَ تَلْبِسُونَ الْحَقَّ بِالْبَاطِلِ وَتَكْتُمُونَ الْحَقَّ وَأَنْتُمْ تَعْلَمُونَ
Wa Qālat Ţā'ifatun Min 'Ahli Al-Kitābi 'Āminū Bial-Ladhī 'Unzila `Alá Al-Ladhīna 'Āmanū Wajha An-Nahāri Wa Akfurū 'Ākhirahu La`allahum Yarji`ūna َ003-072 Kuma wata ƙungiya daga Mutãnen Littãfi ta ce: "Ku yi ĩmãni da abin da aka saukar a kan waɗanda suka yi ĩmãni (da Muhammadu) a farkon yini, kuma ku kãfirta a ƙarshensa; tsammãninsu, zã su kõmõ." وَقَالَتْ طَائِفَة ٌ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ آمِنُوا بِالَّذِي أُنْزِلَ عَلَى الَّذِينَ آمَنُوا وَجْهَ النَّهَارِ وَاكْفُرُوا آخِرَه ُُ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ
Wa Lā Tu'uminū 'Illā Liman Tabi`a Dīnakum Qul 'Inna Al-Hudá Hudá Al-Lahi 'An Yu'utá 'Aĥadun Mithla Mā 'Ūtītum 'Aw Yuĥājjūkum `Inda Rabbikum  ۗ  Qul 'Inna Al-Fađla Biyadi Al-Lahi Yu'utīhi Man Yashā'u Wa  ۗ  Allāhu Wāsi`un `Alīmun َ003-073 "Kada ku yi ĩmãni fãce da wanda ya bi addininku." Ka ce: "Lalle ne, shiriya ita ce shiriyar Allah. (Kuma kada ku yi ĩmãni) cẽwa an bai wa wani irin abin da aka bã ku, kõ kuwa su yi musu da ku a wurin Ubangijinku." Ka ce: "Lalle ne falala ga hannun Allah take, yana bãyar da ita ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadãci ne, Masani." وَلاَ تُؤْمِنُوا إِلاَّ لِمَنْ تَبِعَ دِينَكُمْ قُلْ إِنَّ الْهُدَى هُدَى اللَّهِ أَنْ يُؤْتَى أَحَد ٌ مِثْلَ مَا أُوتِيتُمْ أَوْ يُحَاجُّوكُمْ عِنْدَ رَبِّكُمْ  ۗ  قُلْ إِنَّ الْفَضْلَ بِيَدِ اللَّهِ يُؤْتِيه ِِ مَنْ يَشَاءُ  ۗ  وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيم ٌ
Yakhtaşşu Biraĥmatihi Man Yashā'u Wa  ۗ  Allāhu Dhū Al-Fađli Al-`Ažīmi َ003-074 Yanã keɓance wanda Ya so da rahamarSa, kuma Allah Ma'abucin falala ne, Mai girma. يَخْتَصُّ بِرَحْمَتِه ِِ مَنْ يَشَاءُ  ۗ  وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ
Wa Min 'Ahli Al-Kitābi Man 'In Ta'manhu Biqinţārin Yu'uaddihi 'Ilayka Wa Minhum Man 'In Ta'manhu Bidīnārin Lā Yu'uaddihi 'Ilayka 'Illā Mā Dumta `Alayhi Qā'imāan  ۗ  Dhālika Bi'annahum Qālū Laysa `Alaynā Fī Al-'Ummīyīna Sabīlun Wa Yaqūlūna `Alá Al-Lahi Al-Kadhiba Wa Hum Ya`lamūna َ003-075 Kuma daga Mutãnen Littãfi akwai wanda yake idan ka bã shi amãnar kinɗãri , zai bãyar da shi gare ka, kuma daga gare su akwai wanda idan ka bã shi amãnar dĩnari, bã zai bãyar da shi gare ka ba, fãce idan kã dawwama a kansa kanã tsaye. Wannan kuwa, dõmin lalle ne sũ sun ce, "Bãbu laifi a kanmu a cikin Ummiyyai." Suna faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa suna sane. وَمِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ مَنْ إِنْ تَأْمَنْهُ بِقِنطَار ٍ يُؤَدِّهِ~ِ إِلَيْكَ وَمِنْهُمْ مَنْ إِنْ تَأْمَنْهُ بِدِينَار ٍ لاَ يُؤَدِّهِ~ِ إِلَيْكَ إِلاَّ مَا دُمْتَ عَلَيْهِ قَائِما ً  ۗ  ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوا لَيْسَ عَلَيْنَا فِي الأُمِّيِّينَ سَبِيل ٌ وَيَقُولُونَ عَلَى اللَّهِ الْكَذِبَ وَهُمْ يَعْلَمُونَ
Balá Man 'Awfá Bi`ahdihi Wa Attaqá Fa'inna Al-Laha Yuĥibbu Al-Muttaqīna َ003-076 Na'am! Wanda ya cika alkawarinsa, kuma ya yi taƙawa, to, lalle ne Allah yana son mãsu taƙawa. بَلَى مَنْ أَوْفَى بِعَهْدِه ِِ وَاتَّقَى فَإِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُتَّقِينَ
'Inna Al-Ladhīna Yashtarūna Bi`ahdi Al-Lahi Wa 'Aymānihim Thamanāan Qalīlāan 'Ūlā'ika Lā Khalāqa Lahum Al-'Ākhirati Wa Lā Yukallimuhumu Al-Lahu Wa Lā Yanžuru 'Ilayhim Yawma Al-Qiyāmati Wa Lā Yuzakkīhim Wa Lahum `Adhābun 'Alīmun َ003-077 Lalle ne waɗanda suke sayen 'yan tamani kaɗan da alkawarin Allah da rantsuwõyinsu, waɗannan bãbu wani rabo a gare su a Lãhira, Kuma Allah bã Ya yin magana da su, kuma bã Ya dũbi zuwa gare su, a Rãnar ¡iyãma, kuma bã Ya tsarkake su, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi. إِنَّ الَّذِينَ يَشْتَرُونَ بِعَهْدِ اللَّهِ وَأَيْمَانِهِمْ ثَمَنا ً قَلِيلاً أُوْلَائِكَ لاَ خَلاَقَ لَهُمْ فِي الآخِرَةِ وَلاَ يُكَلِّمُهُمُ اللَّهُ وَلاَ يَنْظُرُ إِلَيْهِمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَلاَ يُزَكِّيهِمْ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيم ٌ
Wa 'Inna Minhum Lafarīqāan Yalwūna 'Alsinatahum Bil-Kitābi Litaĥsabūhu Mina Al-Kitābi Wa Mā Huwa Mina Al-Kitābi Wa Yaqūlūna Huwa Min `Indi Al-Lahi Wa Mā Huwa Min `Indi Al-Lahi Wa Yaqūlūna `Alá Al-Lahi Al-Kadhiba Wa Hum Ya`lamūna َ003-078 Kuma lalle ne, daga gare su akwai wata ƙungiya suna karkatar da harsunansu da Littãfi dõmin ku yi zaton sa daga Littãfin, alhãli kuwa bã shi daga Littãfin. Kuma suna cẽwa: "Shi daga wurinAllah yake." Alhãli kuwa shi, bã daga wurin Allah yake ba. Sunã faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa sunã sane. وَإِنَّ مِنْهُمْ لَفَرِيقا ً يَلْوُونَ أَلْسِنَتَهُمْ بِالْكِتَابِ لِتَحْسَبُوه ُُ مِنَ الْكِتَابِ وَمَا هُوَ مِنَ الْكِتَابِ وَيَقُولُونَ هُوَ مِنْ عِنْدِ اللَّهِ وَمَا هُوَ مِنْ عِنْدِ اللَّهِ وَيَقُولُونَ عَلَى اللَّهِ الْكَذِبَ وَهُمْ يَعْلَمُونَ
Mā Kāna Libasharin 'An Yu'utiyahu Al-Lahu Al-Kitāba Wa Al-Ĥukma Wa An-Nubūwata Thumma Yaqūla Lilnnāsi Kūnū `Ibādāan Lī Min Dūni Al-Lahi Wa Lakin Kūnū Rabbānīyīna Bimā Kuntum Tu`allimūna Al-Kitāba Wa Bimā Kuntum Tadrusūna َ003-079 Ba ya yiwuwa ga wani mutum, Allah Ya bã shi Littãfi da hukunci da Annabci, sa'an nan kuma ya ce wa mutãne: "Ku kasance bãyi gare ni, baicin Allah." Amma (zai ce): "Ku kasance mãsu aikin ibãda da abin da kuka kasance kuna karantar da Littãfin, kuma da abin da kuka kasance kuna karantãwa ." مَا كَانَ لِبَشَرٍ أَنْ يُؤْتِيَهُ اللَّهُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ ثُمَّ يَقُولَ لِلنَّاسِ كُونُوا عِبَادا ً لِي مِنْ دُونِ اللَّهِ وَلَكِنْ كُونُوا رَبَّانِيِّينَ بِمَا كُنْتُمْ تُعَلِّمُونَ الْكِتَابَ وَبِمَا كُنتُمْ تَدْرُسُونَ
Wa Lā Ya'murakum 'An Tattakhidhū Al-Malā'ikata Wa An-Nabīyīna 'Arbābāan  ۗ  'Aya'murukum Bil-Kufri Ba`da 'Idh 'Antum Muslimūna َ003-080 Kuma ba ya umurnin ku da ku riƙi malã'iku da annabãwa lyãyengiji. Shin, zai umurce ku da kãfirci ne a bãyan kun riga kun zama mãsu sallamãwa (Musulmi)? وَلاَ يَأْمُرَكُمْ أَنْ تَتَّخِذُوا الْمَلاَئِكَةَ وَالنَّبِيِّينَ أَرْبَاباً  ۗ  أَيَأْمُرُكُمْ بِالْكُفْرِ بَعْدَ إِذْ أَنْتُمْ مُسْلِمُونَ
Wa 'Idh 'Akhadha Al-Lahu Mīthāqa An-Nabīyīna Lamā 'Ātaytukum Min Kitābin Wa Ĥikmatin Thumma Jā'akum Rasūlun Muşaddiqun Limā Ma`akum Latu'uminunna Bihi Wa Latanşurunnahu  ۚ  Qāla 'A'aqrartum Wa 'Akhadhtum `Alá Dhālikum 'Işrī  ۖ  Qālū 'Aqrarnā  ۚ  Qāla Fāsh/hadū Wa 'Anā Ma`akum Mina Ash-Shāhidīna َ003-081 Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin Annabãwa: "Lalle ne ban bã ku wani abu ba daga Littãfi da hikima, sa'an nan kuma wani manzo ya je muku, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku; lalle ne zã ku gaskata Shi, kuma lalle ne zã ku taimake shi." Ya ce: "Shin, kun tabbatar kuma kun riƙi alkawarĩNa a kan wannan a gare ku?" suka ce: "Mun tabbatar." Ya ce: "To, ku yi shaida, kuma Nĩ a tãre da ku Inã daga mãsu shaida." وَإِذْ أَخَذَ اللَّهُ مِيثَاقَ النَّبِيِّينَ لَمَا آتَيْتُكُمْ مِنْ كِتَاب ٍ وَحِكْمَة ٍ ثُمَّ جَاءَكُمْ رَسُول ٌ مُصَدِّق ٌ لِمَا مَعَكُمْ لَتُؤْمِنُنَّ بِه ِِ وَلَتَنْصُرُنَّه ُُ  ۚ  قَالَ أَأَقْرَرْتُمْ وَأَخَذْتُمْ عَلَى ذَلِكُمْ إِصْرِي  ۖ  قَالُوا أَقْرَرْنَا  ۚ  قَالَ فَاشْهَدُوا وَأَنَا مَعَكُمْ مِنَ الشَّاهِدِينَ
Faman Tawallá Ba`da Dhālika Fa'ūlā'ika Humu Al-Fāsiqūna َ003-082 To, waɗanda kuma suka jũya bãya a bãyan wannan, to, waɗannan sũ ne fãsiƙai. فَمَنْ تَوَلَّى بَعْدَ ذَلِكَ فَأُوْلَائِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ
'Afaghayra Dīni Al-Lahi Yabghūna Wa Lahu 'Aslama Man As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Ţaw`āan Wa Karhāan Wa 'Ilayhi Yurja`ūna َ003-083 Shin wanin Addinin Allah suke nẽma, alhãli kuwa a gare Shi ne waɗanda ke cikin sama da ƙasa suka sallama wa, a kan sõ da ƙĩ, kuma zuwa gare Shi ake mayar da su? أَفَغَيْرَ دِينِ اللَّهِ يَبْغُونَ وَلَهُ~ُ أَسْلَمَ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ طَوْعا ً وَكَرْها ً وَإِلَيْهِ يُرْجَعُونَ
Qul 'Āmannā Bil-Lahi Wa Mā 'Unzila `Alaynā Wa Mā 'Unzila `Alá 'Ibrāhīma Wa 'Ismā`īla Wa 'Isĥāqa Wa Ya`qūba Wa Al-'Asbāţi Wa Mā 'Ūtiya Mūsá Wa `Īsá Wa An-Nabīyūna Min Rabbihim Lā Nufarriqu Bayna 'Aĥadin Minhum Wa Naĥnu Lahu Muslimūna َ003-084 Ka ce: "Mun yi ĩmãni da Allah kuma da abin da aka saukar mana da abin da aka saukar wa Ibrãhĩma da Isma'ĩla da Is'hãƙa da Yãƙũba da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da ĩsã da annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu bambantãwa a tsakãnin kõwa daga gare su. Kuma mũ, zuwa gare Shi mãsu sallamãwa ne." قُلْ آمَنَّا بِاللَّهِ وَمَا أُنْزِلَ عَلَيْنَا وَمَا أُنْزِلَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَالأَسْبَاطِ وَمَا أُوتِيَ مُوسَى وَعِيسَى وَالنَّبِيُّونَ مِنْ رَبِّهِمْ لاَ نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَد ٍ مِنْهُمْ وَنَحْنُ لَه ُُ مُسْلِمُونَ
Wa Man Yabtaghi Ghayra Al-'Islāmi Dīnāan Falan Yuqbala Minhu Wa Huwa Fī Al-'Ākhirati Mina Al-Khāsirīna َ003-085 Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra. وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الإِسْلاَمِ دِينا ً فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ
Kayfa Yahdī Al-Lahu Qawmāan Kafarū Ba`da 'Īmānihim Wa Shahidū 'Anna Ar-Rasūla Ĥaqqun Wa Jā'ahumu Al-Bayyinātu Wa  ۚ  Allāhu Lā Yahdī Al-Qawma Až-Žālimīna َ003-086 Yãya Allah zai shiryar da mutãne waɗanda suka kãfirta a bãyan ĩmãninsu, kuma sun yi shaidar cẽwa, lalle Manzo gaskiya ne, kuma hujjõji bayyanannu sun je musu? Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai. كَيْفَ يَهْدِي اللَّهُ قَوْما ً كَفَرُوا بَعْدَ إِيمَانِهِمْ وَشَهِدُوا أَنَّ الرَّسُولَ حَقّ ٌ وَجَاءَهُمُ الْبَيِّنَاتُ  ۚ  وَاللَّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ
'Ūlā'ika Jazā'uuhum 'Anna `Alayhim La`nata Al-Lahi Wa Al-Malā'ikati Wa An-Nāsi 'Ajma`īna َ003-087 Waɗannan, sakamakonsu shi ne, lalle a kansu akwai la'anar Allah da mãla'iku da mutãne gabã ɗaya. أُوْلَائِكَ جَزَاؤُهُمْ أَنَّ عَلَيْهِمْ لَعْنَةَ اللَّهِ وَالْمَلاَئِكَةِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ
Khālidīna Fīhā Lā Yukhaffafu `Anhumu Al-`Adhābu Wa Lā Hum Yunžarūna َ003-088 Sunã mãsu dawwama a cikinta, bã a sauƙaƙa azãbar gare su, kuma ba su zama ana yi musu jinkiri ba. خَالِدِينَ فِيهَا لاَ يُخَفَّفُ عَنْهُمُ الْعَذَابُ وَلاَ هُمْ يُنْظَرُونَ
'Illā Al-Ladhīna Tābū Min Ba`di Dhālika Wa 'Aşlaĥū Fa'inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun َ003-089 Fãce waɗanda suka tũba daga bãyan wannan, kuma suka yi gyãra, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne Mai jin ƙai. إِلاَّ الَّذِينَ تَابُوا مِنْ بَعْدِ ذَلِكَ وَأَصْلَحُوا فَإِنَّ اللَّهَ غَفُور ٌ رَحِيم ٌ
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Ba`da 'Īmānihim Thumma Azdādū Kufrāan Lan Tuqbala Tawbatuhum Wa 'Ūlā'ika Humu Ađ-Đāllūna َ003-090 Lalle ne waɗanda suka kãfirta a bãyan ĩmãninsu, sa'an nan kuma suka ƙãra kãfirci bã zã a karɓi tũbarsu ba. Kuma waɗannan sũ ne ɓatattu. إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا بَعْدَ إِيمَانِهِمْ ثُمَّ ازْدَادُوا كُفْرا ً لَنْ تُقْبَلَ تَوْبَتُهُمْ وَأُوْلَائِكَ هُمُ الضَّالُّونَ
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Wa Mātū Wa Hum Kuffārun Falan Yuqbala Min 'Aĥadihim Mil'u Al-'Arđi Dhahabāan Wa Law Aftadá Bihi  ۗ  'Ūlā'ika Lahum `Adhābun 'Alīmun Wa Mā Lahum Min Nāşirīna َ003-091 Lalle ne wanɗanda suka kãfirta, kuma suka mutu alhãli kuwa suna kãfirai to bã zã a karɓi cike da ƙasa na zinãri daga ɗayansu ba, kõ dã ya yi fansa da shi, waɗannan sunã da azãba mai raɗaɗi, kuma bã su da wasu mataimaka. إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا وَمَاتُوا وَهُمْ كُفَّار ٌ فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْ أَحَدِهِمْ مِلْءُ الأَرْضِ ذَهَبا ً وَلَوْ افْتَدَى بِهِ~ِ  ۗ  أُوْلَائِكَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيم ٌ وَمَا لَهُمْ مِنْ نَاصِرِينَ
Lan Tanālū Al-Birra Ĥattá Tunfiqū Mimmā Tuĥibbūna  ۚ  Wa Mā Tunfiqū Min Shay'in Fa'inna Al-Laha Bihi `Alīmun َ003-092 Bã zã ku sãmi kyautatãwa ba, sai kun ciyar daga abin da kuke so. Kuma abin da kuka ciyar, kõ mẽne ne, to, lalle ne Allah,gare shi, Masani ne. لَنْ تَنَالُوا الْبِرَّ حَتَّى تُنْفِقُوا مِمَّا تُحِبُّونَ  ۚ  وَمَا تُنْفِقُوا مِنْ شَيْء ٍ فَإِنَّ اللَّهَ بِه ِِ عَلِيم ٌ
Kullu Aţ-Ţa`āmi Kāna Ĥillāan Libanī 'Isrā'īla 'Illā Mā Ĥarrama 'Isrā'īlu `Alá Nafsihi Min Qabli 'An Tunazzala At-Tawrāatu  ۗ  Qul Fa'tū Bit-Tawrāati Fātlūhā 'In Kuntum Şādiqīna َ003-093 Dukan abinci yã kasance halal ne ga Bani lsrã'ĩla, fãce abinda Isrã'ĩla ya haramta wa kansadaga gabãnin saukar da Attaura. Ka ce: "To, ku zo da Attaura sa'an nan ku karantã ta, idan kun kasance mãsu gaskiya ne. كُلُّ الطَّعَامِ كَانَ حِلّا ً لِبَنِي إِسْرَائِيلَ إِلاَّ مَا حَرَّمَ إِسْرَائِيلُ عَلَى نَفْسِه ِِ مِنْ قَبْلِ أَنْ تُنَزَّلَ التَّوْرَاةُ  ۗ  قُلْ فَأْتُوا بِالتَّوْرَاةِ فَاتْلُوهَا إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ
Famani Aftará `Alá Al-Lahi Al-Kadhiba Min Ba`di Dhālika Fa'ūlā'ika Humu Až-Žālimūna َ003-094 "To, wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah daga bãyan wannan, to, waɗannan sũ ne azzãlumai." فَمَنِ افْتَرَى عَلَى اللَّهِ الكَذِبَ مِنْ بَعْدِ ذَلِكَ فَأُوْلَائِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ
Qul Şadaqa Al-Lahu Fa  ۗ  Attabi`ū Millata 'Ibrāhīma Ĥanīfāan Wa Mā Kāna Mina Al-Mushrikīna َ003-095 Ka ce: "Allah Ya yi gaskiya, sabõda haka ku bi aƙĩdar Ibrãhĩma mai karkata zuwa ga gaskiya; kuma bai kasance daga mãsu shirki ba." قُلْ صَدَقَ اللَّهُ  ۗ  فَاتَّبِعُوا مِلَّةَ إِبْرَاهِيمَ حَنِيفا ً وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ
'Inna 'Awwala Baytin Wuđi`a Lilnnāsi Lalladhī Bibakkata Mubārakāan Wa Hudáan Lil`ālamīna َ003-096 Kuma lalle ne, ¦aki na farko da aka aza dõmin mutãne, haƙĩƙa, shi ne wanda ke Bakka mai albarka kuma shiriya ga tãlikai. إِنَّ أَوَّلَ بَيْت ٍ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِي بِبَكَّةَ مُبَارَكا ً وَهُدى ً لِلْعَالَمِينَ
Fīhi 'Āyātun Bayyinātun Maqāmu 'Ibrāhīma  ۖ  Wa Man Dakhalahu Kāna 'Āmināan  ۗ  Wa Lillahi `Alá An-Nāsi Ĥijju Al-Bayti Mani Astaţā`a 'Ilayhi Sabīlāan  ۚ  Wa Man Kafara Fa'inna Al-Laha Ghanīyun `Ani Al-`Ālamīna َ003-097 A cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu; (ga misãli) matsayin Ibrãhĩma. Kuma wanda ya shige shi yã kasance amintacce. Kuma akwai hajjin ¦ãkin dõmin Allah a kan mutãne, ga wanda ya sãmi ĩkon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lalle Allah Mawadãci ne daga barin tãlikai. فِيهِ آيَات ٌ بَيِّنَات ٌ مَقَامُ إِبْرَاهِيمَ  ۖ  وَمَنْ دَخَلَه ُُ كَانَ آمِنا ً  ۗ  وَلِلَّهِ عَلَى النَّاسِ حِجُّ الْبَيْتِ مَنِ اسْتَطَاعَ إِلَيْهِ سَبِيلا ً  ۚ  وَمَنْ كَفَرَ فَإِنَّ اللَّهَ غَنِيٌّ عَنِ الْعَالَمِينَ
Qul Yā 'Ahla Al-Kitābi Lima Takfurūna Bi'āyāti Al-Lahi Wa Allāhu Shahīdun `Alá Mā Ta`malūna َ003-098 Ka ce: "Ya kũ Mutãnen Littãfi! Don me kuke kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa Allah Mai shaida ne a kan abin da kuke aikatãwa?" قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لِمَ تَكْفُرُونَ بِآيَاتِ اللَّهِ وَاللَّهُ شَهِيدٌ عَلَى مَا تَعْمَلُونَ
Qul Yā 'Ahla Al-Kitābi Lima Taşuddūna `An Sabīli Al-Lahi Man 'Āmana Tabghūnahā `Iwajāan Wa 'Antum Shuhadā'u  ۗ  Wa Mā Al-Lahu Bighāfilin `Ammā Ta`malūna َ003-099 Ka ce: "Ya ku Mutãnen Littãfi! Don me kuke taushe wanda ya yi ĩmani, daga hanyar Allah, kuma kunã nẽman ta zama karkatacciya, alhãli kuwa kunã mãsu shaida? Kuma Allah bai gushe daga abin da kuke aikatãwa ba yana Masani." قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لِمَ تَصُدُّونَ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ مَنْ آمَنَ تَبْغُونَهَا عِوَجا ً وَأَنْتُمْ شُهَدَاءُ  ۗ  وَمَا اللَّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'In Tuţī`ū Farīqāan Mina Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba Yaruddūkum Ba`da 'Īmānikum Kāfirīna َ003-100 Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi ɗã'aga wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littãfi, zã su mayar da ku kãfirai a bãyan ĩmãninku! يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ تُطِيعُوا فَرِيقا ً مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ يَرُدُّوكُمْ بَعْدَ إِيمَانِكُمْ كَافِرِينَ
Wa Kayfa Takfurūna Wa 'Antum Tutlá `Alaykum 'Āyātu Al-Lahi Wa Fīkum Rasūluhu  ۗ  Wa Man Ya`taşim Bil-Lahi Faqad Hudiya 'Ilá Şirāţin Mustaqīmin َ003-101 Kuma yãyã kuke kãfircẽwa alhãli kuwa anã karanta ãyõyin Allah a gare ku, kuma a cikinku akwai manzonSa? Kuma wanda ya nẽmi tsari da Allah, to, an shiryar da shi zuwa ga hanya miƙaƙƙiya. وَكَيْفَ تَكْفُرُونَ وَأَنْتُمْ تُتْلَى عَلَيْكُمْ آيَاتُ اللَّهِ وَفِيكُمْ رَسُولُه ُُ  ۗ  وَمَنْ يَعْتَصِمْ بِاللَّهِ فَقَدْ هُدِيَ إِلَى صِرَاط ٍ مُسْتَقِيم ٍ
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Attaqū Al-Laha Ĥaqqa Tuqātihi Wa Lā Tamūtunna 'Illā Wa 'Antum Muslimūna َ003-102 Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, a kan hakkin binsa da taƙawa, kuma kada ku mutu fãce kuna mãsu sallamawa (Musulmi). يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ حَقَّ تُقَاتِه ِِ وَلاَ تَمُوتُنَّ إِلاَّ وَأَنْتُمْ مُسْلِمُونَ
Wa A`taşimū Biĥabli Al-Lahi Jamī`āan Wa Lā Tafarraqū  ۚ  Wa Adhkurū Ni`mata Al-Lahi `Alaykum 'Idh Kuntum 'A`dā'an Fa'allafa Bayna Qulūbikum Fa'aşbaĥtum Bini`matihi 'Ikhwānāan Wa Kuntum `Alá Shafā Ĥufratin Mina An-Nāri Fa'anqadhakum Minhā  ۗ  Kadhālika Yubayyinu Al-Lahu Lakum 'Āyātihi La`allakum Tahtadūna َ003-103 Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã ɗaya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da kuka kasance maƙiya sai Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtanku sabõda haka kuka wãyi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gãɓar rãmi na wutã sai Ya tsãmar da ku daga gare ta, Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayõyinSa, tsammãninku, zã ku shiryu. وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعا ً وَلاَ تَفَرَّقُوا  ۚ  وَاذْكُرُوا نِعْمَةَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ كُنْتُمْ أَعْدَاء ً فَأَلَّفَ بَيْنَ قُلُوبِكُمْ فَأَصْبَحْتُمْ بِنِعْمَتِهِ~ِ إِخْوَانا ً وَكُنْتُمْ عَلَى شَفَا حُفْرَة ٍ مِنَ النَّارِ فَأَنْقَذَكُمْ مِنْهَا  ۗ  كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِه ِِ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ
Wa Ltakun Minkum 'Ummatun Yad`ūna 'Ilá Al-Khayri Wa Ya'murūna Bil-Ma`rūfi Wa Yanhawna `Ani Al-Munkari  ۚ  Wa 'Ūlā'ika Humu Al-Mufliĥūna َ003-104 Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alhẽri, kuma suna umurnida alhẽri, kuma suna hani dagaabin da ake ƙi. Kuma waɗannan, sũ ne mãsu cin nasara. وَلْتَكُنْ مِنْكُمْ أُمَّة ٌ يَدْعُونَ إِلَى الْخَيْرِ وَيَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنْكَرِ  ۚ  وَأُوْلَائِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ
Wa Lā Takūnū Kālladhīna Tafarraqū Wa Akhtalafū Min Ba`di Mā Jā'ahumu Al-Bayyinātu  ۚ  Wa 'Ūlā'ika Lahum `Adhābun `Ažīmun َ003-105 Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka rarrabu kuma suka sãɓã wa jũna, bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu kuma waɗannan sunã da azãba mai girma. وَلاَ تَكُونُوا كَالَّذِينَ تَفَرَّقُوا وَاخْتَلَفُوا مِنْ بَعْدِ مَا جَاءَهُمُ الْبَيِّنَاتُ  ۚ  وَأُوْلَائِكَ لَهُمْ عَذَابٌ عَظِيم ٌ
Yawma Tabyađđu Wujūhun Wa Taswaddu Wujūhun  ۚ  Fa'ammā Al-Ladhīna Aswaddat Wujūhuhum 'Akafartum Ba`da 'Īmānikum Fadhūqū Al-`Adhāba Bimā Kuntum Takfurūna َ003-106 A rãnar da wasu fuskõki suke yin fari kuma wasu fuskõki suke yin baƙi (zã a ce wa waɗanda fuskokinsu suke yin baƙin): "Shin kun kãfirta a bayan ĩmãninku? Don haka sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci." يَوْمَ تَبْيَضُّ وُجُوه ٌ ٌ وَتَسْوَدُّ وُجُوه ٌ ٌ  ۚ  فَأَمَّا الَّذِينَ اسْوَدَّتْ وُجُوهُهُمْ أَكَفَرْتُمْ بَعْدَ إِيمَانِكُمْ فَذُوقُوا الْعَذَابَ بِمَا كُنْتُمْ تَكْفُرُونَ
Wa 'Ammā Al-Ladhīna Abyađđat Wujūhuhum Fafī Raĥmati Al-Lahi Hum Fīhā Khālidūna َ003-107 Kuma amma waɗanda fuskõkinsu suka yi fari, to sũ suna cikin rahamar Allah kuma, su a cikinta, madawwama, ne. وَأَمَّا الَّذِينَ ابْيَضَّتْ وُجُوهُهُمْ فَفِي رَحْمَةِ اللَّهِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Tilka 'Āyātu Al-Lahi Natlūhā `Alayka Bil-Ĥaqqi  ۗ  Wa Mā Al-Lahu Yurīdu Žulmāan Lil`ālamīna َ003-108 Waɗannan ãyõyin Allah ne, muna karanta su a gare ka da gaskiya, kuma Allah bã Ya nufin wani zãlunci ga tãlikai. تِلْكَ آيَاتُ اللَّهِ نَتْلُوهَا عَلَيْكَ بِالْحَقِّ  ۗ  وَمَا اللَّهُ يُرِيدُ ظُلْما ً لِلْعَالَمِينَ
Wa Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi  ۚ  Wa 'Ilá Al-Lahi Turja`u Al-'Umūru َ003-109 Kuma abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allah ne, kuma zuwa gare Shi ake mayar da al'amurra. وَلِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ  ۚ  وَإِلَى اللَّهِ تُرْجَعُ الأُمُورُ
Kuntum Khayra 'Ummatin 'Ukhrijat Lilnnāsi Ta'murūna Bil-Ma`rūfi Wa Tanhawna `Ani Al-Munkari Wa Tu'uminūna Bil-Lahi  ۗ  Wa Law 'Āmana 'Ahlu Al-Kitābi Lakāna Khayrāan Lahum  ۚ  Minhumu Al-Mu'uminūna Wa 'Aktharuhumu Al-Fāsiqūna َ003-110 Kun kasance mafi alhẽrin al'umma wadda aka fitar ga mutãne kuna umurni da alhẽri kuma kunã hani daga abin da ake ƙi, kuma kunã ĩmãni da Allah. Kuma dã Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, lalle ne, dã (haka) yã kasance mafi alhẽri a gare su. Daga cikinsu akwai mũminai, kuma mafi yawansufãsiƙai ne. كُنْتُمْ خَيْرَ أُمَّةٍ أُخْرِجَتْ لِلنَّاسِ تَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَتَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنكَرِ وَتُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ  ۗ  وَلَوْ آمَنَ أَهْلُ الْكِتَابِ لَكَانَ خَيْرا ً لَهُمْ  ۚ  مِنْهُمُ الْمُؤْمِنُونَ وَأَكْثَرُهُمُ الْفَاسِقُونَ
Lan Yađurrūkum 'Illā 'Adháan  ۖ  Wa 'In Yuqātilūkum Yuwallūkumu Al-'Adbāra Thumma Lā Yunşarūna َ003-111 Bã zã su cũce ku ba, fãce dai tsangwama. Kuma idan sun yãƙe ku zã su jũya muku bãya, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba. لَنْ يَضُرُّوكُمْ إِلاَّ أَذى ً  ۖ  وَإِنْ يُقَاتِلُوكُمْ يُوَلُّوكُمُ الأَدْبَارَ ثُمَّ لاَ يُنْصَرُونَ
Đuribat `Alayhimu Adh-Dhillatu 'Ayna Mā Thuqifū 'Illā Biĥablin Mina Al-Lahi Wa Ĥablin Mina An-Nāsi Wa Bā'ū Bighađabin Mina Al-Lahi Wa Đuribat `Alayhimu Al-Maskanatu  ۚ  Dhālika Bi'annahum Kānū Yakfurūna Bi'āyāti Al-Lahi Wa Yaqtulūna Al-'Anbiyā'a Bighayri Ĥaqqin  ۚ  Dhālika Bimā `Aşaw Wa Kānū Ya`tadūna َ003-112 An dõka ƙasƙanci a kansu a inda duk aka sãme su fãce da wani alkawari daga Allah, da alkawari daga mutãne. Kuma sun kõma da fushi daga Allah, kuma aka dõka talauci a kansu. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe annabãwa, bã da wani haƙƙi ba. Wannan kuwa dõmin sãɓãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna yin ta'adi. ضُرِبَتْ عَلَيْهِمُ الذِّلَّةُ أَيْنَ مَا ثُقِفُوا إِلاَّ بِحَبْل ٍ مِنَ اللَّهِ وَحَبْل ٍ مِنَ النَّاسِ وَبَاءُوا بِغَضَب ٍ مِنَ اللَّهِ وَضُرِبَتْ عَلَيْهِمُ الْمَسْكَنَةُ  ۚ  ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ كَانُوا يَكْفُرُونَ بِآيَاتِ اللَّهِ وَيَقْتُلُونَ الأَنبِيَاءَ بِغَيْرِ حَقّ ٍ  ۚ  ذَلِكَ بِمَا عَصَوْا وَكَانُوا يَعْتَدُونَ
Laysū Sawā'an  ۗ  Min 'Ahli Al-Kitābi 'Ummatun Qā'imatun Yatlūna 'Āyāti Al-Lahi 'Ānā'a Al-Layli Wa Hum Yasjudūna َ003-113 Ba su zama daidai ba; daga Mutãnen Littafi akwai wata al'umma wadda take tsaye, suna karãtun ayõyin Allah a cikin sã'õ'in dare, alhãli kuwa sunã yin sujada. لَيْسُوا سَوَاء ً  ۗ  مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ أُمَّة ٌ قَائِمَة ٌ يَتْلُونَ آيَاتِ اللَّهِ آنَاءَ اللَّيْلِ وَهُمْ يَسْجُدُونَ
Yu'uminūna Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri Wa Ya'murūna Bil-Ma`rūfi Wa Yanhawna `Ani Al-Munkari Wa Yusāri`ūna Fī Al-Khayrāti Wa 'Ūlā'ika Mina Aş-Şāliĥīna َ003-114 Suna ĩmãni da Allah da Yinin Lãhira, kuma suna umurui da abin da aka sani kuma suna hani daga abin da ba a sani ba, kuma sunã gaugãwa a cikin alhẽrai. Kuma waɗannan suna cikin sãlihai. يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ وَيَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنْكَرِ وَيُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَأُوْلَائِكَ مِنَ الصَّالِحِينَ
Wa Mā Yaf`alū Min Khayrin Falan Yukfarūhu Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Bil-Muttaqīna َ003-115 Kuma abin da suka aikata daga alhẽri, to, bã zã a yi musu musunsa ba. Kuma Allah Masani ne ga mãsu taƙawa. وَمَا يَفْعَلُوا مِنْ خَيْر ٍ فَلَنْ يُكْفَرُوه ُُ  ۗ  وَاللَّهُ عَلِيم ٌ بِالْمُتَّقِينَ
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Lan Tughniya `Anhum 'Amwāluhum Wa Lā 'Awlāduhum Mina Al-Lahi Shay'āan  ۖ  Wa 'Ūlā'ika 'Aşĥābu An-Nāri  ۚ  Hum Fīhā Khālidūna َ003-116 Lalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu kõ ɗiyansu bã zã su wadatar musu da kõme ba daga Allah kuma waɗannan abõkan wuta ne, sũ, acikinta, madawwama ne. إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا لَنْ تُغْنِيَ عَنْهُمْ أَمْوَالُهُمْ وَلاَ أَوْلاَدُهُمْ مِنَ اللَّهِ شَيْئا ً  ۖ  وَأُوْلَائِكَ أَصْحَابُ النَّارِ  ۚ  هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Mathalu Mā Yunfiqūna Fī Hadhihi Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Kamathali Rīĥin Fīhā Şirrun 'Aşābat Ĥartha Qawmin Žalamū 'Anfusahum Fa'ahlakat/hu  ۚ  Wa Mā Žalamahumu Al-Lahu Wa Lakin 'Anfusahum Yažlimūna َ003-117 Misãlin abin da suke ciyarwa, a cikin wannan rãyuwar dũniya, kamar misãlin iska ce (wadda) a cikinta akwai tsananin sanyi, ta sãmi shukar wasu mutãne waɗanda suka zãlunci kansu, sai ta halakar da ita. Allah bai zãlunce su ba, amma kansu suka kasance sunã zãlunta. مَثَلُ مَا يُنْفِقُونَ فِي هَذِهِ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا كَمَثَلِ رِيح ٍ فِيهَا صِرٌّ أَصَابَتْ حَرْثَ قَوْم ٍ ظَلَمُوا أَنْفُسَهُمْ فَأَهْلَكَتْهُ  ۚ  وَمَا ظَلَمَهُمُ اللَّهُ وَلَكِنْ أَنْفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tattakhidhū Biţānatan Min Dūnikum Lā Ya'lūnakum Khabālāan Wa Ddū Mā `Anittum Qad Badati Al-Baghđā'u Min 'Afwāhihim Wa Mā Tukhfī Şudūruhum 'Akbaru  ۚ  Qad Bayyannā Lakumu Al-'Āyāti  ۖ  'In Kuntum Ta`qilūna َ003-118 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi abõkan asĩri daga waninku, ba su taƙaita muku ɓarna. Kuma sun yi gũrin abin da zã ku cũtu da shi. Haƙĩka, ƙiyayya tã bayyana daga bãkunansu, kuma abin da zukãtansu ke ɓõyẽwane mafi girma. Kuma lalle ne, Mun bayyana muku ãyõyi, idan kun kasance kunã hankalta. يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لاَ تَتَّخِذُوا بِطَانَة ً مِنْ دُونِكُمْ لاَ يَأْلُونَكُمْ خَبَالا ً وَدُّوا مَا عَنِتُّمْ قَدْ بَدَتِ الْبَغْضَاءُ مِنْ أَفْوَاهِهِمْ وَمَا تُخْفِي صُدُورُهُمْ أَكْبَرُ  ۚ  قَدْ بَيَّنَّا لَكُمُ الآيَاتِ  ۖ  إِنْ كُنْتُمْ تَعْقِلُونَ
Hā'antum 'Ūlā'i Tuĥibbūnahum Wa Lā Yuĥibbūnakum Wa Tu'uminūna Bil-Kitābi Kullihi Wa 'Idhā Laqūkum Qālū 'Āmannā Wa 'Idhā Khalaw `Ađđū `Alaykumu Al-'Anāmila Mina Al-Ghayži Qul  ۚ  Mūtū Bighayžikum 'Inna  ۗ  Al-Laha `Alīmun Bidhāti Aş-Şudūri َ003-119 Gã ku yã waɗannan! Kunã son su bã su son ku, kuma kuna ĩmãni da Littãfi dukansa. Kuma idan sun haɗu da ku sukan ce "Mun yi ĩmani". Kuma idan sun kaɗaita sai su ciji yãtsu a kanku don takaici. Ka ce "Ku mutu da takaicinku. Lalle ne, Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza." هَاأَنْتُمْ أُوْلاَءِ تُحِبُّونَهُمْ وَلاَ يُحِبُّونَكُمْ وَتُؤْمِنُونَ بِالْكِتَابِ كُلِّه ِِ وَإِذَا لَقُوكُمْ قَالُوا آمَنَّا وَإِذَا خَلَوْا عَضُّوا عَلَيْكُمُ الأَنَامِلَ مِنَ الغَيْظِ قُلْ  ۚ  مُوتُوا بِغَيْظِكُمْ إِنَّ  ۗ  اللَّهَ عَلِيم ٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
'In Tamsaskum Ĥasanatun Tasu'uhum Wa 'In Tuşibkum Sayyi'atun Yafraĥū Bihā  ۖ  Wa 'In Taşbirū Wa Tattaqū Lā Yađurrukum Kayduhum Shay'āan  ۗ  'Inna Al-Laha Bimā Ya`malūna Muĥīţun َ003-120 Idan wani alhẽri ya shãfe ku sai ya baƙanta musu rai, kuma idan wata cũtar ta shãfe ku sai su yi farin ciki da ita. Kuma idan kun yi haƙuri kuma kuka yi taƙawa, ƙullinsu bã ya cũtar ku da kõme. Lalle ne, Allah ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa ne. إِنْ تَمْسَسْكُمْ حَسَنَة ٌ تَسُؤْهُمْ وَإِنْ تُصِبْكُمْ سَيِّئَة ٌ يَفْرَحُوا بِهَا  ۖ  وَإِنْ تَصْبِرُوا وَتَتَّقُوا لاَ يَضُرُّكُمْ كَيْدُهُمْ شَيْئا ً  ۗ  إِنَّ اللَّهَ بِمَا يَعْمَلُونَ مُحِيط ٌ
Wa 'Idh Ghadawta Min 'Ahlika Tubawwi'u Al-Mu'uminīna Maqā`ida Lilqitāli Wa  ۗ  Allāhu Samī`un `Alīmun َ003-121 Kuma a lõkacin da ka yi sauko daga iyãlanka kana zaunar da mũminai a wurãren zamadõmin yãƙi, kuma Allah Mai ji ne, Masani. وَإِذْ غَدَوْتَ مِنْ أَهْلِكَ تُبَوِّئُ الْمُؤْمِنِينَ مَقَاعِدَ لِلْقِتَالِ  ۗ  وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيم ٌ
'Idh Hammat Ţā'ifatāni Minkum 'An Tafshalā Wa Allāhu Walīyuhumā  ۗ  Wa `Alá Al-Lahi Falyatawakkali Al-Mu'uminūna َ003-122 A lõkacin da ƙungiyõyi biyu daga gare ku suka yi niyyar su karye, kuma Allah ne Majiɓincinsu, don haka, ga Allah mũminai sai su dogara. إِذْ هَمَّتْ طَائِفَتَانِ مِنْكُمْ أَنْ تَفْشَلاَ وَاللَّهُ وَلِيُّهُمَا  ۗ  وَعَلَى اللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ
Wa Laqad Naşarakumu Al-Lahu Bibadrin Wa 'Antum 'Adhillatun Fa  ۖ  Attaqū Al-Laha La`allakum Tashkurūna َ003-123 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a Badar, alhãli kuwa kunã mafiya rauni, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, kuna gõdẽwa. وَلَقَدْ نَصَرَكُمُ اللَّهُ بِبَدْر ٍ وَأَنْتُمْ أَذِلَّة ٌ  ۖ  فَاتَّقُوا اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
'Idh Taqūlu Lilmu'uminīna 'Alan Yakfiyakum 'An Yumiddakum Rabbukum Bithalāthati 'Ālāfin Mina Al-Malā'ikati Munzalīna َ003-124 A lõkacin da kake cẽwa ga mũminai, "Shin bai ishe ku ba, Ubangijinku Ya taimake ku da dubu uku daga malã'iku saukakku?" إِذْ تَقُولُ لِلْمُؤْمِنِينَ أَلَنْ يَكْفِيَكُمْ أَنْ يُمِدَّكُمْ رَبُّكُمْ بِثَلاَثَةِ آلاَف ٍ مِنَ الْمَلاَئِكَةِ مُنْزَلِينَ
Balá  ۚ  'In Taşbirū Wa Tattaqū Wa Ya'tūkum Min Fawrihimdhā Yumdidkum Rabbukum Bikhamsati 'Ālāfin Mina Al-Malā'ikati Musawwimīna َ003-125 "Na'am! Idan kuka yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, kuma suka zo muku da gaugawarsu, irin wannan, Ubangijinku zai ƙãre ku da dubu biyar daga malãiku mãsu alãma." بَلَى  ۚ  إِنْ تَصْبِرُوا وَتَتَّقُوا وَيَأْتُوكُمْ مِنْ فَوْرِهِمْ هَذَا يُمْدِدْكُمْ رَبُّكُمْ بِخَمْسَةِ آلاَف ٍ مِنَ الْمَلاَئِكَةِ مُسَوِّمِينَ
Wa Mā Ja`alahu Al-Lahu 'Illā Bushrá Lakum Wa Litaţma'inna Qulūbukum Bihi  ۗ  Wa Mā An-Naşru 'Illā Min `Indi Al-Lahi Al-`Azīzi Al-Ĥakīmi َ003-126 Kuma Allah bai sanya shi ba, fãce dõmin bushãra a gare ku, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi. Taimako bai kasance ba fãce daga wurin Allah, Mabuwãyi, Mai hikima. وَمَا جَعَلَهُ اللَّهُ إِلاَّ بُشْرَى لَكُمْ وَلِتَطْمَئِنَّ قُلُوبُكُمْ بِه ِِ  ۗ  وَمَا النَّصْرُ إِلاَّ مِنْ عِنْدِ اللَّهِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ
Liyaqţa`a Ţarafāan Mina Al-Ladhīna Kafarū 'Aw Yakbitahum Fayanqalibū Khā'ibīna َ003-127 Dõmin Ya katse wani gẽfe daga waɗanda suka kãfirta ko kuma Ya ƙasƙantã su, har su jũya, suna mãsu ruɓushi. لِيَقْطَعَ طَرَفا ً مِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَوْ يَكْبِتَهُمْ فَيَنْقَلِبُوا خَائِبِينَ
Laysa Laka Mina Al-'Amri Shay'un 'Aw Yatūba `Alayhim 'Aw Yu`adhdhibahum Fa'innahum Žālimūna َ003-128 Bãbu kõme a gare ka game da al'amarin (shiryar da su banda iyar da manzanci). Ko Allah Ya karɓi tũbarsu, kõ kuwa Ya yimusu azãba, to lalle ne sũ, mãsu zãlunci ne. لَيْسَ لَكَ مِنَ الأَمْرِ شَيْءٌ أَوْ يَتُوبَ عَلَيْهِمْ أَوْ يُعَذِّبَهُمْ فَإِنَّهُمْ ظَالِمُونَ
Wa Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi  ۚ  Yaghfiru Liman Yashā'u Wa Yu`adhdhibu Man Yashā'u Wa  ۚ  Allāhu Ghafūrun Raĥīmun َ003-129 Allah ne da mulkin abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, yana gãfarta wa wanda Yake so, kuma yana azabta wanda Yake so, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. وَلِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ  ۚ  يَغْفِرُ لِمَنْ يَشَاءُ وَيُعَذِّبُ مَنْ يَشَاءُ  ۚ  وَاللَّهُ غَفُور ٌ رَحِيم ٌ
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Ta'kulū Ar-Ribā 'Ađ`āfāan Muđā`afatan  ۖ  Wa Attaqū Al-Laha La`allakum Tufliĥūna َ003-130 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci riba ninkininki, riɓanye, kuma ku bi Allah da taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara. يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لاَ تَأْكُلُوا الرِّبَا أَضْعَافا ً مُضَاعَفَة ً  ۖ  وَاتَّقُوا اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Wa Attaqū An-Nāra Allatī 'U`iddat Lilkāfirīna َ003-131 Kuma ku ji tsõron wutã wadda aka yi tattali dõmin kãfirai. وَاتَّقُوا النَّارَ الَّتِي أُعِدَّتْ لِلْكَافِرِينَ
Wa 'Aţī`ū Al-Laha Wa Ar-Rasūla La`allakum Turĥamūna َ003-132 Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, tsammaninku a yi muku rahama. وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَالرَّسُولَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ
Wa Sāri`ū 'Ilá Maghfiratin Min Rabbikum Wa Jannatin `Arđuhā As-Samāwātu Wa Al-'Arđu 'U`iddat Lilmuttaqīna َ003-133 Kuma ku yi gaugawa zuwa ga nẽman gãfara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda fãɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta dõmin mãsu taƙawa. وَسَارِعُوا إِلَى مَغْفِرَة ٍ مِنْ رَبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَاوَاتُ وَالأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ
Al-Ladhīna Yunfiqūna Fī As-Sarrā'i Wa Ađ-Đarrā'i Wa Al-Kāžimīna Al-Ghayža Wa Al-`Āfīna `Ani An-Nāsi Wa  ۗ  Allāhu Yuĥibbu Al-Muĥsinīna َ003-134 Waɗanda suke ciyarwa a cikin sauƙi da tsanani kuma suke mãsu haɗiyẽwar fushi, kuma mãsu yãfe wa mutãne laifi. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa. الَّذِينَ يُنْفِقُونَ فِي السَّرَّاءِ وَالضَّرَّاءِ وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ  ۗ  وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ
Wa Al-Ladhīna 'Idhā Fa`alū Fāĥishatan 'Aw Žalamū 'Anfusahum Dhakarū Al-Laha Fāstaghfarū Lidhunūbihim Wa Man Yaghfiru Adh-Dhunūba 'Illā Al-Lahu Wa Lam Yuşirrū `Alá Mā Fa`alū Wa Hum Ya`lamūna َ003-135 Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfãsha ko suka zãlunci kansu sai su tunã da Allah, sabõda su nẽmi gãfarar zunubansu ga Allah. Kuma wãne ne ke gãfara ga zunubai, fãce Allah? Kuma ba su dõge a kan abin da suka aikata ba, alhãli kuwa suna sane. وَالَّذِينَ إِذَا فَعَلُوا فَاحِشَةً أَوْ ظَلَمُوا أَنْفُسَهُمْ ذَكَرُوا اللَّهَ فَاسْتَغْفَرُوا لِذُنُوبِهِمْ وَمَنْ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلاَّ اللَّهُ وَلَمْ يُصِرُّوا عَلَى مَا فَعَلُوا وَهُمْ يَعْلَمُونَ
'Ūlā'ika Jazā'uuhum Maghfiratun Min Rabbihim Wa Jannātun Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā  ۚ  Wa Ni`ma 'Ajru Al-`Āmilīna َ003-136 Waɗannan sakamakonsu gãfara ce daga Ubangijinsu, daga Gidajen Aljanna (waɗanda) ƙõramu na gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu. Kuma mãdalla da ijãrar mãsu aiki. أُوْلَائِكَ جَزَاؤُهُمْ مَغْفِرَة ٌ مِنْ رَبِّهِمْ وَجَنَّات ٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا  ۚ  وَنِعْمَ أَجْرُ الْعَامِلِينَ
Qad Khalat Min Qablikum Sunanun Fasīrū Fī Al-'Arđi Fānžurū Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Mukadhdhibīna َ003-137 Lalle ne misãlai sun shũɗe a gabãninku, sai ku yi tafiya a cikin ƙasa sa'an nan ku dũba, yãyã ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance. قَدْ خَلَتْ مِنْ قَبْلِكُمْ سُنَن ٌ فَسِيرُوا فِي الأَرْضِ فَانْظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُكَذِّبِينَ
dhā Bayānun Lilnnāsi Wa Hudáan Wa Maw`ižatun Lilmuttaqīna َ003-138 Wannan bayãni ne ga mutãne, kuma shiryuwa ce da wa'azi ga mãsu taƙawa. هَذَا بَيَان ٌ لِلنَّاسِ وَهُدى ً وَمَوْعِظَة ٌ لِلْمُتَّقِينَ
Wa Lā Tahinū Wa Lā Taĥzanū Wa 'Antumu Al-'A`lawna 'In Kuntum Mu'uminīna َ003-139 Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi baƙin ciki, alhãli kuwa kũ ne mafiya ɗaukaka, idan kun kasance mãsu ĩmãni. وَلاَ تَهِنُوا وَلاَ تَحْزَنُوا وَأَنْتُمُ الأَعْلَوْنَ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ
'In Yamsaskum Qarĥun Faqad Massa Al-Qawma Qarĥun Mithluhu  ۚ  Wa Tilka Al-'Ayyāmu Nudāwiluhā Bayna An-Nāsi Wa Liya`lama Al-Lahu Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Yattakhidha Minkum Shuhadā'a Wa  ۗ  Allāhu Lā Yuĥibbu Až-Žālimīna َ003-140 Idan wani mĩki ya shãfe ku, to, lalle ne, wani mĩki kamarsa ya shãfi mutãnen, kuma waɗancan kwãnaki Muna sarrafa su a tsakãnin mutãne dõmin Allah Ya san waɗanda suka yi ĩmãni kuma Ya sãmi mãsu shahãda daga gare ku. Kuma Allah ba Ya son azzãlumai. إِنْ يَمْسَسْكُمْ قَرْح ٌ فَقَدْ مَسَّ الْقَوْمَ قَرْح ٌ مِثْلُه ُُ  ۚ  وَتِلْكَ الأَيَّامُ نُدَاوِلُهَا بَيْنَ النَّاسِ وَلِيَعْلَمَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَيَتَّخِذَ مِنْكُمْ شُهَدَاءَ  ۗ  وَاللَّهُ لاَ يُحِبُّ الظَّالِمِينَ
Wa Liyumaĥĥişa Al-Lahu Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Yamĥaqa Al-Kāfirīna َ003-141 Kuma dõmin Allah Ya ɗauraye waɗanda suka yi ĩmãni,kuma Ya ƙõƙe kãfirai. وَلِيُمَحِّصَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَيَمْحَقَ الْكَافِرِينَ
'Am Ĥasibtum 'An Tadkhulū Al-Jannata Wa Lammā Ya`lami Al-Lahu Al-Ladhīna Jāhadū Minkum Wa Ya`lama Aş-Şābirīna َ003-142 Ko kun yi zaton ku shiga Aljanna alhãli kuwa Allah bai bãda sanin waɗanda suka yĩ jihãdi daga gare ku ba, kuma Ya san mãsu haƙuri? أَمْ حَسِبْتُمْ أَنْ تَدْخُلُوا الْجَنَّةَ وَلَمَّا يَعْلَمِ اللَّهُ الَّذِينَ جَاهَدُوا مِنْكُمْ وَيَعْلَمَ الصَّابِرِينَ
Wa Laqad Kuntum Tatamannawn Al-Mawta Min Qabli 'An Talqawhu Faqad Ra'aytumūhu Wa 'Antum Tanžurūna َ003-143 Kuma lalle ne, haƙĩƙa kun kasance kuna gũrin mutuwa tun a gabãnin ku haɗu da ita, to lalle ne kun gan ta, alhãli kuwa kuna kallo. وَلَقَدْ كُنْتُمْ تَتَمَنَّوْن الْمَوْتَ مِنْ قَبْلِ أَنْ تَلْقَوْهُ فَقَدْ رَأَيْتُمُوه ُُ وَأَنْتُمْ تَنْظُرُونَ
Wa Mā Muĥammadun 'Illā Rasūlun Qad Khalat Min Qablihi Ar-Rusulu  ۚ  'Afa'īn Māta 'Aw Qutila Anqalabtum `Alá 'A`qābikum  ۚ  Wa Man Yanqalib `Alá `Aqibayhi Falan Yađurra Al-Laha Shay'āan  ۗ  Wa Sayaj Al-Lahu Ash-Shākirīna َ003-144 Kuma Muhammadu bai zama ba face manzo lalle ne manzanni sun shũɗe a gabãninsa. Ashe idan ya mutu ko kuwa aka kashe shi, zã kujũya a kan dugaduganku? To, wanda ya jũya a kan dugadugansa, bã zai cũci Allah da kõme ba. Kuma Allah zai sãka wa mãsu gõdiya. وَمَا مُحَمَّد ٌ إِلاَّ رَسُول ٌ قَدْ خَلَتْ مِنْ قَبْلِهِ الرُّسُلُ  ۚ  أَفَإِيْن مَاتَ أَوْ قُتِلَ انْقَلَبْتُمْ عَلَى أَعْقَابِكُمْ  ۚ  وَمَنْ يَنْقَلِبْ عَلَى عَقِبَيْهِ فَلَنْ يَضُرَّ اللَّهَ شَيْئا ً  ۗ  وَسَيَجْزِي اللَّهُ الشَّاكِرِينَ
Wa Mā Kāna Linafsin 'An Tamūta 'Illā Bi'idhni Al-Lahi Kitābāan Mu'uajjalāan  ۗ  Wa Man Yurid Thawāba Ad-Dunyā Nu'utihi Minhā Wa Man Yurid Thawāba Al-'Ākhirati Nu'utihi Minhā  ۚ  Wa Sanaj Ash-Shākirīna َ003-145 Kuma bã ya yiwuwa ga wani rai ya mutu fãce da iznin Allah, wa'adi ne mai ƙayyadadden ajali. Kuma wanda yake nufin sakamakon dũniya Muna bã shi daga gare ta. Kuma wanda ke nufin samakon Lãhira Muna bã shi daga gare ta. Kuma zã Mu sãka wa mãsu godiya. وَمَا كَانَ لِنَفْسٍ أَنْ تَمُوتَ إِلاَّ بِإِذْنِ اللَّهِ كِتَابا ً مُؤَجَّلا ً  ۗ  وَمَنْ يُرِدْ ثَوَابَ الدُّنْيَا نُؤْتِه ِِ مِنْهَا وَمَنْ يُرِدْ ثَوَابَ الآخِرَةِ نُؤْتِه ِِ مِنْهَا  ۚ  وَسَنَجْزِي الشَّاكِرِينَ
Wa Ka'ayyin Min Nabīyin Qātala Ma`ahu Ribbīyūna Kathīrun Famā Wahanū Limā 'Aşābahum Fī Sabīli Al-Lahi Wa Mā Đa`ufū Wa Mā Astakānū Wa  ۗ  Allāhu Yuĥibbu Aş-Şābirīna َ003-146 Kuma da yawa wani Annabi wanda ya yi yãƙi, akwai jama'a mãsu yawa tãre da shi, sa'an nan ba su yi laushi ba ga abin da ya same su a cikin hanyar Allah, kuma ba su yi rauni ba kuma ba su sad da kai ba. Kuma Allah yana son mãsu haƙuri. وَكَأَيِّنْ مِنْ نَبِيّ ٍ قَاتَلَ مَعَه ُُ رِبِّيُّونَ كَثِير ٌ فَمَا وَهَنُوا لِمَا أَصَابَهُمْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَمَا ضَعُفُوا وَمَا اسْتَكَانُوا  ۗ  وَاللَّهُ يُحِبُّ الصَّابِرِينَ
Wa Mā Kāna Qawlahum 'Illā 'An Qālū Rabbanā Aghfir Lanā Dhunūbanā Wa 'Isrāfanā Fī 'Amrinā Wa Thabbit 'Aqdāmanā Wa Anşurnā `Alá Al-Qawmi Al-Kāfirīna َ003-147 Kuma bãbu abin da ya kasance maganarsu fãce faɗarsu cẽwa: "Ya Ubangijinmu! Ka gãfarta mana zunubanmu da ɓarnarmu a cikin al'amarinmu, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai." وَمَا كَانَ قَوْلَهُمْ إِلاَّ أَنْ قَالُوا رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا وَإِسْرَافَنَا فِي أَمْرِنَا وَثَبِّتْ أَقْدَامَنَا وَانْصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ
Fa'ātāhumu Al-Lahu Thawāba Ad-Dunyā Wa Ĥusna Thawābi Al-'Ākhirati Wa  ۗ  Allāhu Yuĥibbu Al-Muĥsinīna َ003-148 Allah Yã sãka musu da sakamakon dũniya da kuma kyakkyawan sakamakon Lãhira. Kuma Allah yana son mãsu kyautatãwa. فَآتَاهُمُ اللَّهُ ثَوَابَ الدُّنْيَا وَحُسْنَ ثَوَابِ الآخِرَةِ  ۗ  وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'In Tuţī`ū Al-Ladhīna Kafarū Yaruddūkum `Alá 'A`qābikum Fatanqalibū Khāsirīna َ003-149 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi ɗa'aga waɗanda suka kãfirta zã su mayar da ku a kan dugãduganku, har ku jũya kunã mãsu hasãra. يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ تُطِيعُوا الَّذِينَ كَفَرُوا يَرُدُّوكُمْ عَلَى أَعْقَابِكُمْ فَتَنْقَلِبُوا خَاسِرِينَ
Bali Al-Lahu Mawlākum  ۖ  Wa Huwa Khayru An-Nāşirīna َ003-150 Ã'a, Allah ne Majiɓincinku kuma ShĨ ne Mafi alhẽrin matai maka. بَلِ اللَّهُ مَوْلاَكُمْ  ۖ  وَهُوَ خَيْرُ النَّاصِرِينَ
Sanulqī Fī Qulūbi Al-Ladhīna Kafarū Ar-Ru`ba Bimā 'Ashrakū Bil-Lahi Mā Lam Yunazzil Bihi Sulţānāan  ۖ  Wa Ma'wāhumu An-Nāru  ۚ  Wa Bi'sa Math Až-Žālimīna َ003-151 Zã Mu jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta sabõda shirkin da suka yi da Allah gãme da abin da bai saukar da wani dalili ba game da shi. Kuma makõmarsu wuta ce, kuma tir da mazaunin azzãlumai! سَنُلْقِي فِي قُلُوبِ الَّذِينَ كَفَرُوا الرُّعْبَ بِمَا أَشْرَكُوا بِاللَّهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِه ِِ سُلْطَانا ً  ۖ  وَمَأْوَاهُمُ النَّارُ  ۚ  وَبِئْسَ مَثْوَى الظَّالِمِينَ
Wa Laqad Şadaqakumu Al-Lahu Wa`dahu 'Idh Taĥussūnahum Bi'idhnihi  ۖ  Ĥattá 'Idhā Fashiltum Wa Tanāza`tum Al-'Amri Wa `Aşaytum Min Ba`di Mā 'Arākum Mā Tuĥibbūna  ۚ  Minkum Man Yurīdu Ad-Dunyā Wa Minkum Man Yurīdu Al-'Ākhirata  ۚ  Thumma Şarafakum `Anhum Liyabtaliyakum  ۖ  Wa Laqad `Afā `Ankum Wa  ۗ  Allāhu Dhū Fađlin `Alá Al-Mu'uminīna َ003-152 Kuma lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi muku gaskiya ga wa'adinSa, a lokacin da kuke kashe su da izninSa har zuwa lõkacin da kuka kãsa , kuma kuka yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma kuka sãɓã a bãyan (Allah) Ya nũna muku abin da kuke so. Daga cikinku akwai wanda yake nufin duniya kuma daga cikinku akwai wanda ke nufin Lãhĩra. Sa'an nan kuma Ya jũyar da ku daga gare su, dõmin Ya jarrabe ku. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Ya yãfe muku laifinku. Kuma Allah Ma'abucin falala ne ga mũminai. وَلَقَدْ صَدَقَكُمُ اللَّهُ وَعْدَهُ~ُ إِذْ تَحُسُّونَهُمْ بِإِذْنِه ِِ  ۖ  حَتَّى إِذَا فَشِلْتُمْ وَتَنَازَعْتُمْ فِي الأَمْرِ وَعَصَيْتُمْ مِنْ بَعْدِ مَا أَرَاكُمْ مَا تُحِبُّونَ  ۚ  مِنْكُمْ مَنْ يُرِيدُ الدُّنْيَا وَمِنْكُمْ مَنْ يُرِيدُ الآخِرَةَ  ۚ  ثُمَّ صَرَفَكُمْ عَنْهُمْ لِيَبْتَلِيَكُمْ  ۖ  وَلَقَدْ عَفَا عَنْكُمْ  ۗ  وَاللَّهُ ذُو فَضْلٍ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ
'Idh Tuş`idūna Wa Lā Talwūna `Alá 'Aĥadin Wa Ar-Rasūlu Yad`ūkum Fī 'Ukhrākum Fa'athābakum Ghammāan Bighammin Likaylā Taĥzanū `Alá Mā Fātakum Wa Lā Mā 'Aşābakum Wa  ۗ  Allāhu Khabīrun Bimā Ta`malūna َ003-153 A lõkacin da kuke hawan dũtse, gudãne. Kuma ba ku karkata a kan kõwa ba, alhãli kuwa Manzon Allah nã kiran ku a cikin na ƙarshenku. Sa'an nan (Allah) Ya sãkã muku da baƙin ciki a tãre da wani baƙin ciki. Domin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi baƙin cikin a kan abin da ya sãme ku. Kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa. إِذْ تُصْعِدُونَ وَلاَ تَلْوُونَ عَلَى أَحَد ٍ وَالرَّسُولُ يَدْعُوكُمْ فِي أُخْرَاكُمْ فَأَثَابَكُمْ غَمّا ً بِغَمّ ٍ لِكَيْلاَ تَحْزَنُوا عَلَى مَا فَاتَكُمْ وَلاَ مَا أَصَابَكُمْ  ۗ  وَاللَّهُ خَبِير ٌ بِمَا تَعْمَلُونَ
Thumma 'Anzala `Alaykum Min Ba`di Al-Ghammi 'Amanatan Nu`āsāan Yaghshá Ţā'ifatan Minkum  ۖ  Wa Ţā'ifatun Qad 'Ahammat/hum 'Anfusuhum Yažunnūna Bil-Lahi Ghayra Al-Ĥaqqi Žanna Al-Jāhilīyati  ۖ  Yaqūlūna Hal Lanā Mina Al-'Amri Min Shay'in  ۗ  Qul 'Inna Al-'Amra Kullahu Lillahi  ۗ  Yukhfūna Fī 'Anfusihim Mā Lā Yubdūna Laka  ۖ  Yaqūlūna Law Kāna Lanā Mina Al-'Amri Shay'un Mā Qutilnā Hāhunā  ۗ  Qul Law Kuntum Fī Buyūtikum Labaraza Al-Ladhīna Kutiba `Alayhimu Al-Qatlu 'Ilá Mađāji`ihim  ۖ  Wa Liyabtaliya Al-Lahu Mā Fī Şudūrikum Wa Liyumaĥĥişa Mā Fī Qulūbikum Wa  ۗ  Allāhu `Alīmun Bidhāti Aş-Şudūri َ003-154 Sa'an nan kuma (Allah) Ya saukar da wani aminci a gare ku daga bãyan baƙin cikin; gyangyaɗi yanã rufe wata ƙungiya daga gare ku, kuma wata ƙungiya, lalle ne, rãyukansu sun shagaltar da su, suna zaton abin da bã shi ne gaskiya ba, a game da Allah, irin zaton jahiliyya, suna cẽwa: "Ko akwai waniabu a gare mu dai daga al'amarin?" Ka ce, "Lalle ne al'amari dukansa na Allah ne." Suna ɓõyẽwa a cikin zukatansu, abin da bã su bayyana shi a gare ka. Suna cẽwa: "Da munã da wani abu daga al'amarin dã ba a kashe mu ba a nan."Ka ce: "Kõ dã kun kasance a cikin gidãjenku, dã waɗanda aka rubũta musu kisa sun fita zuwa ga wurãren kwanciyarsu;" kuma (wannan abu yã auku ne) dõmin Allah Ya jarrabi abin da ke cikin ƙirãzanku. Kuma dõmin Ya tsarkake abin da ke cikin zukãtanku. Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza. ثُمَّ أَنْزَلَ عَلَيْكُمْ مِنْ بَعْدِ الْغَمِّ أَمَنَة ً نُعَاسا ً يَغْشَى طَائِفَة ً مِنْكُمْ  ۖ  وَطَائِفَة ٌ قَدْ أَهَمَّتْهُمْ أَنْفُسُهُمْ يَظُنُّونَ بِاللَّهِ غَيْرَ الْحَقِّ ظَنَّ الْجَاهِلِيَّةِ  ۖ  يَقُولُونَ هَلْ لَنَا مِنَ الأَمْرِ مِنْ شَيْء ٍ  ۗ  قُلْ إِنَّ الأَمْرَ كُلَّه ُُ لِلَّهِ  ۗ  يُخْفُونَ فِي أَنْفُسِهِمْ مَا لاَ يُبْدُونَ لَكَ  ۖ  يَقُولُونَ لَوْ كَانَ لَنَا مِنَ الأَمْرِ شَيْء ٌ مَا قُتِلْنَا هَاهُنَا  ۗ  قُلْ لَوْ كُنْتُمْ فِي بُيُوتِكُمْ لَبَرَزَ الَّذِينَ كُتِبَ عَلَيْهِمُ الْقَتْلُ إِلَى مَضَاجِعِهِمْ  ۖ  وَلِيَبْتَلِيَ اللَّهُ مَا فِي صُدُورِكُمْ وَلِيُمَحِّصَ مَا فِي قُلُوبِكُمْ  ۗ  وَاللَّهُ عَلِيم ٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
'Inna Al-Ladhīna Tawallaw Minkum Yawma At-Taqá Al-Jam`āni 'Innamā Astazallahumu Ash-Shayţānu Biba`đi Mā Kasabū  ۖ  Wa Laqad `Afā Al-Lahu `Anhum  ۗ  'Inna Al-Laha Ghafūrun Ĥalīmun َ003-155 Lalle ne waɗanda suka jũya daga gare ku a ranar haɗuwar jama'a biyu, shaiɗan kawai ne ya talãlãɓantar da su, sabõda sãshen abin da suka tsirfanta. Kuma lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yãfe laifidaga gare su. Lalle Allah ne Mai gãfara Mai haƙuri. إِنَّ الَّذِينَ تَوَلَّوْا مِنْكُمْ يَوْمَ الْتَقَى الْجَمْعَانِ إِنَّمَا اسْتَزَلَّهُمُ الشَّيْطَانُ بِبَعْضِ مَا كَسَبُوا  ۖ  وَلَقَدْ عَفَا اللَّهُ عَنْهُمْ  ۗ  إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ حَلِيم ٌ
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Takūnū Kālladhīna Kafarū Wa Qālū Li'khwānihim 'Idhā Đarabū Fī Al-'Arđi 'Aw Kānū Ghuzzáan Law Kānū `Indanā Mā Mātū Wa Mā Qutilū Liyaj`ala Al-Lahu Dhālika Ĥasratan Fī Qulūbihim Wa  ۗ  Allāhu Yuĥyī Wa Yumītu Wa  ۗ  Allāhu Bimā Ta`malūna Başīrun َ003-156 Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku kasance kamar waɗanda suka kãfirta kuma suka ce wa'yan'uwansu idan, sun yi tafiya a cikin ƙasa kõ kuwa suka kasance a wurin yãƙi: "Dã sun kasance a wurinmu dã ba su mutun ba, kuma dã ba a, kashe su ba." (Wannan kuwa) Dõmin Allah Ya sanya waccan magana ta zama nadãma a cikin zukãtansu. Kuma Allah ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani ne. يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لاَ تَكُونُوا كَالَّذِينَ كَفَرُوا وَقَالُوا لِأخْوَانِهِمْ إِذَا ضَرَبُوا فِي الأَرْضِ أَوْ كَانُوا غُزّى ً لَوْ كَانُوا عِنْدَنَا مَا مَاتُوا وَمَا قُتِلُوا لِيَجْعَلَ اللَّهُ ذَلِكَ حَسْرَة ً فِي قُلُوبِهِمْ  ۗ  وَاللَّهُ يُحْيِي وَيُمِيتُ  ۗ  وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِير ٌ
Wa La'in Qutiltum Fī Sabīli Al-Lahi 'Aw Muttum Lamaghfiratun Mina Al-Lahi Wa Raĥmatun Khayrun Mimmā Yajma`ūna َ003-157 Kuma lalle ne idan aka kashe, ku a cikin hanyar Allah, ko kuwa kuka mutu, haƙĩƙa, gãfara daga Allah da rahama ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa. وَلَئِنْ قُتِلْتُمْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ أَوْ مُتُّمْ لَمَغْفِرَة ٌ مِنَ اللَّهِ وَرَحْمَةٌ خَيْر ٌ مِمَّا يَجْمَعُونَ
Wa La'in Muttum 'Aw Qutiltum La'ilá Al-Lahi Tuĥsharūna َ003-158 Kuma lalle ne idan kun mutu ko kuwa aka kashe ku, haƙĩƙa, zuwa ga Allah ake tãra ku. وَلَئِنْ مُتُّمْ أَوْ قُتِلْتُمْ لَإِلَى اللَّهِ تُحْشَرُونَ
Fabimā Raĥmatin Mina Al-Lahi Linta Lahum  ۖ  Wa Law Kunta Fažžāan Ghalīža Al-Qalbi Lānfađđū Min Ĥawlika  ۖ  Fā`fu `Anhum Wa Astaghfir Lahum Wa Shāwirhum Al-'Amri  ۖ  Fa'idhā `Azamta Fatawakkal `Alá Al-Lahi  ۚ  'Inna Al-Laha Yuĥibbu Al-Mutawakkilīna َ003-159 Sabõda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma dã kã kasance mai hushi mai kaurin zuciya, dã sun wãtse daga gẽfenka. Sai ka yãfe musu laifinsu, kuma ka nẽma musu gãfara, kuma ka yi shãwara da su a cikin al'amarin. Sa'an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dõgara ga Allah, lalle ne, Allah Yana son mãsu tawakkali. فَبِمَا رَحْمَة ٍ مِنَ اللَّهِ لِنْتَ لَهُمْ  ۖ  وَلَوْ كُنْتَ فَظّاً غَلِيظَ الْقَلْبِ لاَنْفَضُّوا مِنْ حَوْلِكَ  ۖ  فَاعْفُ عَنْهُمْ وَاسْتَغْفِرْ لَهُمْ وَشَاوِرْهُمْ فِي الأَمْرِ  ۖ  فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ  ۚ  إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُتَوَكِّلِينَ
'In Yanşurkumu Al-Lahu Falā Ghāliba Lakum  ۖ  Wa 'In Yakhdhulkum Faman Dhā Al-Ladhī Yanşurukum Min Ba`dihi  ۗ  Wa `Alá Al-Lahi Falyatawakkali Al-Mu'uminūna َ003-160 Idan Allah Ya taimake ku, to, bãbu marinjayi a gare ku. Kuma idan Ya yarɓe ku, to, wãnẽ ne wanda yake taimakon ku bãyanSa? Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara. إِنْ يَنْصُرْكُمُ اللَّهُ فَلاَ غَالِبَ لَكُمْ  ۖ  وَإِنْ يَخْذُلْكُمْ فَمَنْ ذَا الَّذِي يَنْصُرُكُمْ مِنْ بَعْدِه ِِ  ۗ  وَعَلَى اللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ
Wa Mā Kāna Linabīyin 'An Yaghulla  ۚ  Wa Man Yaghlul Ya'ti Bimā Ghalla Yawma Al-Qiyāmati  ۚ  Thumma Tuwaffá Kullu Nafsin Mā Kasabat Wa Hum Lā Yužlamūna َ003-161 Kuma bã ya yiwuwa ga wani annabi ya ci gulũlu. Wanda ya ci gulũlu zai je da abin da ya ci na gulũlun, a Rãnar ¡iyama. Sa'an nan a cika wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta. Kuma sũ, bã zã a zãlunce su ba. وَمَا كَانَ لِنَبِيٍّ أَنْ يَغُلَّ  ۚ  وَمَنْ يَغْلُلْ يَأْتِ بِمَا غَلَّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ  ۚ  ثُمَّ تُوَفَّى كُلُّ نَفْس ٍ مَا كَسَبَتْ وَهُمْ لاَ يُظْلَمُونَ
'Afamani Attaba`a Riđwāna Al-Lahi Kaman Bā'a Bisakhaţin Mina Al-Lahi Wa Ma'wāhu Jahannamu  ۚ  Wa Bi'sa Al-Maşīru َ003-162 Shin fa, wanda ya bĩbiyi yardar Allah, yana zama kamar wanda ya kõma da fushi daga Allah kuma makomarsa Jahannama ce? Kuma tir da makõma ita! أَفَمَنِ اتَّبَعَ رِضْوَانَ اللَّهِ كَمَنْ بَاءَ بِسَخَط ٍ مِنَ اللَّهِ وَمَأْوَاه ُُ جَهَنَّمُ  ۚ  وَبِئْسَ الْمَصِيرُ
Hum Darajātun `Inda Al-Lahi Wa  ۗ  Allāhu Başīrun Bimā Ya`malūna َ003-163 Sũ, darajõji ne a wurin Allah, kuma Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatawa. هُمْ دَرَجَاتٌ عِنْدَ اللَّهِ  ۗ  وَاللَّهُ بَصِير ٌ بِمَا يَعْمَلُونَ
Laqad Manna Al-Lahu `Alá Al-Mu'uminīna 'Idh Ba`atha Fīhim Rasūlāan Min 'Anfusihim Yatlū `Alayhim 'Āyātihi Wa Yuzakkīhim Wa Yu`allimuhumu Al-Kitāba Wa Al-Ĥikmata Wa 'In Kānū Min Qablu Lafī Đalālin Mubīnin َ003-164 Lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi babbar falala a kan mũminai, dõmin Yã aika a cikinsu, Manzo daga ainihinsu yana karanta ãyõyinSa a gare su, kuma yana tsar kake su, kuma yana karantar da su Littãfi da hikima kuma lalle, sun kasance daga gabãni, haƙĩƙa suna cikin ɓata bayyananniya. لَقَدْ مَنَّ اللَّهُ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ إِذْ بَعَثَ فِيهِمْ رَسُولا ً مِنْ أَنْفُسِهِمْ يَتْلُوا عَلَيْهِمْ آيَاتِه ِِ وَيُزَكِّيهِمْ وَيُعَلِّمُهُمُ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَإِنْ كَانُوا مِنْ قَبْلُ لَفِي ضَلاَل ٍ مُبِين ٍ
'Awalammā 'Aşābatkum Muşībatun Qad 'Aşabtum Mithlayhā Qultum 'Anná Hādhā  ۖ  Qul Huwa Min `Indi 'Anfusikum  ۗ  'Inna Al-Laha `Alá Kulli Shay'in Qadīrun َ003-165 Shin kuma a lõkacin da wata masĩfa, haƙĩƙa, ta sãme ku alhãli kuwa kun sãmar da biyunta, kun ce: "Daga ina wannan yake?" Ka ce: "Daga wurin rãyukanku yake." Lalle ne, Allah, a kan dukan kõme, Mai ĩkon yi ne. أَوَلَمَّا أَصَابَتْكُمْ مُصِيبَة ٌ قَدْ أَصَبْتُمْ مِثْلَيْهَا قُلْتُمْ أَنَّى هَذَا  ۖ  قُلْ هُوَ مِنْ عِنْدِ أَنْفُسِكُمْ  ۗ  إِنَّ اللَّهَ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِير ٌ
Wa Mā 'Aşābakum Yawma At-Taqá Al-Jam`āni Fabi'idhni Al-Lahi Wa Liya`lama Al-Mu'uminīna َ003-166 Kuma abin da ya sãme ku a rãnar haɗuwar jama'a biyu, to, da izinin Allah ne, kuma dõmin (Allah) Ya san mũminai (na gaskiya). وَمَا أَصَابَكُمْ يَوْمَ الْتَقَى الْجَمْعَانِ فَبِإِذْنِ اللَّهِ وَلِيَعْلَمَ الْمُؤْمِنِينَ
Wa Liya`lama Al-Ladhīna Nāfaqū  ۚ  Wa Qīla Lahum Ta`ālaw Qātilū Fī Sabīli Al-Lahi 'Aw Adfa`ū  ۖ  Qālū Law Na`lamu Qitālāan Lāttaba`nākum  ۗ  Hum Lilkufri Yawma'idhin 'Aqrabu Minhum Lil'īmāni  ۚ  Yaqūlūna Bi'afwhihim Mā Laysa Fī Qulūbihim Wa  ۗ  Allāhu 'A`lamu Bimā Yaktumūna َ003-167 Kuma dõmin Ya san waɗanda suka yi munãfunci, kuma an ce musu: "Ku zo ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kõ kuwa ku tunkuɗe." Suka ce: "Dã mun san (yadda ake) yãƙi dã mun bĩ ku." Sũ zuwa ga kãfirci a rãnar nan, sun fi kusa daga gare su zuwa ga ĩmãni. Sunã cẽwa da bãkunansu abin da bã shi ne a cikin zukãtansu ba. Allah ne Mafi sani ga abin da suke ɓõyewa. وَلِيَعْلَمَ الَّذِينَ نَافَقُوا  ۚ  وَقِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْا قَاتِلُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ أَوْ ادْفَعُوا  ۖ  قَالُوا لَوْ نَعْلَمُ قِتَالا ً لاَتَّبَعْنَاكُمْ  ۗ  هُمْ لِلْكُفْرِ يَوْمَئِذٍ أَقْرَبُ مِنْهُمْ لِلإِيمَانِ  ۚ  يَقُولُونَ بِأَفْواهِهِمْ مَا لَيْسَ فِي قُلُوبِهِمْ  ۗ  وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يَكْتُمُونَ
Al-Ladhīna Qālū Li'khwānihim Wa Qa`adū Law 'Aţā`ūnā Mā Qutilū  ۗ  Qul Fādra'ū `An 'Anfusikumu Al-Mawta 'In Kuntum Şādiqīna َ003-168 Waɗanda suka ce wa 'yan'uwansu kuma suka zauna abinsu: "Dã sun yi mana ɗã'a, dã ba a kashe su ba." Ka ce: "To, ku tunkuɗe mutuwa daga rãyukanku, idan kun kasance mãsu gaskiya." الَّذِينَ قَالُوا لِأخْوَانِهِمْ وَقَعَدُوا لَوْ أَطَاعُونَا مَا قُتِلُوا  ۗ  قُلْ فَادْرَءُوا عَنْ أَنْفُسِكُمُ الْمَوْتَ إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ
Wa Lā Taĥsabanna Al-Ladhīna Qutilū Fī Sabīli Al-Lahi 'Amwātāan  ۚ  Bal 'Aĥyā'un `Inda Rabbihim Yurzaqūna َ003-169 Kada ka yi zaton waɗanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A'a, rãyayyu ne su, a wurin bangijinsu. Ana ciyar da su. وَلاَ تَحْسَبَنَّ الَّذِينَ قُتِلُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ أَمْوَاتا ً  ۚ  بَلْ أَحْيَاءٌ عِنْدَ رَبِّهِمْ يُرْزَقُونَ
Farīna Bimā 'Ātāhumu Al-Lahu Min Fađlihi Wa Yastabshirūna Bial-Ladhīna Lam Yalĥaqū Bihim Min Khalfihim 'Allā Khawfun `Alayhim Wa Lā Hum Yaĥzanūna َ003-170 Suna mãsu farin ciki sabõda abin da Allah Ya bã su daga falalarSa, kuma suna yin bushãra ga waɗanda ba su risku da su ba, daga bayansu; "Bãbu tsõro a kansu kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba." فَرِحِينَ بِمَا آتَاهُمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِه ِِ وَيَسْتَبْشِرُونَ بِالَّذِينَ لَمْ يَلْحَقُوا بِهِمْ مِنْ خَلْفِهِمْ أَلاَّ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ
Yastabshirūna Bini`matin Mina Al-Lahi Wa Fađlin Wa 'Anna Al-Laha Lā Yuđī`u 'Ajra Al-Mu'uminīna َ003-171 Suna yin bushãra sabõda wata ni'ima daga Allah da wata falala. Kuma lalle ne, Allah bã Ya tozartar da ijãrar mũminai. يَسْتَبْشِرُونَ بِنِعْمَة ٍ مِنَ اللَّهِ وَفَضْل ٍ وَأَنَّ اللَّهَ لاَ يُضِيعُ أَجْرَ الْمُؤْمِنِينَ
Al-Ladhīna Astajābū Lillahi Wa Ar-Rasūli Min Ba`di Mā 'Aşābahumu Al-Qarĥu  ۚ  Lilladhīna 'Aĥsanū Minhum Wa Attaqaw 'Ajrun `Ažīmun َ003-172 Waɗanda suka karɓa kira zuwa ga Allah da ManzonSa, daga bãyan mĩki ya sãme su.Akwai wata lãda mai girma ga waɗanda suka kyautata yi daga gare su, kuma suka yi taƙawa. الَّذِينَ اسْتَجَابُوا لِلَّهِ وَالرَّسُولِ مِنْ بَعْدِ مَا أَصَابَهُمُ الْقَرْحُ  ۚ  لِلَّذِينَ أَحْسَنُوا مِنْهُمْ وَاتَّقَوْا أَجْرٌ عَظِيم ٌ
Al-Ladhīna Qāla Lahumu An-Nāsu 'Inna An-Nāsa Qad Jama`ū Lakumkhshawhum Fazādahum 'Īmānāan Wa Qālū Ĥasbunā Al-Lahu Wa Ni`ma Al-Wakīlu َ003-173 Waɗanda mutãne suka ce musu: "Lalle ne, mutãne sun tãra (rundunõni) sabõda ku, don haka ku ji tsõrnsu. Sai (wannan magana) ta ƙara musu ĩmãni, kuma suka ce: "Mai isarmu Allah ne kuma mãdalla da wakili Shĩ." الَّذِينَ قَالَ لَهُمُ النَّاسُ إِنَّ النَّاسَ قَدْ جَمَعُوا لَكُمْ فَاخْشَوْهُمْ فَزَادَهُمْ إِيمَانا ً وَقَالُوا حَسْبُنَا اللَّهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ
nqalabū Bini`matin Mina Al-Lahi Wa Fađlin Lam Yamsas/hum Sū'un Wa Attaba`ū Riđwāna Al-Lahi Wa  ۗ  Allāhu Dhū Fađlin `Ažīmin َ003-174 Sa'an nan sukajũya da wata ni'ima daga Allah da wata falala, wata cũta ba ta shãfe su ba, kuma suka bi yardar Allah. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai girma. فَانْقَلَبُوا بِنِعْمَة ٍ مِنَ اللَّهِ وَفَضْل ٍ لَمْ يَمْسَسْهُمْ سُوء ٌ وَاتَّبَعُوا رِضْوَانَ اللَّهِ  ۗ  وَاللَّهُ ذُو فَضْلٍ عَظِيم ٍ
'Innamā Dhalikumu Ash-Shayţānu Yukhawwifu 'Awliyā'ahu Falā Takhāfūhum Wa Khāfūni 'In Kuntum Mu'uminīna َ003-175 Wancan, Shaiɗan ne kawai yake tsõratar da, ku masõyansa. To, kada ku ji tsõronsu ku ji tsõro Na idãn kun kasance mãsu ĩmãni. إِنَّمَا ذَلِكُمُ الشَّيْطَانُ يُخَوِّفُ أَوْلِيَاءَه ُُ فَلاَ تَخَافُوهُمْ وَخَافُونِ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ
Wa Lā Yaĥzunka Al-Ladhīna Yusāri`ūna Fī Al-Kufri  ۚ  'Innahum Lan Yađurrū Al-Laha Shay'āan  ۗ  Yurīdu Al-Lahu 'Allā Yaj`ala Lahum Ĥažžāan Al-'Ākhirati  ۖ  Wa Lahum `Adhābun `Ažīmun َ003-176 Kuma waɗannan da suke gaugãwa a cikin kãfirci kada su ɓãta maka rai. Lalle ne su, bã zã su cũci Allah da kõme ba. Allah yanã nufin cẽwa, bã zai sanya musu wani rabo ba a cikin Lãhira kuma suna da wata azãba mai girma. وَلاَ يَحْزُنْكَ الَّذِينَ يُسَارِعُونَ فِي الْكُفْرِ  ۚ  إِنَّهُمْ لَنْ يَضُرُّوا اللَّهَ شَيْئا ً  ۗ  يُرِيدُ اللَّهُ أَلاَّ يَجْعَلَ لَهُمْ حَظّا ً فِي الآخِرَةِ  ۖ  وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيم ٌ
'Inna Al-Ladhīna Ashtaraw Al-Kufra Bil-'Īmāni Lan Yađurrū Al-Laha Shay'āan Wa Lahum `Adhābun 'Alīmun َ003-177 Lalle ne, waɗanda suka sayi kãfirci da ĩmani, ba zã su cũci Allah da kõme ba. Koma sunã da azãba mai raɗaɗi. إِنَّ الَّذِينَ اشْتَرَوُا الْكُفْرَ بِالإِيمَانِ لَنْ يَضُرُّوا اللَّهَ شَيْئا ً وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيم ٌ
Wa Lā Yaĥsabanna Al-Ladhīna Kafarū 'Annamā Numlī Lahum Khayrun Li'anfusihim  ۚ  'Innamā Numlī Lahum Liyazdādū 'Ithmāan  ۚ  Wa Lahum `Adhābun Muhīnun َ003-178 Kuma kada waɗanda suka kãfirta su yi zaton cẽwa, lalle ne jinkirin da Muke yi musu alhẽri ne ga rãyukansu. Munã yi musu jinkirin ne dõmin su ƙãra laifi kawai kuma suna da azãba mai wulãƙantarwa. وَلاَ يَحْسَبَنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا أَنَّمَا نُمْلِي لَهُمْ خَيْر ٌ لِأَنْفُسِهِمْ  ۚ  إِنَّمَا نُمْلِي لَهُمْ لِيَزْدَادُوا إِثْما ً  ۚ  وَلَهُمْ عَذَاب ٌ مُهِين ٌ
Mā Kāna Al-Lahu Liyadhara Al-Mu'uminīna `Alá Mā 'Antum `Alayhi Ĥattá Yamīza Al-Khabītha Mina Aţ-Ţayyibi  ۗ  Wa Mā Kāna Al-Lahu Liyuţli`akum `Alá Al-Ghaybi Wa Lakinna Al-Laha Yajtabī Min Rusulihi Man Yashā'u  ۖ  Fa'āminū Bil-Lahi Wa Rusulihi  ۚ  Wa 'In Tu'uminū Wa Tattaqū Falakum 'Ajrun `Ažīmun َ003-179 Allah bai kasance yana barin mũminai a kan abin da kuke kansa ba, sai Ya rarrabe mummũna daga mai kyau. Kuma Al lah bai kasance Yanã sanar da ku gaibi ba. Kuma amma Allah Yana zãɓen wanda Ya so daga manzanninSa. Sabõda haka ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa Kuma idan kun yi ĩmãni kuma kuka yi taƙawa, to, kunã da lãdã mai girma. مَا كَانَ اللَّهُ لِيَذَرَ الْمُؤْمِنِينَ عَلَى مَا أَنْتُمْ عَلَيْهِ حَتَّى يَمِيزَ الْخَبِيثَ مِنَ الطَّيِّبِ  ۗ  وَمَا كَانَ اللَّهُ لِيُطْلِعَكُمْ عَلَى الْغَيْبِ وَلَكِنَّ اللَّهَ يَجْتَبِي مِنْ رُسُلِه ِِ مَنْ يَشَاءُ  ۖ  فَآمِنُوا بِاللَّهِ وَرُسُلِه ِِ  ۚ  وَإِنْ تُؤْمِنُوا وَتَتَّقُوا فَلَكُمْ أَجْرٌ عَظِيم ٌ
Wa Lā Yaĥsabanna Al-Ladhīna Yabkhalūna Bimā 'Ātāhumu Al-Lahu Min Fađlihi Huwa Khayrāan Lahum  ۖ  Bal Huwa Sharrun Lahum  ۖ  Sayuţawwaqūna Mā Bakhilū Bihi Yawma Al-Qiyāmati  ۗ  Wa Lillahi Mīrāthu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa  ۗ  Allāhu Bimā Ta`malūna Khabīrun َ003-180 Kuma kada waɗannan da suke yin rõwa da abin da Allah Ya bã su daga falalarSa su yi zaton shĩ ne mafi alhẽri a gare su A'a, shĩ mafi sharri ne a gare su. Zã a yi musu saƙandami da abin da suka yi rõwa da Shi a Rãnar ¡iyãma Kuma ga Allah gãdon sammai da ƙasa yake, kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Masani ne. وَلاَ يَحْسَبَنَّ الَّذِينَ يَبْخَلُونَ بِمَا آتَاهُمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِه ِِ هُوَ خَيْرا ً لَهُمْ  ۖ  بَلْ هُوَ شَرّ ٌ لَهُمْ  ۖ  سَيُطَوَّقُونَ مَا بَخِلُوا بِه ِِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ  ۗ  وَلِلَّهِ مِيرَاثُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۗ  وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِير ٌ
Laqad Sami`a Al-Lahu Qawla Al-Ladhīna Qālū 'Inna Al-Laha Faqīrun Wa Naĥnu 'Aghniyā'u  ۘ  Sanaktubu Mā Qālū Wa Qatlahumu Al-'Anbiyā'a Bighayri Ĥaqqin Wa Naqūlu Dhūqū `Adhāba Al-Ĥarīqi َ003-181 Lalle ne, haƙĩƙa Allah Yã ji maganar waɗanda suka ce: "Lalle ne, Allah faƙĩri ne, mũ ne wadãtattu." za mu rubũta abin da suka faɗa, da kisan da suka yi wa Annabãwa bã da wani haƙƙi ba kuma Mu ce: "Ku ɗanɗani azãbar gõbara! لَقَدْ سَمِعَ اللَّهُ قَوْلَ الَّذِينَ قَالُوا إِنَّ اللَّهَ فَقِير ٌ وَنَحْنُ أَغْنِيَاءُ  ۘ  سَنَكْتُبُ مَا قَالُوا وَقَتْلَهُمُ الأَنْبِيَاءَ بِغَيْرِ حَقّ ٍ وَنَقُولُ ذُوقُوا عَذَابَ الْحَرِيقِ
Dhālika Bimā Qaddamat 'Aydīkum Wa 'Anna Al-Laha Laysa Bižallāmin Lil`abīdi َ003-182 "Wannan (azãbar) kuwa sabõda abin da hannuwanku suka gabãtar ne. Kuma lalle ne Allah bai zama mai zãlunci ga bãyinsa ba." ذَلِكَ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيكُمْ وَأَنَّ اللَّهَ لَيْسَ بِظَلاَّم ٍ لِلْعَبِيدِ
Al-Ladhīna Qālū 'Inna Al-Laha `Ahida 'Ilaynā 'Allā Nu'umina Lirasūlin Ĥattá Ya'tiyanā Biqurbānin Ta'kuluhu An-Nāru  ۗ  Qul Qad Jā'akum Rusulun Min Qablī Bil-Bayyināti Wa Bial-Ladhī Qultum Falima Qataltumūhum 'In Kuntum Şādiqīna َ003-183 Waɗanda suka ce: "Lalle ne Allah Yã yi alkawari zuwa gare mu, kada mu yi ĩmãni sabõda wani Manzo sai yã zo mana da Baiko wadda wuta za ta ci." Ka ce: "Lalle ne wasu manzanni sun je muku, a gabãnĩna, da hujjõji bayyanannu, kuma da abin da kuka faɗa, to, don me kuka kashe su, idan kun kasance mãsu gaskiya?" الَّذِينَ قَالُوا إِنَّ اللَّهَ عَهِدَ إِلَيْنَا أَلاَّ نُؤْمِنَ لِرَسُولٍ حَتَّى يَأْتِيَنَا بِقُرْبَان ٍ تَأْكُلُهُ النَّارُ  ۗ  قُلْ قَدْ جَاءَكُمْ رُسُل ٌ مِنْ قَبْلِي بِالْبَيِّنَاتِ وَبِالَّذِي قُلْتُمْ فَلِمَ قَتَلْتُمُوهُمْ إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ
Fa'in Kadhdhabūka Faqad Kudhdhiba Rusulun Min Qablika Jā'ū Bil-Bayyināti Wa Az-Zuburi Wa Al-Kitābi Al-Munīri َ003-184 To, idan sun ƙaryata ka, to lalle ne, an ƙaryata wasu manzanni a gabãninka, sun je musu da hujjõji bayyanannu da littattafai, da kuma Littafi mai haske. فَإِنْ كَذَّبُوكَ فَقَدْ كُذِّبَ رُسُل ٌ مِنْ قَبْلِكَ جَاءُوا بِالْبَيِّنَاتِ وَالزُّبُرِ وَالْكِتَابِ الْمُنِيرِ
Kullu Nafsin Dhā'iqatu Al-Mawti  ۗ  Wa 'Innamā Tuwaffawna 'Ujūrakum Yawma Al-Qiyāmati  ۖ  Faman Zuĥziĥa `Ani An-Nāri Wa 'Udkhila Al-Jannata Faqad Fāza  ۗ  Wa Mā Al-Ĥayāatu Ad-Dunyā 'Illā Matā`u Al-Ghurūri َ003-185 Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma ana cika muku ijãrõrinku kawai ne a Rãnar ¡iyãma. To, wanda aka nĩsantar daga barin wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to, lalle ne yã tsĩra.Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce jin dãɗin rũɗi. كُلُّ نَفْس ٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ  ۗ  وَإِنَّمَا تُوَفَّوْنَ أُجُورَكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ  ۖ  فَمَنْ زُحْزِحَ عَنِ النَّارِ وَأُدْخِلَ الْجَنَّةَ فَقَدْ فَازَ  ۗ  وَمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلاَّ مَتَاعُ الْغُرُورِ
Latublawunna Fī 'Amwālikum Wa 'Anfusikum Wa Latasma`unna Mina Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba Min Qablikum Wa Mina Al-Ladhīna 'Ashrakū 'Adháan Kathīrāan  ۚ  Wa 'In Taşbirū Wa Tattaqū Fa'inna Dhālika Min `Azmi Al-'Umūri َ003-186 Lalle ne zã a jarraba ku a cikin dũkiyarku da rãyukanku, kuma lalle ne kuna jin cũtarwa mai yawa daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku da kuma waɗanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, to lalle ne, wannan yana daga manyan al'amurra. لَتُبْلَوُنَّ فِي أَمْوَالِكُمْ وَأَنْفُسِكُمْ وَلَتَسْمَعُنَّ مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِنْ قَبْلِكُمْ وَمِنَ الَّذِينَ أَشْرَكُوا أَذى ً كَثِيرا ً  ۚ  وَإِنْ تَصْبِرُوا وَتَتَّقُوا فَإِنَّ ذَلِكَ مِنْ عَزْمِ الأُمُورِ
Wa 'Idh 'Akhadha Al-Lahu Mīthāqa Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba Latubayyinunnahu Lilnnāsi Wa Lā Taktumūnahu Fanabadhūhu Warā'a Žuhūrihim Wa Ashtaraw Bihi Thamanāan Qalīlāan  ۖ  Fabi'sa Mā Yashtarūna َ003-187 Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin waɗanda aka bai wa Littãfi, "Lalle ne kuna bayyana shi ga mutãne, kuma bã zã ku ɓõye shi ba." Sai suka jẽfarda shi a bãyan bãyansu, kuma suka sayi 'yan kuɗi kaɗan da shi. To, tir da abin da suke saye! وَإِذْ أَخَذَ اللَّهُ مِيثَاقَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ لَتُبَيِّنُنَّه ُُ لِلنَّاسِ وَلاَ تَكْتُمُونَه ُُ فَنَبَذُوه ُُ وَرَاءَ ظُهُورِهِمْ وَاشْتَرَوْا بِه ِِ ثَمَنا ً قَلِيلا ً  ۖ  فَبِئْسَ مَا يَشْتَرُونَ
Lā Taĥsabanna Al-Ladhīna Yafraĥūna Bimā 'Ataw Wa Yuĥibbūna 'An Yuĥmadū Bimā Lam Yaf`alū Falā Taĥsabannahum Bimafāzatin Mina Al-`Adhābi  ۖ  Wa Lahum `Adhābun 'Alīmun َ003-188 Kada lalle ka yi zaton waɗanda suke yin farin ciki da abin da suka bãyar, kuma suna son a yabe su da abin da ba su aikatã ba. To, kada lalle ka yi zaton su da tsĩra daga azãba. Kuma suna da azãba mai raɗadi. لاَ تَحْسَبَنَّ الَّذِينَ يَفْرَحُونَ بِمَا أَتَوا وَيُحِبُّونَ أَنْ يُحْمَدُوا بِمَا لَمْ يَفْعَلُوا فَلاَ تَحْسَبَنَّهُمْ بِمَفَازَة ٍ مِنَ الْعَذَابِ  ۖ  وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيم ٌ
Wa Lillahi Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa  ۗ  Allāhu `Alá Kulli Shay'in Qadīrun َ003-189 Kuma ga Allah mulkin sammai da ƙasa yake. Kuma Allah, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne. وَلِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۗ  وَاللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِير ٌ
'Inna Fī Khalqi As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Akhtilāfi Al-Layli Wa An-Nahāri La'āyātin Li'wlī Al-'Albābi َ003-190 Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa da sãɓãwar dare da yini akwai ãyõyi ga ma'abũta hankali. إِنَّ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَاخْتِلاَفِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ لَآيَات ٍ لِأولِي الأَلْبَابِ
Al-Ladhīna Yadhkurūna Al-Laha Qiyāmāan Wa Qu`ūdāan Wa `Alá Junūbihim Wa Yatafakkarūna Fī Khalqi As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Rabbanā Mā Khalaqta Hādhā Bāţilāan Subĥānaka Faqinā `Adhāba An-Nāri َ003-191 Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da ƙasa: "Yã Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a kan banza ba. TsarkinKa! Sabõda haka Ka tsare mu daga azãbar wuta. الَّذِينَ يَذْكُرُونَ اللَّهَ قِيَاما ً وَقُعُودا ً وَعَلَى جُنُوبِهِمْ وَيَتَفَكَّرُونَ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ رَبَّنَا مَا خَلَقْتَ هَذَا بَاطِلا ً سُبْحَانَكَ فَقِنَا عَذَابَ النَّارِ
Rabbanā 'Innaka Man Tudkhili An-Nāra Faqad 'Akhzaytahu  ۖ  Wa Mā Lilžžālimīna Min 'Anşārin َ003-192 "Ya Ubangijinmu! Lalle ne Kai, wanda Ka shigar a cikin wuta to, haƙĩƙa, Ka tozarta shi kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai. رَبَّنَا إِنَّكَ مَنْ تُدْخِلِ النَّارَ فَقَدْ أَخْزَيْتَه ُُ  ۖ  وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنْصَار ٍ
Rabbanā 'Innanā Sami`nā Munādīāan Yunādī Lil'īmāni 'An 'Āminū Birabbikum Fa'āmannā  ۚ  Rabbanā Fāghfir Lanā Dhunūbanā Wa Kaffir `Annā Sayyi'ātinā Wa Tawaffanā Ma`a Al-'Abrāri َ003-193 "Yã Ubangijinmu! Lalle ne mũ mun ji Mai kira yanã kira zuwa ga ĩmãni cẽwa, 'Ku yi ĩmãni da Ubangijinku.' Sai muka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Sabõda haka Ka gãfarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare miyãgun ayyukanmu daga gare mu. Kuma Ka karɓi rãyukanmu tãre da mutãnen kirki. رَبَّنَا إِنَّنَا سَمِعْنَا مُنَادِيا ً يُنَادِي لِلإِيمَانِ أَنْ آمِنُوا بِرَبِّكُمْ فَآمَنَّا  ۚ  رَبَّنَا فَاغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا وَكَفِّرْ عَنَّا سَيِّئَاتِنَا وَتَوَفَّنَا مَعَ الأَبْرَارِ
Rabbanā Wa 'Ātinā Mā Wa`adtanā `Alá Rusulika Wa Lā Tukhzinā Yawma Al-Qiyāmati  ۗ  'Innaka Lā Tukhlifu Al-Mī`āda َ003-194 "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu abin da Ka yi mana wa'adi (alkawari) a kan manzanninKa, kuma kada Ka tozarta mu a Rãnar ¡iyãma. Lalle ne Kai, bã Ka sãɓãwar alkawari." رَبَّنَا وَآتِنَا مَا وَعَدْتَنَا عَلَى رُسُلِكَ وَلاَ تُخْزِنَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ  ۗ  إِنَّكَ لاَ تُخْلِفُ الْمِيعَادَ
Fāstajāba Lahum Rabbuhum 'Annī Lā 'Uđī`u `Amala `Āmilin Minkum Min Dhakarin 'Aw 'Unthá  ۖ  Ba`đukum Min Ba`đin  ۖ  Fa-Al-Ladhīna Hājarū Wa 'Ukhrijū Min Diyārihim Wa 'Ūdhū Fī Sabīlī Wa Qātalū Wa Qutilū La'ukaffiranna `Anhum Sayyi'ātihim Wa La'udkhilannahum Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Thawābāan Min `Indi Al-Lahi Wa  ۗ  Allāhu `Indahu Ĥusnu Ath-Thawābi َ003-195 Sabõda haka Ubangijinsu Ya karɓa musu cẽwa, "Lallene Nĩ bã zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sãshenku daga sãshe. To, waɗanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidãjensu, kuma aka cũtar da su a cikin hanyaTa, kuma suka yi yãƙi, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musumiyagun ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙoramu ke gudãna daga ƙarƙashinsu, a kan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinSa akwai kyakkyawan sakamako. فَاسْتَجَابَ لَهُمْ رَبُّهُمْ أَنِّي لاَ أُضِيعُ عَمَلَ عَامِل ٍ مِنْكُمْ مِنْ ذَكَرٍ أَوْ أُنْثَى  ۖ  بَعْضُكُمْ مِنْ بَعْض ٍ  ۖ  فَالَّذِينَ هَاجَرُوا وَأُخْرِجُوا مِنْ دِيَارِهِمْ وَأُوذُوا فِي سَبِيلِي وَقَاتَلُوا وَقُتِلُوا لَأُكَفِّرَنَّ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ وَلَأُدْخِلَنَّهُمْ جَنَّات ٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ ثَوَابا ً مِنْ عِنْدِ اللَّهِ  ۗ  وَاللَّهُ عِنْدَه ُُ حُسْنُ الثَّوَابِ
Lā Yaghurrannaka Taqallubu Al-Ladhīna Kafarū Fī Al-Bilādi َ003-196 Kada jujjuyawar waɗanda suka kãfirta a cikin garũruwa ta rũɗe ka. لاَ يَغُرَّنَّكَ تَقَلُّبُ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي الْبِلاَدِ
Matā`un Qalīlun Thumma Ma'wāhum Jahannamu  ۚ  Wa Bi'sa Al-Mihādu َ003-197 Jin dãɗi ne kaɗan sa'an nan makõmarsu Jahannama ce, kuma tir da shimfiɗa ita! مَتَاع ٌ قَلِيل ٌ ثُمَّ مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ  ۚ  وَبِئْسَ الْمِهَادُ
Lakini Al-Ladhīna Attaqaw Rabbahum Lahum Jannātun Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā Nuzulāan Min `Indi Al-Lahi  ۗ  Wa Mā `Inda Al-Lahi Khayrun Lil'abrāri َ003-198 Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa sunã da Gidãjen Aljanna (waɗabda) ƙoramu ke gudãna a ƙarƙashinsu suna madawwama a cikinsu, a kan, liyãfa daga wurin Allah, kuma abin da ke wurin Allah ne mafi alhẽri ga barrantattu. لَكِنِ الَّذِينَ اتَّقَوْا رَبَّهُمْ لَهُمْ جَنَّات ٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا نُزُلا ً مِنْ عِنْدِ اللَّهِ  ۗ  وَمَا عِنْدَ اللَّهِ خَيْر ٌ لِلأَبْرَارِ
Wa 'Inna Min 'Ahli Al-Kitābi Laman Yu'uminu Bil-Lahi Wa Mā 'Unzila 'Ilaykum Wa Mā 'Unzila 'Ilayhim Khāshi`īna Lillahi Lā Yashtarūna Bi'āyāti Al-Lahi Thamanāan Qalīlāan  ۗ  'Ūlā'ika Lahum 'Ajruhum `Inda Rabbihim  ۗ  'Inna Al-Laha Sarī`u Al-Ĥisābi َ003-199 Kuma lalle ne daga Mutãnen Littãfi haƙĩƙa akwai wanda yake yin ĩmãnĩ da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar zuwa gare su, sunã mãsu tawãlu'i ga Allah, bã su sayen tamani kaɗan da ãyõyin Allah. Waɗannan suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu. Lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako da yawa ne. وَإِنَّ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ لَمَنْ يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَمَا أُنْزِلَ إِلَيْكُمْ وَمَا أُنْزِلَ إِلَيْهِمْ خَاشِعِينَ لِلَّهِ لاَ يَشْتَرُونَ بِآيَاتِ اللَّهِ ثَمَنا ً قَلِيلاً  ۗ  أُوْلَائِكَ لَهُمْ أَجْرُهُمْ عِنْدَ رَبِّهِمْ  ۗ  إِنَّ اللَّهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Aşbirū Wa Şābirū Wa Rābiţū Wa Attaqū Al-Laha La`allakum Tufliĥūna َ003-200 Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku yi haƙuri kuma ku yi dauriya, kuma ku yi zaman dãko, kuma ku yi taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara. يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اصْبِرُوا وَصَابِرُوا وَرَابِطُوا وَاتَّقُوا اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Next Sūrah